RASHIN SANI…

60

by @hauwaausmanjiddarh

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''




6⃣0⃣




"Tunda har ka iya kwanciya da ni ina a matsayin matar wani،

Aryan na d'auka kai daban ne a cikin maza,

nayi zaton kana da tsarkin zuciya dana ruhi,

yanzu wanne irin kallo kake so duniya tayi mana....!?


" Idan mun mutu me zamuje muce da mahaliccin mu....!?


"Da wanne irin suna kake so duniya da al'umma su kira mu....!?


" Shi kanshi cikin dame za'a kira shi shege ko d'an zina....!?


"Meyasa zakayi min haka....!?


" Meyasa kai ma zaka taimaka ka sanya hannu wajen rugujewa da tarwatsa rayuwata....!?


"Meyasa...! Why Aryan...!?


" Bayan na sanar dakai ina da auren wani akai na,

ta fad'a had'i da durk'ushewa k'asa tana kukan mutuwa tamkar ranta zai fita,

cikin sanyin jiki, Sir Moli ya durk'usa k'asa ya d'auki takardar sakamakon data yar,

ya duba yaga cikin 4 months ne,

murmushin bak'in ciki yayi gami da sanya hannu ya goge hawayen dake zubo mishi,

kana ya durk'usa gefenta, ya mik'a mata

cikin rawar murya yace " kina tunanin cikin wata nawa ne....!?


Cikin masifa tace " kamar ya nake tunani...!?


 Bayan gashi nan na gani da idona,

na 1 month ne, murmushi ya k'ara yi gami da girgiza kanshi yace " duba dai,

kawar da kanta gefe tayi ta cigaba da rusgar kukanta,

muryarshi na rawa yace " cikin bana wata d'aya bane,

watan shi hud'u (4 months),

cikin tashin hankali ta tsayar da kukanta cak,

tare da d'ago kanta hannunta na rawa ta fisge result d'in tana dubawa,

" hummm kina tunanin san zuciya ta yakai haka ne?


"Ko kina tunanin zan iya cutar dake...!?


" Babu irin damar daban samu akanki ba, amma ko sau d'aya bana tunanin na tab'a attempting yin sex dake,

Sanah inda ace wani abu dake jikinki nake so ko nake sha'awa da tuni na dad'e da wuce wajen,

ya kamata ace ki cire wannan tunanin daga ranki ni AINAHIN KE D'IN NAKE SO,

ba wani abu da kika mallaka ba,

tun kan ki mallaki komai, nake sanki,

tun kan ki zama mace nake sonki Sanah,

kanta ta dafe had'i da cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,

yanzu wani CIKIN HANASH, nake dashi,

harna wata hud'u, kuka ta saka gami da mik'ewa tsaye tana girgiza kanta,

tana cewa " a'a, bazan tab'a bari haka ta sake faruwa dani ba,

na gwammaci mutuwa ta,

wallahi kashe kaina zanyi Aryan,

na gaji da wannan bak'ar wahalalliyar rayuwar,

ta fad'a tana neman abinda zata kashe kanta dashi,

a matuk'ar haukace,

a tunaninshi bada gaske take yi ba,

dan haka bayyi yunk'urin dakatar da ita ba,

ganin babu wani abu cikin d'akin da zata iya amfani dashi wajen kashe kanta,

yasata ta soma buga kanta jikin bango da k'arfi tana kuka tamkar wacce ta shekara 10 cikin ciwon hauka,

sosai take buga kanta jikin bango,

kafin kace me tajiwa kanta mugun ciwo,

while tasa hannayenta duka biyun tana dukan cikinta da k'arfi,

a razane Sir Moli ya mik'e ya nufe ta,

ya rik'e hannunta gam, hauka Sanah ta soma yi tuburan muraran,

tana ihuuuun kuka had'i da k'ok'arin kwace kanta,

cikin b'acin rai Sir Moli ya zuba mata kyawawan marika gudu biyu a jere,

tassssss...! tassssss....! yace " kinyi hauka ne.....!?


