RASHIN SANI…

66

by @hauwaausmanjiddarh

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''




6⃣6⃣




"TAKARDAR SAKI.......!!! nake nufi......!

cikin mahaukaciyar fad'uwa gaba Hanash ya tsaya cak a durk'ushen dayake,

had'i da zuba mata dara-daran idanuwanshi,

 jugum-jugum kowa yayi yana kallan Sanah cike tsantsar mamaki,

da al'ajabin k'iyayyar da Sanah ke yiwa Hanash da har takai haka,

" baka ji me nace bane.....!?


Sanah ta fad'a idonta waje,

cikin rawar murya yace " me....me ki...ke nufi.....!?


"Abinda kaji nace nake nu...!

" ban gane abinda kike nufi ba.....!?


"Takardar saki na nake buk'ata ka bani,

ta fad'a tana ciji hak'oranta,

take duk ilahirin jikinshi ya d'auki rawa da kerrrrma yana tsuma,

cikin tashin hankali ya mik'e tsaye gami da cusa hannunshi cikin sumar kanshi,

tare cije lips d'inshi da k'arfi ya runtse idonshi da k'arfi,

cikin masifa Sanah tace " wai baka ji na ne....!?


Ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa da sauri ta koma ta zauna,

" wayyo Allah na.....! tayi maganar tana dafe kanta, saurin bud'e idonshi yayi tare da  nufarta jikinshi yana rawa,

"karka sake ka k'araso inda nake....!

ta fad'a tana nishi, " wai meye haka kike yi Sanah.....!?


Jin muryar Halan yasata sauri waro idonta tana kallan mutanen dake cikin d'akin,

dan harga Allah kwata-kwata Sanah bata son akwai mutane cikin d'akin ba,

cikin sanyin murya tace " Aunty Halan dama kuna nan....!?


"Dama yaushe zaki san muna ciki marar mutunci.....!!


" Daga haihuwa ko abinda kika haifa baki bari kin gani ba,

baki tambayi lafiyarki da lafiyar yaran ba sai maganar banza,

saboda tsabar rashin mutunci,

Dide ya fad'a yana kallanta, kanta ta sunkuyar k'asa cike da jin kunya,

a hankali ta d'an d'ago kanta ta saci kallan Abbu da Mamu a tare suka watsa mata uwar harara,

wacce ta sata saurin mayar da kanta k'asa,

cikin sanyin murya Mimmee tace " please ku kyale ta haka,

murmushi Halan tayi gami da amsar yaran taje kusa da Sanah ta zauna,

tare da d'ora mata yaran a jikinta,

baki ta turo gami da cewa " Aunty Halan meye haka please.....!?


Ta fad'a cikin shagwab'a, " ban sani ba, Sanah zatayi magana yaran suka sanya kuka lokaci d'aya,

Sanah ta tsuke fuska tace " please kwashe su daga jiki na dan Allah,

" ban gane in kwashe su ba....! idan na kwashe su na kai su ina bayan kina jin suna kuka.....!?


"To ni me zanyi musu dan suna kuka.....!?


" Naji babu abinda zakiyi musu amma ko ganinsu kyayi ko,

a hankali Sanah ta d'aga kanta ta zubawa yaran ido,

daga k'ark'ashin zuciyarta taji so da tsantsar tausayinsu ya kamata,,

a hankali Sultan ya taka gaban ta ya rik'e ta yana murmushi tare da gwarancinshi,

shima ido ta zuba mishi na tsayin lokaci kana ta sauke ajiyar zuciya da k'arfi,

tana bin kowa da kallo ganin Khulud bata nan yasa ta cewa " ina Khulud.....!?


Shiru kowa yayi babu wanda yayi magana,

dan haka ta k'ara cewa " ina Khulud.....!?


"Tana gida, ko kina san ganinta ne....!?


