FreeArewaPen original
RAGAMAR DAMISA
- 1views
- 4chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Sunana Halima.hz, ni marubuciya ce, kuma ƴar kasuwa mai siyar da nau'in sutturun sawa. Ina rubutu don in rayar da abubuwan da mutane ke ji. Ba na rubutu don nishaɗi kawai, ina rubutu don motsa tunani. Kowanne labarina yana ɗauke da murya...
Sample · 1
*RAGAMAR DAMISA* ```FreeBook.```*©️Halimahz**SADAUKARWA GA:-*Muhammad Kareem(MK)_for your business advert DM ***._*_Bismillahir Rahmanir Rahim._*_Hellooo Dearies i'm back again, ku zo mu yi tafiyar tare kamar yanda muka saba, yanda idan an tashi bada labari kune a sahun farko, a wannan karon tafiyar ta daban ce...MssAnyway loves you much, ina miƙa saƙon gaisuwata gare ku a kowacce rana, Alkhairan ubangiji su isar muku a duk inda kuke, ina muku son so fisabilillah._*(1)**Birinin Gwari, Kaduna State...*_ƙililin,ƙililin....._ kamar haka agogon dake akan durowar gefen gadona ya buga ƙara, na juyo da kaina ina ɗora idanuwana akansa, ganin ƙarfe goma sha ɗaya daidai na rana yasa naja guntun tsaki me cike da ƙorafi na takaici.ɗauke idona nayi daga kan agogon na mayar kan madubin da ke gabana, manyan dara-daran idanuwana a kansa kamar zasu zazzago, na yatsine fuska tare da saka hannu na finciko hannun durowar jikin mudubi, a yanda nake komai cikin kokawa kai kace ko kayan kwalliyar da ke zube a gabana ne suka yi min wani mugun laifin da ba zan iya yafe musu ba.ban kammala kwalliyar fuskata ba sai dana ɗauki a ƙalla mintuna ashirin da biyar, kwalliyar da zaka rantse wata shegiyar makeup nake zubawa ta azo a gani a watsa a IG, nan kuwa zallar hauka ne nake zanawa fuskata da baƙin kwalli da janbaki jaa, kana dai yi min kallo ɗaya zuciyarka zata ɗarsa maka cewa ni mahaukaciya ce tuburan ko kuma ƴar wiwi, musamman daga yanayin yacca nake zarewa kaina da kaina idanuwa.a fusace na miƙa daga kan stool na isa gaban ƙatuwar wadrobe ɗina na buɗe, ina kallon kayan ciki na rumtse ido na shiga faman hura hanci ina kumbura kamar zan fashe, hannu na saka nayo watsi da kayan ciki duka zuwa ƙasan tiles, ban bar ko tsinke aciki ba kafin nan na bi uban kayan da ke yashe a ƙasa da kallon wulaƙanci, kafin nan nasa ƙafa ina daɗa barbaza su, a haka har na zaɓo kayan da zan saka da ƙafata nayi cilli da su a saman gado.banɗaki na shiga nayi fitsari na fito, ina fitowa na ɗauki jan wando na saka da farar riga armless tare da ɗora top baƙa akai, na ɗau jar hula chantly na saka tare da ɗora p-cap fara akai.gaban hanger na isa na cizgo jakata irin ta ma'aska wacca ake cewa zabira, na rataya a kafaɗata sannan na tsuguna na saka sneekers ɗina baƙi, sai dana gama shirina tsaf tukunna na cilla cingum orbit a bakina me ƙamshin mint, kafin ƙiftawa da bismillah kuma na bar cikin bedroom ɗin na fito parlo.a lokacin dana iso parlo tsaye nayi tare da kama ƙugu-ƙugu, ba komai na tsaya ina kallo ba face ƴan daban da sun kai su wajen goma, sun yi rukuni rukuni suna buga caca, kowannensu da taba a bakinsa yana zuƙa, sai faman musu suke yi kamar zasu kashe kansu, daga yanayin yanda muryoyin su ke fita zaka shaida tabbacin a buge suke.dogon tsaki naja wanda duk yaja hankal...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.