GADAR ZARE…

21

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*




21




Zaid kwance bisa makeken gadonsa mai kirar royal bed, yana tunanin ta inda zai fara neman matar aure don Abba ya matsa musu da maganar aure kusan kullum sai yayi musu maganar, shi gashi ko a cikin friends d'in su shi ba mai yawan magana bane, he is so silent & hand sum guy, dan Zaid yana matuk'ar kyau daga na fuska harna halitta, tunani yake amma ya rasa ta inda zai b'ullowa al'amarin, yana cikin wannan hali Mukhtar ya shigo d'akin d'auke da sallama. 



Ganin Zaid baima san ya shigo ba balle ya amsa masa sallamar ba, ya sashi tsayawa a kansa yana k'are masa kallo yana murmushi , dan yasan tunanin me yake, a kusa dashi Mukhtar ya zauna amma har a lokacin bai ma san ya shigo ba, a hankali Mukhtar yasa hannu ya shiga jijjiga shi, aiko firgit ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, ya kalli Mukhtar fuskarsa cike da murmushi yace " Friend yaushe ka shigo? 



Dariya Mukhtar yayi yace " tun d'azu mana, "kai haba amma ban san ka shigo ba, " toya za'ayi kasan na shigo bayan ka tsunduma duniyar tunani, murmushi Zaid yayi a karo na biyu ya shafa kwantacciyar sumar kansa yace " hmmmmm dan bai da san mai zai cewa Mukhtar ba, shima murmushi yayi dan yasan halin Zaid da muskilancin tsiya, ya kalle shi yace " kaji Class mate d'in mu sun had'a party ko? 



D'ago kansa yayi yana kallansa daga bisali kuma yace " a'a ban sani ba wanne daga ciki? 



" wad'anda mukayi karatun Mastrs dasu a Dubai, shiru Zaid yayi yana kallon Mukhtar, "ko bazaka je bane? cewar Mukhtar, " eh to gani nan idan ina da time zanje wacce rana ce? 



" this coming weekend ne, Saturday, " ok zaka je? Zaid ya tambayi Mukhtar, murmushi Mukhtar yayi yace " idan zaka je amma idan baka zuwa nima babu inda zani," hmmmmm gadukkanin alamu dai kana son zuwa, " eh mana ko ba komai ai a sada zumunci kuma ma ai munyi missing juna cewar Mukhtar, " ok badamuwa Allah ya kaimu, "Amin Mukhtar yace yana mik'ewa kallonsa Zaid yayi yace " sai ina kuma? 



"Baka ji an kira sallah bane? " banji ba wallahi ya fad'a yana duba agogon hannunsa, ganin lokaci yayi ne yasa shi saurin mik'ewa, yayi toilet, bayan sun idar da sallar direct cikin gida suka wuce a parlor suka samu Ammi zaune tana kallon Aljazira English, har k'asa suka duk'a suka gaida ita, fuskarta cike da fara'a ta amsa, kusa da ita suka zauna gaba d'aya, Mukhtar yace "Ammi da abinci kuwa?



Ban sani ba! kullum kuzo ku dame da neman abinci ance kuyi aure kunk'i sai kuzo ku rink'a cinye min abincin gida acici kawai ta fad'a tana dariya da sigar tsokana, dariya sukayi gaba d'ayan su Mukhtar ya langwab'ar da kai cikin shagwab'a yace " kai Ammi idan bamu ci naki ba nawa kike son muci? "Na matan ku mana, ni fa lokaci na baku idan kuma ya cika ko gida na bazan bari ku rink'a shigo min ba, ni ban tab'a ganin yara irin ku ba kwata-kwata basa san maganar aure balle auren ma, "dariya suka kuma yi Zaid yace " da Abban mu nan daya shigar mana a... "Aiko wannan karon bazan shigar muku ba bayan matata ni ma zanbi cewar Abba dake shigowa cikin parlor d'auke da fara'a Mukhtar yace " kai Abba harda kai kuma yau? " eh harda ni nazan yarda kullum a rink'a damarmin mata da maganar abinci ba ana zuwa ana hana ta baccin dare da hira murmushi Zaid yayi yace " kyale su Friend idan muka tashi mu full tank zamuyi dan sai munyi 4 dariya Abba yayi yace " idan kunji haushi kuyi 1000 yau ma. 