Mimmee ta fad'a, " eh...! dan Allah a taimaka a kawo min ita yanzu please,

d'an kallan Hanash Mimmee tayi taga kwata-kwata baya cikin hayyacinshi,

dan haka ta kira driver tace mishi ya kawo Khulud yanzu,

Mimmee na gama waya Aroos da kakaninsu suka shigo,

cikin fara'a suka d'auki yaran suna yaba kyansu da tsananin kamarsu da Hanash,

a hankali Juju ta mik'e ta zuba abinci a plate ta nufi Sanah tana cewa " kowa ta Baby's yake,

babu wanda yake ta yarinyata,

" zo kici abinci kinji, a baki ma zan bak'i murmushi tayi had'i da cewa " ruwan tea kawai zan sha Juju na,

" idan baki samu kinci abinci ba ta yaya ruwan nono zai zo ki shayar da yaran.....!?


Murmushi Sanah tayi tare da cewa " ai ba yara na bane,

"kamar yaya ban gane ba....!?


Sanah zatayi magana Khulud ta shigo,

cikin matsanancin kuka ta nufi Sanah dake kan gadon marasa lafiya,

ta zube gabanta " please dan Allah ki yafe min my Sanah,

a hankali hawaye suka zubowa Sanah ta mik'awa Khulud hannu tana cewa " ni na dad'e da yafe miki Khulud,

Khulud zatayi magana Sanah tayi saurin sanya hannu ta rufe mata baki,

had'i da cewa " shhhhhhhh! ta kamu hannunta ta zaunar kusa da ita,

kana ta d'auki macen dake ta faman tsotsar hannunta tana wawure-wawure ta mik'awa Khulud,

hannun Khulud na rawa ta amshe ta,

while hawaye na gangaro mata tace "masha Allah mace muka samu,

'yan biyu ne, Sanah ta fad'a tana mik'a mata namijin,

baki Khulud ta kuma washewa tana amsarshi,

ido Sanah ta k'ura mata ganin yadda jikinta yake rawa,

ta kafe yaran da ido hawaye na zubo mata,

cikin sanyin murya Sanah tace " kinga abinda Allah ya kuma baki ko.....!?


Kwata-kwata Khulud bata fahimci maganar Sanah ba, tayi murmushi had'i da cewa " yes....! masu kama da Babansu ba,

kuka namijin ya tsandara yana neman nono,

Khulud tayi dariya tare da mik'awa Sanah shi tace " to goga yana buk'atar tallafi,

hannu Sanah ta d'ora kan hannun Khulud ta turawa Khulud yaron,

fuskarta d'auke da murmushi tace " kin tab'a ganin wani ya shayar da d'an wani......!?


Cikin rashin fahimta Khulud tace " kamar yaya ban gane ba....!?


Murmushi Sanah ta kuma tana kamo hannun Sultan tace " kamar yadda na mallaka miki Sultan duniya da lahira,

haka yanzu ma na mallaka miki su duniya da lahira,

na baki dukansu ukun kyauta halak malak duniya da lahira,

gaba d'ayansu kowa ya zubawa Sanah ido cike da tsantsar mamaki,

" wad'annan yaranki ne my Khulud,

Jaddah tayi wuf tace " uban me zata su.....!?


Batare da Sanah ta kalli inda take ba, tace " da me ta bawa Sultan ya rayu.....!?


Jaddah zatayi magana Sanah ta cigaba da magana " abinda tabawa Sultan yasha ya rayu shi zatawa k'annanshi sushasu rayu,

kana ta mayar da kallanta ga,

tace " gasu nan yaranki ne na baki su kuma ko su kansu yaran bana son su san bake ce kika haifesu ba,

