RASHIN SANI…

23

by @hauwaausmanjiddarh

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''




2⃣3⃣




Tace " wannan kike nufi?


Khulud tace " eh shi My Sanah,

Allah ina sanshi dayawa,

Sanah tayi shiru tana karantar yanayin Khulud,

taga yadda take cikin farin ciki,

tana murna da tsalle, take fad'in she love him so much,

Sanah tayi shiru tana tunanin yadda akayi yasan gidansu,

da yadda akayi har soyayyar su da Khulud tayi zurfi haka batare data sani ba,

Khulud ta fad'a jikin Sanah tace " nasan kema zaki soshi saboda nima ina sanshi,

shima yana sanki sosai,

ya manta da duk abunda ya faru tsananin ku a baya,

kullum bamu da wata hira sai taki,

ko ban yi mishi maganarki ba, 

shi sai yayi man taki, 

murmushin yak'e Sanah tayi, cikin sanyin jiki tace " wow! My Khulud gaskiya nayi murna,

da farin ciki da jin wannan labarin,

kice kun dad'e kuna shan love?



Ta fad'a tana kallanta,

Khulud tace " ba wani dad'ewa mukayi sosai ba,

da bani da lafiya ne ya nuna kulawarsa sosai akaina,

kuma shine yake d'ebe man kewarki,

taja hannun Sanah suka zauna a bakin gado,

kana Khulud ta shiga bata labarin mafarin soyayyarta da Hanash tun daga farko har k'arshe,

" kai amma abin ya burge ni,

Sanah ta fad'a tana b'oye damuwarta,

saboda yadda ta hango soyayyar shi a cikin kwayar idon Khulud,

tasan kuma muddin ta nunawa Khulud bata sanshi, 

bata kuma kula shi, sai dai idan tayi mata haka bata yi mata adalci ba,

musamman ma data fahimci shima yana bala'in san Khulud d'in,

kuma yana kula da ita sosai,

dan haka bazata tab'a b'ata musu farin cikin su saboda wani banzan dalilinta ba,

ta kuma yiwa kanta alk'awarin daga yau har abada bazata k'ara k'insa ba,

saboda soyayyar da yake yiwa Uludinta,

da kuma yadda itama Khulud take sanshi,

ta kuma d'aukarwa ranta komai zayyi mata,

bazata tab'a ramawa ba, zaici arzikin soyayyar Khulud,

zata kuma ta danne komai a ranta,

 ta kawar da komai, ta rink'a kula shi tana bashi girma da mutuncinsa,

saboda Khulud,

kuma koba komai, ai yana d'ebewa Khulud kewa,

yana kuma sanyata cikin farin ciki da walwala,

jin shiru yasa Khulud tab'a tace " My Sanah lafiya naji kinyi shiru?



Sanah tayi saurin k'ak'aro murmushi tana girgiza kanta tace " bakomai My Ulud,

kawai ina jin dad'i da farin ciki ne,

Khulud ta kalle ta k'ura mata ido na wani lokaci kana cikin sanyin murya,

 tace " My Sanah ko baki san alak'a ta da Hanash ne?



Sanah ta zaro idonta,

tace " kai injiwa?


Khulud tace " My Sanah nafi kowa saninki,

nafi kowa sanin wacece ke,

nafi kowa halayenki da d'abi'unki,

dan girman Allah ki sanar dani gaskiyar abunda ke ranki gami da Hanash please,

Sanah ta kuma yin dariya tana rik'o hannun Khulud cikin nata,

tace " my Ulud ki kwantar da hankali,

babu abinda ke raina, kawai dai ina mamaki ne,

"mamakin me?


Khulud ta tambaye ta idanta na kanta,

Sanah tace " yadda akayi my Uludina ta fad'a tarkon love,

Khulud tayi dariya tace " kai my Sanah,

Allah nima ban san yadda akayi na fara ba,

haka nan kawai na ji ni.....

d'an shiru tayi,

Sanah tace " kika ji me?



Khulud ta turo bakinta,

tace " nima ban sani ba,

Sanah tace " a'a ina za'ayi haka ai dolanki ki fad'a man abinda kika ji,

Khulud ta lura akwai abinda Sanah ke k'ok'arin b'oyewa dan haka cikin sanyin jiki tace " my Sanah!

