SANADIN CACA

....04....

by @sadisakhna



 *SANADIN CACA*



Mallakar SADI-SAKHNA



PROFICIENT WRITER ASSOCIATION




*USERNAMES*

FACEBOOK PAGE:Sadisakhna

WATTPAD:@SAKHNA03

AREWABOOKS:@sadeesakhna

PHONE NO:***

________________________________

*Book 1*

Chp[04]




Saida ya daidaita hasken a cikin idonsa kafin ya buɗe idon dukka. A kwance yake a inda ya suma jiya,wato cikin bukkar,yunƙurawa yayi babu salati bare godiya ga Allah.

Kakkaɗe jikinsa yayi daga ƙurar dayayi kafin ya fito daga cikin bukkar yayi wata miƙa.

Ido ya haɗa da karnuka guda uku,murtuƙa murtuƙa a kwance a filin wajen,suna kallon ya fito suka nufi inda yake.

Feɗuwa yayi dukka suka amsa masa kaman sunji mai yace.

Hanyar dazata kaishi cikin gari ya nufah kansa tsaye yana tafe suna take masa baya,yanda yake baƙi fuskarnan duk gashi haka suma suke.

Duk hanyar dayabi yara matsawa suke harda samari.

A wajen mai shayin unguwarsu ya zauna akan benci,su kuma karnukan suka tsaya a bayansa kaman wasu fadawa.

"Kai iliyah yiyomin haɗin shayinnan da kake min,kaga na juyeshi a cikina nan"

Dama murya a shaqe,ta kuma haɗu da tashi a bacci,banda hamami babu abinda yake,amma hakan ko kaɗan bai dameshi ba,haka wanda yake gefensa ma ko mai zayyi bai isa yace ya dame shin ba.

Ido suka haɗa da Iliyah wanda yake ta aikin juyah shayi daga wannan kofin zuwa wannan.

"Amma goje na wata biyar fah ya taru akan ka ko ƙwandala baka rage ba"

"To dolene saina rage koda banni da kuɗi iyee,kai akan shayin zaka dunga tsayarmin,idan bazaka yimin haɗi ba faɗamin naji"

"Ahah ba haka bane,kawai dai nima kuɗin hannun nawa ne ya......"

"Kaga banason jin wannan muryartaka mai kamada ta ƴan hamsin,haɗomin shayin kasamu taska injini ya rage maka wani abun,in kuma kasake magana zan baje rumfar nan yanzunnan,kafi kowa sanin banason ƙorafi tamm"

"To shikenan ogah goje barina gama sheƙawa idi tukunna"

"Wanene kuma idi?"

Goje ya faɗa yana duban mazan dasuke zaune a wajen. Wani tsamurarre a gefe Iliyah ya nunawa goje. Suna haɗa ido yayi saurin kawar da kai tareda cewa.

"Ahh bakomai Iliyah haɗa masa zan jira ai"

Yafaɗa muryarsa tana rawa. Ganin har bayan yayi maganar goje bai daina kallonsa ba.

"Kai ɗan garinnan ne kuwa,bansan ka anan yankin ba,ka sanni?"

Goje ya tambayeshi yana ƙare masa kallo kaman yaga ɗan ƙwaro.

"Eh .......hhhh to rani nazo,wannan shine karona na farko,wata na guda kenan a garin"

"Ohh toh...in kanada dabbobi ko wani abu muhimmi karka barshi a waje har zuwa dare,in ba haka ba yazama na bayin Allah,sannan in faɗa ya kaure a lungunku kaji ƙarar wuƙa kada ka fito, ina tausayinka shiyasa na faɗa maka"

Ɗaga kai yayi alamar yaji.

Suna cikin maganar ne Iliyah ya miƙowa goje ruwan shayin tareda yankan biredi.

Karba yayi maƙwat saida yayi rabin kofin,kafin yanki rabin biredin ya tauna.

Kafin kaceme yatashi dashi,wata gyatsa yayi kana ya miƙe daga kan bencin.

"Sai gobe kuma"

Dukka a tare suka masa a sauƙa lafiya mutanen wajen.

Cikin gida ya nufah yana haɗa hanya.


Wata ajiyar zuciya suka sake a tare,kaman wanda aka basu horon ɗauke numfashi idan ya tafi su sake.

