RASHIN SANI…

56

by @hauwaausmanjiddarh

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''




'''Hak'ik'a dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin sammai da k'assai, wanda ya dai-daita tsakanin wuta da k'ank'ara, ban tab'a sanin ina dubbannan masoya ba, sai a wannan karon, dama hausawa sunce sai wani abun ya faru kake sanin wani abun, haka Allah bai tab'a yin abu babu dalili, ina matuk'ar godiya mai tarin yawa ga masoya na, har dama mak'iya na wad'anda sune sukayi silar bayyanar dandazon masoya na, wallahi nayi kuka harna gaji saboda soyayyar da kuka nuna min, nayi mamaki kwarai dan sai da na gaji da amsa waya, banda texts da WhatsApp message, Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ya Rabbi nagode maka, wai yau ni Hauwa nike da wad'annan dubban nan masoyan, Annabi Muhammad S.A.W yace " idan an b'ata maka ka nuna basoda kai ba jaki bane, idan aka baka hak'uri ka hak'ura saboda kai ba shaid'an bane, wallahi bani da abinda zancewa Allah da masoya na sai godiya, dan babu wata kalma da zanyi amfani da ita wajen gode muku, da kuma bayyana muku tsantsar farin ciki na, but I really really love you so much, I love you more & more most, please wad'anda suka kira ni banyi picking ba, da wad'an da sukayi min texts ta WhatsApp da massage banyi replaying ba kuyi hak'uri'''


_Then wad'an da suka kira mahaifiya ta suka rok'eta ta bani hak'uri, to ku sani tayi min magana, na kuma ji, dan yanzu haka saboda maganar datayi min ne ma zan cigaban, dan ko k'awa ce akayi mata magana akan ta baka hak'uri, an san ta isa dakai ne, shiyasa aka nemi alfarmar a wajenta, balle kuma uwa mahaifiya, kunci darajar Mama da wad'an da suka kira ta._


*A CIGABA DA GASHI.....!*





5⃣6⃣





Iska ta fara hurawa had'i da cewa " hello.....! hello.....! Yaya Aarib bana jinka fa, bari na sake kiranka ta fad'a had'i da kashe wayar,

a matuk'ar razane Khulud ke kallan Sanah da alama tana neman k'arin bayani ne,

" ke...! gaba d'aya mazan family sun tafi Damaturu,

tayi maganar cikin zaro ido da tsantsar tashin hankali,

murya na rawa Khulud" wacce Damaturun....!?


"Damaturun da mukayi musu k'arya,

ta fad'a tana zama bakin gado gami da d'ora hannuwanta duka biyun aka,

" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,

"yanzu meye mafita...!?


Khulud ta fad'a tana zarya cikin d'akin,

yatsanta a baki tana cizawa,

kiran Dide daya shigo yasa su kallan junansu cikin tension,

babu wanda ya iya furta koda kalma d'aya,

" kiyi picking karta yi cutting suyi zargin wani abu,

Khulud ta fad'a rik'e da k'ugunta,

hannunta na rawa tayi picking,

cikin k'arfin hali ta daure tace " Assalamu Alaikum Dide ya gida....!?


"Lafiya lau Alhamdulillah,

muna ta kiranki tun d'azu bakiyi picking ba,

" eh....! ina cikin mota ne bacci ya d'auke ni kuma wayar na cikin jaka,

ta fad'a idanta kan Khulud wacce take tsaye gumi na karya mata,

dan ganin asiri na niyyar tunowa,

jin abinda Sanah ta fad'a yasa ta kallan Sanah da idanuwanta duk waje kamar na mujiya,

Dide yace " mota kuma....!?


"Eh...! Dide jiya munyi magana da Abbu naga ranshi yayi mugun b'aci nayi ta kiranshi bayyi picking ba,

hakan yasani tahowa dan dama mun gama komai,

cikin zak'uwa Dide yace " kina nufin kina hanyar Kano yanzu....!?