Sanah ta kalle ta,

taga Khulud ta k'ura mata ido,

rolling idanta Sanah tayi kana tace " me?



Khulud tace " please kin ban damar cigaba da kula da Hanash,

Sanah ta d'an yamutsa fuska tace " sai yanzu za'a nemi izinina bayan aikin gama ya gama,

Khulud tayi dariya tace " ni dai please ni yes or no?



Sanah tace " hmmmm sai bayan kin gama yanke hukuncin fad'awa a soyayyar sa?


Khulud tace " my Sanah ba mutum ne ke yanke hukuncin fad'awa a soyayya ba,

ita soyayyar ce take lokacin faruwar hakan,

shiru Sanah tayi tana san tuna inda ta tab'a jin irin wad'annan kalaman,

Khulud tace " nasan ba lalle ne yanzu ki fahimci hakan ba,

amma akwai lokacin da ke da kanki zaki fad'awa wasu,

Sanah ta shafa fuskar Khulud tace " karki damu kinji My Ulud,

nayi farin ciki sosai da jin wannan labarin,

Allah ya sanya alkhairi, Ubangiji yabar ku tare,

ya kuma albarci soyayyarku,

ya baku zuria ta gari,

Khulud ta amsa da Amin, idanta yana kan Sanah,

Khulud tace " Yayan su Zohal & Wajnah Waseef ne,

Sabah tace " kai haba?


Khulud tace " Allah da gaske uwarsu d'aya ubansu d'aya su uku ne kawai a wajen iyayensu,

Sanah tayi dariya kana tace " kin san me?


Khulud tayi saurin cewa " a'a,

Sanah tace " naga Sir Moli fa,

cikin zumud'i Khulud tace " kai a ina?


Sanah tace " a makarantar mu,

lecturer ne a department d'in mu,

Khulud tace " kuma ya gane ki?


Sanah tace " ya gane ni ko na gane shi?


" D'an rainin hankali,

Khulud tace " zaki fara ko?


Sanah tayi dariya kana ta shiga bawa Khulud labarin had'uwarta da Sir Moli tun daga farko har k'arshe,

amma ta kasa sanar da ita abinda ya shiga tsakaninsu,

karo na farko a rayuwarta data b'oyewa Khulud wani abu,

haka nan kawai taji bata san sanar da ita,

Khulud tayi dariya kana tace " kai wallahi drmarku na birgeni,

ashe an d'ora daga inda aka tsaya,

dama ina nan dana sha kallo wallahi,

Sanah ta tab'e baki, tace " rabu da rainin sense shi so yake ni na fara nuna na sanshi ko na gane shi,

yadda zai samu damar wulak'anta ni,

ya farfad'a man bak'ak'en maganganu san ranshi,

cikin dariya Khulud tace " durk'usawa wada ai ba gajiyawa bane,

my Sanah in kin nuna kin sanshi sai me,

wani abun ne zai ragu daga jikinki?



Sanah ta nuna kanta tana tab'e bakinta,

had'i da yin rolling sexy eye d'inta,

tace " ni na zan nuna na sanshi God forbid,

ta fad'a tana nuna kanta,

Khulud tayi dariya kana tace " Sir Moli witch kawai,

Sanah ta zaro ido had'i da mik'ewa tsaye tace " what! ni?


Khulud tace " eh mana in ba ke ba da wa!?


Sanah ta d'auki pillow tana bin Khulud,

Khulud tayi baya tana dariya tace " Sir Moli witch,

Sanah ta bita da gudu tana jefa mata pillows,

Khulud ta hau kan bed tana yiwa Sanah kwalo, had'i da tare pillows d'in,

wayar Khulud ta soma ringing,

Sanah tayi saurin d'aukar wayar tace " sake fad'a inba tsoro ba,

Allah yanzu na taro miki March,

Khulud ta rik'e kunnuwanta had'i da d'an girgiza kanta tace " I'm so sorry,

ban k'arawa, Sanah tayi dariya kana ta mik'e mata wayar,

da sauri ta amshi wayar had'i dayin picking,

" hello my life, ya kike?


"Lafiya lau, Alhamdulillah, an u,

yace " ina lafiya kamar yadda kike,

 kin ci abinci?


