45
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
'''DIDECATED TO'''
*YAYA HAYAT*
~(TEAM HANASH)~
4⃣5⃣
Tunawa da yayi jikinshi babu kaya yasa shi mayar da ita saman bed ya kwantar,
a haka ya fita ya shiga bedroom d'inshi duk ilahirin jikinshi na kerrrrma,
Khulud dake lab'e tana ganin ya fito daga d'akin tayi saurin shiga,
had'i da dannawa k'ofar key, gudun kar ya shigo kai tsaye,
a matuk'ar kid'ime cikin tsantsar tashin hankali,
ta hau saman bed d'in had'i da girgiza ta tana kiran sunanta cikin matsanancin kuka,
Sanah! Sanah!! Sanah.....!,
ko matsawa batayi ba ganin haka yasata mik'ewa da sauri ta nufi fridge d'in dake cikin d'akin,
jikinta na rawa ta bud'e ta d'auko ruwa ta shek'a mata,
ajiyar zuciya ta saki had'i sakin gigitaccen,
a kid'ime Khulud ta rungume ta batare data damu da babu kaya a jikinta ba,
jin ana knocking yasa Khulud saurin raba jikinta dana Sanah,
cikin sauri ta kama Sanah ta saka cikin bathroom had'i da rufe k'ofar,
gashin kanta ta yamutsa kana ta bud'e mishi k'ofar,
jikinshi na rawa yace " muje hospital,
a'a ba sai mun je ba tace ,tana komawa saman bed d'in ta kwanta,
jinin dake zube a k'asa yabi da kallo,
wanda Sanah ta zubar had'i da jan k'afarta lokacin da zata shiga bathroom,
tafin k'afar Khulud ya kalla yaga babu komai,
then jikin dake k'asa ya nuna shatin k'afar mutum,
a hankali ya nufi bathroom gabanshi na fad'uwa,
a hankali ya fara jiyo shashshekar kukan Sanah ji yayi gabanshi ya doka da mugun k'arfi,
Khulud dake kwance tayi wata irin muguwar zabura ganin ya nufi hanyar bathroom,
da sauri ta tari gabanshi had'i da cewa " ina zaka...!?
Ido ya kafe ta dashi na tsayin lokaci kafin yace " waye cikin bathroom....!?
" Kamar ya waye cikin bathroom, ban gane tambayar ka ba....!?
"Eh nace waye cikin bathroom yake kuka ina jiyo shashshekar.....!?
Sanah dake cikin bathroom jin abinda yace ya sata saurin sanya hannunta ta rufe bakinta,
cikin mamaki Khulud tace " kuka kuma...!?
" Kuka wanne iri...!?
"Oho yace yana k'ara d'aukar step zuwa bathroom d'in,
while gabanshi na fad'uwa,
tarar gabanshi ta k'ara yi da sauri had'i da cewa " wai me zakayi cikin bathroom my hubby....!?
Ta fad'a cikin kissa tana shafa k'irjinshi,
hannunta ya ture had'i da cewa " bud'e min...!,
sai da gabanta yayi mahaukaciya fad'uwa kafin tace " me...!?
"Bathroom yace batare daya kalle ta,
ya karkata hankalinshi gaba d'aya ga bathroom d'in,
yak'e tayi had'i da cewa " ban bud'ewa ta fad'a tana juyawa had'i da rik'e hannunshi,
hannunshi ya cire daga cikin nata yace " Khulud...!, ya fad'a idanshi kanta,
in banda fad'uwa da dukan uku-uku babu abinda gaban Khulud keyi,
harta kasa controlling kanta tsoron ya fito k'arara ya bayyana a fuskarta,
" wai me zakayi ciki....!?
Ta fad'a while gabanta na cigaba da fad'uwa,
bai kuma yi mata magana ba ya taka a hankali da kanshi ya bud'e k'ofar,
da k'arfi Khulud ta tsunre idanta had'i da cije lips ta dunk'ule hannunta,
lab'ewa Sanah tayi a bayan k'ofa dan haka bai ganta ba,
lallek'awa yayi had'i da cewa " Allah ji nayi kamar akwai mutum ciki fa...!
ya fad'a yana cigaba da lek'awa jin abinda yace yasa Khulud saurin bud'e idanta had'i da sauke nannauyan ajiyar zuciya,
ta nufe shi tana cewa " da wa kake tsammanin gani...!?
