Chapter 16
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 31-32
Dan haka ta zare ido domin tabbatar da abin da kunnenta ya jiyo mata. Sai a yanzun tagane inda tasan kamshin turaren ko tantama babu Poul ne, tambayan kanta ta shiga yi Yaya aka yi ya shigo gidan nan, batare da ta gana nemo amsan ba taga Yana haskata ta da wayar dake hannunsa tare da fadin, "Ki nutsu, nazo ne kawai mu yi magana."
Batare da ta bari ya rufe bakiba ta ce, "Ana jirana agida acikin gida ne."
"Kafin ki shiga ina son zamu yi magana, idan kin bani hadin kai yanzun nan zaki shiga gidan, idan ki kaga kin dade a gurin nan to bansamu hadin kanki bane" Wannan karon Nur Bata iya cewa komai ba in banda kallon shi da take, duk da cewa bata iya ganin fuskarsa sosai amman hancinta na jiyo mata kamshin turaren sa, cikin rawar baki tace "Ka matsa mini in wuce."
"Bazan matsaba sai munyi magana, na aiko Helen kin ki sauraronta mai yasa? Numshi Nur ta maida sannan tace "Wace ce haka?"
"Kanwata Helen nake Magana."
"Zainab? Ita kadai na sani."
Kara matsota ya yi tare da cewa "Helen nake Magana Nur, bana son jin wannan sunan, dagowa Nur ta yi ta tsareshi da Ido, ganin in da yabita da Ido tai saurin sunkuyar da kanta tare da kokarin saka hannunta ta turashi baya, cikin kokarin Kai mishi doka tare da fashewa da kuka, dan haka yai saurin tareta ta hanyar matsaeta jikin bango, ganin duk hakan bazai mishiba ya dawo da ita jikinshi tare da matse mata baki yana fadi kasa-kasa "Ki yi shiri Nur ki tsaya ma yi magana ki wuce abinki"Jin numfashi ta na kokarin barin jikinta tai saurin yin shirun tare da kokarin daidaita numfashinta, har wannan lokacin tana kwance a jikinshi batare da ta sani ba. Jin da yayi ta lafa daga kuka da kokarin tureshi da take yi ya ce, "Haba Nur, menene haka? Na zauna sosai da masu addini irin naki, nasan wasu daga cikin hakayensu inajin suna cewa yafiya abu ne mai kyau, ban dauka zamu kawo har yanzun batare da kin yafe mini ba, Koko dan ni ba musulmi bane yasa bazaki yafe min ba?"
Sai a wannan lokacin Nur ta kula da in da take" Dan haka tafara kokarin tashi, saidai yaki barin hakan ta kasance, cikin kuka take cewa "Ka manta abin da kaimin ne? Saida ka wulakantani sannan zakace min in yi hakuri, duk da kake ganina karama Ina da wayauna, lokacin da nake baka hakuri me yasa baka hakuraba har Saida ka fatantaka min kayan jikina"
"Ai nasan kina da wayau Nur, nasan dole abin yai miki ciwo, shiyasa na ce da kaina zanzo na baki hakuri, duk da cewa ban miki komaiba, na gane ban yi daidai ba Mamma da Helen zansan yadda zanyi in canza su, ke Kuma kifito kije makaranta karatu na wuce ki, don Allah don Allah ki yi hakuri ki fito ki yi harkokin ki kamar da." Kuka Nur ta sake sakawa tare da kara hankadashi ganin haka ya saketa ta rabo daga jikinsa, saidai cikin sauri ya sake yi mata runfa a karo na biyu tare da cewa, kina nufin wucewa zakiyi batare da kince kin yafe ba?"
"Duk abin da zaka mini sai dai kamin wlh bazan yafe ba, haka kawai na riga na gayawa Abba na Kuma yana shirin daukan mataki karka kara shigo mana gida."
"Zan kara bazan daina ba Nur, dole in nemar ma zuciyata sauki akan abin da ta ke so."
"Ka matsamin na wuce ko na fasa maka kai."
