8
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
8⃣
Cak ta tsaya a inda take had'i da runtse idanta ta cije hak'oranta,
a hankali tace " Subhanallah yauma rana ta b'aci,
murmushin takaicin halayyar yarinyar yayi kana yace " zo nan!
a slow ta juyo kanta a duk'e a k'asa tana murza hannayenta,
"zo nan nace,
yayi maganar a d'an hasale, a hankali Sanah ta d'ago kanta,
ta kalle shi, ganin yadda launin idansa ya canja kala zuwa red,
ne yasa jikinta d'aukar kerrrrma,
gaba d'aya yanayinsa da kamanninsa sun sauya,
take tsoro yayi masifar kamata,
jikinta ya d'auki rawa da tsuma,
a tsawa ce yace " ba magana nake miki ba dan ubanki?
Cikin kerrrmar jiki Sanah taje gabansa ta tsuguna had'i da fasa kuka,
dan tasan yau kashinta ya bushe,
takai a k'alla 10 minutes durk'ushe a gabansa ya zuba mata ido batare dayace mata komai ba,
kallanta kawai yake cike da tsantsar mamaki da al'ajabin halinta,
na taurin kai da dakewar zuciya,
tunda yake a duniya bai tab'a yarinya irinta mai shegen rawar kan tsiya da rashin jin magana irin ta ba,
ashe matar da zan aura taga bani da arkani?
Cigaba tayi da kukanta batare datace komai ba,
"me ma kikace d'ayan?
"Yauwa taga izajar rayuwa ko?
Ya kuma tambayar ta, k'ara k'asa tayi da kanta,
tana cigaba da kuka,
"mai baud'add'en hali, ya maimaita yana girgiza kansa,
idansa na kanta yace " wanne irin baud'add'en hali ne dani?
Bai bari tayi magana ba yaci gaba,
meye ma'anar majhulil hali?
yayi maganar cike da rainin hankali,
Ya kuma tambayarta,
to yanzu dai da farko meye ma'anar bani da arkani, da izajar rayuwa?
Shiru tayi batace komai ba, ganin bata da niyyar yin magana ne,
yasa shi daka mata tsawa had'i da cewa " ke dan kan uwarki badake nake ba?
Yayi maganar cikin zafin rai,
yadda yayi maganar ya k'ara firgitata sosai,
jikinta ya k'ara cigaba da kerrrmar da yake yi,
a tsorace tace " bani da arkani yana nufin bala'i da masifa,
"a wanne yaren?
Ya kuma tambayar ta,
cikin kuka tace " Sokkotanci,
"ke basakkwaciya ce?
Kai ta girgiza masa alamar a'a,
"magana zakiyi min dan ubanki kamar yadda nake yi miki magana nima,
ko finki bakin magana nayi?
" A'a,
yace " shegiya mara kunya fitsarariya,
kin iya zagewa kiyi rashin kunya da tsiwa san ranki,
amma da kin shiga hannu sai ki fara kuka,
ga rok'o da ban hak'uri kamar a bakin ki aka saukar dasu,
kince ke ba Basakkwaciya bace,
to gidan uban wa kika iya sakkwatanci?
"Ko wajen rawar kai da fitsarartaki kika iya?
Yayi magana duk a lokaci d'aya,
cikin muryar kuka tace " a'a nima ji nayi ana fad'a,
" wajen ubanki kika ji yana fad'a?
Tace "a'a bakin wata 'yar ajin mu, ita 'yar Sokota ce,
zama ne ya su Kano,
"ke 'yar Kano ce?
Ya kuma tambayar ta,
"eh tace,
"ok meye ma'anar izajar rayuwa?
"Taskun rayuwa, ta kuma bashi amsa,
" shi kuma wannan a wanne yaren ne?
"Larabci tace masa,
"oh dama ke Balarabiya ce?
"A'a tace cikin sanyin murya,
ya kuma cewa " wanne yare ce ke?
Fulani ta bashi amsa, ido ya zaro had'i da cewa " what!?
Tace " eh kakana har yanzu baijin Hausa sosai,
koyaya yayi magana saika gane ba cikekken Bahaushe bane,
yace " haba no wander kike irin wannan iskancin,
ai dama duk wani mugun hali Fulani sun had'a shi,
sune Kidnappings, Robbery, mugunta da k'eta,
ba mamaki dan kinyi irin wad'annan k'ananan halayen,
da wuya a kama Kidnapers ko Army Robbers babu ku a ciki,
kallansa tayi tana mamakin yadda yake d'ebewa fulani albarka,
dan ita a tunaninta shima Bafulati ne,
musamman data ganshi fari sol ga gashin kansa,
a kwance luf kamar na Larabawa,
tace " kai ba Bafulata ni bane?
