CIWON 'YA MACE

Chapter 19

by @fadilalamido

CIWON 'YA MACE

    By

Fadila Lamido

   ADABI WRITER'S ASSOCIATION

Page 37-38

Kallon shi ta sata fuskarta daure sosai sannan ta daga kafa ta shiga motar ta zauna, rufewa Poul yayi sannan ya zagaya ya shiga alokacin da Zainab ke waiwayen Nur tana murmushi, shima kallonta yayi kadan sannan yaja motar, gaba daya hankalin Nur a tashe ya ke, dan haka ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da hannunta, daka ganta zaka fahimci tana cikin bacin rai.

  Tafiya su ke acikin motar shiru sai wata wakar inyamuranci dake tashi a radio motar, zuwa can Nur ta dago kanta, gani ta yi Yana kallonta ta madubin dake gabanshi, dan haka ta karkace da sauri ta juya mashi kafada, murmushi Poul yayi, duk da cewa ta juyar da fuskarta amma ya kasa cire idonshi akanta, abakin makarantar ya tsaya, yana tsayawa Nur ta Bude motar ta fice, idon shi akanta ya ciro kudi ya mikawa Nur yana fadin ke da ita, itama Zainab idonta akanshi ta amsa kudin, mamakine ya kama Zainab ganin in da yake kallon Nur, bayan ta amsa ta kalli kudin sannan tace "Mun gode." Muryanta ne ya dawo da shi cikin hankalinnshi, kokarin tada motar yake batare da ya amsa ba, Saida ya ga shigansu makaranta tukuna ya wuce, sosai jikin Zainab yayi sanyi ganin wannan labari dake faruwa, tunani da yawa azuciyar Nur akan wannan abin, a yanzu ko tantama bata yi yayanta poul ya fada tarkon son, wurin Nur ta maida hankalinta data shige ajinsu afusace.

    Bayan sun zauna a ji ma zama Nur ta yi kamar kurma duk yadda Zainab ta so su yi magana ki ta yi, haka Kuma ko da aka tashi kafin ta farga Nur ta wuce, hanya ta kamo ita daya acikin ranta take sake sake, haka nan take jin tausayin Poul acikin zuciyarta.

    Bayan Nur ta Isa gida sannu da gida tayiwa su Mamy sannan ta wuce dakinta, cak ta tsaya bakin kofar dalilin gani mutum kwance a kan gadonta, sai yanzu ta tuna da dazon tabar Abdallah da Amarya, kenan be wuce da ita ba, jakar makarantar ta ajiye sannan ta nufi falon, tun kafin ta isa take fadin Mamy Yaya Abdallah be wuce bane? Na dauka yaune tafiyarshi ai" Karake maganar ta yi tana kokarin zama kusa da aunty Saratu. Yayin da Mamy ke cewa, "Ya wuce Nur tun safe"

"Toh Kuma naga Aunty Amarya anan" Nur ta fada tana kallon fuskar Mamy, "Eh nan zata zauna"

"Har ya dawo?" Nur ta sake tambaya cike da mamaki, wannan karon Aunty Saratu ce tace, "Ya ce idan ya gama saita komai zai dawo ya dauketa."

  Tabe baki Nur ta yi yayin da Aunty Saratu ta sake cewa "Ta tashi baccin kuwa?"

"A'a Bacci take" Nur ta bata amsa, Mamy ce tace "Kije ki cire kayan makaranta idan kin ta tashi kizo ki dauki abincinta. Mikewa Nur tayi bayan ta amsa sannan ta nufi dakin, kayan makaranta ta cire sannan ta nufi bayi, zuwa can ta fito ta sake bin Bilkisu da kallo, gani ta yi kamar idonta biyu dan haka tace Aunty Amarya! Bata amsa ba, ahankali Nur ta karasa bakin gadon ta zauna tare da leken fuskarta tana sake cewa "Auntymu!"

 Wannan karon hannu Bilkisu ta sa ta share fuskarta sannan ta juyar da kanta dayan gefen tare da cewa "Kin dawo?"

   "Eh na dawo" Nur ta fada na mai nazarin yanayin da Bilikisu ke ciki, kamar kuka take dan haka Nur ta sake cewa, "Aunty ashe kina jina to ki tashi su Mamy nata jira ki tashi kici abinci."