"Kai Iliyah wanann ɗin waye shi,shima a anguwar nan yake"

Idi yafaɗa yana zare ido,har sannan hankalinsa bai koma daidai ba da ganin gojen.

Dariyah wani saurayi yayi a gefe kafin yace.

"Goje kenan kake ji,watansa guda baya cikin garin,jiya dai muka ganshi ya dawo,bakada labarin sunyi caca ne shida baban su ubaidu,ya cinye shi yace yabashi kudinsa shikuma bashida ko sisi. Dayaga yana shirin yankashi ya fanshi kansa da ƴarsa,yanzu haka muna nan mun zuba ido wai wani satin za'a ɗaura aure"

"Kai mtsww yarinyar nan kuwa ga kyau ga hankali,wai a rasa dawa za'a haɗata sai goje,ai an cuceta wlh. Kai mutuminnan fah naji ƙishin ƙishin ma wai asiri ma idan akayi masa baya kamashi,gashi da wani ɗan banzan ƙarfi,sarkin garinnan ma shayin horashi yake,shiyasa idan yaci kayanka yanda kasan yaci kayan uwarsa haka yakeyi"

"To kai bakada labarin abinda yayi yai batan zana bashi ba alamunsa,naji fah wai haddashi a waɗanda suka 'balle masana'antar shinkafa ta garinnan,ƴan sanda sunzo kama su suka kashe guda biyu. Amma suma sun kama barayin guda uku. An kamashi aka kulleshi,bamu san mai yayiwa shigaban fursunan ba da kansa yasako shi......hmmm wannan mutumin ai ya wuce yanda kuke tsammani"

"Kai ku bar wannan zancen haka,tunda munanan dashi ai zaiga komai mah,ya batun ni honarable neh,kuna ga zaici siyasar nan kuwa,naji ance yaraba mashina a hamsin a garinnan"

"Rabu damu da wannan barawon,ko tsafi yake da tsohuwar zaba bazan dangwala masa ƙuri'ah ta ba,haka suke barayin banza,suna zaune a office suna satar kuɗin mutane da biro,shuru bakajin ɗuriyarsu sai siyasa tazo tukunna........


Barina bar teburin mai shayinnan nayi gaba......


      ___**___


Gidan matsakaicine kuma na daidai ƙarfi,ginin ƙasane anyi masa ya'be da sumunti,amma wani wajen duk ya bubbule saboda daɗewa,kuma ba wani kula ake dashi sosai ba.

Kofah biyune a gidan,inda iyayen goje suke,saidai babansa ya rasu sai inna mairo kawai ita kaɗaice a ƙofar. Sai kuma ƙofar malam Audu ƙanin babansa da matarsa gaji da ƴaƴansu,yana aikine a gidan wani alhaji,daga bashi ɗaki a gidan gaji ta tattara da ƴaƴan ta suka bishi,suna can yau kusan wata shida. Ƙofarsu shuru,anan goje ya ɗaure saniyarsa.

Saikuma ƙofar goje,shima ɗaki ɗayane na kasa da banɗaki a gefe,kullum ƙofar ɗakin a garkame take da ƙwado,kaman wani abin arziƙine a ciki ba kayan dauɗa ba.

 Sanda gaji tana nan kullum sai sunyi rigima idan ya daki ƴaƴanta in suka shiga ƙofar,inta fara masifah sai yace zai doketa tukunna tayi shuru,shiyasa tafiyin masifar idan baya nan,dan a gabansa kam ko mijinnata ma albarka.

Kullum cikin ƙorafi take wai inna mairo tazo itada ɗanta sun takura musu. Shiyasa da malam audu yasamu aiki itama tabishi,dan itama inna mairon da a birni suke itada mijinta,yana aikin masinja a kotu,yin ritayarsa ne yasaka su dawowa mahaifarsu,shekararsu biyar kenan da dawowa.

Amma goje ya fitini garin kaman dama anan ya tashi.

A zaune take tasaka kayan yin igiyarta tanan tukawa,gidan tsitt kaman bakowa,tun abin yana damunta har ta saba yanzu.

Bayyi sallama ba dan dama bayi yake ba saidai ta ɗaga ido idan taji motsinsa.

Jijjiga kai tayi tareda yimasa magana,ganin ya yaɗau buta yana jijjiga wa,da alama ba ruwa a ciki.