Ta fad'a tana murmushi,
" no..! ban tunanin komai kawai dai naji kamar matsi da shashshekar kuka ne,
" may be kunnenka ne kawai ko kuma motsin ruwa,
" zai iya yuwa hakan ne..!
ya fad'a yana rufe k'ofar bathroom d'in,
" kana zargin wani abu ne...!?
Ta tambaye shi kai tsaye,
" a'a yace yana k'ara bin jinin dake zube k'asa da saman bed da kallo,
yace " ni fa mamaki nake yi kai na ya kulle wallahi sosai,
" akan me...!?
" Wai wannan jinin daga ina yake kuma na miye...!?
" Ni dai a iya sani na mace budurci d'aya ne tak da ita,
amma wannan abun yayi kama da kamar nayi disvirgin mace,
" cikin tashin hankali tace " kamar yaya fa dama ana disvirgin mace sau biyu ne...!?
" O'o to nima abinda nake san na tabbatar kenan,
abinda ya faru yau kamar na cirewa cikekkiyar budurwa budurcinta ne,
kalli jinin nan fa, sannan dakyar na shiga,
kuma da nazo shiga sai da akayi gigitaccen ihuuuu Khulud,
then...! penis d'ina duk ta kurkurje naji ciwo wajen shiga fa,
impossible ya fad'a yana shafa kanshi idanshi kan jinin,
cikin k'arfin hali tace " ayya na manta dama ban fad'a maka Doctor William na America,
wanda yayi min aikin dashen mahaifa yace dama dole sai hakan ta faru,
saboda anyi min dashen mahaifa kuma bayan an gama sai da aka d'inke ni sosai,
kuma yace dole first sex sai jinin ya zuba...!,
saboda shine karo na farko ga sabuwar mahaifar, amma yace may be jinin yana iya k'ara zuba ko kuma bai k'ara zuba ya dan ganta,
" kanshi ya shafa yana murmushi yace " OMG....!, wallahi na manta da anyi aikin nan hakan tana iya faruwa kam,
amma gaskiya naji matuk'ar dad'in dashen mahaifar nan,
" da gaske...!?
Ta fad'a tana murmushi,
"yes..!, yace yana shafa fuskarta, had'i da cewa,
"tabbas na karb'i budurcin mace yau,
nayi disvirgin mace d'aya sau biyu kenan a rayuwa ta,
nayi abinda babu wani d'a namiji da ya tab'a yi
murmushi yayi batare da tace komai ba,
bari nayi sallah nayi wanka gari ya waye sosai,
idan na dawo daga office mayi maganar ya fad'a yana k'ok'arin shiga bathroom d'in dake d'akin,
da sauri tace " please ka tafi naka nima wankan zanyi kuma ina san yin toilet,
" hummmm shiyasa naji....! ya fad'a yana toshe hancinshi,
yayi waje yana dariya, Sanah dake cikin bathroom tana jin duk maganar da sukayi,
ta sauke ajiyar zuciya jin ya fita,
yana fita ta sakawa k'ofar key,
ta fad'awa bathroom d'in da sauri,
jikinta na rawa ta had'awa Sanah ruwan zafi mai zafi sosai,
ta kalle ta cike da tausayawa tace " shiga my Sanah...!,
jajayen idanta ta d'aga ta kalleta,
" I'm sorry sorry my Sanah ta fad'a cikin kuka,
batayi mata magana ba ta shiga cikin bath tub d'in,
har lokacin jinin bai daina zuba ba,
tana shiga ruwan yayi jajir ya koma tamkar jinin,
sau uku Khulud tana canja mata ruwa amma still b'aci yake,
a d'an tsorace tace " My Sanah bari nazo mu tafi hospital jinin bai daina zuba ba har yanzu,
batayi mata magana ba, Khulud ta fita da sauri ta sallami Hanash da gaggawa har ya so ya d'an fahimci wani abu ta wagarar dashi,