   "Banci Nur, bana jin yunwa." Lumshe Ido Nur ta yi Jim yanayin muryanta sannan tace "Kinci wani abin ne to?"

  "Eh kafin mu fito mun ci abinci." Wannan karon Murmushi Nur ta yi sannan tace "Ke dawa?"

  "Cewa na yi kafin mu taho nan ni dashi mun karya" Dariya Nur ta yi afili tare da cewa "Ki fadi Sunanshi mana"

"Haba Aunty tun safe ne fa, kina son kice har yanzun bakyajin yunwa?"

"Bana ji Nur" Dariya Nur ta sake yi sannan tace "Kenan bazaki sake cin abinciba har sai ranar da Yaya Abdallah ya dawo?" Wannan karon yunkurawa Bilikisu ta yi ta tashi, bayi ta shiga ta wanko fuskarta sannan ta fito, batasan meye dalili ba tun da Nur ta fara magana taji ta samu nutsuwa tun bayan tafiyan Abdallah.

  Nur kuwa har yanzun fuskarta cike take da dariya domin ta gane Bilikisu kewan mijinta take. Mikewa tayi ta fito falon, Aunty Saratu na ganinta tace yaya aka yi Nur da ganin ki akwai magana a bakin ki, kamar jira Nur take ta fashe da dariya tare da waiwayen bayanta cikin dariya tace "Ashe idonta biyu aunty kuka take Yaya Abdallah ya tafi ya barta, Karake magar tayi tana kyalkyata dariya, ita ko Aunty daure fuska ta yi sannan tace "Haka ta gaya miki?"

   Kafin Nur ta yi magana Mamy ta ce, "Ai dole bazataji dadiba Saratu, dashi ta saba kwana shidda da rabota da yan uwanta wa ta saba dashi anan? Amman ya tsallaketa ya barta kuma tafiya ba kwana biyu ba ba uku ba wata da watanni, abin da nake nuna muku kenan, ki dauki abinci kije kuci kema aiki ya same ki" Mamy ta fada tana kallon Nur, tuni Nur ta tabar dariya tunda taji ta bakin Mamy, dan haka koda ta shiga kicin tana deban abincin tana jinjina abin, har ta gama zuba abincin ta koma daki tunanin da take kenan, zaune ta samu Bilkisu ta yi tagumi, wannan lokacin tausayi tabawa Nur, dan haka ta zauna daf da ita tare da cewa, "Aunty kici abincin barin yi sallah inzo" Mikewa Nur tayi saidai har ta idar da sallah Nur bata taba abincinba dan haka Nur ta zuba masu tare sannan ta ce "Muci Aunty" Babu laifi Bilkisu ta danci kadan sannan tace ta koshi, a daidai wannan lokacin aka kira ta a waya, da sauri ta dauka yayin da Nur ta bita da kallo, wayar tasa a kunne tare da komawa bakin gado ta zauna, cikin shagwaba Bilkisu tayi sallama cikin wayar hawaye taga Bilkisu na cirewa a gefen idonta tsayon lokaci batace komaiba, da alama sauraron mgn take cikin wayar, zuwa can taji tace, "In je gida mana to" Shiru ta sake yi zuwa can ta sake cewa, "A'a" Murmushi taga ta yi sannan ta sauke wayar. Tunda ta fara wayar Nur Bata cire idonta akantaba dan haka da taga ta sauke wayar fuskarta sake tare da saurin mikewa tana Murmushi, tun da ga lokacin Bilkisu ta sake jikinta Hira suka yi da Nur tamkar Daman can sunsan juna, misalin takwas da rabi na dare Nur ce zaune adakin Mamy yayin da ke kokarin gyara kaya tana sakawa cikin sif, Waigowa ta yi ta kalli Nur tare da cewa "Taci abincin kuwa?"

"Eh taci Mamy harma sun yi waya da yaya."

"Yauwa ya kyauta yayan, yanzun wani abu kike so?"

"A'a" Nur tace tana kallon cikin idon Mamy. "To ki koma wurinta mana tafi jin dadin zama idan kina wurin ko?" Amsawa Nur ta yi ta fice badan ranta yaso ba, lokacin da ta shiga dakin kan gado ta samu Bilkisu tana danna wayarta tana murmushi da alama chart take, dan haka ta nema wuri daf da Bilkusun ta kwanta saidai ta kasa cire idonta akanta, murmushi take sosai zuwa can Nur taga ta saki wayar ta fashe da dariya cike da mamaki Nur ta kalleta tare da tashi zaune tana sake binta da kallo, ganin irin kallon da Nur ke mata yasata cewa "Nur kina ganin yayanki zai kasheni da dariya ko? Wallahi in dai zaka biye masa sai yasa cikin ka ciwo" Wayarta ta jawo tana fadin "Barin kashe data na kawai Saida safe."