"Ina jiranki na shirya daukan duk wani abun da kike takama dashi" Wanni irin kallo Nur tamai sannan ta sake cewa, "Matsa in wuce"
"Bazan matsa ba" ya fada yana kara matsota Dan haka ta kara mannewa da bango, ganin tana kokarin saka ihu yasa hannunsa ya toshe bakinta tare da cewa "Idan kina son in bar wurin nan sai kince min kin yafe."
Hannunta tasa tana kokarin banbare nashi tare da cewa "Na yafe." Hankali ya karasa sauke hannun sa tare da cewa "Yaushe zaki je makaranta?" Cikin zunbura baki ta ce "Nima ban sani ba."
"Kalla, gobe kuna biki, jibi lahadi, ranar Monday ki fito kije makaranta."
Wannan lokacin bata iya cewa komai ba kokarinta kawai ya cire hannu sa ta wuce, jinsa ta yi ya kuma cewa "Kin ji."
Daga kai ta yi alamar eh, sannan ya cire hannun cikin sauri Nur ta wuce, bayanta ya biyo, ita ko Nur sauri take har Saida taga tabi hanyar da zata sadata da cikin gida sannan ta juyo ta kalleshi a daidai lokacin da ya fice daga cikin gidan. Kai tsaye dakinta da shiga, rabon da ta kwana dakin ta jima, yau daya ta ji tana son kebewa, Sam bata son magana ko hayaniya, ko da ta shiga dakin gado ta fada sannan ta shiga tunani akan zuwa Poul gidan su, tashi ta sake yi acikin zuciyarta take cewa, "Yanxu shikena na yafe mishi?, Haka zamuci gaba da kallon juna alhalin ya kalleni tsirara" Innalilahi wa Inna ilaihir raju'un ta fadi a fili sannan ta sake komawa gadon ta kwanta, wani sabon yanayi taji a jikinta dan haka ta saurara domin tantace wanni irin Yana yi ne take ciki a yanzun, tunata kwance jikin Poul ya sa ta runtse Ido tare da sauke ajiyan zuciya kamar yanzun ne abin ke faruwa, gaba daya ta nemi nutsuwarta ta rasa duk da cewa bata ga fuskarsa ba ayau amman fuskarsa ta baya ke ta dawo mata, fari ne tass, dan gayen gaske maiji da nera, ajiyan zuciya ta sake ja sannan tace a fili "Su Yaya Bashir suna Ina Poul yayi kudi ya barsu alhalin zasu iya girman shi, duk da cewa suma suna da sana'a sai dai ko rabin-rabin shi Basu kai ba a kudi, dan ko Jamal da Jamil da suke takama da narai bzaasu nuna mishi komai ba" afili ta sake cewa "Watakila dan ya fisu kudi yasa ya fisu gaye" jin turo kofar da aka yi ya sata yin shiru tare da kallon Kofar, Aunty ta gani tana shigowa Dan haka ta fara kokarin sake fuskarta domin kada Aunty ta fahimci wani abu. "Nur ya kike dawo nan?" Aunty ta yi tambayan tana kokarin zama kusa da Nur"
"Na ga baki sun yi yawa acan ne." Nur ta fada tana kallon fuskar Aunty, kallonta Aunty ta yi sosai sannan tace "Ki ce min dai kin rage tsoron Paul toh ai shikenan" Mikewa ta yi tana kokarin fifita har ta kai kofa ta juyo ta sake kallon Nur tace "Kin yi sabon turere ne?" Gaban Nur ne ya fadi domun kamshin turaren Poul ne ya cika dakin a tunaninta ita kadai ke ji dan haka yanzun da Aunty ta yi maganar ta daburce, Daker ta iya cewa, "Eh" Ficewa Aunty ta yi, Nur ko na ganin fitan Aunty ta mike ta nufi bayinta dake cikin daki, kayan dake jikinta ta cire ta wanke su sannan tai wanka ta dawo ta kwanta, saidai Tunanin Poul ya hana mata runtsawa, tare da mamaki har lokacin da take wanke kayanta tanajin Kamshin turaren Poul na tashi a jikin su, daker bacci ya iya daukanta, washagari da safe jinta take cikin farin ciki da annashuwa musamman idan ta tuna yaune daura auren Abdallah duk da cewa har yanzun ba magana ya ke da ita ba. Alwala ta yi ta tada sallah saidai ta gaza natsuwa domin sosai Poul ke fado mata, duk da kukarin ganin ta kawar da tunanin shi dake yawan zuwa mata arai, bayan ta idar ta mike tana ninke dadumar acikin ranta take cewa Anya ma sallata ta yi kuwa ace ina sallah ina tunanin katon arne, tsaki taja tare da sake shinfida dardunar ta sake yin wata sallah, sannan ta mike ta shiga cikin gida. Ayau da ga kalli fukar Mamy zaka gane tana cikin farin ciki, hakama aunty da duk sauran mutanen gidan, Shi kanshi Abdallah yana ta shiga da fice a cikin gidan fuskarshi babu yabo babu fallasa, misalin karfe daya gidan ya cika duk dangi sun hallara na kusa Dana nesa.