"Allah ya kike yace da sauri,
ya d'ora da,
Allah ya tsare ni da zama Fulani,
ko kinga nayi miki kama da Fulani?
"Eh tace, yace "dayake kinganni fari ko?
"Ku dayake babu fari mai kyau a duniya sai ku,
"ai munfi yawa ne shiyasa da an ganka fari mai kyau ake cewa Bafulatani ne,
kuma kasan abinda yafi....
shiru tayi ganin irin kallan dayake mata,
kallanta yayi yace " shegiya kuna bayin mu amma kina min fitsara,
da sauri ta kalle shi, yace " eh ko Fulani ba bayin Barebari bane?
Sai yanzu ta gane shi Bababbare ne,
cike da mamaki ta kalle shi tace " kuma ya na ganka fari?
"Au dama Barebari babu farare?
"Eh Kakana yace min duk bak'ak'e ne, kuma masu k'aton kai da balle,
duk abi a cika musu fuska da tsagu tun suna yara,
gasu da san girma da fad'in rai,
kuma yace min Barebari bayin Fulani ne,
"tab Moli yace, amma ko zanso naga Kakan nan ki,
"saboda me?
Ta tamabaye shi,
yace " saboda ba gaskiya ya gaya maki ba,
tunda gashi kema yanzu kinga tabbas da idanki,
tunda kin ganni fari kuma babu tsagu,
murmushi tayi tana goge hawayenta,
danta gano d'an adawa ne yanzu,
dama Ganez yasha fad'a mata akwai zolaya da tsokana,
tare da wasa da dariya a tsakanin Fulani da Barebari,
tace " ai my Ulud ma.....
da sauri ya kalle, ido ya zuba mata na wani lokaci yana tunani had'i da sak'a abubuwa da dama a ranshi,
Allah kad'ai yasan meyake tunanin,
a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya murtuke fuska sosai kamar bai tab'a dariya ba,
fuskarsa kwata-kwata babu annuri,
Sanah na ganin haka jikinta ya soma kerrma,
tsoranta ya dawo sabo fil,
dan tasan andawo maganar laifinta,
tunda taga ya koma asalin Moli,
ya kalleta yace " yauwa dama kince kin saka hular kawai an kusa kashe ki,
ta yanzu kin saka har da takalmi da agogo a kashe ki ko?
Yayi maganar yana kallan kwayar idanta,
kuka ta saka sosai had'i da cewa " dan girman Allah kayi hak'uri,
Allah ban k'arawa, kayiwa darajar Annabi Muhammad S.A.W,
ka dubi darajar iyayenka dan Allah da Annabi,
dan darajar mahaifiyar ka kayi hak'uri ,
tayi maganar tana ci gaba da rikitaccen kuka,
ido ya runtse da k'arfi had'i da komawa kan sofa ya kwanta,
dan ko kashe shi aka ayi, aka had'a shi da girman Allah,
darajar Annabi da mahaifiyar sa,
sai ya hak'ura, duk girman laifin da akayi masa,
muddin aka yi masa wannan magiyar dole ya hak'ura,
amma da yaso ya d'and'ana mata kud'arta,
yaso tayi kuka har sai ta gaji da kuka,
amma taci darajar Allah da Annabi da mahaifiyar sa data had'a shi da su,
taje idan halinta ne zata k'ara,
yayi maganar cikin ransa, cikin kuka Sanah ta kuma cewa,
" wallahi Allah nayi maka alk'awarin ban k'ara yin wani laifin har in bar makarantar nan,
in sha Allah, Allah bama kai ba ko wani Malamin ka kama ni na kuma yi masa laifi,
kayi min duk abinda kaka dama,
a hankali ya bud'e idansa ya sauke su a kanta yace " kin tabbata?
Da sauri tace " Allah,
ya kuma cewa " ke da kanki kika ce duk abinda naga dama nayi miki ko?
Ta d'aga kanta,
yace " to ki rik'e wannan a ranki,
tace " to, in sha Allah ma bazan kuma ba,
yace " tashi kije,
da sauri jikinta na rawa ta mik'e ta fita har tana tuntub'e,
yabi bayanta da kallo,
had'i da cewa " evil girl,
sarai Sanah taji abinda yace amma ko juyowa bata yi ba.
Sir Jeeb gajiya yayi da jira yayi tafiyarsa,
dama cikin garin Roni zasu siyan abinci,
shiyasa yasa a kira Moli ko yana da sautu,
sanda ta koma class har an tashi,
dan haka ta wuce hostel, a tsaye ta iske Khulud tana safa da marwa,
idan Halan ne ya fara sauka a kanta,
da sauri Halan tace " Sanah daga ina kike, ina kika je?