Baya tayi while bata bar dukan cikinta ba,

cikin kuka tace " eh...! na haukace Aryan,

wallahi da irin wannan rayuwar gwara na mutu, na gaji, na gaji Aryan ta fad'a cikin matsanancin kuka,

dai-dai lokacin k'afarta ta zame tayi baya ta fad'i,

ta zub'e k'asa a sume, while jini na zuba daga kanta inda ta jiyawa kanta ciwo,

cikin tashin hankali ya mik'e yayi waje da gudu ya kira Doctor,

tare da nurse's suka shigo,

aka k'ara kwasarta aka shigar emergency room,

sai da aka kwashe kyakkyawar 3hrs kafin Doctors suka samu nasarar ceto rayuwarta,

, duddubata aka sake yi, aka tabbatar cikin jikinta bai zube ba,

kana suka sanya mata k'arin ruwa aka kaita d'akin hutu aka kwantar da ita.


Sir Moli na zaune kan sofa ya zuba mata ido,

yayinda ita har lokacin bata farfad'o ba,

sai lokacin ya samu damar ganin ramarta da bak'in da tayi,

sosai yaji tausayinta yayi masifar kamashi,

dan wannan cikin ma kad'ai ya isa ya k'ara tabbatar mishi rabo bala'i ne,

danya tabbatar rabon cikin yana d'aya daga cikin dalilin mutuwar su Papu,

a hankali Sanah ta motsa tare da yamutsa fuskarta,

ta sanya hannunta mai d'auke da cannula ta dafe goshinta,

cikin rawar jiki Aryan ya mik'e daga inda yake zaune ya nufe ta,

" sannu, kin tashi...!?


Ya fad'a cike da tsantsar tausayawa,

a hankali ta bud'e idonta ta kalleshi,

" ya jikin...!?


Yayi maganar a hankali,

cikin muryar marasa lafiya tace " ban mutu ba ko....!?


Murmushi yayi mata batare daya bata amsa ba,

tace " cikin ya zube....!?


Ido ya zuba mata kawai yana kallanta cike da tsantsar mamaki,

kuka ta saka gami da mik'ewa tana k'ok'arin fisge k'arin ruwan dake hannunta,

" please don't remove it, ya fad'a so calm,

bata kalle shi ba ta cigaba da abinda take niyyar yi ,

cikin zafin rai ya daka mata gigitacciyar tsawa,

" I was said don't remove it ko...!?


A tsorace ta fasa cirewa gami da d'an ja baya,

cikin zafin rai ya tako gaban gadon yace " ko sau d'aya kin tab'a tunanin wanda zai iya jure azabar mutuwa sau dubu akanki.....!?


" Kawai dan Allah ya jarrabe ki sau tak kike san ki mutu....!?


"Akan dalili d'aya kawai zaki mutu...!?


" Amma kin tab'a tuna dalilai dubu daya kamata ki rayu domin su....!?


" Ya kamata ki rayu ko dan wanda aka halucce shi domin ke,

wanda ko sau d'aya bazai tab'a lamunta d'igon hawayenki ba,

wanda kuma bazai tab'a sake hannayenki ba,

tunda kika ga Allah ya barki a raye akwai dalilinshi nayin hakan,

dan komai kika gani a rayuwa akwai dalilin faruwarshi,

Allah bai tab'a yin abu babu dalili,

haka tunda kikaga Allah yasa kin k'ara samun ciki da Hanash to akwai abinda Allah yake nufi da hakan,

a hankali ta share hawayenta kana ta zuba mishi ido cikin nutsuwa,

ya cigaba da magana kina tunanin daga ni har ke ba masu laifi bane....!?


" Ko kina tunanin Allah bazai jarrabe mu, ya hukunta mu akan laifukan mu ba....!?


Cikin rashin fahimta tace " hukunta kuma, akan wad'anne laifikan...!?


"Wato ke har yanzu baki fahimci kin sab'awa Allah ba ko...!?