"Eh..! ai harna kusa k'arasowa gida ma, mumma shigo cikin gari,

" tab...! aiko munyi sab'ani dan mu gamunan munyi tafiya ta kusan 1hr،

 dariya k'arfin hali tayi tace " baku kuka d'aga min hankali na taho babu shiri ba,

amma ai babu damuwa akwai friends d'ina ku k'arasa sai ku gaisa,

kai Khulud ta dafe had'i da cije hak'ora jin Sanah na neman b'allo ruwa,

" yo mai kuma zamu je muyi bayan wacce zamuje dominta ta taho...!?


Ya fato Khulud tayi kusa da ita tayi mata alama data hura iska a jikin wayar,

aiko da k'arfi Khulud ta shiga hura iskar,

"Dide bana jinka ta fara tsinkewa idan na isa gida zamuyi waya,

tayi maganar tana rarrabata,

" to to shikenan muma gamu nan yanzu zamu jiyo،

kashe wayar tayi had'i da dafe kanta ta firzar da iska daga bakinta,

ganin Khulud na niyyar yi mata magana yasata tsuke fuska,

ta k'arasa had'a kayan ta shirya tsaf ta ja trolley d'inta

jikin Khulud na rawa ta biyo ta parlour'n,

" my Sanah da kin d'an k'ara jira kad'an dan karsu ga kinyi saurin komawa,

" a ina d'in zan tsaya....!?


Ta fad'a batare data kalle ta,

Khulud na k'ok'arin yin magana ta d'aga mata hannu tace " enough Khulud time is not under our control,

dan bai jira sai dai mu mujira shi,

cikin marairaicewa Khulud tace ' but please......!

"but please, what....!?


" what do you want again....?


"An what do you mean to me...!?


" the game is over here Khulud,

wasa ya k'are, mu rufe wannan babin mu bud'e wani kuma,

yanzu komai yana hannunki idan kinga dama sai ki saka shi ya sake ni,

"ban gane komai yana hannuna ba....!?


" Yes of course everything is in your hand,

ta fad'a tana jan trolley, murya Khulud ta d'aga tace " karki manta kina da aure a kanki so karki rink'a dating samari,

banza Sanah tayi mata ta fice daga cikin harabar gidan cikin tsantsar bak'in ciki, waje ta samu a k'ofar gidan Khulud ta zauna taci uban kuka,

ta godewa Allah, kana ta mik'e,

mai adai-daita ta tare tace " please ka kaiki inda zan hau motar Damaturu,

tashar Kano line ya kaita ta biyashi,

mutane nata tambayarta inda zata bata kalli kowa daga cikinsu ba,

ta koma gefe tayi dialing number Abbu,

bugu d'aya yayi picking, 

" ina ta kiran wayarku tun d'azu na kasa samunku,

" may be munzo inda ba network,

naji kamar har kun sauka ma ko....!?


"Eh saukar mu kenan yanzu haka muna tasha,

na rasa abin hawa ne, " ok ki tsaya nan bari na turo driver ya d'aukeki,

ta amsa da to,

takai 30 minutes tana jira kafin driver ya k'araso,

"ayi hak'uri manyan gobe garin ne da go slow,

murmushi kawai tayi mishi batace komai,

har suka isa gidan bata ce k'ala ba,

tun daga harabar gidan ta soma kwalawa 'yan gidan kira,

" Juju, Mamu, Aunty Halan, Aroos, Seemah,

" ikon Allah yau muna da manyan bak'i kenan....!?


Halan tayi maganar tana fitowa,

"gani fa na dawo masu murnar gani na nayi da masu black stomach ma gani,

" tom magananniya sarkin bak'ar magana,

tayi maganar suna shiga part d'in Mamu,

ganin Mamu a zaune a parlor yasa Sanah bud'e baki cikin mamaki tace " kina parlor kina ji na amma kikayi shiru....!?


"Kuma kawai saina fita rigid'i-rigid'i muna jerin kwagon tarayyarki,

baki ta tab'e tace " Aunty Halan mu koma ban zama cikin gidan nan tunda ba'a sona,

ta fad'a cikin shagwab'a,

"ayi haka kuwa 'yar Abbu da Dide....!?


" Ai amma yi mu koma kawai,

ban zama, gidan Juju ko gidanki zan koma,

ta fad'a tana jan trolley'n,

" to fa ashe masu gidan ne suka dawo ake kwala mana kira haka....!?