Haka dai suka ci abincin cike da fara da barkwanci dan daga Abba har Ammi sun kasance mutane masu fara'a da wasa da dariya da iyalan su, suna cikin haka Abraham ya shigo da sallamarsa fuskarsa d'auke da murmushi ya nufi wajen Ammi da Abba, burki yaci dan ganin wad'anda yafi tsana a duniya take ya murtuke fuska ya had'e rai yadda kasan anyi masa sammacin mutuwa.



Cikin fara'a Abba yace " yawwa babban d'a k'araso fuska ya k'ara b'atawa yace " no Abba badamuwa bari naje waanka zanyi, murmushi Ammi tayi sannan tace " haba d'ana zo kaci abinci kaji, murmushi yayi mata yace " ok Ammi but not now, Abba ya kalli su Zaid yace " baku ga Yayan ku bane? "Ai da muka ga kuna magana ne, a tare suka had'a baki Yaya ina wuni? ko kallan inda suke bayyi ba a ciki ya amsa da lafiya, hakan ma dan agaban idan su Abba ne, ya wuce abinsa, gaba d'aya suka bishi da ido ita ko Ammi ajiyar zuciya ta sauke tana mai matuk'ar bak'in cikin halin da Abraham yasa kansa, ganin gaba d'aya yanayin Ammi ya canja yasa Zaid da Mukhtar tare da Abba kwantar mata da hankali da bata hak'uri. 



Abraham na shiga d'aki ya banko k'ofar d'akin, yana ta faman huci kamar maciji, kayan jikinsa ya cire ya shiga cilli da dasu, zama yayi a bakin gadinsa yana furzar da iskar bakinsa, da sauri ya mik'e ya d'auko sigarinsa ya hau busawa sai da yasha mai isarsa sannan ya shiga bathroom ya sakarwa kansa shower, yakai kusan 30 minutes sannan ya fito ya fad'a kan gadonsa yayi rigingine kansa yana kallon sama ya shiga tunanin ta inda zai b'ullowa Zaid, sai da ya b'ata lokaci sosai sannan ya samu mafita, mik'ewa yayi zaune yana murmushi gefen baki dan ya samu hanyar dazai k'ullawa Zaida GADAR ZARE. 



Ranar Saturday wajen k'arfe 8:00pm babban hall din kuma tsadadje cike yake da jama'a had'add'u 'yan gayu kuma 'yan book kai gani kasan naira ta zauna da gindinta a wajen, don kuwa ka gani kasan yaci ya tada da ita, yayinda duk jama'ar dake wajen maza da mata fuskokin su cike da fara'a da sanyayyan murmushi Zaid take tsaye ya hango wani abokinsa sosai da tunda suka gama karatu bai ganshi ba, shima abokin nasa idonsa ne suka sauka akan Zaid aiko cikin zumud'i fuskarsa d'auke da wadataccen murmushi ya nufo Zaid shiko Zaid tsayawa yayi yana kallonsa shima yana mayar masa da martanin murmushin suna gaf da had'uwa ne aka kashe wutar wajen. 