sosai Khulud ta fashe da matsanancin kuka tama rasa me zata cewa Sanah,

" nagode sosai, nagode miki matuk'a da gaske,

Allah ya saka miki da alkhairi Ubangiji ya biyaki da gidan aljanna,

yayi miki kyakkyawan sakamako,

thank you....! thank you so much bani da bakin yi miki godiya,

bani da kalanaman da zanyi amfani dasu wajen gode miki,

kin koyar dani idan mutum yayi maka sharri ka saka mishi da khairan,

kin koyar dani dasurusa da dama a rayuwa ta,

cikin nutsuwa ta mayar da kallanta ga iyayensu da kakaninsu dake tsaye tace " kuyi hak'uri na yanke hukunci batare dana nemi izini daga gare ku ba,

cikin zafin rai Dide ya bud'e baki zayyi magana Abbu yayi saurin dakatar dashi,

tare dayi mishi alamar yayi shiru,

" abinda kika yi dai-dai ne Sanah,

Sanah ta cigaba da magana " ina rok'onku da girman Allah ku yafewa my Khulud,

ku sani ko Allah Ubangijin daya halicce mu,

yaba mu rai da lafiya muna sab'a mishi ya yafe mana,

dukkannin mu nan masu laifi ne, ma'abota kuskure,

kuma mu ma muna son Allah ya yafe mana, Allah da kanshi yace " ان الله مع الصابرين,

Allah yana san mutane masu yafiya da hak'uri, duk lokacin da wani bawa yayi yafiya ga wani bawan,

sai Allah ya yafe mishi manyan zunubanshi,

dan Allah ku yafewa my Khulud ni tayiwa laifi na yafe mata duniya da lahira,

Dide dama kace idan na yafe mata kuma kun yafe mata yafiya ta itace taku,

Sanah ta fad'a cikin kuka,

cikin matsanancin kuka Khulud ta zube k'asa gabansu,

Abbu da Dide da Ganez da Danish tana rikitaccen kuka ta shiga basu hak'uri tana rok'onsu,

" dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min wallahi nayi matuk'ar gane kuskure na, nayi nadama sosai,

na gare rayuwa ba'a cikin gida da ahali ba, ba k'aramin bala'i da masifa bane,

a hankali Ganez ya d'agota gami da rungume ta yana shafa kanta yace " mun yafe miki duniya da lahira,

sosai ta kuma sanya kuka yana shafa kanta,

shima Danish ya rungume ta yana murmushi yace " haka ake so dama mutum yayi laifi ya kuma gane kuskurenshi,

a hankali ta zame jikinta ta koma jikin Abbu ta rungume shi,

" yi shiru kinji daughter mun yafe miki Sanah ma har tayi tunanin sanin abinda ya kamata balle mu.....!?


Cikin kuka sosai ta kuma k'ank'ame Abbu, kanta ya shiga shafawa hawaye na k'ok'arin zubo mishi,

ta dad'e jikin Abbu kana ta zame jikinta ta nufi Dide ta tsaya gabanshi,

kafad'arshi Abbu ya dafa gami da d'aga mishi kai,

murmushi Dide yayi had'i da wara mata hannunshi ta fad'a jikinshi tana kuka,

ya mayar hannu ya rungume ta,

" daina kuka na yafe miki you're among us now,

murmushi tayi tana goge hawayenta kana ta nufi gaban Mamu,

tana dariya ta rungume ta, haka ma Juju ta yafe mata, d'ayan bayan d'aya sai da tabi kowa ya yafe mata, har Mimmee da su zohal,

Jaddah ko sama-sama ta amsa mata kawai,

direct wajen Hanash taje daga k'arshe tana k'ok'arin zubewa gabanshi,

yayi saurin tareta had'i da girgiza mata kanshi yana murmushi,

yace " bakiyi min komai ba, nasan duk kinyi hakan ne danni da kuma sanya ni ciki farin ciki,

nagode sosai saboda KIN CIKA MIN BABBAN BURI NA....!,

kin bani farin cikin dana dad'e da fidda ran samun shi,

kin mayar min da mafarkina ya zama gaskiya, thank you so much for making my heart shinning,

cikin rashin fahimta ta kalle shi tace " me ban gane ba.....!?