Kallansu tayi had'i da tab'e bakinta tace " sai yanzu aka ga damar zuwa tarya ta....!?


"Ke fa matsalarki kenan ba'a abun arziki dake،

daga dawowarki har an fara rigima dake,

" Aunty Halan mu tafi kinji kyale wad'annan,

ban zama indai ba'a ban hak'uri ba,

tayi maganar idanta kan Mamu,

deep down kuma tana jin mugun so da k'aunarta fiye da baya,

tana k'ara ganin girmanta, mutuncinta da k'imarta,

Allah kad'ai yasan me Sanah keji cikin zuciyar ta,

daurewa kawai tayi dan kar matan yayyansu su fahimci wani abu ,

amma ji take kamar tayi ta kuka tana ihuuu, babu abinda yafi damunta cikin ranta sai tsantsar jin tausayin mahaifanta,

 Mamu da Abbu,

da sukayi muguwar yarda da ita wanda a koyaushe suke kyautata mata zato,

tunda take dasu basu tab'a yi mata wani abu na rashin adalci ba,

kullum k'ok'arin su bai wuce su kyautata musu, su sanya su cikin farin ciki ba, 

kullum bakinsu cikin yi musu addu'a da sanya musu albarka had'i da fad'ar alkhairi su yake,

bata tab'a jin sun fad'i ai bunsu ba,

amma ita gashi tayi musu rashin adalci, ta ruguza dukkan yardar da suka yi da ita,

taci amanarsu ta watsa k'asa cikin idanunsu,

bata basu dama da hakk'insu akanta ba,

bata basu damar sauke nauyi da amanar da Allah ya basu tata ba,

ta hana su damar aurar da ita da kansu,

duk sanda wata tayi abu mara kyau kalmar iyayenta itace nasan Sanah ta bazata tab'a yin haka ba,

jin Halan na cewa " zauna nan na kawo miki ki sha kinji sister,

"yauwa my special Aunty ai dama me kin iya saukar bak'i,

Aroos da Seemah basu kula ta ba,

suka gaida da Mamu ta amsa cikin fara'a,

kana suka zauna ana hira da su,

Halan ta kalli Sanah tace " kin san Papu ya rasu kuwa....!?


Sanah dake neman haryar kuka dama,

ta samu hanyar da zata fakaice ta shiga rusa kuka kamar ranta zai fita,

shiru sukayi gaba d'ayansu suna kallanta,

Mamu da kallo d'aya tayi mata tasan akwai abinda ke damunta,

ta k'ura mata ido, danta tabbatar ba kukan mutuwar Papu kad'ai take yi ba,

ta hango d'unbun damuwa, bak'in ciki k'unshe cikin kwayar idonta,

sosai jikin Halan ma yayi mugun yin sanyi dan itama tasan Sanah dai-dai gwargwado,

a k'alla yanzu sun kai 10yrs da sanin juna yanzu,

take ta fara zargin akwai abinda ke damunta,

amma su Aroos basu fahimci komai ba,

Halan ta mik'e rik'e da hannun Sanah ta jata bedroom d'inta,

Mamu tabi bayansu da kallo،

 zaunar da ita tayi saman bed,

while Sanah tana kukan, Halan ta dafata tace " kiyi hak'uri kiyi wanka ki huta kinji,

kai ta d'aga mata, kana Halan ta fita had'i da ja mata k'ofar ta rufe suka koma parlor suna hira,

gaba d'aya hankalin Mamu na kan Sanah,

Allah Allah take su fita taje gareta,

sai da sukayi hira sosai kana fita,

a hankali Mamu ta mik'e ta shiga bedroom d'in Sanah, 

isketa tayi zaune k'asa ta kifa kanta saman bed tana risgar kuka haik'an kamar ranta zai fita,

cikin sanyin jiki ta zauna a kan gadon had'i da sanya hannunta a saman bayan Sanah,

"me ke damunki Sanah....!?


