Episode6&7
💅SARKI SAMEER....💅
by❤xeemat....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Episode 6&7🖋
****Ameesha****
Tun wajen qarfe 7 nasafe ta tashi ta fara shirwa wajen 7:30 tagama kamai ko abinci bata tsaya taci racewa dadda idan tadawo taci tai mata sallama tafita tana tafi tana karanta
( Allahumma lasahala illa maja'altahu sahala wa'anta taj'alal hazna iza shita sahala)
Dakuma duk addu'ar datazo bakinta harta qarasa bakin gate din gidan tabuga me gadi yazo ya bude mata tare da lekowa beyima maganaba tace baba barka da safiya ina kwana da fara 'a afuskarshi ya amsa mata da lfy qalau KHADIJATU shi haka yake kiranta saboda shine sunan ta na gaskiya yace harkin qaraso kenan tace eh wlh harma naso in dan makara tafada tanasa kai cikin gidan yamatsa mata tawuce tana ce mishi sai anjima yace Allah yakkaimu afito lfy tace Ameen sannan ta wuce gudan kar suhadu da mutanan gidan yasa tabi ta baranda tashiga kitchen da sallamarta lami dake tsaye gaban gas tana preparing din breakfast tajuyo ta amsa mata tana cewa hajiya Ameesha sai yanzu kuma jiya dana dawo banganki ba ina kikaje ina tajiranki baki dawo ba dan sai wajen magriba natafi daga gidannan amma shiru me yahanaki dawowa ince da lfy ko qarasa shiga tai taqaraso inda take tace lfy amma qalau ba da mamaki lame take kallonta da cewa me yafaru kikace haka tace hmm kede bari kawai zan baki labari sai munsamu lokaci mun zauna tace to shikenan kishiga kifara naki aikin danni harna kusa kammala karin kumallon ba abun dazaki tayani tace to shikenan dake kullum tana riga lamin zuwa idan tazo tafara yin nata sai suyi abinci tare tana dan tai maka mata da wasu abubuwan saboda bazasu bata girki ba ita kaidai tayi yarinta dayawa gashi kuma tana zuwa school shiyasa suka qara dame yi musu girki itakuma tayi share share da goge goge da wanki toilets to tana gamawa sai ta tsaya suyi girkin tare saboda tanason girki arayuwarta komai taga ta dafa sai tayi qoqarin taga ta iyashi zuwa yazu kwa saidai muce Masha Allah dan ba kallar abuncin da bata iya ba saboda lame ta qware gurin iya girki,har zata fita daga kitchen din sai kuma tadawo da sauri tace aunty Lami ina fatande masu gidan nan basu tashi ba ko dan wlh banaso muhadu har inbar gidan nan da rashin fahimta lame take cewa baganeba me kikayi da bakyason ku hadu sai kace yau kikafara aiki tace ai labarin dazan baki kenan wlb laifi nayi musu jiya tace ke daman ai bakya gajiya dayi musu laifi kullumma cikin laifi kike tace ai najiya yafi na kullumma dan saida suka lakadani son ransu tace tabb kina ruwa kam kishiga kifara kar kiqarawa kanki laifi kuma da kike cewa baza kuhaduba har kitafi yazaki da gyaran bedrooms dinsu da kuma wankin bandakunan zaro ido tayi tare da dora hannunta akai tace nashiga aljanna nayi tsudum tsudum yazanyi dan Allah danni wlh nama manta dahakan tace keki sani kuma kitsaya kitazuba anan harsu sufito suga baki komai ba kinga sai sukara maimaita miki abun da suka yimiki jiyan dasauri tayi gaba tana fadin Allah yaqara kiyayeni dan bana fatan hakan tasake faruwa tana tafiya tana magana har taqarasa cikin falon cikin sauri tafara gyarawa adan qan qanin lokaci tagama duk abun daya kamata tayi tana tuna nin yanda kuma zata haura upstair din dan tafiso ma sai sunfito waje yin breakfast sai ta salallaba taje ta gyara musu tai sauri tafiti batare da sungantaba tana cikin wannan tunanni kawai taji takun takalmi amun za asakko qasa sai tai sauri tashi ge kitchen tana shiga suaki karo da lame saura qiris tabugeta kayan hannun ta suzube da sauri tamatsa tana cewa dan Allah aunty lame yi hakuri wlh ban luraba tace bawani nan wai ke baza kinutsu ba sai wani zagaye zagaye kike sai kace wani ne yace kiyi laifin wuce mokama ciki marairaicewa tayi tace Dan Allah kibarni inshiga tafiyafa naji alamun wani daga cikinsu zai sakko tace sai kuma me dalla wuce muje ungo wannan ruqemin mukai dinning mujera kan suqarasa fitowa badan taso ba dan bataso taringa yawan yi mata musu dan haka kawai sai tasa hannu