" Baki fahimci dalilan da yasa Allah yake hukunta ki ba ko...!?


Ido ta zuba mishi batare data ce komai ba,

ya cigaba daga ni harke duk masu laifi ne,

kuma dole mu fuskanci abubuwa da dama a rayuwa,

bari na fara miki ta kai na,

duk abinda ya faru a Roni tsakani na da Seeyah akan idonki ya faru,

Allah Ubangiji da kanshi ya fitata d'an Adam akan ko wacce halitta dake duniya,

mutum yana da matuk'ar daraja da k'ima wanda Allah yayi mishi,

Allah da kanshi yace " na fitata bani Adam a saman kowacce halitta,

na daraja su,

 duk wanda ya wulak'anta d'an Adam,

ko ya muzantashi ya tona mishi asiri shima sai Allah yayi mishi fiye da abinda yayiwa wancan,

sannan Allah da kanshi yayi magana akan mata da rauninsu a cikin suratur Nisa'i,

Allah ya daraja mace, ya bata martaba da k'ima ya kuma mutunta ta,

amma ni na kasance mai izgili da wulak'anci,

na wulak'anta Seeyah dan kawai Allah ya jarrabeta da abinda ba ita ta d'orawa kanta ba,

na k'ask'antar da ita, na wulak'anta ta, ta disgata, na ci mata mutunci,

na tuzartata a bainar jama'a,

bawai ina danganta ko alak'anta abinda ya same mu da ita ba,

a'a ina tuhumar kai na ne,

bawai dan Seeyah tafi wani a wajen Allah ba,

kuma ba dan bata da alak'a dani Allah nazai saka mata ba,

Seeyah 'yar Adam ce, Allah kuma da kanshi yace karya a wulak'anta d'an Adam,

kuma ni nayi, Seeyah macece,

Allah da kanshi yace yana jin tausayayin mata,

ya kuma umarce mu maza damu tausaya musu,

amma ni nak'i bin maganar Allah,

Allah yace mu rufawa d'an Adam asiri ni na tona mata,

Allah yace " muji k'an su, saboda su ni'ima ce a gare mu,

 mu so wad'anda suke son mu,

koda bamu sansu, amma ni duk nak'i yi,

Allah yace addu'ar wanda aka zalitta bata da hijabi ga al'arshe,

direct take shigewa wajen Ubangiji,

addu'ar wanda aka zalunta tafi bakin iyayen kaifi,

na zalunci Seeyah, ta kuma yi min addu'a,

Allah kuma ba azzalumin sarki da bayinsa bane,

duk abinda Allah ya hana muyi akan muzanta mutum ni nayi,

duk yadda Annabi SAW ya horar damu akan mata ni nak'i bi,

ya fad'a mana mata masu raunani ne,

mu so su, su tausaya musu, mu lallab'a su,

amma ni duk nak'i yi, yaya za'ayi Allah bazai jarrabe ni da irin abinda ya jarrabe ta dashi akaina ba....!?


"Ya za'ayi Allah yak'i d'and'ana min irin abinda taji.....!?


" Tamkar mayaudaran masoya ne dole suma tun a duniya sai Allah ya d'and'ana musu irin abinda sukayiwa wata ko wani,

komai darandad'ewa koda akan 'ya'yan cikin su ne,

haka ma mazinata Allah yace duk wanda yayi zina da 'yar wani,

sai anyi da tashi, idan bashi da 'ya sai anyi da k'anwarshi,

idan bashi da k'anwa sai anyi matarshi,

idan bashi da mata sai anyi da mahaifiyarshi,

saboda itama wacce kayi da ita,

matar wani ce, 'yar wani ce, k'anwar wani ce,

haka kuma mahaifiyar wani ce,

wannan fad'ar Allah ce duk abinda kayi sai anyi maka,

shiyasa ake cewa zina jini take bi,

ba lalle sai bakin iyayenka kad'ai yake binka ba,

bakin wanda ka zalunta, ma yana binka,

musamman wanda nan take yakai kukan shi ga Allah,

akwai mutane masu tsarki da daraja a duniya da wajen Allah,

 wad'anda idan sukayi maka baki sai ya bika,

idan sukayi mata addu'a Allah yana saurin amsa addu'arsu,

Allah yace " badan dabbobi da yara k'anana wad'anda basu balaga ba,

da Allah bayyi mana ruwa ya bamu tsirrai ba,

saboda darajar da Allah yayiwa yara idan mutum ya shiga aljanna yara ne zasu tare shi,