Da sauri Khulud ta juya ta kalli inda Halan ke kallo,
ido kawai ta zubawa Sanah tana kallanta,
a hankali Sanah ta duk'ar da kanta k'asa,
tana wasa da 'yan yatsunta, Khulud tace " yauma laifin kika kuka yi masa ko?
Tayi maganar idanta na kanta,
cikin sanyin jiki Sanah ta d'aga kanta,
alamar eh, Halan tace " yau kuma me kika yi masa?
Cikin sanyin murya tace " irin na last week,
ido Khulud ta zaro a tsorace tace " yauma hular tasa kika kuma sawa?
"Na yau yafi haka ma,
Halan tace " yafi haka ma kamar ya?
"Yau har da takalmi da agogonsa na saka bayan hular,
Khulud da Halan suka zaro ido had'i da cewa " me!?
A lokaci d'aya sukayi maganar,
cikin sanyi Sanah ce " eh Allah,
Halan tace " yau kuma dawa ya had'aki ta baki punishment d'in?
Khulud tace " wanne irin punishment aka baki yau?
" Dan nasan na yau sai yafi na last week,
shiru Sanah tayi kanta a k'asa,
cikin tashin hankali Halan da Khulud suka ce " mai matuk'ar wuya aka baki yau ma ko?
Baki ta tab'e kamar zatayi, Khulud ta runtse idanta da k'arfi,
Sanah ta buga tsalle had'i dayin ihuuuu,
tace " yau kam naci mubus,
Halan da Khulud suka had'a baki wajen cewa " bulus kamar?
"Tana dariya ta fad'a musu duk abinda ya faru a tsakanin su,
Halan cike da mamaki ta tsaya tana kallan Sanah,
cikin ranta tace " yau Sir Moli ne ya tsaya da wata d'aliba sukayi magana haka?
Bayan tayi mishi laifi mai girma irin haka,
har ya tsaya yana fad'a mata yare da jinsa sa?
Rasa abin cewa tayi saboda tsananin mamaki,
shiru kawai tayi ta k'urawa Sanah ido,
Sanah tayi murmushi kana tace " Aunty Halan lafiya, wannan kallan fa?
Tayi maganar cikin shagwab'a,
Halan tayi dariya had'i da cewa " wallahi ina mamakin wannan abu ne kawai,
gaki yarinya k'arama ba babba ba balle ace ko sanki yake,
Khulud da Sanah suka had'a baki tare suka ce " SO!!!?
Murmushi Halan tayi had'i cewa " eh mana,
zasu kuma yin magana Halan tace " ban san yawan surutu ku tashi kuje kuyi wanka,
kuci abinci ku tafi karatu kun san dai ranar Monday za'a fara exam ko?
"Eh duk suka ce, kana suka mik'e suka fita,
sosai Sanah da Khulud suka dage da karatu baji ba gani,
ko baccin kirki basu samu har sai da aka gama Exam kana Halan ta sarara musu,
dan hana su sakat tayi da karatu,
Sanah ta d'auki 1st result Khulud ta d'auki na 2rd,
dama haka abin yake tun suna primary school,
Sanah ke d'aukar na d'aya Khulud na biyu,
Ranar Friday ta kama ranar hutu duk d'alibar daka gani cikin murna da matsanannacin farin cike take,
kasancewar ranar duk wani d'an boarding school zai samu 'yan cin kai,
ranar zasu koma gida su sadu da dangi da iyayensu,
ana gama assembly bankwana,
students d'in suka fara watsewa dan komawa hostel ,
dan makarantar akwai tsaro sosai basu sakin yara sakaka,
kamar dabbobi su fita ranar hutu,
dole sai anzo d'aukar d'aliba sannan zata fita,
koda a cikin garin Roni kike wanda gangarawa kawai zasu yi,
amma doka ce dole sai an zo d'aukar d'aliba,
wanda yazo d'aukar yaje ya bada sunanta da sunanshi,
yayi signing,
an kira d'alibar dayazo d'auka an tambaye ta sanshi,
an tabbatar akwai dangantaka a tsakanin su sannan za'a bashi ita,
idan Sir Moli ya sauka akan Sanah da Khulud,
"ke ku zo nan, ya kira su,
jiki na rawa suka k'araso suka zube a gabansa,
hannu ya mik'a musu alamar su bashi result d'in su,
dake rik'e a hannunsu, ba musu suka mik'a mishi ya amsa ya bud'e yana dubawa,
na Sanah ya fara gani ya d'ago kai ya kalle ta yace,
"ashe dai ba laifi, ba iskancin kad'ai bane,
ana fahimtar karatu,
sunkuyar da kanta tayi k'asa batare datace komai ba.
Na Khulud ya bud'e, ganin na biyu yasa shi had'e fuska yana kallan Khulud,
kanta ta sunkuyar k'asa,
"ke ya akayi wannan ta fiki k'ok'ari?