takarba tabita abaya suna qarasawa suka ga mom din agurin harta rigasu zuwa tana mamakin meyasa basu jere abincin da wuriba gashi da wata irin yunwa ta tashi daman tasaba bata wasa da cikin ta shiyasa kullum hawa take kamar anasawa fulawa yis gabanta sai faduwa yake tunda tahangota agun ahankli take tafiya kamar munafuka lame ce ta ajiye na hannuta tanacewa hajiya barka da safiya dafatan kin tashi lfy bata jira amsar taba dan tasan daman ba lalle ta amsamata ba saboda tsabar wulakanci da rashin sanin darajar dan adam irin nata sannan tace hajiya ina neman afuwa aga farceni rashin gammawa da wuri wlh yar matsala aka samu bata kulataba har saida tagama maganarta sannan tace mata dalla malama rufemin wannan banzan bakin naki kizuba min abinci bayan batan lokacin dakikai kuma kinzo kina cikani da surutu dasauri tabude tafara zuba mata abun da tadafa sai lokacin ta lura da bataga flacks din tea ba tajuya tana kallon Ameesha da ta rakube abayanta tace bani to tafada tana mika mata hannu itkuma tabata tanshirin juyawa tace baki iya gaisuwa bane kin wani tsaya sai kace munafuka Ameesha runtse ido tayi jin abun da lame din take mata sai kace bata San halin da take ciki ba meyasa zatai mata wannan tonan siririn ba saida tagama karanto addu'a acikin ranta sannan tadaga qafa da kyar taqarasa gaban yar sukuta😅 ta tsugunna tace mom ina wuni itade baza tadena cemata mom ba dan aganinta ai tahaifeta tunda ta ajiye manyan 'ya'ya kuma harga Allah gani take intace mata aunty kamar tayi rashin kunya sannan taka cewa dan Allah kiyi hakuri wlh bazan qaraba ta qarasa fada idonta na ciccikowa da kwalla kawai jira kawai take taji shaqa amma sai taji shiru kamarma ba mutum agurin ahankali ta dago ta saci kallonta taha abuncita take tafama ci kamar ma batasan da zanmata agun ba haka tai ta zama hat ta kammala cin abinta ta mike zatabar gurin Ameesha taqa cewa kinji mom dan Allah kiyi hakuri wlh b....bata qasaraba takatsata da cewa idan kika kara min magana wlh sai na canza miki kamanni agunnan sha sha sha kawai tafada tana barin gurin wani irin mamakine ya rufeta da taga batai mata komai ba doguwar ajiyar zuciya tasauke harda dafe qirjinta sannan tamike tana makale kafada irin I don't Care dinan tunda de ba abun tai mata ai da sauqi sai taje tai tayin kunbure kunburen ta ita badamuwarta bace damuwarta daya shine ace za ataba lfyr jinkinta shine zata damu tana shiga ta rungume lame tabaya tace kinga ba abun da taimin Allah yataimaki inji lame tace wlh kuwa Allah yasade ta hakura kenan Tace mata ameen sannan suka cigaba da aikin gabansu......
Rasheeda da tana daki takasa fitowa saboda kukan da tasha jiya yanzu kuma sai tashi da ciwon kai dalilin da yahanata fitowa da wuri kenan da kyar ta iya tashi taje tayi wanka tashirya cikin dogurar riga blue ta daure kanta da mayafinta ta fito saboda yanzu ta danji sauqi kan nata yadena yimata ciwo saide bata jin dadin jikin sosai dakin mom din tata tafara shiga ta tarar da ita tana waya tana ganin yar tata tacewa wanda suke wayar to shikenan sai kajini sannan ta kashe wayar tana kallon yarta ta tace daughter kin tashi lfy sai yanzu kika tashi bata amsa mata duka tambayoyin datake mata taqarasa ta zauna akusa da ita tare da dora kanta akan kafadarta kawai sai tafashe mata da kukan shagwaba hankali tashe ta dagota daga kan kafardata tana ruqe fuskarta tace me kuma yafaru waya taba min ke wayajawa kansa bala'i kina dani kike barin damuwa tayi tasiri akanki tafada tana goge mata hawayen ta sannan taqara rungumeta tana bubuga bayanta sai da tabari kukan nata ya lafa sannan ta dago ta tace shalelena gaya min wanda yabata miki ra yanzu muhaura gadon mahaukaciya dashi da sanyin sa safiyar nan za asaki zubar da hawaye taqarasa fada tana tana tsareta da ido tace kenake saurare cikin shashsheqar kukan da ta gama tace mom wlh Allah akori yarinyar can tabar gidan nan wlh na tsaneta so take ta rabani da babyna cike da rashin fahimtar inda maganar tata tadosa tace wai mekike maganane akai jiya