"Eh, kai fa, murmushi yayi mai sauti har dimples d'insa suka lotsa kana yace " yanzu Mimmee ta gama bani,

Khulud tace " dear wai meyasa baka san cin abinci?


Dariya yayi yace " ni ma ban sani ba,

Mimmee dai tace haka nake tun ina Baby,

idan kika zo sai ki wakilci Mimmee ki rink'a baki ko?


Ya fad'a cikin shagwab'a,

fuskarta ta rufe kamar yana ganinta,

tace " hmmmm, 

yace " Papu yace nayi miki magana kan zasu zo wajen Abbu,

tun last week na sanar dake amma kink'i cewa komai,

murmushi tayi kana tace " dama jira nake ayi approving d'in mu kuma anyi,

cike da mamaki yace " approving!?


Tace " yes!

Yace " waye zayyi approving d'in?


Tace " My Sanah mana,

ji yayi kamar ta watsa masa wuta,

amma sai ya kanne yace " to tayi yanzu?


Tace " eh tayi, dama ai na fad'a maka bata tab'a kin amincewa da abinda nake so,

Allah baka ga yadda taji dad'i tayi murna da farin ciki ba,

" shegiya karuwa 'yar iska ba,

ai dole ta yarda saboda tana tsoran kar na tuna mata asirin iskancin da take yi,

ya fad'a cikin ransa,

a fili kuma yace " masha Allah,

kana yace " yanzu if she's saying no ,

shikenan our true love has been cancel,

da sauri tace " wallahi capital latter YES!,

dan ban ko k'ara kallan inda kake balle nayi maka magana,

so put it your mind albarkacin My Sanah kaci,

ido Hanash ya runtse da k'arfi yana jin kamar zai mutu,

yana jin yadda zuciyarsa ke k'una had'i da tafasa,

in banda yana mugun san Khulud da tuni ya rabu da ita,

amma rabuwa da ita dai-dai yake da fitar numfashinsa,

daurewa yayi yace " ok any way,

yanzu yaushe su Papu zasu zo?


" Bari na nemi izini wajen my Sanah,

zayyi magana yaji ta kashe wayar,

wayar kawai Hanash yabi da kallo yana sak'e-sak'e da tunani a ransa,

Khulud ta juya ta kalli Sanah tace " my Sanah!

"na'am Sanah ta amsa,

Khulud tace " wai iyayen su Hanash ne zasu zo,

Sanah tayi saurin mik'ewa zaune tace " kai haba, yaushe?


" Ai shine nace bari na tambaye ki,

Sanah tace " ok bari naje na sanar da Mamu,

in yaso sai ta sanarwa da Abbu ko?


Khulud tace " ni dai a'a kunya nake ji,

Sanah tace " to mu sanar da Aunty Halan inyaso saita sanarwa da Yaya Ziyad shi sai ya sanarwa Abbu da Didi,

Khulud tace " ni dai kunya nake ji,

Sanah tace " to za'ayi idan ba'a sanar da su ba?


"Ko haka nan kawai zasu ga mutane da ka?


Khulud zatayi magana Sanah ta mik'e,

Khulud ma tayi saurin mik'ewa ,

Sanah zata fita Khulud ta rik'o tace " no,

Sanah ta fisge ta fita da gudu,

Khulud tayi saurin bin bayan ta,

da gudu suka yi parlor,

Abbu da Mamu na zaune suka gansu da gudu,

Abbu yace " lafiya!?


Sanah zatayi magana Khulud tayi saurin rufe mata baki,

 tana yak'e tace " bakomai Abbu,

Sanah na k'ok'arin kwace bakinta ta d'aga hannunta alamar k'arya take,

Mamu tace " wai ku meye haka?


"Kun girma amma baku san kun girma ba,

kuna abu irin na yaran goye,

Sanah ta kwace bakinta tana hak'i,

Khulud na k'ok'arin sake rufe mata bakin tace " iyayen Hanash zasu zasu zo,

Khulud na jin Sanah ta fad'a ta saka kuka,

Abbu yace " to ikon Allah meye abin kuka kuma?


"Zonan kinji d'iyata ya fad'a yana mik'awa Khulud hunnu,,

ba musu Khulud ta nufi wajen Abbu ta zauna kusa da shi,

cikin rashin fahimta Mamu tace " waye Hanash?