Cikin sanyin murya Khulud tace " dama haka muke d'auka tun daga primary,
rai ya k'ara had'ewa kana yace " to nan ba Primary school bane,
Secondary school ne, dan haka ki dage sosai,
kema ki fita, dan so nake ki zarce ta komai a rayuwa kinji ko?
Shiru tayi batare data ce komai ba,
tsawa ya daka mata had'i da cewa "ba magana nake da ke ba?
Jikinta na rawa tace " bana fatan Allah ya bani abinda zanfi Sanah a rayuwa,
duk abinda zaizo mana na cigaba da k'aruwa ina fatan Allah ya bamu tare,
ina addu'a ina rok'on Allah, kada ya bani ikon mallakar abinda Sanah bazata tab'a samun abinda ya fishi ba,
idan ko har zan samu ina addu'ar Allah ya sanwantar dashi,
daga gare ni ya bata,
a d'an tsorace Moli yace " ke kina da hankali kuwa?
"Sosai tace had'i da d'aga kanta sama ta kalli al'arshe tace " ina fata Allah da Mala'iku su zama shaida,
akan abinda na fad'a yanzu, koma miye a duniya muddin na samu abinda Sanah bazata samu mafificinsa ba,
Allah ka kwace shi daga gare ni ka bata,
ka mallaka mata shi mallakawa ta har abada,
koda tare da rai na da rayuwa ta ne,
shiru Moli kawai yayi yana kallan su cike da mamaki,
dakyar ya iya mik'a musu result d'in tare da cewa " ku tashi ku je,
suka mik'e a tare suka bar wajen,
ya bi bayan su da kallo yana jinjina abin a ransa.
Hango Yayyan su Zafran da Ziyad da sukayi tsaye,
yasa rugawa a guje suka fad'a jikin su,
kowa ya d'aga d'aya sama suna dariya,
batare da b'ata lokaci ba aka sallami su Sanah,
a Hard'o Family kowa ka gani cike yake da murna da farin cikin ganin Sanah da Khulud,
an shirya musu abinci kala-kala na tarbar su,
Sanah sai zuba surutu take tana bada labarin boarding school,
yayinda Khulud tayi shiru tana tunani,
wanda ita kanta bata san tunanin me take yi ba,
haka nan kawai ta tsinci kanta a cikin k'unci da kewar dabata na meye ba,
Sanah ta kalli Khulud tace " muje na raka ki, ki kwanta,
kasancewar a gidan su Sanah suka sauka,
Khulud tayi dariya tace " a boarding school ma bamu rabu ba balle a gida,
daga yau har muyi AURE a part d'aya bedroom d'aya zamu rink'a kwana,
daga yau bedroom d'in mu ya dawo d'aya,
cikin murna Sanah ta kalli Abbu da Mamu (iyayenta Hamraz & Hassana) tace " Abbu kaji wai Khulud ta dawo nan,
dariya yayi yace " sai aji dad'in k'iriniya ba,
Mamu tayi murmushi tana jawo su jikinta ta rungume tace " Allah ya barku tare,
Ubangiji ya k'ara had'e mana kanku,
duk suka ce Amin,
Khulud tace " raka ni na kwaso kaya na daga part d'in Juju da Dide (iyayenta Rawan & Usaina),
Mamu tace " ku bari mana sai gobe da safe,
"a'a suka ce tare,
Abbu yayi dariya had'i da cewa " maza a dawo lafiya.
A parlor suka iske Juju da Dide,
da gudu suka fad'a jikinsu Sanah tace " albishirinku, Dide da Juju suka amsa da "goro suna dariya,
kasancewarsu masu sauk'in kai da wasa da dariya,
Sanah tace " my Ulud yau zata bar part d'in nan,
Dide da Juju suka cewa " zuwa ina?
Sanah tace " zuwa part d'in Abbu da Mamu,
dariya sukayi, Juju tace " Allah ya raka taki gona, kuje can ku k'arata kuda Mamunku,
ni nama huta, Sanah tace " au dama an gaji damu?
Dariya suka kuma yi, Abbu yace " ku dai da Mamu kusan halinta,
suka yi dariya suna shiga d'akin Khulud,
Dide da Juju suka ce "Allah kabar min kan yaran nan a had'e har abada,
Ubangiji karka kawo sab'ani a tsakanin su,
suka amsa da "Amin lokacin da suke fitowa,
ko tsinkenta basu bari ba, sai da suka kwashe komai, suka mayar dashi d'akin Sanah,
tun daga wannan rana Khulud ta koma part d'in su Sanah,
suka koma bedroom d'aya kansu ya k'ara had'ewa shak'uwa da sabo mai k'arfi ya k'ara shiga tsakanin su.
Don't forget to vote, follow and comments
MOMYN ZARAH