RASHIN SANI…

61

by @hauwaausmanjiddarh

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''




6⃣1⃣




Fuskarshi d'auke da silent killer smile ya amsa had'i da juya ta a hannunshi،

tace " yanzu duk abinda ya faru ta d'auka....!?


"Tasss ma kuwa, har zuwanku hospital da komai da komai,

babu abinda bata d'auka ba

kinga ta fad'a da bakinta gashi kuma live za'a ganta balle tace k'arya ne ba ita bace ,

da muryar ta akayi amfani,

wannan kad'ai ma ya ishemu shaida,

" yanzu meye next plan d'in mu...!?


D'an shiru yayi kana yace " ai ina ganin wannan ma kad'ai is okey ko...!?


"Ni ma haka nake gani, to amma ya zamuyi dashi family meeting zamu had'a ko me.....!?


" Eh family meeting zamu kira amma bamu bari ta fahimci komai,

dan gobe zaki koma gidanta saboda karta yi zargin wani abun,

ido ta zaro cike da tsoro tace " in koma gidanta kamar yaya....!?


"Daga can nake son ki tafi meeting d'in،

ai intasan wata bata san wata ba,

k'ofar rago zamuyi mata, mu kuma yi mata rik'on talala,

mu had'a mata *GADAR ZARE* itama kamar yadda tayi miki,

muyi mata shigogo ba zurfi, ta yadda ita da kanta zata d'auki wuk'a ta dab'awa kanta,

kallan mamaki tayi mishi cike da rashin fahimta,

ganin irin kallon da take yi mishi ya sashi cewa " hummm kin manta yadda muka tsara kenan....!?


D'an shiru tayi tana tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyi tace " kawai dai ina jin tsoro ne,

"tsoron me bayan gani kina tare da ni tsoran me zaki ji....!?


" Akwai abinda ya rage wanda dashi zan k'ara tabbatarwa da kowa gaskiyar al'amari,

" me kenan....!?


Sanah ta tambaye shi idonta kanshi,

no ki bari kawai idan munje zaki gani,

" to amma wannan shaidar kad'ai bata isa ba....!?


Rolling idonshi yayi yace " to tambai,

"nayi shiru tace tana dariya, wanda rabonta da dariya harta manta a rayuwarta,

dukkaninsu shiru sukayi kowannensu da abinda yake sak'awa cikin ranshi,

Sanah tace " kasan me nake tunani...!?


"A'a yace batare daya kalle ta ba,

" na tabbatar yau ko gobe Khulud zata cewa Hanash tana da ciki,

murmushin gefen baki yayi had'i da cewa " ai abinda nake so kenan,

ta sanar dashi tana da cikin bayan ba haka bane,

hummm shege ai shi yasan makwantar shege,

so nake ita da kanta ta illata kanta,

tayi ihuuuu da kuruwa kana da fallasa kanta,

yadda muka bi da plan d'in mu nasan nan da jibi duk dangi da 'yan uwa zasu san Khulud tana da ciki,

nasan zata fad'a musu kamar yadda tayi wancan,

kinga next idan asiri ya tonu zata gane kuranta,

har suka k'arasa gidan suna magana,

bayan yayi parking babu wanda yayiwa wani magana kowa ya nufi part d'inshi.


Khulud kishingid'e saman sofa yayinda Hanash ke kwance saman sofa 3 sitter,

babu wanda ke kallan d'an uwanshi kowa da abinda yake sak'awa cikin ranshi،

gaba d'aya hankalin Hanash nagan TV yana kallan labaran BBC,

while ita kuma Khulud hankalinta na kan tunanin yadda zatayi da ciki gashi Doctor ya mutu,

bata kuma san inda zata samu kwayar fake pregnancy ba,

" to yanzu ya zanyi, ina zan nufa, ta ina ma zan fara neman tablet d'in....!?


Ta fad'a cikin ranta, a hankali ta sauke ajiyar zuciya،

ta kuma cewa " gaskiya wannan karon akwai babbar matsala fa,

dan kwata-kwata babu mafita balle madogara da madafa,

yanzu idan ma nace mishi ina da ciki ya zanyi a gaba....!?