Nur zaune gaban Mamy sai danna wayar aunty da ke hannunta take, Umma dake zaune can gefe ne ta kalli Nur ta ce, "Gaskiya Hajiya Halima kin sangarta Nur da yawa, ji inda ta zauna tun tuni tana faman wasa da waya saikace wata karamar yariya."
Gefen da Nur take Mamy ta kalla sannan tace "Aiko duk wadda ya kalli Nur yasan babu alamar sangarta a tattare da ita."
"Idan ba lalacewa ba ko kamar Nur yanzun ai kamata yayi ace ta na can tsakar gida ta kama wani aikin Itama." Wannan karon Mamy fuskartar Umma tayi tare da cewa, "Ba aikin da zatayi yau, wannan aiki ai na manya ne" Wurin Nur ta juyar da kallonta tare da cewa tashi kije ki shirya" Mikewa Nur ta yi batare da ta ce komai ba ta nufi dakinta tura kofar, cike da mamake take kallon gadonta kaya maza ne farare kalla aje akan gadon, a gefe guda Kuma ga takalmi da agogo tare da turaroka, ajiyan zuciya ta yi domin ta tabbatar da babu wadda zai ajiye kayan nan sai Bashir, zama ta yi abakin gadon domin gudun karta shiga wanka Bashir ya shigo ya dauki kayansa batare da ya bata kudin da yace zai bataba, sai dai ga mamakin ta tazama taji motsin watsa ruwa a bayinta, dan haka ta saurara jin tabass wanka ake yasata mikewa ta nufi kofar tare da tambayan waye? Tsawon lokaci tana sauraro ba'ace komai ba, dan haka ta sake cewa waye aciki? Wannan karon ma abace komai ba, duk da haka Nur Bata hakura ba murya ta daga ta sake cewa Wai waye aciki ne? Awannan karon batare data rufe baki Bata ji ance Ubanki ne!" Da baya ta koma bakin gadon ta zauna tare da mamakin me ya kawo Abdallah wanka dakinta, bata gama mamaki ba ta mike da nufin fita dakin domin karma ya fito ya sameta aciki, saidai harta taba kofar ta tuna da sabulonta dan haka tai saurin komawa wurin kofar bayin tace "Yaya Abdallah karka taba min sabulona!" Saurarawa ta yi ko zaiyi magana, jin bece komai ba ta sake ce "Dan Allah karka taba min sabulo kaji" Wannan karon ma dai bece mata komai ba dan haka ta tsaya a wurin bayan tsayon wani lokaci ya bude kofar ya fito yana daure da towel daga kugunsa zuwa guiwa, kallo daya yai mata sannan yace, "Au dan Ubanki tsayawa kika yi anan? Sabolun naki na gwal ne da baza'ayi amfani dashi ba?" Kokarin kutsawa take ta gefen sa cikin turo baki gaba tace "Yaya Bashir ne ya saya min sau daya na yi amfani dashi"
"Toh ya kare dashi na yi amfani sai ki gaya mishi ya sake sawo miki wani" Kutsawa ta yi ta gefensa bata damu da gogan jikinshi da ta yi ba har sai da yai saurin rike towel dinsa tare da bin bayanta da kallo,
guntun sabolun ne rike a hannunta yayin da ta fara kuka tana fadin yau fa na bude, shine har ya kare haka? ta kare maganar tana kallon fuskar Abdallah, cike da mamaki yace "Zo ki fita kibani wuri na lura ma ba hankali ne da ke ba." Tsuganawa ta yi ta dauki soson wankanta ta kalla sannan ta fashe da kuka tare da kokarin ficewa a bayin adaidai lokacin da Abdallah ke cewa yau na gama masifa soson naki ma laifine dan na yi amfani dashi?