" Tunda na ganki nasan akwai abinda yake damunki،

kanta dake kife ta d'ago ta d'ora saman cinyar Mamu ta rungume ta,

tana cigaba da kukan batare datace komai ba,

hummmm uwa dabance babu wanda ya fuskanci halin da take ciki sai mahaifiya ta,

ta fad'a cikin ranta,

" Sanah...! Mamu ta kira sunanta a hankali,

" duk duniya babu wanda yafi ni cancanta daya san damuwarki da matdalarki sama dani dan ni na haife ki,

cikin kuka Sanah tace " bakomai kawai mutuwar Papu ce ta d'aga min hankali,

shiru Mamu tayi had'i da kafe ta da ido,

tana karantar yanayinta, kafin tace " kin tabbatar babu wani abun bayan wannan....!?


Kanta ta d'aga alamar eh batare datayi magana ba,

" ok to ki tashi kiyi wanka kici abinci,

sai ki kwanta ki huta, "to tace cikin sanyin murya,

har Mamu ta d'ora hannunta akan handle d'in k'ofa zata bud'e,

sai ta juyo tace " mai ya hana ki zuwa lokacin da Khulud ta haihu.....!?


"Abubuwa ne sukayi min yawa a lokacin,

" kin tabbatar babu wata matsalar a tsakanin ku.....!?


Murmushin yak'e tayi tace " haba Mamu ai babu abinda zai shiga tsakanin mu in sha Allah,

"Allah yasa, Mamu tace tana fita, kanta ta mayar kan gadon ta kifa ta cigaba da kuka,

ga muguwar kewar Sultan data dame ta, ashe dama saboda tana ganinshi kullum ne yasa ta d'an samu sauk'i,

hawayen dake zubo mata ta sanya bayan hannunta ta goge kana ta mik'e ta shiga bathroom،

tana cikin shiryawa ta jiyo muryar su Abbu da Dide sun dawo,

cikin murna ta k'arasa shiryawa ta fita,

da gudu ta rungume Dide tana cewa " I missed you so much my Dide,

kanta ya shafa yana murmushi yace " I missed you too dear,

daughter ta girma yanzu saura aure,

Abbu yayi murmushi had'i da cewa " kamar kasan abinda ke raina kenan,

baki ta turo had'i da cewa " aure ni dai ba yanzu ba,

duk sukayi dariya.


Bayan wata d'aya


Kusan kullum sai Abbu da Dide sun yiwa Sanah maganar aure,

wanda hakan yayi masifar d'aga mata hankali dan tasan ba'a tab'a yin aure akan aure,

gashi idan ta kira number Khulud bata shiga kwata-kwata,

Sanah na zaune a parlor tayi tagumi idanta yana kallan k'asa,

Aarib ya shigo ya zauna kusa da ita had'i da dafa ta,

yace " meke damunki sister...!?


Ajiyar zuciya ta sauke had'i da mayar da kallanta gare shi,

" tunda kika dawo naga gaba d'aya kin canja kin zama so silent,

dan Allah meke damunki....!?


Murmushi tayi mishi tace " wallahi su Abbu ne suka saka ni gaba,

" akan me...!?


Ya tambaye ta idanshi kanta,

"maganar aure mana,

" to ke baki san auren ne ko ya....!?


"So nake su d'an k'ara min lokaci،

shiru yayi na d'an wani lokaci

kafin yace " gaskiya nima naji suna yawan yin maganar,

wai daga ni sai ke kad'ai muka rage basu aurar damu ba,

idan suka gaji zasu d'au mataki akan mu,

wata irin muguwar fad'uwa gaban ta yayi,

a tsorace tace " wanne irin mataki zasu d'auka....!?


"Wallahi ban sani ba,

cikin sanyi tace " badai had'a mu aure zasuyi ba ko.....!?


Murmushin bak'in ciki yayi yace " no ai ni ina da wacce nake so,

saboda ke nak'i gabatar da ita gabansu,

dan nasan da zarar na fito da wacce nake so sai buzunki,

numfashi ta fitar da k'arfi kana ta marairaice fuska tace " dan Allah ka basu hak'uri kace su d'an k'ara d'aga mana k'afa,

zatayi magana Mamu ta fito daga part d'in Abbu,

ta zauna kusa dasu tana murmushi tace " me ake shiryawa....!?