Cikin sanyin jiki ta gyara kwanciyarta gami da cewa " koma dai meye dole daga yau yanzu na fara pretending zuwa gobe ko jibi muje hospital،

wata sabuwa kuma, ai shi kanshi k'aryar cikin dole sai an had'a baki da Doctor,

OMG...! nan ma akwai matsala,

d'an shiru tayi gami da k'urawa ceiling ido,

ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na biyu,

tace " zanyi k'unar bak'in wake na fad'a kawai komai ta fanjama fanjan,

d'an guntun murmushi tayi tace " ina da makaman aiki a hannu na ai,

tunda ina da kud'i ai an gama dan babu abinda bazasu iya siya min ba,

sai da ta gama tsara komai cikin ranta,

kana ta d'an saci kallan Hanash taga kwata-kwata hankalin shi bai kanta,

" hummm yanzu nan zaka dawo da gaba d'aya hankalin ka da nutsuwarka kai na,

zaka shiga lallab'ani kamar kwai,

tana gama ainayana haka ta mik'e da gudu tayi bathroom,

hannunta rufe da bakinta,

bayanta yabi da kallo ya d'an kalle ta na kamar 2 minutes kana ya mayar da kallanshi ga TV,

ganin bai biyo bayanta ba, yasa Khulud d'aga murya sosai tana kakarin amai،

jin tana amai yasashi mik'ewa da sauri yabi bayanta batare daya kawo komai cikin ranshi ba,

" sannu dama baki jin dad'i ne...!?


Ya fad'a yana dafa bayanta, batayi mishi magana ba ta cigaba da kakarin amanta,

while shi kuma yanata jera mata sannu,

gami da bubbuga bayanta a hankali,

sai da ta gama kana ya tayata ta wanke bakinta ta gyara jikinta,

kana ya tallafe ta sukayi bedroom ya kwantar da ita saman bed,

" sannu...!

" yauwa, 

" dama baki da lafiya ....!?


"Eh..! bana jin dad'i ina yawan kwana da zazzab'i da ciwon kai,

ga yawan amai dan duk abinda naci bai zama sai ya dawo،

cike da tsantsar tausayawa yace " ayya sannu kinji،

amma kinje hospital....!?


"A'a tace tana raurau da ido،

" meyasa....!?


Yace idonshi kanta, 

cikin shagwab'a tace " to ba kai ne baka kula ni ba,

kwata-kwata ka daina kula ni, ka dai na bani kulawa da lokacinka,

na rasa dalili، " kiyi hak'uri ni kai na ban san meke damuna ba,

amma in sha Allah I will try my best,

" tom! please bani tea yunwa nake ji,

ba musu ya fita، tabi bayanshi da kallo had'i da cewa " hummmm ka shigo hannu sai buzunka kuma,

ta fad'a tana dariyar mugunta,

bai jima ba ya dawo, hannunshi d'auke da cup d'in tea ya mik'a mata,

ta amsa tana yayyamutsa fuska,

takai bakinta ta kurb'a, fakar idonshi tayi ta cika bakinta da tea d'in kana ta mik'e tayi bathroom da gudu,

ta soma kakarin amai kamar gaske,

cikin sanyin jiki ya bi bayanta, ya sake wanke mata jiki,

ya d'auko ta cak ya kwantar saman bed,

ya shiga jera mata sannu, 

cikin muryar marasa lafiya tace " mekake tunanin yana damu na.....!?


Cikin rashin fahimta dan harga Allah shi bai kawo komai cikin ranshi ba,

 yace " kamar ya ban gane ba fa...!?


" Yau fa nayi wajen wata hud'u banyi period,

(saboda matsalarta tana dad'ewa wani lokacin batayi period ba),

" ban fahimce ki ba....!?


"Ka sani ko Allah ne zai k'ara yi mana wata kyautar ayiwa Sultan k'ani ko k'anwa,

idanuwanshi ya zaro gaba d'aya waje,

cikin zumud'i da d'oki yace " haba da gaske....!?