yana fita ta dawo ta isketa,
ta sunkuya had'i da dafa mirror dan ko zama ta kasa,
kasancewar ta saka kaya yasa Khulud bud'e wardrobe d'inta,
ta d'auko hijab ta sanya mata,
gami da kamata suka fita, dakyar Sanah ke takawa tana cije lips had'i runtse ido,
driver yana ganinsu yayi saurin tasowa ya shiga motar,
d'an d'osa mazaunanta tayi ta zauna cikin motar a karkace dan bata iya zama sosai,
a k'ofar standard hospital sukayi,
Khulud ta fito da sauri ta shiga ta taho da nurses had'i da gadon tura marasa lafiya,
a gaggauce Doctor ya dubata
" babu abinda yake damunta kawai ta jiga ta ne,
jinin kuma dayake zuba saboda an shige ta da k'arfi ne,
sosai tausayin Sanah ya k'ara ka mata,
cikin kuka tace " I'm so sorry my Sanah,
emergency room aka shiga da ita nurse's suka gyara ta,
basu fi 20 minutes ba suka fito aka kaita d'akin da aka kwantar da ita,
Khulud zaune saman sofa tana jiranta ta farka,
wayar ta soma ringing tana dubawa taga sunanshi,
" ya naji muryarki kamar kinyi kuka...!?
Batare data sani ba, cikin sub'ul da baka tace " my Sanah ce bata da lafiya....!,
sai bayan ta fad'a ta tuna,
sai da yayi d'an jimmmm! kana yace " meke damunta...!?
Cikin rawar murya tace " zazzab'i da ciwo kai,
yanzu haka ma muna standard hospital,
ta fad'a dan babu yadda zatayi tunda ta riga tayi sub'ul da baka tun farko,
" Allah ya sauwak'e..!,
" dan Allah kazo ka duba ta please,
dan girman Allah kar kace a'a kaji,
" kina can ne..!?
"Eh..!,
" Ok idan na tashi a office zan biyo na d'auke ki,
" to Allah ya kawo Ka lafiya,
"Amin yace had'i da kashe wayar,
bata farka ba sai wajen k'arfe 7:40pm na dare,
Khulud tana ganin ta soma motsi tayi saurin mik'ewa taje bakin gadon,
" sannu kinji my Sanah,
kanta ta kawar gefe batare data kalli Khulud d'in ba,
" I'm so sorry my Sanah please,
dan Allah kiyi......!,
jin an turo k'ofa yasata yin shiru,
wata nurse ta shigo, murmushi tayi musu kana ta soma duba Sanah,
ta cire mata k'arin ruwan da aka saka mata,
tana murmushi ta kalli Khulud tace " ke kinje kinga Doctor d'in kin kuma karb'i magungunan ki ne naga zai fita....!?
Da sauri Khulud ta k'ifta mata ido had'i da d'ora yatsa saman lips d'inta alamar tayi shiru,
sannan ta wagarar da maganar tayi kamar bata ji ba,
duk abinda suke yi akan idan Sanah,
amma sai ta share itama tayi kamar bata ji ba,
Khulud ta kalli nurse d'in tace " dan Allah idan ba damuwa ko zaki kular min da ita kafin na rink'a zan biyaki 30k kullum please,
cikin nutsuwa nurse d'in tace " badamuwa zanyi,
" nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,
"amin tace kana ta fita,
text ta turawa Hanash " _dan Allah ka taho mana da abinci da ni da my Sanah har da kai ma please_
doguwar rigar atamfa ce kawai a jikin Sanah babu ko d'an kwali,
amsa Hanash ya turowa Khulud " _ok to, a wanne b'angare kuke then room no_
bata b'ata lokaci ba ta tura mishi amsa,
a hankali Khulud ta taimaka mata ta tashi zaune,
" dan Allah kiyi hak'uri my Sanah...!,
" wai wani abu kika ji nace miki ne...!?