Murmushi yayi gami da kawar da maganar yace " nima na yafe miki,

cikin murna tayi niyyar fad'awa jikinshi,

ido ya zaro gami dayi mata alamar da mutane cike da jin kunya ta kalli bayanta,

gaban Sanah ta koma ta rik'e hannayenta cikin nata suna fuskantar juna,

tace " me yasa kike damuwa da damuwar azzalumai iri na, masu san kansu.......!?


Murmushi Sanah tayi tare da cewa " ko dabba idan aka cutar da ita kuka take yi,

mutum na asali shine wanda idan aka cutar da d'an adam yake kuka,

doka ce ta zubin rayuwa in kayi za'ayi maka, abinda yake k'asa wataran yakanyi sama, yadda akayi dare haka gari yake wayewa,

rungume ta Khulud tayi tana kuka,

kowa ya shiga cikin farin ciki banda Sanah da yak'e kawai take,

amma burinta bai wuce su keb'e da Hanash ya sake ta,

macen na hannun Dide ya kalli Hanash yace " ya kamata ayi musu hud'uba ko....!?


"Eh...! Hanash yace yana shafa kanshi,

Dide yace " wanne suna za'a saka mata....!?


Kai tsaye Hanash yace " a mayar mata da sunan mahaifiyarta,

Dide yace " wa....!?


"SANAH....! ya bashi amsa, " ba ni ce mahaifiyarta ba, Khulud ce mahaifiyarta,

Sanah ta bashi amsa, batare data kalle shi,

Dide bayyi magana ba yayi mata hud'uba da sunan Jaddah,

ya d'ago kanshi ya kalli Hanash yace " na sanya mata sunan Jaddah HAJAARAH,

baki Jaddah ta washe cike da murna tace " Alhamdulillah na samu takwara,

Khulud tace " a rink'a kiranta da HAJEER...!,

Abbu ya kalli Hanash yace " to shi wannan wanne sunan za'a saka mishi.....!?


Hanash yace " a saka mishi sunan Dide,

sosai Abbu yaji dad'i dan dama haka yayi niyyar sawa yaron sai kuma ya tambayi ubanshi ko yana da zab'inshi,

Abbu yayi mishi hud'uba da RAWAN....!?

Hanash yace " a rink'a kiranshi da ZOLTAN,

cikin farin cikin kowa yabar hospital d'in,

Mimmee da Jaddah Khulud suka tafi gida da yaran danyi musu wanka,

Halan ce kad'ai ta zauna sai Hanash,

ai Sanah tana ganin kowa ya fita ta sake kallan Hanash tace " baka bani ba,

ya yayi tamkar bai san abinda take magana akai ba yace " me....!?


Kai tsaye tace " takardar saki,

yace " saki kuma wanne iri....!?


"Sakin aure nake nufi, dan Allah Hanash ka sake ni, duk abinda zanyi muku nayi muku,

nima ku barni na samu salama da farin ciki cikin duniya ta dan Allah,

" amma kin san ai Allah baya san sakin aure ko....!?


"Eh...! amma ai ba'a haramta ba, dan haka ka sake ni yanzu,

murmushi yayi mai sauti yace " kina tunanin akwai saki ko mutuwar aure tsakanin mu....!?


Kallanshi take yi cike da mamaki tace " kamar yaya ban gane ba....!?


" Idan ma kina tunanin ni Hanash zan sake ki to tun wuri ma ki janye wannan tunanin daga cikin ranki,

auren mu ni da ke mutu ka rana ne takalmin kaza,

ko auren kowa zai mutu a duniya banda namu,

cikin matsanancin kuka tace " wallahi sai ka sake ni ban sonka ban k'aunarka ban kuma zama dakai,

ni ARYAN....! nake so, dashi kuma zan rayu,

danne abinda ya taso mishi yayi,

yayi murmushi yace " wallahi kome za'ayi bazan tab'a iya sakin ki ba Sanah,

" wallahi sai ka sake ni tunda dai ba'a aure dole,

ganin ta tada hankalinta sosai yasashi fita.