"Yau kuma daga ina"

"Daga jeji a can na kwana"

"Ohhh gari ya hargitse da abinda ka jawo na auren ƴar gidan uwaisu,sunzo nan jiya akan batun,Nayimusu kwatancen gidan da kawunka yake,amma sunce abin baya wani buƙatar manya. Nayi ta zuba idon shigowarka amma banganka ba sai yanzu,wai dan Allah yaushe zaka daina........"

"Ina zuwa inna barina rage marata tukunna,nasha shayi yanzu a wajen Iliyah"

"Yau ɗin ma,kabiyashi kuɗinsa ne,do Allah ka tausayawa mutuminnan da shan shayinsa karka karya masa jari"

"Kai daɗina dake inna kowa yazo yamiki ƙorafi akaina saiki yarda wai,Allah zan fara karya ƙafar duk mai shigo gidannan yana kawo zancena,yanzu dai barina zaga bayan gida,banyi sallannan da ake da safe bama fah"

"Ehhh bakayi sallahr asuba ba,har goma tayi,goje yanzu goje kanaso kuwa........"

"Kai kai kai inna wai abin magana baya miki yawane,yanzu da kika rikeni da yanzu nayi alwala,kinga kenan laifinki ne idan banyi da wuri ba koh"

Sakin baki tayi tareda tsayawa da murɗa igiyar tana kallonsa har ya shige cikin banɗakin,rabonta da ganinsa tun jiya da safe data saka masa koko yasha ya fice,wai yanzu kuma yazo yana cemata laifinta ne da bayyi sallah da wuri ba,hmmm babu mamaki ma sauran sallolin babu wacce yayi a ciki,dan hakan ba ƙaramin aikinsa bane.

"Allah ya kyauta"

Tafaɗa tana cigaba da tukarta.

Bayan ya fito daga banɗakin bai tashi zuge zee ɗin wandon a ko ina ba saida yazo gaban inna mairon.

"To wata sabuwa,shi wandonne duk ka baro banɗakin baka jugeshi ba sai a gabana?"

"Mtsww bazaki gani ganeba wandonne ya matseni daƙyar nage zugeshi"

"Sai akace kuma dole sai kasaka shi koh,zauna muyi maganar nan,dan tana nan a ƙahon zuciyata da ita na kwana. Inaso kayi aure goje ina so naga wanann rana,amma ban taba tunanin irin wanan auren zakayi ba,wanda ko a tarihi ban daba jinsa,yanzu kaida shi babban kobon kunyiwa yarinyar nan adalci kenan iyee,ace kuna wai caca ku saka rayuwarta a ciki?"

"Inna mai nayine anan wajen,ina lafina a cikin wannan lamarin,ko saboda kullum ni laifi nake kai. Gayennan bani nace yayi caca dani ba bashi da ko sisi,shikansa yasan bana ɗaukar asara,kuɗi nace yabani bashida shi yabani ƴar sa. Yanzu ni bakiga ma cuta tah yayi ba,nifah saniya tah sailuba tah na saka a cacar nan,daya cinyeta fah shikenan zuwa zayyi ya siyarta,shiƙuwa ƴar sa da mutanen wajen suka roƙeni na karba wazan kaiwa yasiye ta,dole fah saidai nasaka ta a gidannan nayita kiwon da babu riba,amfanin ɗayane zata dunga yimiki aiki kinga saiki huta dama bakida lafiyar ƙafah. To banda wannan ta ina zan ƙaru da ƴarsa faɗamin shi"

"Yanzu ƴar adam ƴar mutane kake haɗawa da wata can dabba,nidai dan Allah in an kawo yarinyar nan karka cutar da itah kaji?"

"Dan ta wannan ne bani zaki faɗawa ba,ba a kaina zata zauna ba,in ta kiyaye abinda aka ce mata to ta tsira"

"To naji daɗin hakan,yarinyar nan tausayi take bani sosai. Ya batun inda zaku zauna toh,ko kai a gyaramuku sashen Kawunnaka ku tare a can,tunda shi baya nan"

"Nida wa zamu tare ɗin,dan Allah ki bar wannan zancen,ba ga nan ɗaki a gefenki ba ta zauna mana,in zancen Waccan dattijon kike kwanannan zaki gansu sun dawo,waye zai zauna da wannan matar itada tambadaɗɗun ƴaƴannata"

Inna mairo taji haushin abinda yace,to amma yazatayi ,tasan a kaff rayuwarsa babu wanda baya maidawa magana in ka ɗauketa,ciki kuwa harda sarkin garin.

