πŸ’žπŸ’žπŸ’žLAILAHπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Chapter 11&12

by @gimbiyaayshu2503

πŸ’žπŸ’žπŸ’žLAILAHπŸ’žπŸ’žπŸ’ž


STORY AND WRITTEN BY 


AISHA MA'ARUF(GIMBIYA AYSHU)


ELEGANT ONLINE WRITERS


Page 11-12 


  ********TUSHEN LABARI********


________________________Alhaji Ibrahim ya kasance uba ga Alhaji Harun da Alhaji Muhammad, Alhaji Harun ne babba sai Alhaji Muhammad,su kadai Allah ya basu,Matar shi daya sunan ta hajiya Khadija,suna zaune a garin kastina Amma yan asalin gombe ne,aiki ne ya kawo su kastina, suna da rufin asirin su masha Allah,Alhaji Harun da Alhaji Muhammad sun yi karatu tun daga primary har zuwa secondary,Alhaji Harun nada shekara ashirin da biyu(22) ya gama while Alhaji Muhammad nada shekara (21),sakanin su shekara daya ne,bayan sun kammala seconday school din su da shekara daya Allah yayiwa iyayen su rasuwa a hanyyan su na dawowa daga Gombe a sakamakon hatsarin motar da suka yi,bayan rasuwar iyayen su da shekara daya aka raba musu gado,akwai fahimta da jituwa sossai a tsakanin su,bayan an raba musu gado suka fara business,suna samu sossai Dan Allah yasa musu Albarka,suna sana'an sai da atanfa,shaddah da duk wani nau'in kayan sawa na Mata,suna da babban shago guda uku,bayan shekara daya Alhaji Harun ya kawo shawaran su koma makaranta,Alhaji Muhammad ko yayi na'am da shawaran yayan shi suka koma,Alhaji Harun ya samu Admission a fudma a nan kastina university while Alhaji Muhammad ya samu a kasu,Alhaji Harun ne ya cigaba da kula da shagunan su in yana da lectures zai bar yaran shagon su kula da komi har zuwa lokacin da zai dawo,inko babu yana shago,Alhaji Muhammad kuwa sai anyi hutu ko sun dan samu break yake komawa gida su cigaba da kula da kasuwancin su, bayan samun Admission din su da shekara uku wato suna three hundred level "300" Alhaji Harun ya hadu da wata budurwa wacce tazo shagon shi,yarinyar na da hankali, da natsuwan,gidan su yarinyar ya je ya naimi izini gun baban ta,ya ko ci sa'a ba'a sayar mata da kowa,nan baban ya ba shi izinin zuwa wurin ta,a hankali soyayya mai karfi ya kullu a tsakanin su. 


Alhaji Muhammad kuma ya hadu da tashi budurwar a makaranta,department din su ba daya ba,daga dan gaisawa na mutunci,soyayya ya kullu tsakanin su amman basu sanar da juna ba,dan yarinyar akwai natsuwa ga tarbiya,ana cikin haka ya bayyana mata da soyayyar shi a gare ta,i kuwa ta ji dadi sossai dan dama ta kwadaita wa kanta,dan yana da natsuwa ga Addini,i kuwa ta amince ba bata lokaci suka fara soyayya mai tsabta dan sai da ya naimi izini a gidan su kuma an bashi,amman ance sai ta kammala karatu za'ayi mata aure,nan ya amince dan dama ya fisan haka.


Bayan sun kammala karatun su da shekara biyu Alhaji Harun yayi aure, bayan auren shi da wata shida Alhaji Muhammad yayi aure,an yi barin kudi a bikin kaman ba'asan ciwan su ba,duk sunyi ginin gidan su a nan kastina,kowa da gidan shi,bayan shekara daya da auren Alhaji Harun matar shi ta haihu namiji,anci an sha anyi rabo masha Allah,yaro yaci sunnan baban su Ibrahim Ana kiran shi da Abba,sai dai muce Allah ya raya mana Ibrahim"Abba",bayan shekara goma kuma ta haifi twins duka mata zo kuga Murna gun family,yara suka ci suna Raihan"Hassana" da Ramlat"Hussaina",bayan shekara uku ta haifi namiji yaci a ka rada mishi suna Muhammad Auwal,shekaran Ibrahim "Abba" 28 twins nada 18 auta nada 15,Abba ya gama university har ya fara aiki a company baban shi,da yake sun bude company sarrafa atanfa da nauyikan kayan sawa na mata,an ba shi matsayin MD,twins na university 200 level auta kuma na Sss3.