Bayan Sati Uku



Sosai Sanah ta saka Hanash gaba da bala'i kan sayya sake ta, kullum tana cikin kuka ko abinci bata iya ci,

ganin haka yasa ya daina barin su keb'e daga shi sai ita,

kwata-kwata ba'ayi taron suna ba, saboda su Abbu sun hana,

walima kawai akayi cikin gidansu,

kasancewar ta warke sumul yasa Doctor ya rubuta musu sallama yau,

koda Hanash zai zo d'aukarta k'in zuwa shi kad'ai yayi sai da ya sako Jaddah gaba,

kana yazo ya d'auke ta, fuskar nan tata a tsuke kamar an saukar mata da bala'i,

dakyar Jaddah ta sata ta shiga gaban mota,

ganin sun d'auki hanyar gidan Mimmee yasata kallanshi tace " ina zaka kai ni....!?


"Gidanki mana....!

" ina ne kuma gida na, ni ai bani da wani gida daya wuce gidan iyayen na,

dan baka can zaka kaini, murmushi yace " har gidan mijinki.....!?


Ji tayi kamar ya watsa mata wuta amma kasancewar da Jaddah tayi shiru dole,

koda suka isa gida k'in fitowa daga cikin motar tayi,

Jaddah batayi musu magana ba ta fita tayi shigewarta cikin gida ta barsu nan,

cikin sanyin murya da rarrashi Hanash yace " dan Allah tashi mu shiga cikin gida,

a zafafe tace " dan girman Allah Hanash ka sake ni wallahi ban sanka,

duk abinda zanyi muku nayi muku,

" wallahi ban iya rabuwa dake Sanah ko da za'a d'ora bakin bingina akai na,

wallahi bazan iya sakin ki ba, 

" nace bana sanka ko.....!?


"Ni kuma INA MUTUWAR SANKI fiye da yadda nake san rayuwa ta,

wallahi numfashi na bai tab'a fita batare da tunaninki ba,

KE CE HASKE NA, KECE MACEN DANAKE SO a rayuwa ta,

ke kad'ai na tab'a so Sanah bayan ke ban tab'a sanin yadda so yake ba,

cike da tsantsar mamaki da al'ajabi Sanah ke kallan Hanash bakinta bud'e,

ta jima tana kallanshi ido cikin ido kana tayi murmushi gami da cewa,

" hummmm NAMIJI..... kenan maza sai a barku, yawancinku kunya bata ishe ku ba,

yau ni Sanah kake cewa kana so Hanash.....!?


" Ni kake cewa baka tab'a san wata mace bayan ni ba....!?


"Har ka manta duk abubuwan da suka faru a baya....!?


" Ka manta yadda ka rink'a kira na KARUWA.....! MAZINACIYA FASIK'A.....!?


"Ka manta maganganun daka rink'a jifa na dasu......!?


" Yanzu dayake ka tabbatar ni ba karuwar bace, kasan ka karb'i budurci na shine zaka lallab'o kayi min dad'in baki.....!?


"Ka gaggaya min maganganu akan k'addarar Khulud ka manta cewar Allah ne meyin yadda yaso,

yanzu dana haifa na baku na biya ku shine zaka ce kana so na....!?


" Ba haka bane Sanah Wallahi ina san ki, kece rayuwata,

ke kad'ai na tab'a so bayan ke ban tab'a son wata 'ya mace ba,

dan Allah ki tausaya min please,

Hanash ya fad'a hawaye na zubo mishi,

kanta ta shiga girgizawa tare da cewa " k'arya kake yi Hanash,

ba gaskiya kake fad'a ba kana fad'ar san ranka ne kawai,

ni yanzu bani da sauran alak'a dakai duk wani bashi na biya ku,

na baku yara har uku na kuma baka abu mafi muhimmanci ga rayuwar mace,

budurci na, cikin sanyin murya yace " Allah da gaske nake miki,

cikin masifa tace " k'arya kake wallahi na riga da na biya ku,

shine zaka lallab'a kace kana so na ko kunya baka ji ba....!?