Sanah ta fad'a a fusace,
" a'a baki ce man komai ba amma please kiyi hak'uri,
kukan bak'in ciki Sanah ta saka had'i da cewa " amma ke fa kika ce min babu zafi kuma a hankali zai bini amma gashi nan har da zuwa hospital.....!,
dai-dai lokacin da Hanash yake shigowa d'akin,
bakinshi d'auke da sallama Khulud ce kawai ta amsa mishi sallamar,
amma Oga Sanah kawar da kanta tayi gefe,
cikin nutsuwa ya taka zuwa bakin gadon da take kwance ya d'an kalleta had'i da kawar da kanshi yace " sannu ya jikin......!?
Sai da ta d'an d'auki lokaci kafin tace " Alhamdulillah,
daga shi har ita babu wanda ya kuma yiwa wani magana,
a hankali ya juya yana k'ok'arin fita Khulud tayi saurin cewa " please ka zauna ka jira na na bata abinci karka je mota kayi ta zaman jira na,
bayyi nata magana ba ya koma ya zauna akan sofa had'i da zaro wayarshi cikin aljihu ya shiga latsawa,
" please my Sanah ki tashi ki ci abinci ko kad'an ne,
" ban cin tace batare data kalle ta ba,
" please mana dan Allah kinga gashashshan kifi ne da chips,
cikin masifa tace " wai ce miki akayi yunwa nake ji ko me...!?
Cike da mamaki ya d'aga kai ya kalle ta,
danya tabbatar yau Sanah keyiwa Khulud haka,
yana d'ago kanshi ta watsa miji harara,
shima harararta yayi had'i da zare mata ido,
itama ta zare mishi idon kamar yadda yayi mata,
duk abinda sukayi Khulud na kallansu,
tayi dariya tace " ikon Allah yau kuma fad'an kurame aka koma....!?
Itama Khulud d'in hararta yayi batare dayace mata komai ba,
Khulud ta kuma yin dariya tace " wallahi fad'anku da dramarku na birge ni dan Allah ku cigaba karku dai na,
ina san nayi ta gani ina dariya,
k'ok'arin mik'ewa yayi tayi saurin maida shi zaunen had'i da cewa " I'm sorry ban k'ara yin magana,
bayyi magana ba ya koma ya zauna,
" please my Sanah ki ci ko kad'an ne,
" idan bata ci ki kyale ta mana cikin ta ne, ina ruwanki ita daba yarinyar goye ba,
cikin tsiwa tace " ai dama bance cikinka bane, kuma ban ce ka bani ba,
My Khulud matso ki bani a baki kinji,
d'an black stomach kuma sai a mutu,
dariya sosai Khulud tayi kana ta shiga bata abincin a baki,
ido ya k'ura mata yana kallan yadda take taunar abincin da biyu,
murmushi kawai yayi had'i da girgiza kanshi,
yace " hmmm mai hali dai baya fasa halinshi,
" da ina ka tab'a jin mai hali ya fasa halin shi.....!?
"Ai hali na yana nan daram sai ma abinda ya k'aru ehee!,
" Allah ya shiryi d'an iska yace idanshi kan wayarshi,
" haka kuma Allah ya shirya masu sa ido, sa idanawa ana ruwa suna irgawa,
" Khulud kin tsaida ni ne dama tayi min rashin kunya...!?
"A'a ni ina ruwa na kunfi kusa nima 'yar kallo ce,
" idan mutum yaja mai zai hana ayi mishi,
" ke...! ki kama kanki yace yana kallanta,
da sauri ta rik'e kanta had'i da cewa " na kama! kamar haka...!?
Dariya Khulud ta sanya sosai while tana bata abincin,
idanshi ya mayar kan wayar shi batare da yayi mata magana ba,
ya cigaba da latsa wayarshi,
sai da Khulud ta bata abincin taci ta k'oshi sosai kana tayi mata sallama suka tafi,
nurse zaune tana jiran su fito ta,
tana ganin sun fito ta mik'e ta nufe ta,
Khulud ta tsaya shi kuma yayi gaba,
" kinji dai abinda nace miki ko..!?