"Allah abinda nake tsammani kenan,

amma bari gobe zanje hospital danna tabbatar, tunda kaga cikin Sultan ma fa haka nayi tayi,

" no ai gobe tare dani zamuje hospital d'in,

murmushi tayi kana tace " yanzu kuma sai mu gani ko Sanah zata kuma dawowa tace kai kai mata ciki,

shima wannan cikin nata ne,

simple smile yayi batare daya ce komai ba,

" kuma fa tana iya dawowa tace nata ne ko....!?


"Aiko wallahi danayi mata hauka,

dan rufe ido na zanyi ruf na zage ta zuba mata zunzurutun zallar rashin mutunci wallahi,

tunda na lura bata da hankali kamar 'yar kwaya,

" hummm kawai Hanash yace,

shiru tayi gami da k'ura mishi ido na tsayin lokaci,

" wai Hanash meyasa baka san nayi maka maganar Sanah ne....!?


" Me kika gani....!?


" Na lura duk sanda nayi maka maganar ta saika rink'a basarwa,

kana daddojewa meyasa please...!?


"To tunda kin fahimci haka meyasa kike yi min maganar...!?


Zatayi magana yace " mubar maganar nan please,

muyi abinda ke gaban mu....!

kuka Sultan ne ya katse shi, cikin rawar jiki ya nufi falon da sauri,

tunda nake a duniya ban tab'a ganin abinda Hanash ke bala'in so kamar Sultan ba.


A b'angaren su Mimmee rayuwa na tafiyar musu yadda ya kamata,

Alhamdulillah masha Allah, dan babu abinda suka nema suka rasa,

babu abinda ya canja a gidan, sab'anin wasu gidajen da zaka gani,

da zarar mai gidan ya mutu gidan zai fara tarwatsewa yana lalacewa,

amma su kan Alhamdulillah komai normal,

yayinda daga b'angare d'aya soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Aarib da Wajnah,

har ma sun fara k'ok'arin kai maganar gaban iyaye.


A b'angaren Mamu kuwa sosai ta dage da yiwa Sanah addu'a tana rok'on Allah kan ya taimake ta akan dukkan lamuranta,

" wai ni ko Halan kin kuma komawa gidan Sanah...!?


Mamu ta tambaye ta,

" a'a amma in sha Allah cikin satin nan nake son zuwa,

" yauwa dan Allah kije kiga halin datake ciki ki kuma kwantar mata da hankali,

sannan ki sanar mata ranar Saturday muka gama tsara komai za'a d'auki Sultan aje ayi DNA,

in yaso bayan anyi sai a sanar da family kowa da kowa,

" ba damuwa in sha Allah zanje,

naga kamar Juju ma fa taje har sau biyu,

" kai haba yaushe taje ...!?


" Last week da kuma tun farkon kai ta,

" ayya ai ban sani ba, 

ya kuma kukayi da Aarib d'in....!?


"Shima cewa yayi a fara yin DNA test in yaso daga baya sai a sanar da kowa,

" to Allah ya taimake mu ya kuma rufa amana asiri,

"Amin Mamu.


Da daddare bayan Sanah ta gama girki ta zuba tana ci,

ya shigo, dan tun daga abinda ya faru bai kuma gigin k'in shigowa ba,

a rana sai ya shigo sau hud'u sau biyar,

daga tsaye yace " ni zan kwanta ko kina buk'atar wani abu ne....!?


"A'a, bana buk'atar komai, batare daya kuma cewa komai ba,

ya juya zai fita, da sauri tace " ba zaka ci abinci ba...!?


Batare daya juyo ba, yace " na k'oshi,

" please kaci dan Allah ko kad'an ne,

ni fa na dafa da kai na, da sauri ya juya ya kalle ta tare da cewa " badai ke kike yi girkin da kanki ba....!?


Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa,

" tambayarki nake yi, kin kuma san ban san ina magana ayi min shiru ko...!?


Kanta k'asa tace " eh...! nina yi,

" bana hana ki girki ba....!?


