Episode 8
💅SARKI SAMEER.....💅
by❤xeemat.....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Episode8🖋
******************
MASARAUTAR SARKI SAMEER
******************
*masarautar sarki sameer* gagarabadau masarauta ce datake cikin wani yanki a qasar laraba me cike da dumbin tarihi masarauta me adalci dajin tausayin al'umma me jinkan bayinta awasu shekarun baya da suka wuce amma banda yanzu da komai yacanza saka makon sarkin da yake kai ayanzu kwata kwata ba imani atattare dashi bayajin tausayin talakawa da duk wani wanda yake karkashin ikonsa zalinci da mugunta da cin zarafin mutum ba abune me wahala agareshi ba kuma inde mutum yanaso tasu tazo daya tofa dole shima sai yazama me irin halinsa watakon mugu irinsa me irin banzan halayensa yanzuma hakanne ke faruwa wani tsohon mutum ne ya hade hannayen sa waje daya hawaye na zuba akan fuskarsa kamar tap yace ya me martaba dan Allah naroqeka kaimin rai badan halina ba wlh nabaro matata cikin mawuyacin hali bata da lfy rai ahannun Allah wlh asibiti zan kaita shiyasa harnazo nawuce ban lura da motarku ba wlh kwata kwata hankalina ba a kwance yakeba ba kataimaka kabarni intafi karkasa su rufeni tuba nake wata mahaukaciyar tsawa wani bafade yabuga mishi yace yiwa mutane shiru anan gurin dasauri ya hade bakinshi guri daya daya yana kumashe kukan da yakeson kwace mishi dan takaici yagama cikashi na wannan tsawar da yaron nan ya buga mishi dukansu dagashi harsarkin bawanda be haifa ba amma suke mishi wannan cin mutun cin saboda kawai Allah yabasu mulke sai suringa cin zalin mutane yana wannan tunanin
wannan bafadan da ya bugamishi tsawa yace Allah ja daranka sarkina me dara taci gida sai ceto wanda bayason akawo masa wurgi cikin lamuransa meyanke hukunci cikin adalci(nace hmm ko ina adalcin yake anan wai me adalci ko kunyar fadama beji ba tir da halinku)
saida yagama kodashi sannan yace hukuncinka muke jira ya shugaban mu saida yagama shan qamshinsa yasaki wani qasaitaccen murmushi sannan yace inaso afara rabashi da kayan jikinshi sannan ayi masa doruna hamsin abaya guda ashirin kuma akan ruwan cikinshi sai shabiyar a hannunsa na dama shabiyar kuma ahannun sa na hagu in aka hada duka bulala dari kenan kafin kuma afara inaso afara zuba mishi ruwan sanyi idan angama kuma kar abari yasa kayan akaishi dakin qasa akulle har sai yayi kwana uku aciki sannan kuma banyarda akai mishi abinci kullumba yau kar abashi gobe abashi saudaya jibi kar abashi washe gari kuma idan anfito dashi wajen qafe bakwai nasafe sai abashi sannan anuna mishi inda sashen bayi suke abashi daki da safe kuma zafara aiki a qarqashin ikona daga yau ya dawo bawa acikin masarautar nan yana gama fada yajuya ze bar gurin
dasauri bawan Allah nan ya rarrafa gabanshi yana cewa dan Allah kayi hakuri ka yafemin duk hukuncin dazaka min kaminshi amma dan Allah kar ka hanani komawa gida matata da yayana zasu shiga wani na rashin gani na dan basu san inda natafi ba ko kuma kabarni inje insanar dasu halin danake ciki na roqeka kaimin rai Dan Allah yana roqonsa yana faman goge hawaye danshi duk abun dasuka fada zasuyi mishi baidaga mishi hankali ba sosai kamar maganrsa ta qarshe akan cewa yazama bawa agidan idan yazauna waze kula mishi da iyalansa sarki daya gama fusata da tare shin dayayi yadaga qafa ya take mishi hannu yaqara gaba yana cewa kukara mishi hamsin akan darin sannan kugaya mishi ko dawasa yayi niyar barin gidan nan daga shi har iyalan nasa sai sun ziyarci lahira gaba dayansu yafada yana tafiya tare da maqarrabansa suna goya mai baya
jin wannan batun yasa bawan Allahn nan kamewa agurin be kera motsawa ba saida yaji anfara daga shi anfara qoqarin za'a cire mishi riga haka yanaji yana gani yatsaya kamar mutum mutumi yakasa ko motsi har akagama cireta akatafi kan wando shima akacire akabarshi daga shi sai boxes suka fara aiwatar da abun da aka umarcesu suyi mishi........