kuma dasu zai rayu cikin aljanna,

duk duniya ance babu abinda Annabi yafi so yafi tausayawa kamar yara da mata,

akwai ruwayar data zo idan Annabi SAW yana Sallah, yakai sujjada,

 jikokinshi Hassan da Hussain suka hau bayanshi baya d'agowa har sai sun sauka dan kansu,

to a lokacin danayiwa Seeyah wannan abun yarinya ce k'arama kuma na tabbatar bata labaga ba.


" Sannan ke kuma iyayenki، wad'anda suka so ki, 

suka sauke duk wani nauyi da hakk'in ki da Allah ya d'ora musu,

suka fita hakk'inki suka baki damarki,

ina da yak'in tunda kike a rayuwarki baki tab'a neman wani abu kin rasa ba,

tun daga ci da sha, sutura, ilimi da wajen kwana,

na tabbatar duk sun fita hakk'in ki,

amma ke kika kasa fita hakk'in su guda d'aya tak dake kanki,

kika k'i basu damar aurar dake kamar yadda Allah ya koyar a musulunce,

ya kuma basu dama,

kika zab'i ki faranta ran wata sab'aninsu,

kika butulce musu, bayan sun d'auki yarda da amana sun baki,

kika ci amanarsu kika kuma watsa musu k'asa a ido,

kin san meyasa Khulud tayi miki haka....!?


Ya tambaye ta idanshi kanta,

cikin sanyin jiki ta girgiza mishi kai,

saboda Allah ya d'and'ana miki zafin cin amana,

ya d'and'ana miki zafin wanda ka yarda dashi kake so ya butulce maka,

abinda kikayiwa iyayenki shi Allah yasa Khulud tayi miki,

dan ya koyar dake hankali, da ilimin rayuwa,

kin san wad'anne abubuwa ne Allah baya barin hakk'in su sai anje lahira, yake yin hisabinsu tun a duniya....!?


Kanta ta girgiza mishi, hawaye na zubo mata,

yace " hakk'in iyaye ne na farko,

duk wanda ya shukawa iyayenshi ba dai-dai ba dole tun a duniya sai tsinke abinda ya shuka tasss,

sai zalunci, tun a duniya Allah yake sakawa duk wanda aka zalunta,

sai hakk'in auratayya shima shikanin miji da mata duk wanda ya cuci wani,

tun daga duniya Allah yake yin sakayya,

sai hakk'in maraya, shima tun a duniya Allah yake soma yin hisabinsa,

so kodan gaba karki k'ara yin wasa da hakk'in iyayenki da wad'annan abubuwan dana lissafa miki,

dan Allah baya yafe su, Sanah kin zalunci iyayenki kin cuce su, kin kuma ci amanar su, 

dan haka dole kema kiga ba dai-dai ba a rayuwa,

saboda Allah bai barin hakk'in wani akan wani,

kin san meyasa Allah ya kyale fir'auna har tsayin shekaru arba'in yana tsula tsiyarsa, bai halakar dashi ba....!?