Ya fad'a idonshi kanta, 

"kayi hak'uri tace tana kama kunnuwanta kamar yadda suka saba,

ta bashi dariya sosai, ta kuma tuno mishi da baya, dan duk lokacinsu da d'ayansu yayi haka,

sai d'ayan ya kama hancinshi ya ja,

" ba damuwa amma karki kuma,

abinda yake tunani itama shi take tunani cikin ranta, 

dan tasan da da ne da hancinta zai ja,

katse mata tunani yayi ta hanyar cewa " sai da safe,

da sauri tace " a'a please ka tsaya kaci dan Allah,

Allah idan baka ci ba nima ban ci,

ta fad'a gami da ture abincin daga gabanta,

" hummm rigimammiya, ya fad'a cikin ranshi,

" me kika dafa...!?


Cikin zumud'i tace " tuwon shinkafa da miyar egusi,

ido ya zaro yace " tuwo da cikin....!?


Ya fad'a yadda kasan bai ga wanda take ci ba,

sanin halinshi da rainin hankalinshi yasata turo baki had'i da cewa " amma fa gani,

"Eh..! na gani amma ban san ke kikayi da kanki ba,

wai meye amfanin kukun gidan nan, dan me aka aje shi....!?


" Na fad'a miki duk abinda kike so zai dafa maki,

batayi mishi magana ba sai ido data kafe shi dashi,

tana mamakinshi da halayyarshi,

tunda akace tana da ciki yake lallab'a kamar shi yayi cikin ko cikin nashi ne,

kwata-kwata baya k'aunar yaga tana aiki, 

idan ko yaga tana yi ya rink'a fad'a kenan, wai bata san lafiyarta,

a hankali ta mik'e ta shiga kitchen zobo mishi abincin,

tana shiga yasa yannu ya soma cin nata,

ya d'ebo zai kai bashi dai-dai lokacin ita kuma ta fito,

cak ya tsaya da bakinshi bud'e hannunshi saitin bakin,

" hummm ka kuma kenan!?


Murmushin yak'e yayi yace " da yaushe na tab'a yi balle ace na kuma...!?


"Hummm ranar nan ma fa haka kayi akan jallop rice،

basarwa yayi ya cigaba da cin nata,

sosai Sir Moli yake bala'in kula da ita da cikin jikinta yana lallab'a su tamkar ranshi,

duk wata kulawa da mai ciki ke buk'ata yana bata fiye da haka,

yayinda sosai Sanah ta k'ara ganin kimarshi da darajarshi fiye da koyaushe a rayuwarta.


A ranar kwana Khulud tayi tana shek'a amai yayinda Hanash ya kwana yana tarairayarta,

washe gari tana ganin ya shirya ta soma baccin k'arya dan karya ce mata suje hospital,

shi kuma ganin ta kwana batayi bacci ba,

yanzu ta samu baccin ya hanashi tashinta,

light kiss yayi mata goshi kana ya fita,

sai data tabbatar da ya fita kana ta mik'e ta shirya a gaggauce ta fita,

direct wajen masu buga katin d'aurin aure da buga stickers da calendar taje,

result d'in tsohon cikin Sultan ta bawa mutumin data gani a wajen,

tace " please irin wannan sak nake so ka buga min,

karka banbanta komai, amma banda rubuta ciki na likitan,

" guda nawa kike so Hajiya....!?


D'aya tak nake so,

" kiyi hak'uri bama iya buga guda d'aya kawai,

batare datayi mishi magana ba, 

ta ciro bundle na 500 hundred na 50k ta aje gabanshi,

tace " zakayi akan wannan kud'in ko a'a....!?


Ta fad'a idanta kanshi tana nuna masa kud'in da ido d'aya,

baki ya washe gami da tattare kud'in jikinshi na kerrrrma yace " jira ni nan, bani 5 minutes yanzu zan kawo miki,

murmushi Khulud tayi had'i da cije lips tace " money monger!

bai jima ba ya dawo, jikinshi sai rawa yake ya mik'a mata,

amsa tayi ta duba taga komai yayi sak tamkar su sukayi na farkon ma,

murmushi tayi tana kallanshi tace " kayi karatun boko....!?


Da sauri yace " eh..!

"please zaka iya rubuta min duk abinda ke cikin d'ayan a jikin sabon...!?