Cikin kuka ta ce "Ai babu wadda ke dauka soson wani agidan nan sai ni za'a dauki nawa?" Bata rufe bakiba ya dauketa da Marin tare da cewa "Fita kibani wuri." Fashewa ta yi da kuka sannan ta nufa kofar fita a dakin, bata dire ko Ina ba sai adakin Mamy, tun kafin ta shiga take cewa "Mamy Kinga Yaya Abdallah ko!" Duk mutanen dakin hankalin su dawowa yayi gareta, Mamy kuwa cike da fusata tace "Me ya faru?"
"Mari na yayi Mamy" Cikin kuka sosai Nur ke maganar har yanzun tana dafe da kumatunta"
"Kin mishi wani abun ne?" Daga yadda Mamy ke maganar zaka gane ranta a bace ya ke. "Saboluna ya karar min Kuma jiya Yaya Bashir ya saya mim"
"Wato shi dai Abdallah matsala gareshi banda abinshi Ina ruwanshi da sabolon ki? Yana ina? Ni fa bana son mugunta, menene nashi da duka kuma? shi baya yin laifin ne me yasa ba a dukan shi? Mu je" Cike da fada Mamy ta fice a dakin, Aunty ce ta kalli Ummy Dake gefe tace "Kingani ko? in da kike ma Nur bata kalla ba, ita ta sabulon ta take, ita Kuma Mamy in dai kaji tana fada a gidan nan to akan Nur ne, dan ayanzun kam ita da Abdallah basa shiri sam, abin da ba'ayi da kuriciya ba shi ake yi yanzun." Murmushi Ummy ta yi tare da fadin "Allah ya shiryeta dai, banda abinta da yau daya har ta yi magana" Mikewa Aunty ta yi tare da cewa "Barin je, dan shima fa ba kanwan lasa bane, Mamy Kuma akan Nur Bata da dama" karake maganar ta yi tare da ficewa a dakin.
*****
Abdallah na daura agogo su Mamy suka shigo, be yi mamaki ba dan yasan dole Nur takai karanshi, kallo yabi Mamy dashi yayin da take fadin "Ya zaka daketa ka hanata kuka?" Cikin San yin murya sosai ya ce "Mamy kiyi hakuri, idan mutanen dake dakina sun fita taje ta kwashe duk sabolo dake dakina na bata."
"Ba ason sabolun naka, Kai kasan kana dashi me ya kawo ka nan wanka?" Wannan karon lebensa ya lasa alamar Yana cikin damuwa sannan yace, "Mutane sunyi yawa ne Mamy, kuma kowa wanka yake son yi"
"Idan hakane sai ka dauka sabulonka kazo dashi, Kai baka siya mata sabuloba baka da damar zuwa ka yi amfani da nata"
"Toh a yi hakuri Mamy baxan karaba" yana fada idonshi cike da farin ruwa.
"Dama neman magana kawai kake, da gangan ka yi, in ba hakaba wanka daya a karar sa sabolu haka?" Mamy ta fada tana nuna mishi sabulon da Nur tazo mata dashi. Satan kallon Nur ya yi ya gallara mata harara sannan ya kalli Mamy yace "Nawa ne sabulon in bata ta saya wani?