Bai jira amsarta ba ya cigaba ,

saboda biyayyar da yakewa mahaifiyarshi Allah ya kyale shi har tsayin 40yrs, 

yana yin yadda yaso da abinda yaga dama,

duk wanda zakiga ya gagari duniya da abinda ke cikinta,

ya zama kainuwa dashen Allah,

ya zama murucin kan dotse gagara badau,

ki bincika yana tsananin bin iyayenshi,

yana yiwa iyayenshi muguwar biyyya,

idan kuma sun mutu to tabbas ya rabu dasu lafiya,

matuk'ar kina neman dacewa duniya da lahira dole ki gaggauta neman yafiyar iyayenki,

ki kuma yi musu biyayya ki lallab'a ki rabu dasu lafiya,

dan duk abinda kike nema a duniya,

yana wajen Allah, dan shi ke bayarwa,

 amma nema shi ta hanyar hannun iyayenki.


Sosai Sir Moli yayi tayiwa Sanah nasiha, yana nusar da ita kuskuran da suka tafka a rayuwa,

har sai da yaga ta fahimta sosai kana ya kyale ta,

cikin sanyin murya tace " to yanzu ya za'ayi da cikin nan...!?


"Komai da kika gani akwai dalilinshi na faruwa,

wannan wata dama ce da Allah ya bamu wacce zamuyi amfani da ita wajen kawo k'arshen komai,

" ban fahimce ka ba...!?


" Duk da cewa zunubai sukanyi kerere suyi fad'i, ki sani tubalunsu bashi da kwari,

wata rana dole zasu rufta dole suma zasu rufta,

cikin zafin rai tace " na fahimce ka muje kawai ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa,

murmushi yayi idonshi kanta yace " meye na d'aukar zafi haka...!?


 " Zafin rai mak'iyin me shi ne,

domin ya kan saka ka aikata aikin nadama,

haka kuma nasara tana tare da wanda ya nutsu,

dole duk abinda zamuyi sai mun saka hankali da nutsuwa gami da tunani،

dan itama muyi mata kamar yadda tayi mana,

kana ya soma fad'a mata duk tsarin da zasuyi,

ido Sanah ta zuba mishi har ya dasa aya,

tana tsantsar mamakinshi

idonta a kanshi tace " waye kai....!?


"Kamar ya waye ni...!?


" Eh...! tabbas har yanzu akwai sauran abinda ban sani ba dangane da kai ba,

dan wannan zurfin tunanin da basirar,

da low d'in nan da hanyoyin daka kawo gaskiya ba'a banza ka same su ba,

tabbas akwai wani abu a k'asa,

shiru shima yayi batare dayace mata komai ba,

" ka sanar da ni sauran abinda ya rage na sani daga gare ka,

shiru ya sake yi mata baice komai ba,

tace " please kai waye, me kuma kake b'oye min....!?


Kamar bazayyi magana ba, sai kuma yace " ki bari kiji sauk'i a sallame ki,

idan mun koma gida zan fad'a miki duk abinda kike san sani,

zatayi magana yace " please no argument,

shiru tayi mishi na d'an wani lokaci kana tace " amma meyasa lokacin da Doctor yace ina da ciki kayi murna sosai, farin ciki ya bayyana a gare ka.....!?


Murmushi yayi yace " so kike na bari na ya fahimci wani abun.....!?


"Ko baki ji sunan daya kira mu dashi ba....!?


Cikin ranta ta maimaita sunan love birds,

" kinga ai bazan bari ya fahimci wani abun ba ko....!?


"Dan karma yayi tsammanin ko shege ne,

kuma koma dai meye ai d'anki ne, jininki ne,

daga kuma tsatsonki zai fito,

kinga ai dole na soshi, duk mai son uwa yaso 'ya'yanta, 

shi d'a ba'ayi mishi bak'in ciki da mugunta dan ba'a san mai morarshi ba,

ko da ke da Hanash baku raye zan iya rak'e abinda zake haifa koda ace sun kai dubu,

shi kanshi Sultan ina mugun sonshi duk da ban tab'a ganinshi ba,

amma saboda jininki kine har d'okin ganinshi nake yi,

idan zaki haifi duniya ina sonsu zan kuma so su,

idan kuma na samu dama zan iya rik'e su,

sosai kalaman Sir Moli sukayiwa Sanah mugun dad'i,

a hankali ta goge hawayen dake zubo mata,

tace " thank you so much Aryan, ka cika cikekken masoyi,

I'm very sorry, dan Allah kaima ka yafe min dan nasan harda hakk'inka ke d'awainiya dani,

guntun murmushi yayi mata yace " no karki damu baki tab'a yi min abinda naji bazan iya yafe miki ba,

na dad'e da yafe miki duk laufi kan da kikayi min,

har da wanda zakiyi min ma gaba na yafe miki gaba d'aya,

Allah ya yafe mana baki d'ayanmu,

 cikin sanyin jiki ta amsa da " Amin ya Rabbi.