Murmushi Aarib yayi yace " kan maganar aure ne dasu Abbu suka matsa mana,

Mamu ta tab'e baki tare da cewa " hummm kudai kuka sani,

dama dai-daita kanku kukayi daya fiye muku sauk'i,

ido Sanah ta zaro tace " dawa zamu dai-dai d'in Mamu....!?


"Ban sani ba, tunda kun rasa mataya daga ke har shi ai gwara ku rufawa kanku asiri,

Mamu tayi maganar idanta kan Aarib,

wanda shi kuma idanshi yana kan Sanah,

" ni dai Allah Mamu kibar ma wannan maganar please,

ki rok'ar mana su Abbu su k'ara mana lokaci dan Allah,

kunfi kusa kuje da kanku ku tambaye shi,

amma ni ba ruwa na.....!

" bari naje na dawo...! Aarib ya fad'a yana mik'ewa,

da sauri Sanah tace " ina zaka....!?


"Kina san wani abu ne...!?


Ya tambaye ta cikin sanyi,

" a'a, please gobe ka kai ni gidan Khulud,

"Allah ya kaimu، yace yana fita,

cike da tsantsar tausayawa Mamu tabi bayanshi da kallo،

Sanah ta kalli Mamu tace " me...!?


Cikin nutsuwa Mamu ta maida idanta kan Sanah kana tace " wai ke dan ubanki baki da hankali da lura ne.....!?


Cikin shagwab'a ta turo baki had'i da cewa " me kuma nayi ......!?


"Wai kina nufin baki san Aarib yana sanki bane.....!?


A razane ta zaro ido kamar zasu fad'o k'asa tace " so fa kika ce Mamu...!?


"Eh...! so، ko so kike kice min baki tab'a lura da zallar muguwar soyayyar da yake yi miki tun kina yarinya ba.....!?


Cikin sanyin jiki da murya Sanah tace " wallahi Mamu ban tab'a sani ba,

" amma ke ko anyi k'idahuma,

ke ko daga yanayin kallan dayake yi miki da wasu abubuwan ai yaci ake kin fahimta.....!,

" wallahi Mamu ban tab'a kawo hakan a raina ba,

bakin k'ofar daya fita tabi da kallo cike da tsantsar tausayawa kamar shi take gani tace " ayya Yaya Aarib,

daga haka bata k'ara yin magana ba,

Mamu tace " saboda ke yak'i fito da matar da aura har yanzu,

"hummmm....! tace had'i da mik'ewa ta shige bedroom d'inta ta rufe k'ofar,

saman bed ta fad'a had'i da sakin kuka,

saboda mugun tausayin Aarib take ji،

dan itama tasan zafin so, da d'acin rabuwa da masoyi.


Bayan kwana biyu Abbu da Dide suka turo a kira musu Aarib da Sanah,

Sanah na kwance saman bed ta fad'a duniyar tunani,

Mamu ta shigo ta sanar mata kiran da Abbu yake yi mata,

cikin fad'uwar gaba ta mik'e ta nufi part d'inshi,

a gefe ta iske Aarib durk'ushe kamar mai neman gafara,

kusa dashi taje ta zauna tana nunnok'ewa bayanshi,

Abbu ya kalle su yace " Aarib bari na fara ta kanka saboda kaine babba kuma namiji,

kanshi ya k'ara duk'arwa, cike da girmamawa,

Abbu yace " da farko dai kasan shekarunka sun isa kayi aure koma nace ka wuce dan duk cikin 'yan uwanka babu babu wanda yakai shekarunka a yanzu bayyi aure ba,

baka buk'atar komai gida, aiki mota kud'i duk Allah ya rufa maka asiri akansu dan haka na baka nan da sati biyu ka fito da matar aure,

cikin girmamawa yace " in sha zan fito da ita,

kana ya mayar da kallanshi ga Sanah yace " a matsayinki na 'ya mace,

nayi miki duk wani abu da zanyi miki,

nayi miki adalci kin gama karatunki,

na fita hakk'ink'i na baki duk wata damarki,

'yar uwarki yanzu ta kusa 4yrs da aure,

dan haka daga ke har shi na baku 2weeks ku fiddo wad'anda kuke so in ba haka ba,

mu zamu san yadda zamuyi akan ku,

" in sha Allah Abbu zamuyi yadda kuke son,

"ku tashi kuje Dide ya basu amsa,

jikinta na kerrrrma ta mik'e suka fita,

jikinta na rawa tace " Yaya bari na d'auko hijab d'ina ka kaini gidan Khulud,

"ok yace batare daya kalle ta ba ya fita harabar gidan.