Sanah tace " saurayin Khulud ne,

shine iyayensa suka ce suna san zuwa,

shine tace wai kar a gaya maku kunya take ji,

da gudu Khulud tayi bedroom d'insu cike da kunya,

cikin mamaki Abbu ya kalli Mamu yace " dama kin san da maganar ne?


Mamu tace " eh! 

Abbu ya kalli Sanah yana murmushin jin dad'i cikin murna yace " zanyi magana da Didi,

sai na sanar daku ranar da zasu zo,

Sanah tace " tom, kana ta nufi bedroom,

ta iske Khulud, Khulud na ganinta mik'e tana dukan Sanah cikin wasa,

Sanah tayi dariya tace " wannan duk murnar ce, uhnnn amaryar Hanash,

Khulud ta kuma kaiwa Sanah duka,

wayar Khulud ta soma ringing,

Khulud tayi banza da wayar cike da murna Sanah tayi picking,

tace " hello!

jin muryarta yasa shi jin zafi har cikin ransa,

" hello ta kuma cewa,

sai da ya runtse idonsa kana yace " ina mai wayar?


Sanah bata d'auki wani abu ba,

tace " gata nan kusa dani,

a dak'ile yace " bata,

jikin Sanah a sanyaye ta mik'awa Khulud wayar tana yak'e,

cikin ranta kuma tana mamakinsa,

Khulud ta amshi wayar kana tayi masa bayanin komai,

guntun murmushi yayi kana yace " kiyi mata godiya,

Khulud tace " gata kayi mata da kanka,

yace " no ba sai kin bani ba,

kiyi mata kawai,

nima sallah zanyi,

shiru Khulud tayi batare data ce komai ba,

yace " I love you, good night,

bata bashi amsa ba,

ta kashe wayar,

kana ta tura masa text,


_Ka sani ban tab'a auren mutumin da baya san my Sanah baya kuma shiri da ita duk son danake yi masa,_

_wallahi koda sanka zai zama ajalina muddin baka san my Sànàh ko babu good understanding tsakaninku zan iya hak'ura da kai,_

_na barka har abada na kuma manta da kai da rayuwarka_

_so gwara ma ka sani ka kuma lura,_

_muddin kana so na kana kuma san aure na ka kasance da ni har rai da mutuwa to ka fara koyar yadda zakayi kà so Sanah ka kuma yi mu'amula da ita,_

_dan ko a ranar d'aurin auren mu Sanah ta nuna bata amince da kai bà wallahi sai na fasa,_



Murmushin takaci Hanash yayi bayan ya gama karanta text d'in,

yana jin inama zai iya rabuwa da Khulud da ya rabu da ita ya hutawa ransa da rayuwarsa,

sai dai bai iya rabuwa da ita a yadda yake jin mugun santa har cikin kwakwalwarshi,

text ya tura mata shima,


_I'm so sorry if I hurt you_

_ba da wata manufa nayi hakan ba, amma kiyi hak'uri please,_

_gobe zanzo na baku hak'uri ke da our Sanah, I love you so much_


Murmushi tayi kana tayi cilli da wayar ta kwanta.



Washe gari da wuri Sanah ta shirya kasancewar suna da lectures da Sir Moli 8:30am na safe,

tun da wannan abun ya faru Sanah ta shiga taka tsantsan dashi,

data ga suna da lectures dashi take sauri ta shiga class ta samu can baya lungu ta zauna,

a hankali Sanah ta shiga cikin class d'in tana takawa a hankali,

ta samu wajen a baya ta zauna tana jiran lokaci yayi ya shigo,

kan motarsa ya danno cikin makarantar,

a parking space yayi parking,

ya kai wajen 15 minutes kana ya zuro k'afarsa d'aya waje,

kai da kanin k'afar sanye cikin takalmin Nike,

kasan mamallakin k'afar yana cin duniyarsa da tsinke،

a hankali ya zuro d'aya k'afar kana ya fito gaba d'ayan sa,

sanye yake cikin arnan Man material,

mai laushi, color blue black,

takalmi, agogo da hularsa black color,

cikin nutsuwa ya d'auki laptop & brief case d'insa,

ya fara takawa a hankali ya nufi class d'insu.