Bayan kwana biyu aka sallami Sanah daga hospital suka koma gida,

suna shiga cikin gidan Sir Moli ya nufi part d'inshi,

cikin sanyi ta kalleshi tace " dan Allah karka k'ara bari na ،

murmushi yayi kana yace " never in sha Allah, yanzu we are together to fight,

so karki damu wanka zanyi sai na dawo dan yau zamu fara plan d'in mu,

murmushi tayi mishi tare da cewa " ka manta baka fad'a min ba fa....!?


"Me kenan..!?


Baki ta d'an turo kana tace " who are you & what you hidden me?


Idonshi kanta yana mamakin mai hali dai baya tab'a fasa halin shi duk halin datake ciki bai hana ta turo bakin ba,

"kayi shiru...!?


" Bari nayi wankan na fito gaba d'aya,

ya fad'a yana shigewa batare daya jira amsarta ba,

itama mik'ewa tayi ta shiga kitchen dan matsananciyar yunwa take ji،

a gaggauce ta dafa jollop rice with dry fish, & vegetables,

ta zuba wanda zataci a plate kana ta zuba sauran cikin food flak,

ta d'auki wanda zataci ta nufi parlor'n,

saman center carpet ta zauna ta soma cin abincin،

bata jima da soma cin abincin ba ya fito,

daga gefe ya zauna kan sofa,  batare daya kalle ta ba yace " gama sai muyi magana,

"ok bari na zubo maka to kaima,

" no karki damu ni ban cin abinci, 

" please kaci wannan ko kad'an ne mana,

" a'a kici kawai,

" bafa ka tab'a cin girki na ba dama,

kuma nasan kana jin yunwa dan banga kaci abinci a hospital ba har muka gama zamanmu,

dan Allah kaci please, ta fad'a kamar zatayi kuka,

kawar da kanshi yayi gefe yana murmushi yace " bani,

da sauri ta mik'e har tana neman fad'uwa,

" please ki rink'a bi a hankali,

bata saurare shi ba, ta shige kitchen,

abincin datake ci ya k'urawa ido,

haka nan yaji yana san cin wanda take ci,

a hankali ya mik'a hannu ya d'auki spoon d'in gami da d'ibar abincin yakai bakinshi,

saboda dad'in abincin sai da ya lumshe ido,

nan take yaji duk wata tsohuwar yunwar dayake ji ta motsa,

idonshi lumshe ya sake d'iba yakai bakinshi,

yakai spoon na uku bakinshi kenan yaji motsinta,

da sauri ya maida spoon d'in ya koma normal yadda yake.


" Na kawo maka nan ko na kai maka kan dinning table....!?


Kasancewar akwai abinci a bakinshi ya hana shi yin magana sai muzurai yake,

tace " na kawo maka nan...!?


"Uhmmm yace, kallanshi tayi cikin rashin fahimta tace " me...!?


"Dara-daran idanuwanshi ya zuba mata batare dayace komai ba,

" hummm tace kana takai tray d'in gabanshi ta taje,

ta koma ta zauna inda take abincin ta ta kalla ganin ba yadda ta barshi yake ba,

yasata yin murmushi had'i da girgiza kanta,

saboda dad'in abincin Sir Moli bai san sanda ya cinye abincin tassssss ba,

sai da ta kwashe kayan takai kitchen kana ta dawo parlor'n ta zauna,

" na gama ina jinka,

batare daya kalle ta ba yace " yanzu ta ina zamu fara.....!?