"Bayan ka tabbatar zargin da kake yi a kaina ba haka yake ba,

to tallahi ko zaka mutu sai ka sake sani,

dan ban sanka ina da wanda nake so dashi kad'ai zan rayu,

tana kaiwa nan ta bud'e motar ta fita,

sai da Hanash ya tsaya yaci kuka ya godewa Allah kana ya fita.


Bayan sati d'aya


" Wallahi Allah sai ka sake ni Hanash,

Sanah ta fad'a cikin kuka tana rik'e da rigar Hanash,

murmushi yayi had'i da rausaya kanshi,

yace " ni da ke mutu ka raba takalmin kaza,

auren mu auren zobe ne ba saki ba yaji har abada, ko mutuwa nayi bazaki aure wani namiji ba,

ya fad'a gami da kashe mata ido yana dariya,

" Allah sai ka sake ni, tunda ba'a aure dole,

ni ban sanka ban k'aunarka ban kuma zama dakai,

wannan ma k'addara da rabon 'ya'ya ne,

" to yanzu ma kika sani ko da wasu rabon 'ya'yan kinga idan na kuma d'ura miki cikin sai ki haifu min 'yan uku,

yayi maganar yana rungumo ta, 

gami da goga sajenshi saman fuskarta yace " kwanta na kuma buga miki iska,

da k'arfi ta hankad'a shi baya tace " wallahi danayi zaman aure tare dakai na gwammaci mutuwa ta,

ido ya kashe mata yana murmushi yace " MUTU KA RABA....! SANAH & HANASH for ever & ever,

yawu ta tofar a k'asa tace " Allah ya tsare ni da zama dakai,

" ni kuma Allah ya tabbatar min zama dake har gaban abada,

" ai na biya ku komai da kuke bina haka zargin da kake min shima na cire shi,

dan haka sai ka sake ni.


Sosai Sanah ta sanya Hanash a gaba ta kunna mishi wutar bala'i kan sai ya sake ta,

hakan ya haifar mishi da muguwar rama sosai ya fita daga hayyacinshi,

lokaci d'aya ya canja ya shiga mawuyacin hali duk tsananin k'iyayyar ka dashi idan ka ganshi sai ka tausaya mishi,

dan ko abinci bai iya ci kullum yana cikin rok'o da rarrashinta kan ta taimake shi tayi hak'uri,

amma fafur tak'i ta zubawa idonta toka ta buga k'asa tace sai ya sake ta,

itama sosai ta lalace ta rame ta koje,

yana k'ok'arin fita tayi saurin shan gabanshi had'i da kama k'ugunta,

cikin rarrashi tana kuka tace " dan girman Allah ka tausaya min ka tausayawa rayuwa ta,

Hanash idan har soyayar da kake ik'irarin kana yi min da gaske ne ai a soyayya akwai sadaukarwa,

kuma zaka so abinda nake so please ka sauwak'e min,

" wallahi ban iya sakin ki koda za'a sanya gaba na gabas a yanka,

sadaukarwa kuma nayi ta farko ban iya sadaukarwa ta biyu,

nima ya kamata a tausaya min,

" wallahi ina sanki sosai dan Allah ki zauna dani kodan yaran mu please,

ya fad'a hawaye na gangaro mishi,

matsanancin kuka Sanah ta sanya tana cewa " wallahi ban iyawa, nafi son Aryan akan su,

nafi son na rayu dashi fiye dasu, shine kad'ai farin ciki na dan Allah ka tausayawa rayuwa ta,

wallahi ina sonshi dayawa idan kak'i saki na mutuwa zanyi,

a hankali ya zub'e k'asa bisa gwiwoyinshi a gabanta gami da rik'o hannayenta,

cikin matsanancin kuka Hanash yace " wallahi nima idan kika rabu dani mutuwa zanyi,

kece kad'ai wacce nake so kece rayuwa ta,

dan Allah ki zauna dani karki rabu dani,

" bazan iyaba Hanash ban iyawa nima shi nake so shine rayuwa ta,

dashi kad'ai zan rayu nasa mu farin ci please,

sosai Hanash yake kuka wiwi yana rok'anta tayi hak'uri kan ta zauna amma ina tayi nisa.


