Episode 9
💅SARKI SAMEER.....💅
by❤xeemat....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Episode 9🖋
****************
Cikin tsanani mamaki da yagama cika zuciyarsa wata kon Rasheeda da kuma hajiya sadaiya ita tana tuna nin me hadawo da mijinta a irin wannan lokacin da safe kuma ma be sanar da ita kwasam sai ganinshi sukayi itama Rasheeda na tuna nin me yadawo da abbanta yau bata saniba kode mom daman tasan da dawarta sa amma bata gaya mataba duk suna cikin wannan tunanin yakatse musu ahi da tambayar me yafaru me ya kawo wannan rikicin ne me ya haddasa fadan haka harta kai ake doke doke cikinsu bawanda ya iya bashi amsa saida yaqara buga musu tsawa yace wai ba magana nake muku ba cikin inda inda hajiya sadiya tace alhaji bafa wani abune ya faruba kawai fa....
Wata uwar harara da yabuga mata ita ta sata saurin hadiye maganar da take yace bafa nason sha shancin nan irin naki ko ya ina ganin abu da idona kice min ba komai dan kin maidani mahaukaci shiru tayi tana sauraron magan ganun dayake gaya mata ji take kamar ta shake mishi wuya yaza ai yazo yana mata fada agaban kaskantunan batare da tace mishi komai ba tajuya tabar gurin tana faman sambatu acikin ranta tacika tai fammm da haushi ganin tafiyar tata ne yasa ahi dawo da hankalin sa ka su dadda yace dan Allah baiwar Allah kuyi hakuri nasan halinta akan fadan rashin gaskiyar ta dadda ta jinjina kai tace ba komai alhaji amma fa kaja mata kunne akan abun da takeyiwa jikata dan ina hakuri akan komai amma bana hakuri idan aka taba min jika ta tofa sai inda qarfina yakare bana ganin kowa da gemu Ahe tana kaiwa nan taja ta suka fita da kallo yabita kamar wani sakarai sannan yajiyo da kansa yana kallon yar tasa da takasa barin wajen kanta akasa yace ke uban me yahadaku fada da wannan tsohuwar daga inama take cikin da shashshhiyar muryar ta daba ta fita tace kakar me aikin muce yace um hum inajinki yimin baya nin abun da ya hadaku kasa magana tayi saboda batasan ma ta inda zata fara yi masa bayani ba ya fahimceta ganin bata da niyar magana yasashi cewa bace min daganan kafin in tattakaki agurin nan marar kunya kawai sai na saita muku zama daga ke har uwar taki me daure miki gindin zama yana kaiwa nan amaganr sa yabi bayan matar tasa yaje yaci yaci gaba da zazzaga mata masifar daman sun saba kwata kwata basa jituwa kamar ba mata da miji ba fahimtar juna atsakanin su shiyasa ma idan yayi tafiya sai ya kusan wata uku hudu be dawoba kuma idan yadawo ko wata bayayi yake kara komawa itama kuma tafi son hakan saboda tafi samu tasaqa ta tawala tai abun da ranta yakeso batare da shakkar uban kowa ba saboda ta tsani atakura mata arayuwar ta tafiso duk abun da ta qudurta yinsa to sai ta cimmashi shiyasa tasu batazo daya ba inde yana nan fa to duk abun datai laifini dan badan son datake mishi ba da tuni ta rabuda shi saidai kuma baza ta taba iyawa ba saboda ba karamin sonshi take shikuma da wannan damar yake mata abun da yaga dama idan tayi mishi hauka kuma yace wlh zata bar masa gida idan bata dena ba haka zataja bakinta tayi shiru dan ta tsani yafada mata haka arayuwar ta haka kullum suke yi ahaka suke rayuwa cikin musgunawa junan su..........