"Kanka mana,

" me kike san ji gami dani....!?


"Komai ma, ta bashi amsa a tak'aice,

shiru yayi kana yayi d'an gyaran murya yace " I'M ARAYAN RAYYAN MOLI CHAIRMAN OF BAR ASSOCIATION OF NIGERIA,

(SHUGABAN K'UNGIYAR LAUYOYI TA K'ASA BAKI D'AYA),

da sauri Sanah ta mik'e jikinta na rawa tace " what....!?


"Me kake nufi ban gane ba....!?


"Hummm kamar yadda kika ji haka nake nufi,

so ki koma ki zauna muyi magana cikin nutsuwa,

jikinta a sanyaye ta koma ta zauna,

tace " to meya kai ka BUK kuma...!?


"Meye had'in Lawyer da Lecturer....!?


" Sorry ni ba Lecturer bane, ba kuma malami bane a BUK ba,

ba koyarwa nake kamar yadda kika sani ko kika gani ba,

"to me kaje yi....!?


Murmushi yayi kana yace " wani aiki ne ya kai ni,

zatayi magana yayi saurin dakatar da ita,

"please kibar wannan maganar sai zuwa gaba,

mu fara gamawa da abinda ke gabanmu daga baya zan fad'a miki,

ido ta kafe shi dashi na tsayin lokaci kana tace " such is life, never trust anybody in life,

" hummm ko...!?


"Eh...!, 

yace " tom yanzu yaushe zaki ki je gidan Khulud....!?


"Ni koyaushe ma, kai kad'ai kawai nake jira,

" ok so nake muyi duk abinda zamuyi da sauri, if you're ready shiga ki shirya ki fito mu soma tun yau,

ba musu ta mik'e ta shiga bedroom ta d'auko hijab،

maganganun yadda zasu shirya abun suka cigaba da yi har suka k'arasa gidan Khulud,

Sir Moli yayi parking a harabar gidan,

yace " shiga ki fito, ki kuma tabbatar kinyi yadda na saki,

kai ta d'aga mishi cikin sanyin jiki,

kana ta shiga, bata iske ta a parlor ba, dan haka ta d'aga murya tayi sallama da k'arfi,

" a'a muryar wa nake ji haka kamar ta my lovely Sanah....!?


Khulud ta fad'a lokacin datake k'arasowa parlor'n fuskarta d'auke da shu'umin murmushi,

fuska Sanah ta b'ata had'i da mik'ewa Khulud result d'in hospital 

Khulud tace " na miye..!?


"Ki duba ki gani mana,

idanuwan Khulud duk waje tace " me ciki fa....!?


Sanah tace " eh..! ina da ciki na wata hud'u,

sororo Khulud tayi a tsaye ta rasa abunyi,

ta dad'e idonta kan Sanah kana tace " gaskiya ban yarda daku ba,

may be wata mak'ark'ashiyar kuke shirya min,

amma bari ina zuwa ta fad'a tana komawa cikin bedroom da sauri ta shirya ta fito,

batayiwa Sanah magana ba ta rik'e hannunta,

cikin masifa Sanah ta fisge hannunta tace " karki kuma, koda wasa karki kuma gigin tab'a ni,

" sorry muje, Khulud tace,

cikin wani irin wulak'antaccen kallo Sanah tace " ina....!?


"Asibiti zamu je a gwadaki a gaba na,

ta cikin earpiece Bluetooth dake manne a kunnenta Sir Moli yace " ki bita ta karki damu,

ba musu Sanah tayi gaba Khulud tabi bayanta,

murmushi Khulud tayi ganin Sir Moli,

ta kalle shi ido cikin ido ta watsa mishi uwar harara had'i da jan tsoki,

kana ta shiga mota suka tafi,

a k'ofar wani private hospital Khulud tayi parking kana ta fito,

direct office d'in babban Doctor ta nufa,

tayi mishi bayanin abinda take so,

batare da b'ata lokaci ba, aka soma yiwa Sanah test,

kamar yadda Sanah ta fad'awa Khulud haka Doctor ya fad'a mata,

tana da ciki na wata hud'u,

ai Khulud najin da gaske ne, ta rik'o hannun Sanah suka fito waje harabar hospital d'in,

