1
by @halimahz
*RAGAMAR DAMISA*
```FreeBook.```
*©️Halimahz*
*SADAUKARWA GA:-*
Muhammad Kareem(MK)
_for your business advert DM ***._
*_Bismillahir Rahmanir Rahim._*
_Hellooo Dearies i'm back again, ku zo mu yi tafiyar tare kamar yanda muka saba, yanda idan an tashi bada labari kune a sahun farko, a wannan karon tafiyar ta daban ce...MssAnyway loves you much, ina miƙa saƙon gaisuwata gare ku a kowacce rana, Alkhairan ubangiji su isar muku a duk inda kuke, ina muku son so fisabilillah._
*(1)*
*Birinin Gwari, Kaduna State...*
_ƙililin,ƙililin....._ kamar haka agogon dake akan durowar gefen gadona ya buga ƙara, na juyo da kaina ina ɗora idanuwana akansa, ganin ƙarfe goma sha ɗaya daidai na rana yasa naja guntun tsaki me cike da ƙorafi na takaici.
ɗauke idona nayi daga kan agogon na mayar kan madubin da ke gabana, manyan dara-daran idanuwana a kansa kamar zasu zazzago, na yatsine fuska tare da saka hannu na finciko hannun durowar jikin mudubi, a yanda nake komai cikin kokawa kai kace ko kayan kwalliyar da ke zube a gabana ne suka yi min wani mugun laifin da ba zan iya yafe musu ba.
ban kammala kwalliyar fuskata ba sai dana ɗauki a ƙalla mintuna ashirin da biyar, kwalliyar da zaka rantse wata shegiyar makeup nake zubawa ta azo a gani a watsa a IG, nan kuwa zallar hauka ne nake zanawa fuskata da baƙin kwalli da janbaki jaa, kana dai yi min kallo ɗaya zuciyarka zata ɗarsa maka cewa ni mahaukaciya ce tuburan ko kuma ƴar wiwi, musamman daga yanayin yacca nake zarewa kaina da kaina idanuwa.
a fusace na miƙa daga kan stool na isa gaban ƙatuwar wadrobe ɗina na buɗe, ina kallon kayan ciki na rumtse ido na shiga faman hura hanci ina kumbura kamar zan fashe, hannu na saka nayo watsi da kayan ciki duka zuwa ƙasan tiles, ban bar ko tsinke aciki ba kafin nan na bi uban kayan da ke yashe a ƙasa da kallon wulaƙanci, kafin nan nasa ƙafa ina daɗa barbaza su, a haka har na zaɓo kayan da zan saka da ƙafata nayi cilli da su a saman gado.
banɗaki na shiga nayi fitsari na fito, ina fitowa na ɗauki jan wando na saka da farar riga armless tare da ɗora top baƙa akai, na ɗau jar hula chantly na saka tare da ɗora p-cap fara akai.
gaban hanger na isa na cizgo jakata irin ta ma'aska wacca ake cewa zabira, na rataya a kafaɗata sannan na tsuguna na saka sneekers ɗina baƙi, sai dana gama shirina tsaf tukunna na cilla cingum orbit a bakina me ƙamshin mint, kafin ƙiftawa da bismillah kuma na bar cikin bedroom ɗin na fito parlo.
a lokacin dana iso parlo tsaye nayi tare da kama ƙugu-ƙugu, ba komai na tsaya ina kallo ba face ƴan daban da sun kai su wajen goma, sun yi rukuni rukuni suna buga caca, kowannensu da taba a bakinsa yana zuƙa, sai faman musu suke yi kamar zasu kashe kansu, daga yanayin yanda muryoyin su ke fita zaka shaida tabbacin a buge suke.
dogon tsaki naja wanda duk yaja hankalin su, kafin nasa ƙafa nayi fatali da ƙatuwar kwalbar giyar da ke gabana, take kuwa kwalbar ta fashe, duk suka ɗago suka yi min kallo ɗaya suka watsar, nasa ƙafa na taka kwalbar na murza babu ko tsoron zata iya huda ƙasan takalmina taji min ciwo.