Hankalin Zaid kwance ya k'arasa nufar abokin nasa ya rungume gam cike da farin ciki " I miss you so much frien...... maganar tasace ta sark'e masa a mak'ogwaro sanda aka maido da wutar hall d'in, ya sandare a tsaye yana kallon yarinyar daya rungume a tunaninsa abokin nasa ne, sakinta yayi da sauri yayi baya durk'ushewa tayi a wajen d'an kwallin kanta ya fad'i gashin kanta daya sha gyara ya zubo mata a fuska ya rufe mata face, cikin b'acin rai ta mik'e tasa hannu ta kawar da gashin daya zubo mata, baki Zaid ya bud'e yace " am sor.... kasa k'arasa maganar yayi sakamakon kyau da had'uwar yarinyar daya firgita shi, take nutsuwarsa ta d'auke ya k'ura mata ido baya ko kiftawa, itama cikin tsiwa ta bud'e baki tace "Would take your hand off, please, tana sauke idonta a kansa gabanta yayi mummunar fad'uwa, shida baima ma san har a lokacin hannunsa na kanta ta yayi saurin d'auke hannunsa amma idonsa na kanta fuskarta ba yabo ba fallasa tace " what are you staring at?, never seen a girl before? ta fad'a tana barin wajen, murmushi Zaid yayi yabi bayanta da kallo yace "I have but not a girl who entered my heart, at first sight. 



Duk inda yarinyar tayi idonsa yana kansa, ya kasa daina kallonta, tana sane dashi amma tayi kamar bana tasan tana yi ba, haka har aka gama taro, Mukhtar yace " muje ko? " kaje kawai ni ba yanzu zan tafi ba, cikin mamaki yace " me zakayi, ina zaka biya? "kaje kawai zamu had'u a gida cewar Zaid yana barin wajen, da ido Mukhtar ya bishi kawai, duk yadda Zaid yaso yayi magana da yarinyar amma taki bashi dama, har taron ya watse, cike da matsanancin bak'in ciki yake tuk'in motar yayinda yake cizon d'an yatsansa, danja ce ta tsaida shi dole ya tsaya badan yaso ba, wasu samari ya gani cike da mota suna bin wata motar a guje, da gudu motar da ake bin ta bigi wani gani dake gefe ganin haka yasa samarin barin wajen a guje, da sauri Zaid ya fito ya nufi motar da k'arfi ya b'elle k'ofar motar, tsaywa yayi cak dan ganin yarinyar ce acikin motar amma ta suma, gabansa ne yayi muguwar fad'uwa, da sauri ya d'auke ta yasa a cikin motarsa yayi aaibiti da ita. 



Bayan Doctor ya gama duba ta ya fito yana yiwa Zaid bayani "her blood pressure is low, but everything is okay otherwise, not a serious wound, I think she has lost consciousness because of fear, I have administered the injection she'll be fine by morning, murmushi Zaid yayi yace thank you doctor, you are welcome Doctor ya fad'a yana barin wajen, a d'akin da aka kwantar da ita anan Zaid ya kwanta kan doguwar kujera, tun asuba daya farka yayi sallah bai koma bacci ba, zama yayi a kusa da ita ya k'ura mata ido yana ganin tsantsar kyau ya hankali yace " da gani ba baushiya bace dan tafi kama da turawa, sai wajen 8:00am ta farka bakin ta d'auke da salati hannunta ta saka duka biyun ta dafe kanta da sauri Zaid ya nufe ta, a hankali ta tashi zaune ta fara ware idonta tana bin ko ina da kallo, idonta ne sauka akan Zaid da sauri ta k'ara zaro ido tana kallon sa tace "you agai? 



Murmushi yayi hannunwasa had'e a k'irjinsa " yes, yaci gaba da cewa " can't help it, you run into my life, without even knocking, murmushi tayi tace " thanks for last night, ido ya k'ura mata, alama tayi masa da idon sa na wannan kallan fa a hankali ya shiga furta " looking at you, I think the astrologer's words might come true, cikin rashin fahimta yace " astrologer? " you see.. , yaci gaba da cewa " in the last twelve hours, this is our third meeting, did some trait of catch your eye back at d party? 