Dadda na fitowa hannun ta ruqe da na Ameesh tana faman zazzaga mata fada tace na hanaki na hanaki aiki a gidan nan amma bakyajin magana gashi nan ai yanda suke cimiki mutun ci ai wlh tunda naga kinfata ko sallama bakimin ba nasan nan din kika taho bayan dukan da suka yi miki jiya sabo da baki da zuciya shine kika kara debo qafafu kika dawo ko tace dadda nifa sabo da makaran tata nake yi ina so inyi karatu wlh tace makaran tar dole ce kibari nan gaba idan kina da rabo kyayi ko kuma idan kinyi aure mijinki ya tsaya miki kiyi tace dadda waye ze aure ni bayan banda asali gashi ma naji aunty Rasheeda tace min ni yar shegiya ce a hanya aka haifini dadda dan Allah dagaske ne ni yar shegiy....daddace taisaurin rufe mata baki tace kar ki kuskura inkara jin wannan maganar abakin ki kinji nagaya miki suna kawowa dede wajen gate din gidan tafusge hannun ta tace haba dadda kigaya min gaskiya inde bada gaske bane maganar da ta fada me yasa baza kigaya min gaskiya ba kullum inna tambayeki iyayena sai kice mun sun mutu kuma daman ni banyarda dake ba wlh kina boye min wani abun to nagaji wlh inde baki fada min ba yau to nima zan shiga duniya kifada min gaskiya tafada da dan daga murya sama tana fashewa da wani irin kuka dadda da tai shiru tarasa amasar dazata ba ta batasan me zatace mata ba bataso kuma tagaya mata gaskiya yanzu harsai taqara hankali amma taga alamun yarinyar nan baza ta barta ba tunda har tafara irin wannan furucin tana cikin wannan tunanin taje hone din mota akunnen ta daka suka dago suna kallon gurin da motar take basu gama tunanin wanda yake cikin motar ba suka ga Bossay yafito dauke sa murmushi a fuskarsa saida yakaraso kusa sasu sannan yaga kukan da Ameesha take da sauri yace subhanallahi baby meesha me yasa meki haka me yafaru kike kuka haka wa ya dakeki duk yabi ya rikice yana ta fam jero mata tambayoyi wani kukan taqara fashewa da shi bata iya ce mishi komai ba kallon sa yamaida ga dadda yace me yasameta ne cikin inda inda tace tambayar ta gata nan taga ya maka ni bari in wuce gida in tagaya maka tashigo gida tana gama fadar haka tayi gaba harda gudu gudu sauri sauri dan ba qaramin jin dadin zuwan shi tayi ba adede wannan lokacin dan itade har ga Allah bata san me zata cewa yarinyar nan ba da tasa ta agaba shiyasa ma tayi saurin barin wajen da tasan ze rarrasheta kuma idan tashigo gida bazata kulata ba daga haka kuma har tabar zance dan bata da tada magana idan ta tambayi abu bata samuba har lokacin ya wuce shikenan kuma tabarsa saide kuma idan anqara tayar dashi haka halinta yake dadda na wuce ya tako har zuwa gabanta sosai kamar ze shige jikinta cikin wata irin murya me kwantar da hankali yace ya furta babyyy da wani irin salo yaja sunan tare da fidda numfashi ahankali ita kuma ana ta bangaren wata irin faduwara gaba taji kirjinta sa dukan uku uku yake tunda take bata taba tsayawa da namiji ba irin haka sai taji ta duk wani iri kamar an daddaure ta dan haka sai ta danja dabaya kadan gani duk yanda tayi kuma hawayen bedena zubo mata ba kawai sai yadanyi shiru yana sakin wani site smiling ahankali yakara cewa gaya min mana nan ma shiru ba magana da yaga haka kawai sai ya riqo hannun ta yafara janta itama kuma batai mishi musuba tashiga binshi har saida yakai ta girin motar yabude mata back seat ya sakata sannan shima yazagaya ya shiga yazauna akusa da ita tare da kamo hannuwanta duka biyun yariqe qam sakuma yasaki daya yadaga dayan hannun sa ya dora akan kyakkyawar fuskar ta ya fara share mata hawayen amma saide kamar qara zuga ta yake yana share wa wasu na qara kwararo wa dayaga ji yana ta tuna nin shi yanzu me ze mata tasaura reshi dan yagaji daga nin hawayen nata baya so yaga tana damuwa shima sai yaji gaba daya garin ba dadi da yarasa me zeyi mata kawai sai yajanyo ta jikinshi ya rungume ta tsamm a faffadan qirjinshi sannan ahankali yashiga hura mata isaka adede qofara kunnen ta yana hura mata yana cewa shishhh ya isa haka ki kwantar da hankalinki kiyi shiru kinji kai ta daga mishi kawai tayi mamaki jin lokaci daya kuma taji duk wata damuwar ta tafara raguwa sai taji zuciyar ta tayi sanyi lamo tayi ajikinsa tana shakar daddadan kamshin jikinsa sai sukai wajen minti goma kafin yadago ta tare da tallafo fuskart suna fuskan tar juna yama kallon cikin kwayar idonta yace um uhum tell me what happene to you ahankali ta kwace fuskarta daga hannun shi sannan tafara yi mishi bayanin komai da yafaru ba abun da ta boye mishi komai saida tafada mishi ranshi ba kara min baci yayi ba dajin labarin da tabashi akan dukan dasukai mata da ci zarafin da sukai mata akan dan wannan abun da be taka kara yakar ba shi kwata kwata bega abun magana ba anan da har zatakai ga irin wannan danyan hukunci da suka yanke mata yadade yana jima min abun ku ashema duk wannan damuwar tata duk akanshine shene sila kuma saida yagama jima min wajen 5 minutes dakuna irin abun daze yiwa Rasheeda akan wannan danyan laifin da ta tafka sannan yace dan Allah kiyi hakuri ashe duk ni naja miki kiyi hakuri to kuma kar kidamu ni da kaina zan rama miki kai tashiga kada mishi tace kawai ka rabu da ita kar ka qara jamin laifi ta qarasa maganar da kuka dafe goshin shi yayi tara da qara riqe hannun ta yace to shikenan naji kukan ya isa haka ki nutsu muyi magana jin hakan yasata tsayar da kukan tana qara nutsuwa da maida dukkan hankalinta garshi.......
************************
Anan zan tsaya sai kuma Allah yakaimu gobe in sha Allah zakujini...
*********
daga sabuwar matubuciyar ku🖋
By
❤xeemat.....love❤
Don't forget pls comment and share it
My WhatsApp number ***
Pls banda kira
****************************