ga mamakin Sanah, sai gani tayi Khulud ta zube k'asa gabanta,

had'i da sanya gigitaccen kuka,

" dan Allah my Sanah kiyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an da zuciya ne suka sanya nayi miki haka,

amma kema kin san ina matuk'ar so da k'aunar ki,

dan Allah ki dawo gidana ki haihuwa kamar yadda mukayi waccan lokacin haihuwar Sultan idan kika haihu sai ki k'ara bani,

ni kuma nayi miki alk'awarin da kaina zan fad'awa kowa gaskiyar al'amari,

zan fad'awa su Abbu ke MATAR HANASH CE kuma duk abinda kika fad'a gaskiya ne,

Sultan ma d'anki ne, murmushi Sanah tayi ganin hak'onsu yana neman cimma ruwa,

tace " na yarda zanyi miki duk abinda kike so,

amma da sharad'i d'aya, 

da sauri Khulud ta k'ara rik'e kafafunta tana daga durk'ushen tace " fad'i kowanne irin sharad'i ne zanyi,

Sanah tace " kin san dai ni matar Hanash ce tunda a gabanki aka d'aura auren mu ko.....!?


Khulud tace " eh...!,

" kin kuma san gaba d'aya shaidu sun mutu ko...!?


"Eh...!,

" kin kuma san Sultan d'ana ne baki shi nayi....!?


"Eh,

" tom ina fuska da voice maker d'in da akayi mana a America...!?


"Suna gida, Khulud ta fad'a da sauri,

" to ina san muje yanzu gidan ki bani su,

da sauri ta mik'e jikinta na rawa tace " muje,

har suka je gidan Khulud na bawa Sanah hak'uri tana rarrashinta,

duk abinda suke yi Sir Moli na jinsu,

duk duniya a halin yanzu babu abinda yafi d'aure mishi kai,

yake kuma bashi mamaki kamar Khulud,

jikin Khulud na kerrrrma ta d'auko fuskar da voice maker ta bawa Sanah,

Sanah tace " ina passport d'ina....!?


Da sauri Khulud ta koma ta d'auko ta bata,

" yauwa yanzu na yarda dake hankali ya kuma kwanta,

karki damu kinji my Khulud bari naje nayiwa Sir Moli wayo،

zuwa dare idan ya fita ni kuma zan fito sai kizo ki d'auke ni,

" to ai ban san gidan naki ba,

" karki damu zanyi miki kwatance ta waya, bari na koma karyayi zargin wani abu,

har bakin mota Khulud ta raka Sanah,

sai nan-nan take yi da ita tana lallab'a ta,

jikinta na rawa ta gaida Sir Moli،

dayake lawyer ne yadda kasan bai san akwai wani abu k'asa ba,

ya sakar mata fuska sosai suka gaisa,

kana yaja motar ya fita, 

" hummmm mutum sai Allah,

mutum mugun icce, Sanah tace cikin mamaki,

batare daya kalle ta ba, yace " ni kaina ina mamakinta wallahi,

amma barta mugu shi yasan makwantar mugu,

maganin biri karan maguzawa,

kamar yadda tayi mana haka zamuyi mata,

zamu nuna mata, mun fita, wayo, ilimi, sanin takan duniya da zamantakewar rayuwa,

bani camera ya fad'a yana kallanta fuskarshi d'auke da silent killer smile,

itama murmushin tayi kana ta ciro 'yar k'aramar cameran dake manne cikin kwayar idanta,

(Eyeball camera) ta mik'a mishi,

idan kaga cameran saika rantse irin kwayar idon nan ce da ake kwalliya da ita.............







MOMYN ZARAH  'YARBAIWA