yanda ban tanka su ba haka cikin su babu wanda ya tanka ni har na bar wajen ina faman jera uban tsaki kamar tsohuwar tsaka.
tsakar gida na fito, takaicina ya ƙaru a sa'ilin da nayi tozali da karikecen kwanuka a bakin famfo, na gyaɗa kai tare da yin ƙwafa kafin na zagaya ta baya inda kitchen yake, ruwan shayi na zuba a kofi, na juye rabin gwangwanin nescafe a ciki tare da gutsirar burodi sannan na fito na komo parlo.
zaman dirshen nayi a tsakiyar center carpet, na ƙyasta yatsun hannuna, kuma kafin na kai ga sauke ƙwayar idona ƙasa naji saukar kwalin sigari a jikina. ɗauka nayi na zari guda ɗaya nasa lighter na kunna na fara zuƙa, ina shan shayina me zafi da daɗi ina zuƙar sigari haka har sai da nayi maƙil abina da ƙaton bread ɗin da nake ci.
ina kammala breakfast ɗin na ɗauki danƙareriyar wayata ƙirar iphone 14promax, contact na shiga nayi searching sunan Dillaliya, sai dana kira har sau uku ba'a ɗaga ba wanda hakan ya ƙara ɓata min rai.
na jera ƙwafa tafi ƙarfin guda 30 a jere ina aikin girgiza ƙafa, ganin ɓacin ran na neman saka min ciwon kai yasa ni janyo kwalbar giya, sai dai a lokacin dana kafa baki zan sha sai na kasa kamar dai kullum, hakan yasa na dunƙule a waje ɗaya domin samun sassaucin zafin zuciya.
"dalla gafara Malami menene hakan da kake yi?, ba zaka saka ba wai?".
Ƙaura ya faɗa cike da zafin tafasar zuciya, ga cacar ta ɗauki daɗi amma Goje yana neman ɓata musu wasa, gefe ɗaya kuma a mugun tsorace yake da wasan na su, domin komai daf yake da iya faruwa in aka ci shi.
Goje da ke fuskantar Awarwasa yay wani miskilin murmushi yana juyi da yatsansa ɗaya akan teburin dake gaban su. ya cije leɓe kafin ya ɗago da rinannun idanuwansa da suka yi jawur ya kalli Ƙaura tare da kiran sunansa a hankali.
daga yanayin yanda amon muryarsa ta fito zaka tsammaci ko wani basaraken gaske ne, sai dai gani da ido zai kore hakan, amma kuma zaka iya rantsewa cewa akwai jinin sarauta da ke ratsawa a jikinsa, amma fa sam ba hakan ba ne, babu haɗi kwata-kwata haka Allah yay shi, me haƙuri ne kawai ke iya rayuwa da shi, domin idan yay magana ɗaya sai an ɗauki kusan mintuna biyar kafin ya ƙara furta komai.
"ko ranka ko kuma abinda ka saka, cikin biyu dole ka zaɓi ɗaya". cewar Goje a lokacin da idanuwansa ke hasko masa ƙyallin wuƙar da ke soke a ƙugunsa.
lokaci guda hantar cikin Ƙaura ta kaɗa, gabansa ya shiga dukan tara-tara, cikin kumfar baki ya shiga cewa,"me tunaninka ke baka?, kai ka taɓa ganin anyi caca da ni kuma anyi nasara akaina?, ƙaryar mutum wallahi, ko a mutu ko ayi rai ni ɗin dai ke da nasara".
ya faɗa yana gyara zaman hular kansa sai aikin huci yake yi yana maganganu da gadara.
Goje ya kalli hannunsa yaga duk katin ƴan wasa iri ɗaya ne, don haka ya kwantar da kansa jikin kujerar yana shafo ƙeyarsa tare da fitar sautin murmushi a saman leɓensa, dariyar gefen baki ne ke son suɓuce masa amma ba zai yita a yanzu ba sai wasa ya ƙare.