" Eh...! zan iya, 

" amma fa ka kula sosai dan ban son a samu matsala,

ka fara rubuta kwanan watan yau,

sannan idan kazo wajen cikin wata hud'u zaka sanya,

" to, yace, kana ya soma, yana yi tana kallo tana fad'a mishi abinda take so,

har ya gama ya bata, godiya tayi mishi while tana murmushin،

shima sosai yayi mata godiya batare daya kula da komai ba,

ya k'ara adana kud'ad'anshi،

sai da ta bari Hanash ya dawo yayi wanka yaci abinci,

kana ta kalle shi tace " albishirinka...!?


"Goro,

" fari ko ja...!?


"Fari fat, ya fad'a yana dariya, 

cikin kissa ta mik'a mishi result d'in,

ido ya zaro ganin tana da ciki harna wata hud'u,

cak ya d'aga ta sama yana juyi da ita cikin parlor,

kafin ya sauke ta yayi sujudul shukru yana mik'a godiyarshi ga Allah,

kana ya shiga kwarara mata godiya sosai kamar itace tayi cikin,

jikin Hanash na rawa ya kira Jaddah da Mimmee ya sanar dasu Khulud nada ciki,

yana kashe wayar ya kira Mamu ma ya sanar da ita, ganin Halan tana bin bayan Sanah,

yasa Khulud cewa " please ka kira Aunty Halan ma ka sanar da ita,

ba musu Hanash ya kira Halan ya sanar da ita,

cikin k'ank'anin lokaci gaba d'aya dangi da 'yan uwa kowa ya d'auka Khulud nada ciki,

" oh..! kinga ikon Allah ko, da har mun cire rai, sai gashi Allah zai bamu biyu a shekara d'aya,

"hummm dama haka Allah yake ikonshi akan wanda yaso a kuma inda yaso....!

washe gari tunda sassafe Khulud ta kira Sanah kan taji ta shiru bata zo ba,

" hello my sweet Sanah ya kike....!?


"Lafiya lau,

" ya Sir Moli..!?


"Yana nan lafiya, Alhamdulillah,

" dama najiki shiru ne, shiyasa nace bari na kira baji ko lafiya, ta fad'a so calm

" la bakomai lafiya k'alau, 

" my sweety Sanah amma shine baki zo ba, baki kuma ban address d'in nazo ba....!?


"Ayya karki damu zan zo in sha Allah,

kwantar da murya tayi tace " heartbeat wallahi harna fad'awa Hanash ina da ciki shi kuma yabi gaba d'aya families ya sanar dasu,

" no karki damu hakan da kukayi shine dai-dai ai,

" please my love ki taimaka min a karo na biyu ki k'ara ceton rayuwata,

dan Allah in sha Allah bazan k'ara butulce miki na juya miki baya ba,

" Allah zanzo karki damu, nan da jibi zanzo in sha Allah,

" yauwa thank you so my Sanah Allah ya barmu tare yabar zumuncin mu har gaban abada,

" hummm amin nagode, batare da Sanah ta jira amsarta ba ta kashe wayar,

Sir Moli dake gefe yace " kinyi recoding...!?


"Eh...nayi,

" yauwa bani shi, shima na d'auka,

wayar ta mik'a mishi tana mik'ewa,

tace " bari nayi sallah.


Bayan kwana biyu


Kullum Khulud cikin zullumi da fad'uwar gaba take kan anya kuwa Sanah zata zo,

yayinda a rana sai ta kira ta kusan sau goma,

" kai nasan ma she most come saboda tana so na da yawa tana kuma san farin ciki na,

nasan tabbas lalle zata zo ma,

tayi maganar tana kai komo cikin bedroom d'inta,

hannunta hard'e a bayanta tana ta faman sintiri,

tana safa da marya had'i da sauke ajiyar zuciya,

" ba dai baki shirya ba...!?


Hanash ya fad'a yana sanya link d'in hannun rigarshi,

" ina zamu kuma...!?


"Ban gane ina zamu ba....!?