Wasa-wasa magana ta zama babba tun Sanah na b'oyewa tana yiwa su Mimmee da Jaddah kara,

batayi mishi magana gabansu har ta gaji ta fara k'ok'arin fito da maganar,

ta kunna mishi wutar masifa ta sanya shi gaba da zalzala,

kullum cikin zazzaga mishi bala'i take, yayinda shi kuma yake ta rok'onta yana bata hak'uri gami da lallab'a ta,

cikin nutsuwa ta shiga parlor'n Mimmee ta iske Khulud zaune rungume da Hajeer tana bata nono,

 (dan tun ranar da aka haife su Doctor ya bata magani tasha ruwan nono yazo)

Jaddah na gefe, cikin matsanancin kuka Sanah ta zube gaban Mimmee,

a rud'e Mimmee ta d'ago ta tana cewa " lafiya.....!?


Kukan ta cigaba dayi batare datace komai ba,

Jaddah dake rik'e da Zotal tace " subhanallah meke damunki.....!?


Cikin kuka Sanah tace " dan girman Allah Mimmee ki sanya Hanash ya sake ni,

dan Allah wallahi ban iya zama dashi na had'a kishi da my Khulud,

mu had'a miji d'aya dan Allah Mimmee ki taimaka ki ceci rayuwa ta ki saka shi ya sake ni,

ta b'oye mata cewar bata sanshi saboda ko mutuwa tana tsoran idon mahaifi,

duk rashin kunyarta bazata iya kallan tsabar idon Mimmee tace bata san Hanash ba,

Mimmee ta kalli Jaddah suka had'a ido,

Mimmee na k'ok'arin yin magana Jaddah tayi saurin cewa " wani abun yayi miki.....!?


Cikin kuka tace " a'a ni dai kawai ban zama dashi nayi kishi da Khulud,

" wallahi koda zan rasa rai na ban tab'a sakinki Sanah,

Hanash ya fad'a yana shigowa,

cikin masifa da tsiwa ta mik'e tsaye tace " wallahi nima koda zan rasa rai na ban zama dakai sai ka sake ni,

" ina sanki Sanah ko shi wanda kike son ina da tabbacin bai kai ni sanki ba,

balle ya fi ni, shi meya sani akan sanki....!?


"Ni da na bada rayuwata, farin ciki na, da komai nawa dominki,

wallahi duk duniya babu wani d'a namiji da zai bugi k'irji yace ya fini sanki,

" hummmm namiji kenan yanzu kai har zaka bud'i baki kace kana so na,

har zakayi tak'ama da kambabar kana so....!?


"Kana son nawa ka rink'a ci min mutunci kana tuzarta ni....!?


" Duk masoyi na hak'ik'a bai tab'a yiwa masoyiyarshi abinda kayi min,

" ina sanki fiye da komai Sanah,

ina sanki fiye da rayuwata dan haka kima daina kawo maganar saki tsakanin mu,

dan babu shi a auren mu,

takawa tayi har zuwa gabanshi ta yadda suna jiyo numfashin juna,

ta jefa idonta cikin nashi, tana kallanshi tarrrr,

tace " yanzu dayake ka tabbatar ni fa mazinaciya bace ko.....!?


"Saboda na haihu dakai na baka yara shiyasa kake so na...!?


" Saboda ha had'a jiki dani ka samu abinda kake so, ka d'and'ani zuma ta,

ina kuma biya maka buk'atarka......!