"Dukan Kuma da kamata fa? Nace idan ka biyata sabulu barin daka mata fa? Zaka hada duka ka biya ne?"
Shigowan Aunty ya sa duk duka juya suka kalleta Abdallah ko takalmi sa da kularsa ya dauka ahannu yana kokarin fita acikin dakin, cikkn sauri Aunty tace "Ina Kuma zaka? Ka tsaya ka gama shiryawa mana." Toh aunty bakya ganin abin da Mamy ke min ne" Ya fada cikin nuna bacin rai, da alama ya fara fusata, "Kibarahi gara ya fita din,idan ba neman rigima ba shida yazo cin arziki har ya daketa.?"
"A'a wallahi, ita dai kecin arziki" Aunty ta fada tare da amsan takalman Abdallah ta aje kasa tana fadin "Karasa shiryawa sannan ka fita."
"Au waton goya mishi baya kike har zakice haka? Ai ba'a canzawa tuwo suna, yadda zaiyi takama gidan ubanshine itama haka gidan ubantane, ba'a fimu tsumma ba bare ace za'a bada mana kwarkwata, kuma yazo ya fita tunda ba dakinshi bane"
Aunty kan Nur ta maida kallonta tana fadin "Wallahi Nur baki da kirki, yau daya kin kasa hakuri da dan'uwanki, yanzun ke wannan abin da ke faruwa dadi ya ke miki? Gida cike da mutane kika iya ratsasu kikai kara?
Batare da Abdallah yaji me Nur zatace ba ya fice a dakin, da alama yaji haushi sosai Dan ko kallon Inda Nur ta ke biyi ba, Aunty ma ficewa ta yi yayin da Mamy ta Kara rarrashin Nur sannan ta fita.
Har wannan lokacin Nur haushi take ji domin ita ta tsana a taba mata sabulo, daker tayo wankan sabo da haushi tana fitowa ta sake kwanciya a godo batare da shirya ba, wayar Aunty dake gefenta ta ji ta fara kara, dan haka ta mike tasa hijjabi domin ta mika mata, katsewa ta yi bayan ta saka hijjabin aka sake kira, wannan lokacin ne ta kalli wayar ganin Yaya Bashir ne tai saurin dagawa tare da cewa "Yaya!" Daga can cikin wayar yace "Na'am kanwata, Amman kin gama fushin dai ko?
"Yaya Abdallah ne ya karar min da sabulon daka kawo min."
"Yanzu Mamy ta gaya min, zan kawo miki wani amman ki saki ranki, Kuma kiyi maza ki shirya ganinan zuwa in dauke ki muje wurin dinner.
Cikin ranta taji farin ciki sai a yanzun ta tuna biki fa ake agidan cike da murna tace "An daura auren ne?"
"Eh yanzun dai za'a daura."
"Toh Yaya Bashir da an daura ka kirani ka Gaya min in ruga in yiwa Mamy albishir."
"Karki damu kanwata, idan ma kinason kiji kamar kina wurin sai in kira ki da zaran zara'a daura auren."
"Ina son Yaya Bashir dan Allah ka kirani."
"An gama kanwata, amman wai ni in tambayeki mana."
"Inajin ka."
"Ba yanzun kika gama fada da Abdallah ba amman Kuma kina murna da auren shi.?"
"Ai dan uwana ne Yaya, daman shine yake tsokana ta yanzun dai karka manta ka kirani, Kuma yanzun zan shirya karfa ka manta ka wuce dinner bakazo ka daukeni ba."
"Yaya za'ayi in manta? kiyi maza ki shirya dai."
Nur na sauke wayar ta mike, kayan da zata saka ta dauko, duk abin da zata bukata ta aje bakin gado, bayin ta nufa da nufin yin waka taji wayar na kara, dawowa ta yi ta zauna ganin Yaya Bashir ne ta zauna domin sauraron daurin auren...