Alhaji Muhammad basu samu haihuwa da wuri ba sai bayan shekara tara Mama ta samu ciki,zo kuga murna gun family sossai Daddy ke tattalin Mama kaman kwai,mosi kadan zai ce mai kike so,meke damun ki,wata tara chif Mama ta santalo yar baby ta kyaukyawa,ranar suna baby taci sunnan Maman Daddy khadija ana kiran ta da Lailah,anyi rabo a sunnan sossai mai jego da baby sun samu kyauta sossai,Daddy akwati uku yayima baby,Maman baby ko set yayi mata Alhaji Harun Wanda ake Kira da baba set yayima baby Maman baby ta samu akwati biyu banda Wanda suka samu wurin abokan Arziki,bayan suna suka cigaba da kula da babyn su, bayan shekara biyar mama ta kara samun ciki Daddy yayi murna sossai har sadaka yayi nagode ma Allah daya kara bashi haihuwa har ya cire rai da kara samun baby,bayan wata tara ta haihu baby girl ran suna baby taci sunan Asma'ul Husna amma ana kiranta da Husna daga kanta haihuwa ya tsaya mata,Lailah na university yanzu tana karantar nursing tana level 300 inda Husna ke sss2,Lailah nada shekara 19 husna nada 14.


Alhaji muhammad Aliyu shahararen mai kudi ne wanda aka san da zaman shi a Nigeria gaba daya,yana da mata daya da yara hudu,mata biyu maza biyu,Aisha,Izzatu,Zaid sai auta Sa'ad, sunan mahaifiyar su Hajiya Fatima Muhammad kabir,tana da shekara 70 kyaukyawan dattijuwa ce kaman balarabiya,Aisha wacce take babbar diyar su nada shekara 36,tana da yara biyar,Afra,Ashna,Fauwaz,Suhail,Jawad tana zaune a garin Abuja,tana auren wani babban dan kasuwa,izzatu nada shekara 34 tana da yara hudu Amra,Hydar,Suhan,Ammar,tana auren wani dan siyasa,tana zaune a garin kaduna,Zaid nada shekara 32 ya karanci doctor(likita)har ya gama karatun shi yanzu haka Akwai Asibitin da daddyn shi ya gina mai suna "AIZS SPECIALIST HOSPITAL"shi qaurarran likita ne ta bangaran zuciya,Zaid nada aure ya hadu da matar shi a wani course da yaje yi a makkah last three(3) years,sunnan ta Airah,Airah nada shekara 23,sun shekara uku da aure,yaran su biyu Muhammad ana kiranshi da Amin sai Hauwa'u ana kiranta da Jiddah,sai auta sa'ad ya karanci doctor bangaren mata,yanzu haka yana lecturing kuma yana zuwa asibitin su,Sa'ad hadadan guy ne son kowa kin Wanda ya rasa,dogo ne fari,yana da saje da kwantattcen gashi kai baki sidik ya sha gyra zan ban sha'awa kaman balarabe,ga sajen shi gwanin kyau,yana da dan jiki kadan his not slim nor fat,just chobby,yana da shekara 28,sa'ad miskili ne na bugawa a jarida baya magana sai ya kama, in kaga yayi magana mai dan tsayi to yana tare da family shi,Mummy kance ni kam zan ga matar da zata aure ka da irin wannan halin,"Sa'ad nada hankali ga natsuwa,haiba,respect,hakuri, sadaka, tausayi,ba zaka gane hakan ba sai ka zauna da shi,wasu na mishi kallon mai girman kai ko mai takama saboda rashin hayaniyan shi da son magana. 


********CIGABAN LABARIN**********


Mln Sa'ad na fita wani lecturer ya shiga,ba shi ya fita ba sai hudu,School mosque ta shiga tayi sallah,tana fitowa da minti biyar driver yazo. 


Saura sati daya su fara exam,sossai Lailah ta ke karatu ba dare ba rana,washe gari Friday taje makaranta,bayan sun gama lectures suka fito ita da wata friend dinta suka je duba time table dinda aka manna a notice board,snapping suka yi suka dawo suna tafiya sun hira,daga kan da zata yi taga driver yazo,da hanzari suka karasa su kayi sallama ta tafi. 