" Bayan kin sani na bar office,

"ayya sorry mana dear kasan masu juna biyu,

" please ban san rainin hankali ki fito mu tafi,

ya k'arasa maganar yana d'aukar Sultan,

hijab ta zura tabi bayanshi, a harabar Hard'o family's yayi parking motarshi,

ya fito yana rungume da Sultan,

direct part d'in Mamu suka nufa suka iske Mamu da Halan zaune a parlor,

cikin girmamawa suka durk'usa har k'asa suka gaida ita,

Mamu ta amshi Sultan tana yi mishi wasa,

baki ya washe yana dariya, mahaukaciyar fad'uwa gaban Mamu yayi,

ganin tsananin kamar da Sultan yake yi da Sanah,

ido ta k'ura mishi ta kasa koda k'ifta idanuwanta,

kamar tashi da Sanah ta fito sosai musamman ma yanzu da yayi hak'ori,

kuma cikin ikon Allah yayi irin hak'uran Sanah sak har wushiryarta bai bari ba,

dukkansu sun lura da irin kallan da Mamu keyiwa Sultan,

dan gani take tamkar Sanah take rik'e da ita tana yarinya,

murmushi Halan tayi tace " kema Mamu kinga tsananin kamar Sultan da Sanah ko....!?


Ta fad'a da gayya, 

"hmmm Mamu tace,

Halan tace " wallahi har dariyarshi da hak'oranshi irin na Sanah ne,

jifa harda wushiryarsu iri d'aya,

dai-dai da yatsunsu iri d'aya sak,

kuma shima gashi da dimples,

kallan Sultan Hanash yayi karo na farko dayaji gabanshi yayi mahaukaciyar ranazananniyar fad'uwa,

Halan na niyyar yin magana Khulud tayi saurin cewa " ai jini ne kuma koya yake sayya nuna,

ko kin manta Mamu da Juja 'yan biyu ne uwa d'aya uba d'aya.....!?


Murmushi Halan tayi tana k'ok'arin yin magana Mamu ta kalleta had'i da yi mata alama data bari,

dole tasa Halan yin shiru, jikin Hanash a matuk'ar sanyaye ya mik'e yayi musu sallama,

kana ya fita, ya dad'e zaune cikin mota yana tunaninnika da dama,

dan shi kanshi yau kamar da Sultan yayi mishi da Sanah ta b'aci,

dama sau da dama mutum baya gane abu koya fahimta sai an saka shi a hanya ko an nusar dashi,

idan kuma magana ce sai an jefa mishi maganar a bakinshi yake ganewa,

dan haka maganar da Halan tayi ba k'aramin tasiri tayi ga Hanash da zuciyarshi ba,

cikin sanyin jiki yayiwa motar key yabar harabar gidan,

bai dawo d'aukarta ba sai dare, bayan ya gaisa dasu Abbu ya d'auke ta suka tafi,

ita kanta Khulud ta lura da canji da Hanash ya samu danta fahimci an koma 'yar gidan jiya,

saboda tunda suka shiga cikin motar take ta zuba mishi suturu,

da hirar cikin jikinta amma bai ko kalli inda take ba,

har suka k'arasa gida.


" Nifa gaba d'aya na rud'e na shiga kokwanta akan abun nan,

Mamu ta fad'a cike da confuse,

Halan tace " meyasa Mamu....!?


"Yanzu ga Khulud tace tana da ciki, 

sannan shi Sultan ko makaho ya kalle shi yasan yana tsananin kama da Sanah,

gaba d'aya na rasa wake da gaskiya cikin Sanah da Khulud wallahi,

murmushi Halan tayi had'i da cewa " hummmm wallahi koda ace yanzu Khulud na da ciki،

gaskiya Sultan d'an Sanah ne dan kallo d'aya mutum zayyi mishi ya hango tsagwaron kamarsu,

sai dai idan akwai wani abu a k'asa,

danna tabbatar yanzu ta samu cikin,

amma ni gaskiya Sultan d'an Sanah ne،

cikin sanyin jiki Mamu tace " to koma dai miye Allah ya bayyanar da gaskiya,

" amin ya Allah.


"Sanah yau fa zaki tafi gidan Khulud،

 " na sani ai tun jiya ma na gama shiryawa,

amma dan Allah yaushe za'ayi family meeting d'in.....!?


"Gobe in sha Allah shiyasa nake son ma ki tafi tun yau,

saboda na riga da na gama had'a duk wasu hujjojin da nake buk'a,

" wad'anne hujjoji ne please....!?