Take gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka fito sukayi rad'o-rad'o,

idanuwanshi suka yi jajir kamar gauta,

cikin huci ya rik'e gashin kanta yace " turrrr dake da tunaninki daya saki tsammanin jiki ko sex yasa nake sanki,

Allah ya wadaran wannan tunanin naki dake baki hakan,

sakinta yayi, ya ja baya a fusace ya daki bango kana ya tako zuwa gabanta da sauri,

yana huci yace " baki gane waye ni ba ko....!?


" Kin manta ni ko....!?


"Ni kin san waye ni....!?


" TUN KAFIN KI ZAMA MACE KI MALLAKI KOMAI NAKE SANKI.....!

a kid'ime Khulud ta mik'e tsaye,

har Hajeer na neman sub'uce mata

" TUN KAFIN KI MALLAKI ABINDA KIKE TUNANIN A KANSHI NAKE SANKI NA FARA SANKI,

TUN KINA YARINYA K'ARAMA NAKE D'AWAINIYA DA FAMA DA SANKI,

"Ko shi ARYAN dayake tak'amar yana sanki bayyi miki halacci da rik'e miki alk'awari da amanar da nayi ba,

idonshi kan Sanah ya nuna Khulud yace " ITA KANTA NA AURE TA NE DOMIN KE DA CIKA MIKI ALK'AWARINKI,

son da nake yi miki yasa na auri Khulud amma ba wai dan ina santa ba,

wallahi Allah ban tab'a jin koda d'igo da kwayar zarrar son Khulud cikin rai na,

a kanki na aure ta, ke nayiwa sacrificed na soyayya ta, zuciya ta da son danake yi miki,

saboda ke nayi hak'urin zama da KHULUD duk da ke kin san wacece ita akan sex,

saboda na cika miki alk'awari nake bata kulawa 100% nake bata duk abinda take nema take so,

saboda soyayyar da nake yi miki yasa ban tab'a bari Khulud ta fahimci ban san ta ba,

SABODA KE SANAH NAYI KOMAI,

AKANKI NA WATSAR DA RAYUWATA,

ya fad'a da k'arfi yana juya mata baya,

cikin tashin hankali Khulud take kallan Hanash da Sanah,

yayinda itama Sanah Hanash d'in take kallo kukanta ya tsaya cak,

juyowa yayi hawaye na gangaro mishi yace " baki gane ni ba....!?


" Har yanzu baki gane waye ni ba.....!?


Da sauri Mimmee ta mik'e tsaye tace " a'a Hanash please kabar maganar nan karka sake ka fad'a dan fad'ar yana iya haifar da wani abun,

"kiyi hak'uri Mimmee yau kan zan fad'a dan nagaji da gorin da Sanah ke yi min,

ko ba komai ta kalle ni da mutunci amatsayin wanda ya sadaukar da komai dominta,

kana ya juya ya mayar da kallanshi ga Sanah yace " bake da an tashi magana kice saboda kin ban budurcinki da yara bane yasa nake sanki ba....!?


"To ni rayuwata na baki bayan bama kisan ina yi ba, baki san ina haukan sonki ba,

lokacin baki da komai kina k'aramar yarinya,

wallahi nasan nafi ARYAN sanki, na fishi sanin k'ima da mutuncinki,

na fishi sanin darajar soyayyarki,

shi mema ya sani akanki.....!?


" Me ya sani akan so da tsantsar soyayyarki....!?


Ido Sanah da Khulud suka k'ura mishi tana k'ok'arin tuno waye shi...!,

 sai yanzu suka fahimci sun sanshi since before,

cikin rawar murya Khulud da Sanah suka had'a baki wajen cewa " waye kai......!?


Murmushin bak'in ciki da takaici yayi kana yace " NI NE WANDA KIKA...........! KINA YARINKA A LOKACIN BAZAKI WUCE 9 to 10YRS BA........................!






MOMYN ZARAH    'YARBAIWA