ba mungama mganaba gaba daya me kuma ya qara dawo da maganar bayan ta wuce cikin jin haushin abun da Bossay yayi mata a daren jiya tafara korawa uwar tata yanda sukai dashi jiya tace to kuma shine kike wannan damuwar haka ni ai banga wani abun tada hankali awannan maganr ba gaba daya kinsande ko giyar wake yake sha be isa yafasa aurenkiba kuma muddin ya aure ki shida kuma auren wata macen saide alahira idan anayi kuma bama wannan ba ki tuna asalin yarinyar nanfa bata da asali bata da gata bata da galihu ina zatai wata daraja a idonshi barema har yayi tunanin sonta kuma uwarsama baza taba yarda ba ya auro mata yar talakawa marar asali ba turo mata baki tayi tace Bakiga ayanda nagansu bane jiya kuma haka mafa yake ce mata wai baby meesha in basonta yake ba meyasa zena kiranta da hakan tace kika sani kodan haga tayi mishi yarinta ne shiyasa yake cemata haka tace nimafa baby yake cemini tace ai ana fada wannan ai nasoyayane bayanzu naji kema kina cemishi babyn ba kinga shima dole yace miki haka tunda babynce agurinshi gashi kuma yakawo kudin auren ki (hmm Allah yakyauta wai uwace take cewa yar ta haka Tabb bakamar Muba kayi zancen sauryi ma agabansu acima uwa wlh) dan haka kikwantar da hankalinki kawai kinji shalelena kai ta gyada mata Kawai taciga ba sacewa yanzu kitaahi muje kiyi breakfast nasan kinajin yunwa batai mata musu ba ta mike suka fita tare amma duk dahaka bataji zata iya barin yarinyar nanba hakan nan batare da ta dauki kwakwaron matakiba dan wlh ta tsaneta har cikin ranta take jin tsanarta suna fitowa suka nufi kan dinning taja mata kujera tazauna da kanta tayi serving dinta tazauna akusa da ita tana kallon ta har takammala sannan suka dawo falo ta zauna ita kuma mom tace Mata bari tashiga daga ciki tafito Kai ta daga mata kawai ita kuma tawuce sama wayarta ta dauka ta fara daddannawa Ameesha data gama bawa lame labarin abun da yafaru jiya cike da tausaya mata tace Allah sarki gaskiya kinji jiki sannufa tace hmm jin jiki ai ba kadan ba amma ni tunda yau basuyi mini komai ba ma da sauqi tace aikam de kinga kitashi kije kar ki fusatata tayo kanki tunda daman haushinki mikewa tayi tare dacewa bare inje ingyaro bedrooms din inzo intagi gida dan wlh wani bikin yayar kawarmu akeyi inje inshiraya dawuri kar lokaci ya qure min gashi sai naje gurin telama na karbo ankona tana gama fatada bata jira cewar taba tafice tana dab daza ta haura upstairs din taji ance keee zonan ita kwakwata ma bata lura da ita ba cike da zulumin me kuma zatai mata tajuyo tadawo gaban ta kai qasa tare datacewa aunty gani ina kwana bata amsaba ta kawai saiki tayi ta kamo kunnnan ta da qarfi tancewa ke marar kunaya ko marar mutunci kirasa da wanda zaki tsaya kina wa dariya sai babyna to inaso inga ya miki cewa yafi qarfin ki nesa ba kusaba hanyar jirgi daban ta mota daban yatara komai kyau,gayu,dukiya,asali,arzuqi,ilimi babu abun da yarasa ke koma gaya min me kike dashi waye ubanki marar asali yar tsintuwa kawai waya sanima ko uwarki ayawan ta zubar tasameki ayawan gantalinta nabin maza dan da alamabaki kama da 'ya'yan sunna ba daga ganinki kinfi kama da 'ya'yan shegu tasakar mata kunne tanaqarsa da cewa yar titi kawai yar bakin kasuwa shegiyar yar shegiya ke shegiya uwarki ma sheg......bata qarasaba sakamakon jin wani hadaddan maruka har biyu akan kyakkyawar fuskarta da saida taga *ster* ta dafe fuskarta tare da dagowa ta tabbabtar da abun dataji da gaske ne ko kuma mafarki take.........🖋
******************
MASARAUTAR SARKI SAMEER
*******************
Karkubari abaku labarin wannan littafin me salo iri iri daban daban kubiyo ni domin jin yanda wasan ze fara meyeke wakana acikin masarautar sarki sameer kuma waye ya zabgawa RASHEEDA maruka kuma da gaskene AMEESHA yar shegiya ce kamar yanda Rasheeda tafada?muje zuwa amsarku tana gaba zuwa gobe in Allah yakaimu...
daga sabuwar marubuciyarku🖋
*************
❤xeemat....love❤
Don't forget pls comment and share it
My WhatsApp number ***
Pls banda kira
**************************