    Nur kasa cewa komai ta yi sabo da mamaki, sai take ganin kamar mafarkine take yi, wannan fuskar tashi har ta iya bada dariya, wani sashi na zuciyarta kuwa farin cikine ya kamata, tunda dai har Yana son matarshi har yana wasa da dariya da ita ai AlhamduLillahi, wayar Bilkisu ne ta sake daukan Kara, dauka ta yi tasa a kunnenta zuwa can tace "Bacci nake ji" shiru ta sake yi zuwa can ta sake fashewa da dariya tare da cewa "Ka bari karkasa cikina ciwo, gashi barin bawa Nur ku gaisa" shiru taga ta yi tare da ya mutsa fuska, harta sauke wayar fuskarta bata dawo daidai ba, ganin haka Nur ta juya mata baya domin tasan bazai wuce akan sunanta data Kira bane, ita Bilkusu kallon Nur ta yi sosai sannan ta kwanta cike da tunani, washegari da safe bayan Nur ta tafi makaranta Abdallah ya kira Bilkisu bayan sun gaisa ta ce, "Baby jiya daga cewa ga Nur ku gaisa sai ka hau fada" Lumshe Ido Abdallah yayi sannan yace "Banson maganar yariyar ne kawai, ko sunanta banson naji an kira" Cikin son taga ya sakko tace "To aini ban saniba dasai ka gaya min, jiya daker na yi bacci"

  "Ki yi hakuri bansan lokacin dana fara fadan ba amman ba'a dakinta aka barkiba ko?"

Jimmm Bilkisu ta yi zuwa can tace "Tare muke adakinta ne"

  "Zanyi magana da Aunty a baki dakina ki zauna bana son alakanki da ita."

  "Baby saboda me? Ni Inajin dadin zama da ita, tana da kirki"

"Eh, Nima ba cewa na yi bata da kirkiba, karkiga wai tana kusa da sa'arki ki saki jiki da ita, ba kowanni abu Zaki dinga bari tanaji ba, kuma idan na kiraki a waya ki daina amsawa a gabanta" Cikin rashin fahimta Bilikisu tace "Amman in tambaye ka?"

"Ina jinki?"

"Wai Nur ba kanwarka bace?" Ajiyan zuciya Abdallah yayi sannan yace "Wacce irin tambaya ce Wannan kuma? so nawa zan gaya miki adadin 'yan gidanmu?" Cikin kwalwakl da Ido tace "Ai ce min ka yi Nur ce autarku" Cikin son kawar da baccin ranshi yace "Eh itace auta"

"Mamy ce ta haifeta?"

Cikin sauri yace "Eh, Bakiga suna kama ba?"

"Na gani, to kaifa?" Wannan karon dariya Abdallah yayi sannan yace "Ai na gaya miki nine na farko a wurin Mamy da Abba" Cike da gamsuwa tace "Na gane, to amma Nur ba Abba bane ya haifeta?"

"Waye to?" Abdallah ya jefa mata tambayar, jin haka yasa Bilikisu cewa "Aini kai nake tambaya"

"To Abba da Mamy sune iyayenmu gaba daya Baby, idan dan abin da kikaji na fada ne akanta kike tunanin ba kanwata bace akwai abin da tamin ne."

"Toh ka yi hakuri kaji"

"Ai na hakura, amman dai bana wasa da ita, kema kuma bana son ki sakar mata fuska"

 Dole Bilikisu tabar mgnr badan ankai inda take son akai ba domin har yanzun zancen be shigeta ba. Hira suka ci gaba dayi kafin su kare har ta manta da zancen Nur.

                                 ****

 "Mai yasa zaki firgice haka" Poul ke fadin Haka alokacin da ya tare Nur adaidai kofar gidansa bayan sun rabo da Zainab. Kokarin gewayeshi take ta wuce saidai sai shan gabanta yake ya hana mata wucewa, kwalkwal Nur ta yi da Ido tare da cewa "Ni ka rabu dani banso" lumshe idon sa yayi tare da cewa magana zamu yi sai ki wuce.