"Kabar wannan zancen dama nasan shi kakeson yi,ɗakinnaka dai zaka gyara ku zauna a can,wanne irin aurene kai kana can ita tana nan,taya zaku fahimci juna a haka."

"Fahimtar juna hhhhhhh wai to kawai tazo gidan ta zauna mana toh,dole sai anyi mata aure dani tukunna ......afff banyi sallar ba ashe,barina je na gurguzata kafin ta anjiman tazo"

Tashi yayi da sauri ya nufi ƙofar tasa,inna mairo ta share masa harabar wajen kuwa. Makulli yasaka ya buɗe ɗakin,bayan ya shiga ya maida ƙofar kaman munafuki.


      ___***___


Kaya take naɗewa na wankinsu da tayi a injin wanki tana waƙar ado gwanja,kana ganinta kasan duniya tana gara masa.

"Sakwara daɗi luwai mun samu guri luwai,kai wlh rayuwar masu kuɗi da daɗi sosai. Ba ruwanka da surfe,ba ruwanka da hura wutar murhu,gas ne kana ɗorawa ka gama,ga wanki ma hajiya tabarka ka saka a inji,ga cin daɗi ga albashi. Kai kuɗi yayi ni gaji"


Lace na a jikinta mai tsada doguwar riga wanda hajiya matar mai gidan tabata kunce,tsabar samun guri ƴaƴanta su Atika har kunna kallo suke a babban falo.

Ita tanayi mata wanke wanke da abinci,shikuma Malam audu yana gadi da kuma ban ruwa ga fulawoyi.

Karaff Atika ta bugo ƙofar ta shigo da gudu cikin ɗakinnasu da aka basu,wanda yake a boys quarter na gidan.

"Gaji gaji nashiga uku shikenan asirina ya tonu tawa ta ƙare gaji"

Riƙota gaji tayi tana tambayar ta lafiya take wannan hakin kaman ta kashe wani.

"Kee lafiya atika mai yasameki haka,ki nutsu kiyimin bayani mana mai ya faru ne"

"Gaji ki tattara kayanki mubar gidanann,baba ma ki faɗamasa kar ya dawo gidannan mu tafi gida gaji,mu koma gida kawai"

"Ke dallah kimin bayanin mai yafaru ne wai,mai kikayiwa hajiyanne,naga ɗazu ta fita daga gidan ma bata nan"

"Eh ta tafi amma komai ta manta saita dawo,shine.....shine.... Tasameni nida alhaji akan gadonta toh. Toh saita yanki jiki tafaɗi,kuma dama tanada hawan jini.......wlh gaji inaga ta mutu,idan ta mutu wannan sojan ɗan uwannata bazai ƙyalemu ba sam,kizo mukoma gida wlh kafin su kashemu"

Sakin hannun Atika gaji tayi ta faɗa akan gado yaraff mai kunnenta yake jiyo mata haka.

"Atika mai kikace wai...hajiyah ta kamaki da mijinta a kan gadonta,idan ma iskanci zakiyi kiyi mana,amma taya daƙiƙancinki zaisa ki bari ta kamaku,ni ai mai farinciki ce idan har yaga yana sonki zai aureki,amma kafin komai ya tabbata shikenan kin zawo mana asarar wannan arziƙi da muka fara lasa. Taya kike ganin zasu barmu mu fita daga gidannan iyee batareda sun lahanta muba"

"Gaji bama wannnan ba,ƙanwarta wannan fatin itama ta ganmu,kuma shi sojan yana waje shiya dawo dasu ɗaukar wani abu a mota"


"Meeee kikkka ceeee shikkenan tafaru ta ƙare,wlh bazan faɗawa malam ba,dolene shima ya dawo ya karbi nasa luguden,ban isa shansa nikaɗai ba aradu. Ke kuma bari a gama yimana na nan kema mu tsira na baki naki...........




Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.


3131951977

Auwal Sadiya

First bank


Ko katin mtn ta nan

***


VTU ta nan

2347068390570


Ƴan niger ku tuntubi wanann number.

+227 97 21 16 15

----------------------------------------------------


Sadi-sakhan ceh

***

Share please