Sir Moli na gaf da shigà yà fara jiyo hirar su rose,

dan haka ya d'an tsaya kad'an,

Sanah na zaune a baya taji wasu Christians suna hira,

d'ayar mai suna Rose tace " ni fa ina mamakin Muslim,

d'ayar tace " mamakin me?


Rose tace " yadda suke bautawa wanda basu sani ba,

ba kuma su tab'a ganinsa ba,

d'ayar ta tab'e baki tace " nima abin nan yana bani mamaki fa,

yanzu da zaka tambaya su ina Allah su yake shiru zasuyi suyi tsuru-tsuru,

a zafafe Sanah ta mik'e ta nufi inda suke zaune,

tana zuwa bata jira wata-wata ba ta kifawa kowacce mari bibbiyu,

Sir Moli dake tsaye jikin window yayi saurin kallan Sanah cike da mamakin rashin tsoranta,

dan dukkannin su gidiga-gidiga ne,

masu k'irar k'atti babu wacce bazata iya sab'ar Sanah ta zagaye garin Kano kaf da ita ba,

Rose da d'ayar suka mik'e da sauri cike da mamaki,

suna kallan Sanah Rose dafe da kuncinta tace " kika mare mu?


Sanah ta zaro idanta kamar gaske tace " ni yaushe na mare ku?


Sir Moli ya gyara tsaiwarsa yana kallan ikon Allah,

Rose tace " yanzu fa kika mare mu,

Sanah tace " idan har da gaske kuke yi na mare ku,

ku nuna min marin,

Rose ta nuna kuncinta tace " gashi,

Sanah ta kalli kuncin had'i da sanya hannunta ta rik'e fuskokinsu tana duddubawa kamar gaske,

tace " ni fa banga komai ba,

gaba d'aya ajin akayi tsit kowa ya maida hankalinsa kansu,

Rose tace " kamar ya baki ga komai ba?


Sanah tace " eh banga marin ba,

amma ke tunda kina ganinsa kina iya nuna min shi na ganshi,

d'ayar tace " ke karki raina mana wàyo,

Sanah ta sanya hannunta ta rik'e hab'arta had'i yin sautin da bakinta,

tana kallansu cike da rainin hankali,

" in banda rainin hankali dama ana ganin mari ne?


D'ayar ta fad'a,

Sanah tayi murmushi kana tace " au dama ba'a ganin mari?


Rose tace " tayaya za'a ga mari?


Sanah tace " to yaya kika san na mare ki?


Rose tace " naji shi ne,

Sanah tace " yauwa anzo wajen,

kin tabbata ba'a ganin mari,

amma ana jinsa,

dana mareki baki ganshi ba amma kinji shi har cikin kwakwalwarki da zuciyarki,

to kamar yadda bakiga marin nan ba,

amma kika yarda akwai shi, zuciyarki da kwakwalwarki suka amince suka kuma gaskata shi gaskiya ne,

haka Allah Ubangijin mu mai komai da kowa yake,

shi dayake shine Ubangijin gaskiya shiyasa ba'a ganinsa,

amma zuciya, rai ,ruhi , kwakwalwa, duk suka yarda suka kuma amince akwai shi,

zati da k'udurar Ubangijinmu tafi k'arfin ido ya ganshi,

yafi k'arfin zuciya ta siffatanshi,

yafi k'arfin rai ya misaltashi,

kana ta kalli jakarta tace " yanzu Rose idan kika shigo ajin nan kika ga ba kowa sai wannan jakar kad'ai,

kin san akwai mai ita,

akwai kuma wanda yake mallakinsa ce,

sannan kin tabbatar akwai wanda ya k'era ta ko?