Tun kafin ya k'arasa yin parking ta bud'e motar ta fito cikin zafin rai ta nufi cikin gidan,

a parlor ta iske ta zaune tana bawa Sultan nono,

tana ganinta tayi saurin mik'ewa fuskarta d'auke da murmushi,

" sannu da zuwa my Sanah dam......!

" dakata ba abinda ya kawo ni kenan ba, 

takardata tazo karb'a dan Abbu sati biyu kawai ya bani na fiddo miji،

ido Khulud ta zaro had'i da cewa " what sati biyu ....!?


" Eh..! kin dai san kuma ba'a aure akan aure ko....!?


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya zamuyi yanzu....?


" Meye mafita ....!?


"Ni ma abinda ya kawo ni gareki kenan,

Khulud karki jefa mu a wuta karki sanya mu a halaka na rok'e ki da girman Allah ki saka Hanash ya sake ni dan Allah،

" bari ya dawo yayi tafiya baya nan kuma a k'alla zayyi 2weeks d'in shima,

idan ya dawo sai ayita ta k'are kawai,

in yaso sai ya sake ki idan aka tashi sai w saka bikin 4months kinga zuwa lokacin kinyi idda,

" Hanash d'in ne yayi tafiya?


"Bayan muna shigowa shi kuma yana fita,

" eh yanzu ai yayi tafiyar, Khulud ta fad'a cikin rashin gaskiya da kame-kame,

"Khulud kenan, ni dai Allah ya sani alkhairi nayi miki amma zaki iya saka min da duk abinda kika yi niyyar,

ta fad'a had'i da ficewa,

tsaye ta iske Aarib yana jiranta dan dama tace mishi ya jira ta ba dad'ewa zatayi ba,

ta shiga ya mayar da ita gida.


Bayan sati biyu


Sosai Sanah tayi muguwar shiga matsananciyar damuwa,

hankalinta yayi mugun tashi dan sau uku Abbu yana jajjada mata idan sati biyu ta cika yasan me zayyi,

tasan kuma yana iya had'a su aure da Aarib,

ita bawai auren take k'i ba, tashin hankalinta d'aya ayi mata aure akan aure,

tana zaune parlor ta rafka uban tagumi,

Aarib ya shigo batare daya kalle ta ba yace " kizo,

a tsorace tace " inji wa.....!?


"Su Abbu،

 " lafiya dai ko Yaya Aarib.... !?


"Kema ai kin san maganar,

" mun shiga uku Yaya Aarib,

" a'a kin shiga uku dai dan ni kam yau zan gabatar musu da wacce nake so,

" Yaya Aarib yau fa kace...!?


"Eh....! dama ke nayiwa kara, so yanzu na gaji nima ina buk'atar auren,

cikin tashin hankali tace " dan Allah Yaya kayi hak'uri ka rufa min asiri,

ka bani last chance, daga wannan karon shikenan,

" kin tabbatar next time zaki gabatar musu da wanda kike son....!?


Da sauri tace " eh Yaya Aarib in sha Allah,

"Ok to muje muji,

tana b'oye a bayanshi suka shiga parlor'n,

Dide yace " ina Sanahr.....!?


D'an matsawa Aarib yayi yace " gata nan,

cikin nutsuwa suka zauna tare da gaidasu suka amsa,

Abbu yace " ina alk'awarin mu daku.....!?


Kanshi ya d'an shafa kana yace " da.....ma....!

"kai dakata ban san rainin hankali, nace ya maganar mu....!?