"mun ci dubu sai ceto wallahi". Awarwasa ya faɗa yana bushewa da dariya, sannan ya ƙara da cewa,"sai Oga Goje, ranka shi daɗe muje zuwa, ka riga ka gama kaɗa hantar ƴan banza don haka ɗago ka saka su kuka...Seeee Oga, a kaɗa a raya teburi namu ne".
magangaun da Awarwasa ke yi kenan yana faman layi daga kan kujerar da yake zaune wacce ke fuskantar Goje.
ɗago da kai Goje yayi yana lasar leɓe, kafin ya fara zarar katin wasan yana ajiyewa ɗaya bayan ɗaya akan teburin har sai da ya gama ajiye su a gaban Ƙaura, ta tabbata dai Goje shi ya lashe wasa.
jikin Ƙaura yay mugun sanyi, tsananin tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarsa, har bai ma san lokacin da sigarin bakinsa ta suɓuto ta faɗi ƙasa ba.
Awarwasa ya miƙe tsaye yay shewa iya shewa sannan ya shiga kirari wa uban gidansa Goje, kirari irin nasu na ƴan daba, sai da yayi iyaka yinsa tukunna ya zago ta gaban kujerar Ƙaura ya ajiye tafin hannunsa a gabansa.
ya bushe da wata iriyar dariya ta riƙaƙƙun ƴan daba tukunna ya buɗe baki cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa yace,"rai ko kuma dukiya...".
Ƙaura ya ɓata rai yana aikin zare idanu ya kasa cewa komai, sai faman rausaya da kai yake yana ƙifta idanuwa cike da tsoro kamar ba ɗan daba ba, duk da yasan dama a cikin ƴan daba Goje daban ne.
duk wannan abu da ake Goje dai bai ce komai ba, idonsa ne kawai akan Ƙaura yana binsa da cikakken kallo irin na mashaya, kana ganin irin kallon kasan lissafi yake yi acikin kansa, lissafin hukuncin da zai ɗauka akan nasarar da yay idan har Ƙaura bai ajiye masa alƙawarin da suka yi ba.
tuni jikin Ƙaura ya fara rawa ganin irin kallon da Goje ke jifansa da shi, waigawa yay ya kalli Daɓalo da yake ɗaya click ɗin, suna haɗa ido suka yi maganarsu da ba kowa ke ganewa ba, Ƙaura ya kaɗa kai sannan yay ƙasa da kansa yana kallon ƙafar Goje ta ƙasan teburin, yana lissafin yacca zai yi ya tsere cikin dabara.
duk wani takun karatu na dabarar tserewa da Ƙaura ke yi akan idon Goje, yayi lamo ne kawai domin ganin iyaka gudun ruwansa. Ƙaura na yunƙurawa zai miƙe ba zato ba tsammani yaji an sarƙe ƙafafunsa, take ya koma yay zaman dirshen akan kujerar.
"zatonka zaka iya tsere min?, shin ka manta wai da wa ka gabza wannan wasan ne?, Ƙaura buɗe idonka da kyau ka kalla Goje ne fa a gabanka, nayi nasara akanka sannan kace zaka tsere min ba tare da ka dire kuɗin wasa ba?...look karka fusata ni, don ka ɓata naka lokacin wannan ba damuwata ba ne, amma ɓata nawa lokacin ɗorawa kai laifi ne, don haka kamar yanda ka faɗa tun farko cewa ka saka naira dubu ɗari biyar, to ka direta a gabana, ko kuma ka ajiye ATM naka, idan kuma ba haka ba na zubar da kai anan na fille kanka, babu kuma wani mahaluƙi da ya isa ya hukunta ni akan hakan duk faɗin duniyar nan, idan kuma kana ganin zance ne kawai nake yi to mu zuba mu gani".
kallo ɗaya zaka yiwa Ƙaura a lokacin ya baka tausayi, domin ba shi da kwatankwacin kuɗin da ya saka, rarraba ido kawai yake yi yana jiran ko Uwar gidan nasu zata raba gardama amma shiru, babu alamar ma zata saka baki cikin lamarin na su.