"Eh..! nurse d'in tace, ki fa tabbatar kinyi min yadda nake saki,
ki fad'a mata ina da hawan jini da ciwon zuciya , then abu kad'an ana iya rasa ni,
danna tabbatar taga abinda muka yi d'azu na kuma tabbatar sai ta tambaye ki,
murmushi nurse d'in tayi had'i da cewa " karki damu in sha Allah zanyi yadda kika ce,
hannu ta sanya cikin hand bag ta zaro 1k bandir d'aya na 100k ta bata,
ta masa had'i da yin godiya, kana ta shiga d'akin wajen Sanah,
bakinta d'auke da sallama,
murmushi tayi mata had'i da komawa ta kwanta,
kallanta nurse d'in tayi had'i cewa " baki buk'atar komai...!?
"Eh..! kiyi zamanki kawai,
saman sofa nurse d'in ta zauna,
har Sanah ta rufe idanta tayi saurin bud'ewa had'i da mik'ewa zaune,
ta kalli nurse d'in tace " dan Allah tambayarki nake san yi idan ba damuwa,
kuma dan girman Allah ki fad'a min gaskiya,
wayarta dake hannunta ta kifa had'i da tattara gaba d'aya hankali da nutsuwarta,
gareta tana murmushi tace " uhummm ina jinki ba damuwa,
" kiyi min alk'awarin zaki fad'a min iyakar gaskiyarki,
" in sha Allah nurse d'in tace,
" dan Allah meke damun Khulud danaji kince tana zuwa ganin Doctor harta karb'i magani....!?
D'an shiru nurse d'in tayi kana tace " kiyi hak'uri ban iya fad'a miki dan ta yi min kashedi sosai ta kuma rok'e ni akan karna sake na fad'a miki,
ji tayi gabanta yayi muguwar fad'uwa,
cikin marairaice fuska tace " dan Allah ki fad'a min,
kinyi min alk'awari fa...!,
sosai Sanah ta shiga rok'on nurse d'in had'i dayi mata magiya kan ta taimaka ta fad'i mata,
d'an shiru nurse d'in tayi kana ta sauke ajiyar zuciya,
tace " tou nima kiyi min alk'awari baki tab'a yi mata maganar,
cikin zak'uwa Sanah tace " in sha Allah nayi miki,
" tou dama CIWON ZUCIYA da HAWAN JINI ke damunta kuma sunyi mata mugun kamu,
sosai dan sunyi masifar cin jikinta abu kad'an yana iya sawa a rasata,
tace karna fad'a miki ne dan bata so ki saka kanki cikin damuwa,
dan ta san yadda kike mugun santa kina iya kamuwa da irin ciwon kema ita kuma ta gwammaci duka cututtukan duniya,
su fad'a mata akan ke kiyi koda ciwon kai ne,
ta gwammaci tayi mutuwa sau dubu idan anayi data ganki cikin damuwa,
kuma a 'yan kwanakin nan ciwon yana yawon matsa mata sosai,
danna fuskanci tana cikin damuwa,
tunda Nurse d'in ta soma magana Sanah taji wani mugun shock a gaba d'aya sassan jikinta,
duk ilahirin jikinta ya d'auki kerrrrma da tsuma,
dan Allah idan har kina san kwanciyar hanklinta karki nuna mata kin san da wannan maganar,
sannan ki rink'a k'ok'arin kwantar mata da hankali,
ko k'ala Sanah batace ba sai wani abu mai tuk'uk'i da take ji a zuciyarta,
kwata-kwata ta nemi kuka da hawayenta ta rasa,
take taji tsananin so da k'aunar Khulud d'inta ta dawo mata sabuwa fil fiye da da,
cikin mutuwar jiki ta koma bed ta kwanta batare data k'ara furta ko da kalma d'aya ba.
Su Khulud suna shiga cikin mota tace " kayi hak'uri kaji nasan yau nayi laifi ko...!?
Kallanta yayi yana murmushi yace " inji wa yace kinyi laifi yau...!?
" Ai koda kina yin laifi kullum yau baki yin laifi,
yau kam its your day kiyi komai baki yin laifin,
cikin mamaki ta kalleshi tace " meyasa...!?
Yace " ai yau kin biya ni...!
" da akayi me..!?