Rose tace " haka ne, duk wani da kika gani akwai meshi,

Sanah tace " good, to kamar haka be akan duniya,

Rose ko kwano kika gani ajiye kin san akwai meshi,

balle kuma duniya da abinta ke cikinta,

ke kanki kin san akwai mai ita,

saboda babu abinda yake halittar kansa

komai kika gani a duniya yinsa akayi,

idan kika kalli shuke-shuke da ruwa, jini da mutum kad'ai ya isa ya tabbatar miki akwai Ubangijin gaskiya,

so please ku bar irin wad'annan maganganun a cikin al'umma saboda hakan yana iya haifar da fitina,

ayi ta kashe rayukan da basu ji ba,

basu gani ba,

ba su Rose kad'ai ba, duk wanda ke wajen sai da jikinsa da zuciyarsa tayi sanyi,

Sanah ta koma inda take zaune ta zauna kamar babu abinda ya faru,

Rose ta kalli Sanah tace " I'm sorry,

then thank you so much,

Sir Moli dake tsaye yayi guntun murmushi,

yau karo na farko da Sanah tayi abu a rayuwarsa yaji ta burge shi,

sosai yayi mugun mamakin basira da hikimarta,

a hankali ya taka ya shiga class d'in,

sai da ya gama koyar da su as usual kana ya fita.



Hanash sai da ya tabbatar Sanah ta tafi makaranta kana ya shirya cikin Man lace,

ash color, takalmi, agogonsa gucci,

hularsa kalar aikin jikin kayan yayi masifar kyau,

idan ka ganshi sai ka rantse bai san Hausa ba,

dama abinka da bafulatani usul back and front,

duk inda kake tunanin had'uwa ko kyan namiji Hanash ya kai koma in ce ya wuce,

yana da bala'in kyau kamar aljani,

dan da yawa wad'anda sukayi karatu tare basu yarda d'an Nigeria bane,

waya ya ciro daga aljihunsa ya sanar da ita yazo yana set room,

itama tayi kwalliya cikin riga da skirt na atamfa tayi simple make up,

bakinta d'auke da sallama ta shiga,

har k'asa ta durk'usa ta gaida shi,

ya amsa fuska cike da fara'a,

a hankali ta zauna akan sofa had'i da satar kallanshi,

karaf suka had'a ido,

tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa,

yayi murmushi cikin nutsuwa yace " ya dai ake satar kallo na,

a fito kai tsaye a kalle ni mana,

kiga angon naki sosai, kar sai daga baya kice nahi,

tayi murmushi,

yace " ina our Sanah,

tana ji yace " our Sanah, tayi saurin d'ago kanta ta kalle shi cikin jin dad'i,

tace " tana makarata,

kansa ya d'an dafe yace " oh! zuwa fa nayi na bada hak'uri,

ance jiya nayi laifi,

dariya tayi had'i da saka hannu ta rufe face d'inta,

yace " ya kukayi da Abbu yau?


Tace " ai my Sanah bata dawo ba,

dole sai idan ta dawo zamu ji komai,

sannan koma meye kayi magana da ita kawai, duk abinda tace is okey to me,

murmushi yayi yana danne abinda ke ransa,

sosai sukayi hira kana da zai tafi ya mik'o mata laida,

k'in amsa tayi,

dan dama sun saba haka duk lokacin da zai mata kyauta sai ya sha fama kafin ta amsa,

yace " to zaki fara ko?


"Wannan ai ba naki bane ke kad'ai,

ke da our Sanah ne,

jin yace harda Sanah ta amsa had'i dayi masa godiya,

har bakin mota ta raka shi ya fita,

tana shiga gida ta aje kyautar tak'i b'ud'ewa tana jiran Sanah ta dawo.



Ko da Abbu yajewa da Didi da maganar masu neman auren Khulud zasu zo,

cewa yayi shi ina ruwansa ai shine ubanta yayi duk abinda ya dace kawai,

hakan da Didi yayiwa Abbu yasa Abbu yaji dad'i sosai,

Didi yana komawa gida ya sanar da Juju,

jikinta a sanyaye tace " to ita Sanah fa?


Didi yace " itama Allah zai kawo mata,

mu dai addu'a ce tamu,

Abbu ya sanar da Mamu ta fad'awa su Sanah cewa su zo ranar Friday,

kana Abbu ya Sanar da Ziyad da Zafran,

ko da Ziyad ya sanar da Halan itama cewa tàyi Sanah fa,

Sanah yau da wuri ta dawo daga school,

wanka tayi kana tayi sallah taci abinci,

sai data gama komai kana Khulud ta d'auko ledar da Hanash ya kawo musu,

tace " My Sanah Hanash yazo ganinki baki nan,

amma yabar sak'o,

Sanah tayi dariya kana tace " ayya dan Allah ki bashi hak'uri,

Khulud tace " ai badamuwa ya fahimta yace zai dawo da weekend sai ku gaisa,

Sanah ta amshi ledar ta bud'e wasu arnan perfumes suka gani masu shegen kyau da k'amshi,