Yau Monday inda a yau za su fara exams,daga karfe takwas na safe zuwa goma,suna da physiology,bayan sun gama aka basu break na awa daya suka dawo,11 suka shiga Anatomy daya suka gama,masallaci su ka je dan yin sallah,bayan ta idar ta dawo ta zauna karkashin bushiya tana jiran driver tsawon awa daya amman bai zo ba,kiran shi tayi tace ta gama tun da zu,kuma ta yi ta jiran shi bata gan shi ba,nan ya bata hakuri yace Mama ce ta aike shi,kuma da nisa bai tunanin zai dawo da wuri,"mai yasa baka kira ni ka gaya min ba",kiyi hakuri,Mama tace zata kira ki shiyasa ban kira ba,kila ta shafa'a ne,"toh shikenan babu komai sai ka dawo",ashe duk abinda take sir Sa'ad na zaune a mota yana kallon ta,mikewa tayi ta saka wayar a jaka ta kama hanyyar fita daga makaranta,tayar da motar yayi yabi bayan ta,yana isowa gab da ita ya tsaya ya sauke glass yace "ina driver naki yake",Gud Afternoon sir,ya amsa sannan tace "he won't be able to come",okh let me drop u,kallan shi tayi taga bai ko kalli bangaran da take ba,"ganin taki shiga kuma taki magana ne yasa shi fadin u are wasting my time get in",da sauri ta bude kofan ta shiga ba tare da wani tunani ba,fita su kayi daga makarantar,"tell me the Address,ya fada yana kallon titi",gayamai tayi nan ya juya akalar motar shi zuwa hanyan gidan su,yana isa ta sauka ta mai godiya,"kanshi kawai ya daga mata bai ko kalle ta ba ya ja motar shi yabar layin",ohhh!ni,Allah ya jarabceni da son wanda yafi karfi na,bai masan inayi ba,tura kofan get tayi ta shiga,a parlor ta sami Mama tana kallon wa'azi a sunna Tv,kwantawa tayi ta aza kanta bisa cinyar Mama tace"Mama na gaji sossai wlh,yau kan mu ya dau zafi wlh,Mama tace yan zu dai yayi sanyi dai ko,tunda anfita hall din,"dariya Lailah tayi",ya exams din,"Alhamdulillah fst luv,a dage dai banda wasa,insha Allah fst luv,ana mana Addu'a,ina yi i Mama na,yauwa first luv dina,ina son ki gatso-gatso,bari na watsa ruwa sai nazo naci abinci,toh sai kin dawo,tashi tayi ta haura sama,tubewa tayi ta daura towel ta shiga wanka,dama lokacin sallah ya kusa ta hado har da arwalla,bayan ta fito mai kawai ta shafa da kwalli sai turaren data fesa,drawer ta bude ta dau inner wears da dogon riga na atanfa ta shirya sannan tasa hijab ta tada sallah,bayan ta idar ta je ta dauki abincin ta a kitchen taci,daki ta koma ta dau book din ta ta kishingida kan gado tana karatu,daganan barci ya dauke ta,ba ita ta tashi ba sai da aka kira magriba,kiran sallan ne ya tada ta,salati tayi hadi da addu'an tashi daga barci,bayi ta shiga tayi brush da alwal,bayan ta fito tayi sallah tayi azkar na yamma,book din ta ta ja ta cigaba da karatu har lokacin isha'i yayi tayi ta hada da shafa'i da wutiri,bayan ta gama ta cigaba da karatun nan kan darduma,jin shiru Lailah bata sauko bane yasa Mama aiken Husna taje ta kira ta,sauko aci abinci ba ta sa husna taje ta kirata,bayan sun kammala cin abicin "Lailah tayi wa iyayen ta sai da safe ta shige daki ta cigaba da karatu,ba ita ta kwanta ba sai karfe biyu da rabi bayan tayi nafila................................................. 




Comment 

And

Share 


Kuci gaba da bin alkalamin Gimbiya AyshuπŸ’žπŸ’žπŸ’ž



By Gimbiya AyshuπŸ’žπŸ’žπŸ’ž.