Ta kuma tambayar shi cikin mamaki,
kanshi tsaye yace " wallahi tunda nake a rayuwata ban tab'a samun gamsuwa da nutsuwa irin yau ba,
yau kam kinyi abinda baki tab'a yi ba cikin 3yrs I proud of you today dear,
ya fad'a yana shafo fuskarta,
shiru tayi had'i da zuba mishi idanuwanta da suka k'ank'ance saboda tsabar tashin hankali,
" I love you more today yau kam yaci ace ma nayi kyauta mai girma,
ya kuma fad'a cikin walwala yana tuk'inshi hankali kwance,
" yana ji kinyi shiru ya fad'a yana kallanta....!?
Murmushin yak'e tayi had'i da cewa " nima yau nayi enjoyed sosai da sosai,
" kice yanzu ma idan mun koma zamu k'ara raya sunnah..!?
Ya fad'a had'i da kashe mata ido d'aya,
cikin k'arfin hali tace " uhummmm jiya ka wahalar dani ka jigata ni sosai,
ai yau ranar hutu ce,
" gaskiya ban iya hak'ura dake muna komawa gida zan k'ara jona sirdi,
tou naji amma ka bari nayi bacci na tashi dan bacci nake ji sosai,
zayyi magana tayi saurin cewa " idan har kana san ka kuma jin yadda kaji yau ka bari nayi bacci na tashi,
murmushi yayi yace " ni ko ke san na kuma jin yadda naji,
ai komai kika ce haka za'ayi,
murmushi tayi batare data kuma cewa komai ba,
suna isa gida tayi wanka had'i da kwanciya dan masifaffan bacci take ji,
saboda kwata-kwata jiya bata samu bacci sosai ba, saboda her Sanah.
Idan hankalin Sir Moli yayi million to ya tashi,
ya rasa meyasa kwata-kwata bai samun number ta idan zai kira sau dubu switch up ko not reachable take ce mishi,
haka ma idan ya tura mata text bai shiga,
ya rasa in da zai saka ranshi da rayuwarshi yaji dad'i,
gashi a 'yan kwanakin nan idan yaje gidansu mai gadin bai barinshi ya shiga,
ya rasa dalili, ya shiga matsananciyar damuwa kullum addu'arshi d'aya Allah yasa tana lafiya,
dan ranshi yana bashi akwai wani abu dan muddin babu wani abu,
yasan bata iya tsayin lokacin nan batare datayi waya dashi ba,
gashi ko makaranta ta daina zuwa,
gaba d'aya ya tashi hankalinshi sosai ya shiga damuwa sosai,
kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin wani yanayi...!
kwata-kwata Sir Moli ya rasa inda zai saka ranshi da rayuwarshi yaji dad'i,
ko abincin bai iya ci komai bayyi mishi dad'i...!
A week letter
Kwanan Sanah uku aka sallamota daga hospital,
suka dawo gida, tun bayan dawowar su gida Khulud ke ta faman rok'onta kan ta komawa Hanash amma tak'i yarda,
yauma suna zaune a parlor Khulud sai naci take yi mata,
" dan girman Allah my Sanah kije yau,
Allah bazai kai wancan zafi ba,
wancan ma danna farko ne shiyasa kike ji zafi haka amma daga na farko ba'a sake jin zafi sai dad'i,
please my Sanah, ta fad'a cikin marairaice fuska,
ido Sanah ta zuba mata tana kallanta harta kai k'arshen maganarta,
kana tayi murmushi had'i da cewa " hmmm my Ulud,
kin manta wancan ma haka kika ce ne...!?
" Eh...! haka nace ban manta ba,
amma shi dan na farko ne shiyasa kika ji zafi amma wannan baki jin zafin,
" yanzu so kike na yarda da maganar ki na sake komawa wannan bak'ar azaba da wahalar ko me...!?
" A'a bawai haka nake nufi ba,
kinga mijinki ne kamata yayi mu raba kwana saboda fitar da hakk'in juna,
" idan na fahimce ki haka kike san ayi mu raba kwana ko...!?
"Eh..! dan Allah,
shiru Sanah tayi tana tunanin abinda nurse ta fad'a mata kan Khulud,
dan haka ta sauke ajiyar zuciya,
had'i da cewa " tou raba,
ta fad'a dole badan taso ba,
murmushi Khulud tayi kana tace " yes..! dear ina ganin kwana bibbiyu is ok ko..!?