da gani kasan masu shegiyar tsada ne,

Sanah tace " wow! amma gaskiya naji dad'in kyautar nan,

please kice masa nagode sosai,

Khulud tace " in ce masa kodai ki kira shi kiyi masa godiya da kanki,

Sanah zatayi magana Mamu ta shigo,

a bakin bed ta zauna kana ta kallesu tace " to ku sanar da su suzo ranar juma'a,

Khulud tasa hannu ta rufe fuskarta,

Mamu tace " kwaji dashi dai 'yan nema,

ta fita tana dariya,

Sanah tace " kira shi a fad'a masa,

ba musu Khulud tayi dialing number sa,

kashewa yayi ya kira ta, tayi picking sai da ta gaida shi kana tace " magana zakuyi da my Sanah,

yayi murmushin k'arfin hali yace " ok bata,

Sanah ta amsa tana murmushi ta gaida shi,

ya amsa ba yabo babu fallasa,

godiyar perfumes ta fara yi masa,

kana ta sanar dashi sak'on Abbu,

yayi d'an murmushi yace " nagode,

a tak'aice, itama murmushin tayi kana ta mik'awa Khulud wayar,

suka shiga shan love,

suna gama wayar Hanash ya nufi part d'insu Mimmee,

a parlor ya tararda su,

har k'asa ya durk'usa ya gaida su,

suka amsa cikin so da k'auna,

zayyi magana Papu yace " ya kukayi a BUK?


Kansa ya shafa kana yace " Papu ban samu ganin shi ba,

Papu yace " kamar ya baka ganshi ba?


Hanash yace " naje har sau biyu amma ban samu ganinshi ba,

kana yace " wai Papu dole ne sai su Zohal sun cigaba da karatu?


" Mai zai hana ayi musu aure kawai,

Allah yawancin malaman jami'a 'yan iska ne,

basu da wani aiki sai lalata yaran mutane,

a d'an hasale Papu yace " saboda baka san suyi karatun shiyasa kak'i maida hankali?


A hankali Hanash yace " kayi hak'uri Papu ban san magana ta zata b'ata maka rai ba,

kayi hak'uri in sha Allah ranar Monday zan koma, 

zan kuma yi iya bakin k'ok'ari na,

zuciyar Papu tayi sanyi jin kalaman Hanash,

cikin sanyi Papu yace " yauwa nagode Allah yayi maka albarka,

Ubangiji ya baka zuri'a ta gari,

Allah ya albarkaci rayuwarka,

Hanash da Mimmee suka amsa da Amin,

Papu ya kalle shi yace " naga kamar da magana a bakinka ko?


Hanash ya d'an shafa kansa kana yace " eh!,

Papu ya karkata hankalinsa gaba d'aya gare shi,

yace " ina jinka,

baki Hanash ya d'an turo kana yace " to ka daina kallo na Papu,

yayi maganar cike da shagwab'a,

Papu yayi dariya yace " nama rufe ido na,

Hanash yace " iyayen Khulud ne suka ce ku je ranar juma'a,

Papu da Mimmee suka bud'e baki cikin matsananciyar murna,

Papu yace " kai masha Allah, rabon danaji labari mai dad'i irin wannan har na manta,

Hanash yasa hannu ya rufe fuskarsa wai shi kunya,

Papu yace " kayi min text d'in details na gidan,

Hanash yace " tom,

Mimmee ta mik'e zata fita,

Papu yace " ina zaki?


Tace " wajen Jadda mana a sanar mata abin farin ciki,

abinda ta dad'e tana jira,

Zohal da Wajnah dake lab'e suka fito da gudu suka yi waje suna dariya,

sukace " Mimmee mu zamuyi mata albishirin,

koda suka sanar da ita bata yarda ba,

sai da tazo har part d'in Mimmee,

suka fad'a mata da kansu kana ta yarda,

dan murna har rawa ta taka.