"ni bani da adadin kuɗin da na faɗa, hasali ma ban san a ina zan samo su ba, dama na faɗa ne da yaƙinin ni zanyi nasara, sai kuma aka sami akasin hakan, saboda haka ka manta da wannan sabgar kawai Goje, aci gaba da sha'ani".
ya faɗa tare da miƙewa tsaye zai bar wajen, Awarwasa ya ba shi hanyar wucewa, yasa kai ya wuce yana takun ƙwambo acikin jemammen kwambas ɗinsa fari, yana shirin fita a parlon yaji an doki tebur da wani mugun ƙarfi wanda da alama ma teburin sai da ya tsage, hakan ya dakatar da shi daga tafiya ya waigo don ganin meke faruwa.
juyawar da zai yi yaga Goje tsaye yana huci jijiyoyin jikinsa sun bayyana raɗau, babu shiri yay azamar ficewa a guje caraf yaji an cafki hannunsa, kuma ba tare da wata-wata ba yaji saukar wuƙa a ƙafaɗarsa, ƙarar yankar fatar jikinsa tayi amsakuwa acikin parlon ji kake ƙetttt tamkar ana keta atamfa.
wannan fitar ƙarar yankar naman jikin Ƙaura yasa ni ƙwala uwar ƙara tare da dafe kaina ina rumtse ido gudun ganin jinin dake malala daga jikinsa.
"Wayyooooo". ihun farko da Ƙaura yayi kenan sai kuma shi ma ya fusata ya zaro wuƙa a wandonsa yana faɗin,"idan na ƙyaleka shege nake, idan ba kaima sai na keta fatar jikinka ba Allah ya tsine min".
ya faɗa yana tafiya gadan-gadan kan Goje, sai dai kamin ya kuma yin wani yunƙuri Goje ya sake yi masa babbar yanka a gefen ciki, wanda yasa shi zubewa a wajen yana kururuwa yana ba zai yarda ba sai ya feɗe Goje, duk kuwa da irin uban jini da ke fita daga jikinsa, haka naman cikinsa na bullutsowa amma tsabar taurin rai haka ya miƙe ya tafi a sukwane yayi kan Goje, nan take faɗan daba na gaske ya kaure, mabiya bayan Ƙaura da Goje kowa ya zare wuƙa aka shiga soke-soke da yanke-yanke, sai dai duk irin saran juna da suke jini na zuba a jikin kowanne su amma ko kaɗan wuƙa taƙi ɓula jikin Goje.
"Rashid!!!". na ƙwala kiran sunan da ƙarfin gaske a dalilin yankar jikina da Ƙaura yayi, a sukwane Goje yayo kaina yana rufe ni da jikinsa ganin Ƙaura na neman ƙara kawo wuƙa jikina.
"Awarwasa kar ku bar shi da rai". Goje yay maganar a saman kaina yana ƙara rufe ni da faffaɗan ƙirjinsa, kuma cikin cika umarninsa faɗa ya ƙara kacamewa, babu abinda kunnuwana ke ji sai sautin wuƙaƙe.
"Asma". yay kira sunana cikin amon sautin murya na tsananin fusata.
"ka hana su don Allah, ka san bana son wannan faɗan".
"in hana fa su kika ce?".