" Hakan yayi miki...!?
"Eh...! yayi,
" tau shikenan yanzu ke sai ki fara bayan kwana biyun sai na amshi girkin ta fad'a tana murmushi,
"a'a dan Allah ki fara, tunda kinga ko amarci dama baki ci ba,
ta fad'a tana kanne dariya,
harararta Sanah tayi had'i da cewa " in baki so shikenan ki barshi yayi ta kwana haka,
duk ranar da kika shirya sai a raba,
sosai Khulud tayi dariya kana tace " tom naji na yarda,
daga yau zan fara jibi ke kuma sai ki amshi girkin,
baki ta tab'e had'i da cewa " oho ke dai kika sani,
" tou amma yanzu idan kwananki ya zagayo ya zakiyi dash........!
cak ta tsayar da maganarta ganin Hanash tsaye a gabansu..........!
Sir Moli tsaye yana ta faman safa da marwa cikin d'akinshi abin duniya ya taru yayi mishi yawa,
gaba d'aya duniyar tayi mishi bak'i k'irin,
wayarshi naga ya d'aga yana k'ara dialing number ta a karo na 50 a yau amma still not reachable,
tsoki ya ja had'i da jefa wayar saman bed,
zazzafar iska ya fuszar daga cikin bakinshi had'i da cusa hannunshi cikin sumar kanshi,
ya d'auki lokaci a haka kana yace " aiko rabuwa Sanah zatayi da nayi bai kamata ta rabu dani ta wannan hanyar ba,
idan bata aure na bai kamata tayi watangariri da rayuwata ba,
kamata yayi ta fito ta fad'a man gaskiya bawai tayi wasa da hankali na dana iyaye na,
a fusace ya zari key d'in motarshi bai ko tsaya d'aukar wayarshi ba,
yayi waje, cikin sauri ya fita harabar gida,
ya shiga cikin motarshi had'i da figar motar tamkar zai tashi sama,
zuciyarshi na tafasa ji yake tamkar ana zare mishi ranshi ne daga cikin gangar jikinshi.
A bakin get d'in gidan su yayi parking,
had'i da tsuke fuskarshi ya d'auke gaba d'aya annurin fuskarshi,
ya fito daga cikin motar, batare daya rufe motar ba,
ya k'arasa bakin get d'in,
knocking yayi, mai gadi ya lek'o ta k'ofa,
shi kanshi mai gadin sai da gabanshi yayi muguwar fad'uwa saboda ganin yanayin Sir Moli,
cikin rawar murya yace " Malam lafiya....!?
" Matsa min na wuce....!
kallanshi mai gadin yayi while gabanshi na fad'uwa yace " nace ka bani hanya na wuce ya fad'a a tsawace,
Abbu dake k'ok'arin shiga ya jiyo kamar hayani a waje,
fasa shiga motar yayi had'i da takawa ya nufi get d'in yana d'an lek'awa,
ganin Abbu yasa Sir Moli sunkuyar da kanshi k'asa dan kar Abbu yaga yanayin fuskarshi,
da halin dayake ciki,
fuska a sake Abbu ya mik'awa Sir Moli hannu,
cikin nutsuwa shima ya mik'e mishi hannun suka gaisa,
d'an shiru Sir Moli yayi had'i da shafa kanshi,
kallanshi Abbu yayi yace " mu shiga ciki naka kamar magana kake sanyi,
kanshi ya k'ara shafawa cikin alamun jin kunya yace " dama wajen Sanah nazo..!,
ya fad'a gabanshi na fad'uwa da mugun k'arfi gudun kar a a fad'a mishi wani mugun abunne ya same ta,
ko a fad'a mishi bak'in labari,
cikin mamaki Abbu yace " kai ba lecturer su bane...!?
Cikin ladabi yace " eh...! ina koyar dasu,
Abbu yace " amma baka san ta tafi service ba ......!?
Cikin rashin fahimta Sir Moli yace " service...!?
"Eh...! ta tafi bautar k'asa Damaturu tun last month...........!
MOMYN ZARAH