   Dagowa ta yi ta kalleshi cikin sauri tai kasa da kanta dama can bata iya hada Ido dashi domin sosai ya ke mata kwarjini, yau kuwa wani irin abu ne taji wadda ta rasa da wanni sunan zata kirashi, gaba daya ji ta yi kamar zazzabi na son rufeta dan haka ta tsaya ta kasa cewa komai, ita bata wuceba ita Kuma Bata dago ta kalleshi ba, zuwa can ya ce, "Nur yanxu bana iya bacci sosai kodayaushe sai inji Ina son kallonki, gashi kin min nisa ban isa inzo gidanku ba, ke Kuma ko kinzo nan bakya bani fuska." Sunkuyar da kai Nur ta yi bakinta zunbure batare da tace komai ba, zuwa can ya sake cewa "Ina son ki dinga bani ko minti goma ne kowacce Rana nayin magana dake" Can kasan makoshi ta ce "Sabo da me?" Lumshe Ido Poul yayi zuwa can ya sauke akanta tare da cewa "Sabo da ina son ki."

"Mu ba haka muke yi ba" Cikin Ido ya kalleta sannan yace "Yaya kuke yi to?"

"Gidanmu zakaje sai ka gayawa Abbanmu " Da sauri ya dago ya kalleta tare da kiran sunanta ahankali ta dago ta kalleshi, jawur taga idonshi cikin yanayin dake nuna yanajin tashin hankali, cike da muwa taga ya bude bakin sa idonsa cike da ruwan hawaye yace, "Amman kina ganin idan naje zai amince?" Tsintan kanta ta yi da cewa "A'a bazai aminta ba" Tsayon lokaci taji bece komaiba dan haka ta dago ta kalleshi, gani tayi yana kawar da fuskarshi duk Yana yinshi ya canza da ga ishashshe mai takama da naira ya koma kamar mai zama da damuwa, daker ya iya cewa "Amman ke kin amince dani?"

  Cikin Sauri Nur ta girgiza kanta duk da cewa tana tuna zancen Aunty Saratu amman ta kasa yi kamar yadda tace. Bayan ya gama kare mata kallo yace "Mai yasa Nur?" Wannnan karon ma tsintan kanta ta yi da cewa "Bakeje gidanmu ka gayawa Abbanmu ba." Jimmm, yayi zuwa can yace "Na gane, to ai kince bazai yadda ba ko? Kina da wadda zaki aura ne?" Wannan karon kai ta girgiza alamar a'a dan haka ya sake cewa to meye dalinlin? Sunkuyar dakai tayi tana mai takaicin yadda take kulashi har yanzun ta kasa wacewa ta barshi, idon shi akanta ya sake cewa "Ina jinki." Can kasan makoshi ta ce "Kai ba musulmi bane" Wannan karon shiru yayi tsayon lokaci, zuwa can ya ce, "Amman ai addinin ku be hana ba." Can kasan ta sake cewa A'a addinimu be yadda da mace ta auri na miji wadda ba musulmiba." Jimmm, yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa, gani yayi Nur tana kokarin wucewa Dan haka yai saurin cewa "Dan tsaya" Tsayawa ta yi kamar yadda yace sannan ya ce, "Ni Kuma Gashi Ina son ki yaya kenan?" Wasa Nur ta shiga yi da hannunta tsayon lokaci batare da ta ce komai ba, bayan Poul ya gama kare mata kallo yace, "Ina jinki?" Dagowa Nur ta yi ta sata kallonshi sannan tace, "Hakan ba daidai bane" Kallonta Poul yayi sosai sannan yace, Na gane, shikenan amman yanzun kinsan mene ne?" Kai Nur ta girgiza tare da cewa A'a, Kara matsowa Poul yayi tare da cewa "Nasan kin sanni barin sani, ina neman wani taimakone a wajenki, idan bazakiyi dan niba inci albarkacin Helen."

Nur na wasa da hannunta tace "Mene ne shi?"

"Sai kin min alkawari tukuna in fada miki" Batare da Nur ta yi tunanin komai ba tace "Na yi"

"Na farkon shine kizo mu dan shiga daga cikin gida kin ga nan akwai idon mutane, na biyu kuma sai mun shiga zan gaya miki...