"ehh Rashid ka hana su bana so, wai so kuke dole sai kun kashe kan ku ne?, sau nawa zan faɗa muku duk sanda zaku yi caca kuyi a wani wajen amma ba'a gidana ba tun rigima take zamar muku".
bai ce da ni ƙala ba ya ɗaga daga jikina, na ɗago ido ina kallonsa, yayi tsaye a kaina idonsa ƙyam akan yankan da ke kafaɗata, farar rigar jikina duk ta ɓaci da jini, haka shima tasa fuskar duk ta ɓaci da jini.
hannu ya miƙo min yana daga tsaye, cikin jin zafin ciwon jikina na miƙa masa nawa hannun ya miƙar da ni tsaye, sililin mayafin da ke kafaɗata ya fizge ya ɗaure min damtsen hannuna da ke zubar da jini.
yaja ni muka fita waje, hankalina ya ƙara tashi sanda muka fita, yaran Goje sun rufe Ƙaura sai dukansa suke yi, sun yi masa jina jina, amma tsabagen taurin rai irin na Ƙaura faɗi yake wallahi ko bai illata Goje ba to sai yaje har gida ya kashe babarsa.
Goje na jana muka ƙarasa gaban su, ya bawa yaransa umarnin su matsa akan Ƙaura, suka kauce yasa ƙafa ya taka ruwan cikin Ƙaura, shi kuma sai murƙususu yake yana so ya ƙwace amma ya kasa saboda sam ƙarfin su ba ɗaya ba ne.
wucewar mintuna uku sannan Goje ya furta,"Ƙaura ni ne na yanke ka, ni naji maka ciwo, kome ya sameka ni ne ba wani ba, me yasa kasa wuƙa a jikinta?, a wanne dalili zaka ji mata ciwo?, me yasa bakinka ke ambaton mahaifiyata a wannan faɗan?".
yay ƙarashen maganar cikin zafin rai da ɗagowar murya.
"saboda kai na yanke ka jini yaƙi fita a jikinka shisa na sauke a nata saboda ai itane ta tara mu a gidan...". bai bari Ƙaura ya ƙarasa abinda zai faɗa ba ya soka masa tsinin wuƙa a maƙogoro yana murza wuƙar har sai da ta fasa maƙogoronsa ta shige cikin ƙashin, take kuwa Ƙaura ya shiga shure-shuren ƙafafu yana wata iriyar barƙala.
hankalina ya kai ƙololuwar tashi, duk yanda naso na hana Rashid abin yaci tura, sai roƙon yaransa nake yi akan su janye Ƙaura amma su ma ba wanda zai ita aiwatar da wani abun, bai ɗauke wuƙar a maƙoshinsa ba har sai da ya tabbatar da numfashin Ƙaura ya daina fita sannan ya finciki wuƙar yana ƙara buga masa ita a ƙirji duk da ya raba shi da ransa hakan bai wadatar da shi ba.
"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Rashid me yasa baka da imani?, ka kashe shi fa Rashid, Rashid ya mutu fa, na shiga ukuna, Rashin me zaka ce da Allah me zaka ce da hukuma?, me yasa ka zaɓi kayi ta rayuwar gidan kurku ne Rashi?".
furucin da nayi kenan lokacin da nake ƙwacewa daga hannunsa in duƙa a gaban gawar Ƙaura, na fashe da kuka sosai, ina cikin girgiza gawar tasa Rashid ya sunkuyo ya jawo ni na miƙe tsaye.
ina tsayawa akan ƙafafuna na ɗaga hannu a zafafe na wanke shi da zazzafan mari, ban bari ya dawo daga mamaki ba na ƙara masa wani, nasa hannayena biyu na tankaɗa shi gefe ɗaya.
ina kuka ina share hawaye na ɗauki wuƙar da ya jefar a ƙasa nayi kansa gadan gadan, gwara in kashe shi shima mu samu duk ma huta da masifaffiyar zuciyarsa da babu imani.
"ahhhhh". ihun dda Rashin yay kenan a sa'ilin dana huda ƙirjinsa da wuƙar hannuna...
________________________________
_*Aha my people what do you think about this novel?, how it all started is all you need to know right?, buh before the answer how was it?, good, fair, boring or confusing?...vote and comment if you would like me to continue, and then recommend to your friends☺...Much ƙauna my fans.*_
#MssAnyway
#Gamjiwriters
#23feb2023
#wattpad:-mssanyway
#arewabooks:-mssanyway
#share fisabilillah