Kamar yadda aka tsara ranar Friday iyayen Hanash suka je,

Yayyan Papu biyu da abokinsa ne suka je,

an karb'e su hannu bibbiyu, cikin mutunci da girmamawa,

suka gabatar da kansu, ashema sun san juna sosai,

Papu abokin Didi da Abbu ne tare sukayi primary da secondary,

set d'in su d'aya, sosai sukayi farin cikin sake ganin juna rayuwarsu,

dan sun nemi juna har sun gaji da neman junansu har sun hak'ura,

dayake an san juna Abbu yace karsu damu zai sanar dasu duk halin da ake ciki,

a cikin kwana biyu Abbu yayi bincike sosai akan Hanash dama gidansu,

babu wani abun k'i a tattare dasu,

sai ma yabo da suka samu daga wajen mutane,

sosai Abbu da Didi sukayi farin cikin jin yabon da al'umma keyiwa Wassef,

duk da dama sun san halayyarsa,

Abbu ne ya kira a waya cewar sun gama duk abinda ya kamata,

mutanen da suka zo da farko su suka k'ara dawowa,

duk abinda ya kamata sunyi,

sun kawo goro da alawa da kud'in neman aure,

goro da alawa kad'ai Abbu ya amsa shima dakyar,

yace " sadaki kawai zasu kawo shima sai ranar d'aurin aure,

aka sanya bikin wata biyu kad'ai,

shima dan Mamu ta dage ne,

saboda tanasan shirya 'yarta sosai,

amma da wata d'aya aka saka.



Tafiya kawai take a matuk'ar gajiye lik'is,

dan dakyar take iya d'aga k'afarta,

ga yauma Aarib yana busy bazai samu damar zuwa d'aukarta ba,

fita tayi daga get tana neman mai adai-daita,

daga gefenta taji haushin kare,

a hankali ta juya taga wasu tik'a-tik'an karnuka guda biyu,

suna lasar harshe,

da k'arfi gabanta ya fad'i, jikinta ya d'auki kerrrma,

saurin tafiyarta ta k'ara,

taga karnukan sun mik'e daga kwancen da suke, suna kallanta,

juyawa tayi taga lungun babu kowa,

dan haka tsoro ya k'ara kama ta,

ta fara gudu-gudu sauri-sauri,

ganin yadda jikinta ke tsuma yasa karnukan zaton ko bata da gaskiya,

san haka suma suka fara binta a hankali suna haushi,

jin haushinsu yayi masifar gigita ta,

dan haka ta tattare doguwar rigar material dake jikinta,

ta zage iya k'arfinta ta soma gudu,

aiko karnukan suka ce dawa Allah ya had'a mu,

suka bi bayanta a guje,

ganin sun biyota yasata yin cilli da mayafinta datayi rolling dashi,

gaba d'aya gashinta kanta ya zubo bayanta ya barbaje,

ya hargitse, 

tayi kuma yin cilli da takalmi da jakarta,

tana gudun tana kuka,

tana kuma juyawa baya tana kallan yadda karnukan ke binta,

direct baya Sanah ta koma ta nufi cikin makarantar,

karnukan suka bi ta,

a hankali ya fito daga office d'insa,

ya nufi motarsa cikin takunsa na izza,

cikin nutsuwa ya bud'e d'ayan b'angaren ya ajiye laptop da brief case d'insa,

kana ya zagayo zai shiga motar,

hangota yayi tayiyo kansa gadan-gadan,

American dogs na biye da ita,

bako d'an kwalli bare takalmi da mayafi,

sai iska dake faman kad'awa  tana yin baya da rigar jikinta,

had'i da d'aukar gashin kanta yayi sama ya barbazu,

ganin direct shi ta nufo yasa shi zaro ido,

had'i da girgiza mata kansa alamar no,

saboda yadda compound d'in ke cike da students,

ganin bata fasa nufo shi ba,

yasa shi ce mata " a'a fa,

amma kafin yayi aune ta fad'a kansa,

daga shi har ita sukayi baya,

suka fad'i k'asa,

shiya fad'i a k'asa ita kuma ta kansa, gashinta ya bazu ya rufe musu fuska,

fuskarta kan tashi,

bakinta kan nashi, hancinta na gogar nashi,

hannayenta duka akan k'irjinsa,

ita kuma gaba d'ayanta akan jikinsa................





MOMYN ZARAH