"Idan munje can kya gani,

" to baka fad'a min abinda ya kai ka BUK ba,

kanshi ya dafe had'i da cewa " oh my God!

yanzu da abinda ke gaban mu zamu ji ko kuwa...!?


"I'm sorry,

" ki kira ta, yanzu kice mata gaki nan zuwa,

ba musu tayi dialing number Khulud,

ta sanar da ita yanzu zata zo, ai Khulud tana jin haka jikinta ya d'auki rawa yana kerrrrma,

dama ta riga ta gama gyara d'akin da Sanah ke zama,

sosai ta shiga yi mata godiya, suna kashe wayar ta mik'e ta koma aikin tarbar Sanah,

" mik'ewa yayi a hankali yana cewa " muje ko...!,

batayi magana ba ta mik'e ta shiga bedroom ta shirya kana ta fito,

a harabar gidan ta iske shi yana jiranta,

cikin sanyin jiki ta bud'e motar ta shiga,

shi kuma yaja, daga d'an nesa daga gidan Khulud ya tsaya ya sauke ta,

bayan ya k'ara yadda mata karta sake ta nuna mata komai,

a harabar gidan ta iske Khulud tana jiranta, tana hango Sanah ta washe baki had'i da nufarta,

"I love you so much my Sanah,

duk duniya nan babu wanda ya kai mu so da k'aunar junanmu،

 ina kuma k'ara baki hak'uri akan abinda ya faru,

fuskar Sanah a sake tace " haba my Khulud bakomai fa,

aiko tsakanin harshe da hak'ori ana sab'awa,

sosai Khulud ta shiga lallab'a Sanah, tana nan-nan da ita tamkar kwai،

Aryan yana aje Sanah ya nufi Hard'o family's,

yana parking ya hangi Abbu da Dide na shirin fita,

ganinshi ya sasu dakatawa,

cikin nutsuwa da girmamawa ya gaidasu,

kana yace " dan Allah ina neman alfarmarku،

cikin rashin fahimta Dide yace " wacce irin alfarma Aryan....!?


"Dan Allah ina so gobe gaba d'aya Hard'o family's babba da yaro,

maza da mata, harda su Jaddu ma mu had'u a gidan marigayi Alhaji Waseef Papu,

d'an jimmmmm sukayi kana Dide yace " lafiya dai ko.....!?


"Lafiya lau, amma dan Allah kar'a sanar da Khulud da Sanah cewar akwai Family meeting d'in,

a dai sanar da da Hanash cewa yazo da Khulud,

nima zanzo da Sanah in sha Allah,

" ba dai wannan maganar ce zaku kuma taso da ita ba....!?


"A'a wannan wata ce sabuwa daban،

Abbu zai kuma yin magana Dide yace " badamuwa Allah ya kai mu goben zamu zo,

k'asa ya k'ara yi da kanshi yayi musu godiya sosai kana ya tafi,

Abbu yace " Allah yasa dai lafiya,

" amin ya Allah, cikin k'ank'anin lokaci Dide ya sanar da kowa cewar gobe akwai family meeting a gidan Papu,

har shi Hanash d'in Dide ya sanar dashi,

ya kuma fad'a mishi karya sake ya fad'awa Khulud komai,

Sir Moli yana barin gidansu Abbu gidan Papu ya wuce,

yaje ya sanar da Mimmee da Jaddah cewa gobe akwai family meeting a gidan،

suma sai da suka tambaye shi lafiya,

amma yace musu babu komai,

a ranar Mimmee ta saka ma'aikatan gidan suka gyara ko'ina tassss.


WASHE GARI RANAR FAMILY MEETING


" Wai har yanzu baki gama shiryawa bane....!?