" Ka bani amsa kai tsaye bana san nuk'e-nuk'e,

kanshi k'asa yace " zan kawo,

" ohhhhh...! Abbu yace yana girgiza kanshi,

kana ya mayar da kallanshi ga Sanah yace " ke fa....!?


Cikin muryar kuka tace " kuyi hak'uri dan Allah,

" keep quite , am I your mate.....!?


"Da kuke neman raina min wayo,

suna k'ok'arin yin magana Abbu yace " to ku tsaya kuji na baku duk wata dama da zan baku,

ku bud'e kunnuwanku ku saurari abinda zan fad'a muku,

yau wacce rana.....!?


Shiru suka kansu duk'e,

cikin fad'a Abbu ya daka musu tsawa yace " ba tambayar ku nake ba.....!?


Bakinsu na rawa suka ce " juma'a,

"wallahi wallahi wallahi na rantse da girman Allah rana ita yau zan d'aura muku aure ko kun kawo ko baku kawo ba,

cikin tashin hankali Sanah ta d'ago tace " Abbu.....!?


"Eh ...! then ku tashi ku bani waje,

da sauri ta mik'e jikinta na rawa tayi harabar gidan kota kan Aarib bata bi ba,

da sauri yabi bayan ta yana kiran sunanta,

baya ta dawo ta warce key d'in motarshi dake hannunshi,

ta bud'e motar ta shiga, ta fige ta da mugun gudu,

bayan motar yabi da kallo daga ganin yadda ta figi motar yasan ta kware sosai a driven,

" dama Sanah ta iya mota, waya koya mata.....!?


Ya tambayi kanshi, cikin ranshi yana addu'ar Allah ya kaita lafiya,

bata iske Khulud a parlor ba dan haka ta danna kai bedroom d'inta kai tsaye,

yadda Khulud ta ganta a rud'e yasata mik'ewa da sauri tace " meke faruwa my Sanah....!?


Cikin matsanancin kuka Sanah tace " Khulud Abbu ya rantse kona kawo miji koban kawo ba,

ranar Friday zai d'aura min aure,

cikin tension Khulud tace " wai yau.....!?


"Next Friday mai zuwa,

cikin matsanancin kuka Sanah ta durk'usa k'asa gaban Khulud,

tace " dan girman Allah ki taimake ni karki kai ni wuta,

kin san mace bata auren maza biyu a lokaci d'aya,

Khulud alkhairi nayi miki karki saka min da sharri,

ki dubi soyayyar dake tsakanin mu da zumuncin dake tsakanin ahalin mu,

dan Allah karki ban kunya ki taimaki rayuwata ki saka Hanash ya sake ni nayi aure dan Allah,

ta fad'a cikin kuka, cikin tsantsar tausayawa Khulud ta sanya hannu ta d'ago Sanah,

itama tana kuka tace " har abada bazan tab'a sakin hannunki ba,

in sha Allah yau zan kawo miki takardarki,

" dan Allah Khulud ki taimake ni ki rufa min asiri, karmu kai kan mu wuta please,

Abbu ya rantse sai ya yi min aure,

" karki damu my Sanah ta fad'a tana goge mata hawaye,

ajiyar zuciya ta sauke danta hango tausayawa acikin kwayar idan Khulud,

kana sukayi sallama ta koma gida.


Tana komawa gida ta fad'a bedroom d'inta tana d'an jin sanyi cikin ranta,

 danta tabbatar Khulud bazata tab'a juya mata baya ba...!,

tana haka bacci mai nauyi ya kwashe ta....!


Bayan kwana biyar


Iya tashin hankali da masifa Sanah ta shige shi, dan kwata-kwata Khulud ta daina d'aukar wayar ta,

wani lokacin ma idan ta kira ta rejecting take yi,

sosai Sanah tayi muguwar rama ta k'ek'ashe kallo d'aya zagayi mata,

kasan tana cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali,

ko bacci bata iya yi, rabonta da abinci ko harta manta,

kullum cikin kuka take,

tana kwance cikin bedroom d'inta Mamu ta shigo tace kizo kinji Abbu,

ta fad'a had'i da ficewa, zaune ta iske Abbu da Aarib a parlor'n,

Abbu ya kalle ta yace " tom lokacin dana d'ibar muku ya kusa dan jibi ne,

kuma kunsan na rantse har yanzu kuna da sauran kwana bibbiyu,

dan babu makawa jibi ne ranar d'aurin aurenku,

ganin babu sarki sai Allah, bata da mafita ko madogara data wuce ta fad'a musu gaskiya kawai،