Murmushi tayi kawai tace " i'll leave now, ta fad'a tana saukowa daga kan gadon, a hankali ta fara takawa dan barin d'akin karaf taji yace " strange! you vanish to meet again, & u meet only to vanish again, u may leave, but won't u tell me whom I ought to thank, a hankali ta juyo tana fuskantarsa tace " pardon me? " I mean, who was dat person, who made u take 2 ur heels, if not 4 dat soul, neither would u hv collapsed, nt would I hv brought u here, & all my life, I would've felt sorry 4 nt asking ur name, b4 u vanish again, hurry up and tell me ur name, murmushi tayi dan ta fahimci ya zata bata jin hausa dan haka ta kalle tace " sunana Fatima amma amfi kira na da TEEMAH, ido ya zaro yace " kina jin hausa? 



"Gashi kuwa na tabbatar maka, ni cikekkiyar bahaushiya ce, ni bani da wani yare sai hausa dan ban taso a gidan mu naga ana yin wani yare bayan hausa ba, murmushi yayi yace " masha Allah, ni sunana Zaid Muhammad Bature, gabanta ne ya fad'i dan duk Nigeria baby wanda baisan Alhaji Bature ba, da sauri ta d'ago kai ta kalle shi tace " kai d'an Alhaji Baturen dana sani ne? 



Murmushi ya kuma yace " when tym has come u know, babu yadda Zaid bayi ba yakai Teemah gida amma fir taki yarda, sai exchanging numbers da sukayi a junansu, Zaid na zuwa gida direct d'aki ya wuce, yana zuwa ya fad'a gado yana sakin murmushi yace " nisa tazo kusa an kusa daina yi min gorin aure, Mukhtar dake toilet ya fito, idonsa ya sauke akan aminin nasa daya dad'e da fad'awa duniyar tunani kai ya girgiza ya jingina da bango yana kallonsa dan yasa tunanin dayake a hankali yace "haba Friend ka daina matsawa kanka akan maganar auren nan by God grace a beautiful and charming girl will walk into your life for ever, mik'ewa zaune Zaid yayi yana murmushi yace " she already walk into my life, I pray to stay with me for ever, cikin mamaki Mukhtar yake kallansa alamar tambaya yayi masa da idon sa, Zaid yace " yes I told you d true, hankali Mukhtar ya tako inda Zaid yake ya zauna a kusa dashi his face with smile yace " are serious friend? 



Dariya Zaid yayi har fafaren hak'oransa suka bayyana yace " yes nan ya shiga bashi labarin Teemah, " Alhamdulillah masha Allah, yau aboki na ya samu soulmate d'insa, toya take? "Kai dai bari ai duk yadda nake mafarkin samun mace Teemah ta wuce haka, yarinyar ta had'u fa, " to ya ka gani a b'angaren tarbiyya d'a addininta? "Eh to ai bamu zauna ba balle na fahinci hakan, " ok badamuwa friend in sha yadda ka sameta a zahiri haka zaka sameta a bad'iri, " Amin ya Allah, ni dai na kusa na wuce gorin Ammi, na kusa zama mai gida gaba kad'an kuma na zama Dady, wasu ko oho. 



Duka Mukhtar yakai masa yana cewa " nima ai ba haka zan zauna ba, kai zan ma k'ok'ari na samu Matar aure dan bazan bari ka riga ba, dan idan na bari ka rigani na shiga uku, " oho dai gwara ma dai mutum yayi zuciya ya d'au himma danbazan rink'a barin k'atti suna shigar min gida pillow ya d'auka ya jefa mishi "au nine ma k'aton banzan, shima Zaid pillow ya jefa masa yana dariya.



Shiko goga Abraham duk ya samu kansa da neman hanyar da zai kawai dai Zaid da Mukhtar babban burinsa a duniya bai wuce yaga Zaid da Mukhtar basa raye ba safa da marma ya shiga yi a d'akin hannunsa sak'ale a bayan say yana ta sak'a da warwara yayi nisa cikin tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya had'a musu GADDAR ZARE, makeken gadonsa ya fad'a yana dariyar mugun dan samun mafita....... 



MOMYN ZARAH