***********
*RASHEEDA*
dagowar dazatai idanun ta ya sauka akan DADDA dasauri ta zaro ido waje tana qare mata kallo awulakane cikin zafin nama ta daga hannu itama zata mayar mata da marukan da tai mata saide hannun ta baikai ga qarasa wa fuskarba taji anruqe mata hannu tajuyo tana kallon ta Ameesha da ta ruqe hannun ta tace kar ki kuskura hannun ki yataba ta dan wlh na lahira sai yafiki jin dade kuma daman ko bata mareki ba ni da kaina sai na mareki nazubar miki da hakora nafasa miki baki inga da wanne zakiringa zagin matane ko angaya miki shiru shiru tsoro ne ta fada tana sakar mata hannu ta sa hannu tana goge hawayen dasuke zubowa har yanzu sun kasa tsayawa dadda da har yanzu bata furta komai ba tace ai da kin barta dana tantance mata aya da tsakuya da tagane shayi ruwane tana gama fadar haka taja hannun da niyar su fita taji anruqeta ta juyo taga waye yariketa sai taga matar gidance fuska adaure tace sakar mata hannu mutafi daga yau kuma baza ku qara ganin qafarta agidan kuba bare har kuji dadin wulakan tata ba ko angaya muku talauci haukane dazesa kuna wulakanta ta ba daga yau tabar gidan marar sa mutunci kawai kuma wlh...bata gama fada ba taga tadaga hannu zata mari Ameesha tayi saurin janye ta ta mari iska aikwa a haukace tayo kanta zata wawurota taji andaka mata wata irin tsawa ance wlh kika kuakura kika taba yarinyar nan sai ranki yayi mummunan baci da sauri duka suka dago suna kallon me yin wannan maganar.....
**************
*AZEEMA*
tana zaune aga ban maman ta sai shashsheqar kuka take yiwa mamanta sannu tanacewa mama ki kwantar da hankalinki dan Allah wlh nasan baba ba abun da ze same shi duk inda yake nasan yanzu tunda safiya tayi yana kan hanyar dawowa gida kuma kinga yaya saleem ma yatafi nemanshi yanzu zasu dawo kinji ki kwantar da hankalinki kar ciwon ki yakara tashi kinga da kyar muka samu jiya ya lafa kinji dan Allah tafasa tana kama hannun ta da dan girgizata alamun tafahimce ta tade na faman zubar da hawayen datake suna cikin haka sukaji sallamar saleem da sauri Azeema ta mike tana cewa yaya saleem kasamo labarin inda yake cike da rashin jindadi yagirgiza mata kai yace wlh har yanzu de bawani labari har gurin aikinsu naje amma suka ce min sude sunga ya hau mashin hankalinsa atashe yana ce musu sai gobe matarsa ce ba lfy suka ce mishi Allah yabata lfy yace ameen ya taho tundaga nan basu qara ganin saba yaciga ba da cewa kuma duk inda nasan yana zuwa naje amma bansame shi ba kuma banji wanda yace min yagan shi ba saida ya numfasa sannan yace bari inyi wanka inkara komawa ko Allah zesa adace tace ameen Allah yasa haka ya nufi dakinshi jiki babu kwari ko kallon maman tasa beyiba dan bayaso yana ganinta a irin wannan yanayin shima ba qaramin tashin hankali yake shigaba yana wuce kwa takara fashewa da kuka dasauri taje gabanta ta rungume ta itama tana qara fashewa da kuka haka sukai ta kuka ba wanda ze rarrashi wani sai da sukai me isarsu sannan Azeemar tafara janye jikinta tana qara rarrashin mamam tata da kwantar mata da hankali duk de itama nata hankalin ba akwance yake ba
da rashin dawowar mahaifin nasu gida....
Wasa wasa de sai gashi har wajen magariba babushi babu dalilimsa ba alamar sa babu alamar me kama dashi zuwa lokacin kuwa ba karamin tashin hankali suka shigaba kowa da irin tuna nin da yake wani yana tuna nin ko ansace shi wani kuma yana tuna nin ko wani abunne mummuna yasame shi ko kuma ma mutuwa yayi awani wajen basu saniba kowa de da irin nasa hasashen........
(nace Kutambayi xeemat.... watakil tasan inda yake wlh😜)
***********************
daga sabuwar marubuciyarku.🖋
❤xeemat....love❤
Don't forget pls comment and share it
My WhatsApp number ***
Plssss banda kira