duk abinda ma zai faru ya faru yafi ayi mata aure akan aure,

matsanancin kuka Sanah ta saka,

had'i da rungume k'afarun Abbu,

kallanta Abbu yayi kana ya kalli Mamu da Aarib,

yace " ke meye haka....!?


Cikin rikitaccen kuka tace " Abbu nayi muku laifi, dan Allah ku yafe min,

nasan saboda hakk'i ku ne yasa Khulud tayi min,

saboda hak'k'in ku bai tab'a bari na na zaune lafiya,

na gama da rayuwa da duniya lafiya,

cikin tashin hankali da rashin fahimta,

Abbu yace " me kike fad'a haka Sanah.....!?


Yayi maganar bakinshi na rawa,

"Eh...! Abbu nayi muku babban laifin dan Allah ku yafe min,

Mamu ido ta kafe ta dashi tana kallanta bata ko blinking,

while gabanta na fad'uwa, 

" Abbu a had'a family meeting yanzu kowa da kowa,

harda family'n su Hanash dashi kanshi Hanash d'in,

a tsorace Abbu yace " meke faruwa?


"Abbu fad'ar babu su aikin banza ne dole sai dasu,

babu yadda Abbu bayyi akan ta fara sanar dasu ba amma tak'i,

kasancewar da safe ne around 12:00am yasa shi kiran Hanash,

yace " yazo da Khulud, Jaddah, Mimmee,

" lafiya Abbu....!?


"Ku dai kuzo yanzu kawai, hankalinshi tashe ya fita daga office ya biya gida ya sanar musu abinda ke faruwa,

ba musu Jaddah da Mimmee suka shirya suka fita,

kana ya biya ya d'auki Khulud,

while acan gidan an had'u a babban parlor kowa da kowa su kawai ake jira,

su Hanash na k'arasowa gidan Khulud tayi murmushi danta gane abinda ke faruwa,

Hanash ya ciro waya ya kira Abbu ya sanar dashi sun k'araso,

Abbu yace " su k'araso baban parlor,

bayan kowa ya zauna, Abbu ya kalli Sanah yace " muna jinki kince faki fad'a sai a gaban kowa,

tana kuka ta d'ago kai ta kalli Khulud tace " I'm so sorry my Khulud,

bani da yadda zanyi ne shiyasa zan fad'a dan aure akan aure haramun me,

cikin rashin fahimta Abbu yace " wake da auren....!?


Sanah tace " NI.....! Abbu, cikin tashin hankali Abbu yace " aure kuma kamar yaya...!?


"Waye mijin......!?


" HANASH......!


Ta bada amsa,

a firgice kowa ya kalli Sanah, shiko Hanash mik'ewa yayi da sauri yace " what aure kuma.....!?


"Eh...! HANASH NI MATARKA CE HALAK MALAK,

..............! kana ta shiga basu labarin abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,

gaba d'aya shiru kowa yayi akayi jugum-jugum,

babu wanda ya iya koda kwakkwaran motsi,

sai can Dide ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Khulud yace " ke haka akayi,

mahaukacin kuka Khulud ta sanya had'i da d'ora hannunta a ka,

" wayyo na shiga Sanah yanzu ni zakiyiwa sharri da k'age....!?


"Wallahi tallahi na rantse da girman Allah,

ban san wannan maganar ba,

bamma tab'a jinta ba, yama za'ayi ace Papu ya shiga cikin wannan shirmen,

ai duk mai hankalin dayaji wannan yasan maganar banza ce,

cike da tsantsar mamaki Sanah ta kalli Khulud tace " my Khulud....!?


"Eh wallahi ban san wannan maganar ba,

ban kuma tab'a jin koda makamanciyarta ba...................!!!!!







MOMYN ZARAH    'YAR BAIWA