"Yi hak'uri Hanash yanzu zan fito,

ni na rasa inda zaka kake ta sauri haka wallahi,

" ni dai ki fito karki b'ata min lokaci nasan ana can ana jiran mu,

" na gama tace tana sanya hijab,

batare dayayi mata magana ba ya kalle ta kana ya juya ya fita,

haka nan Hanash yaji hankalinshi yak'i kwanciya,

gabanshi sai fad'uwa yake yana dukan uku-uku,

gaba d'aya jikinshi yayi mugun yin sanyi, dan ko abinci ya kasa ci,

harta fita sai kuma ta tuno da Sanah,

da sauri ta koma da baya tana ce mishi " ina zuwa nayi mantuwa,

zaune ta iske Sanah bakin bed ta fito daga wanka tana shafa mai jikinta,

"zamu fita ni Hanash amma nasan bazamu dad'e ba,

dan Allah ki kula da kanki kafin indawo kinji ,

murmushi ta sakar mata had'i da cewa " I will, 

Sanah tana tsaye jikin window tana kallansu har suka fita,

da sauri ta kira Sir Moli a waya ta sanar dashi sun fita,

" yauwa ki shirya ki sanya fuskar da voice maker yanzu,

sannan ki saka irin kayan data saka a jikinta kafin ta fito yanzu,

"Ok, idan na shirya na taho ko kai ne zaka zo ka d'auke ni.....!?


" No ki jira ni, ni zanzo d'aukarki,

yanzu haka ma ina yanzu, 

"ok sai ka k'araso, da sauri ta mik'e ta shirya tsaf ta sanya fuskar Khulud ta roba da voice maker,

ta tsaya a gaban mudubi ta kalli kanta fuskarta d'auke da murmushi,

tace " sorry Khulud it's my time now,

ta fad'a da muryar Khulud sak,

tana cikin haka Sir Moli ya kira ta,

yace ta fito ya k'araso, shi kanshi da yaga Sanah yayi mugun tsananin mamaki,

sosai shock da firgici ya kama shi,

dariya tayi tace " mamakin me kake yi.....!?


"Hmmmm bature dai sai a barshi,

ya fad'a yaba barin harabar gidan,

" wallahi daga ni har Khulud lokacin dana fara sawa munyi mugun mamaki،

" su ai tuni cigaba ya dad'e da je musu,

jifa har muryar ta koma tata sak,

" hmmmm yau sai buzun Khulud,

dama ina ita ina shugaban k'ungiyar lauyoyi ta k'asa baki d'aya,

guntun murmushi kawai yayi batare da yayi magana ba,

 babban parlor'n gidan Alhaji Waseef cike yake da mutane,

gaba d'aya Hard'o family's sun hallara mazansu da matansu,

yara da manyansu, haka ma family'n Papu kowa yana zaune a wajen,

Jaddah na hakimce, ana gaggaisawa su Khulud suka shigo,

tare da Hanash, ganin gaba d'aya dangi da 'yan uwa gasa gaban Hanash cigaba da bugawa da tsananin k'arfi,

itako Khulud ko a kanta dan bata kawo komai cikin ranta ba,

tayi tsammanin matsalar wani ce,

cike da girmamawa suka durk'usa suka gaida iyayensu,

kana suka koma gefe suka zauna while gaban Hanash sai k'ara tsananta fad'uwa yake,

basu dad'e da zama ba motar Sir Moli tayi parking a harabar gidan,

Sir Moli ya kalle ta yace " karki ji tsoro ko kunyar kowa kiyi duk abinda ya kamata dan dawo da martabarki،

cikin izza tayi mishi murmushin gefen baki,

yace " oh! na manta fa ashe baki dasu,

yayi maganar yana barin gurin,

tana dariya tabi bayanshi, shine gaba tana biye dashi a baya suka shiga parlor'n,

bakinshi d'auke da sallama,

"ina yini...!?


Sir Moli yace, suna k'ok'arin amsawa Sanah ta shigo sanye da irin kayan jikin Khulud sak,

da kuma fuskarta, cikin irin muryar Khulud sak tace " ina yininku،

cikin tashin hankali, tsoro da firgice,

razana da rud'ewa gaba d'aya mutanen dake parlor'n suka mik'e tsaye,

Jaddah ko saboda tsananin tsoro kasa motsi tayi,

yayinda Hanash yake tsaye kamar an dasa shi idonshi kan Sanah,

wacce zamu kira ta da Khulud,

gaba d'aya parlor'n aka shiga kallan-kallo,

idan aka kalli Khulud sai a juya a kalli Sanah dake photo copy'n Khulud........................!







MOMYN ZARAH   'YARBAIWA