22
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
22
Sannu a hankali wata irin muguwar shak'uwa ta rink'a shiga tsakanin Teemah da Zaid, sosai suka saba ta saki jiki dashi, ta yadda kowannen su baya jin dad'i idan baya tare da junansu, har yawo suke zuwa tare, sune shan ice cream, kallon films zuwa garden ko park, sosai suka shak'u da junan su fiye da tunanin mai karatu, shi dai ya kasa fitowa ya fadawaTeemah yana santa.
Zaid kwance akan gado sai juyi yake yana waya da Teemah hankali kwance, Mukhtar yana gefe ya zuba masa ido yana kallon ikon Allah har Zaid ya gama wayar, a hankali Mukhtar ya kalle shi yace " why not bazaka fito ka sanar da ita kana santa ba? "shiru Zaid yayi ya kasa cewa komai, "kasan dai hausawa na cewa abari ya huce shike kawo rabon wani ko? murmushi Zaid yayi yace " babu ma rabon wani anan sai nawa, "murmushi Mukhtar yayi yace " Allah yasa friend koni ina fatan haka, amma wanne aiki take? "she is jobless cewar Zaid "ok to yanzu wanne plans ne dakai akanta?
"I employed her as my secretary, "what! yaushe? "gobe ma zan tabbatar da ita a office, sosai Mukhtar yayi murna da aikin da Zaid ya bawa Teemah dan koba komai yayi taimako, washe gari around 9:00am Zaid ya gabatar da Teemah a company dinmu a matsayin secretary d'insa, a hankali ya dafa kafad'ar Mukhtar yace " and dis is my dear friend and our company's legal advisor Mukhtar, he is my best friend, murmushi Teemah da Mukhtar sukayi ma junansu tace " sannu abokin mu "yawwa amaryar mu, tun daga ranar Teemah ta fara aiki a company din Zaid, a office d'in ta same shi tana yi masa maganar akan office da kasuwanci sanye take da doguwar riyar materials mai shegen kyau ya kuma karb'i jikinta d'as, tana zaune akan kujerar dake fuskantar shi kanta yana kallon system ta shiga yi mishi bayani.
" Thought our marketing plan, we are planning toto set up a central customer service cell, to help support investor who sell their products thought us, we will also have a customer service support website, ok and ta d'ago taga mai yake dan jin baice komai ba, duk maganar da take Zaid bai fahimtar komai dan gaba d'aya bai ma san inda kansa yake ba, ya zabga tagumi hannu biyu ya k'ura mata ido sai sakin murmushi yake, kallansa tayi cike da mamaki tace " sir! sir!! shiru bai ma san tana yi ba idonsa na kanta ya kafe ta dasu, table d'in dake gabansu ta d'an buga a hankali ta kuma cewa " sir firgigit Zaid yayi ya dawo daga duniyar tunani ya sauke ajiyar zuciya da k'arfi ya fara kame-kame " uhn ummm marketing plans d estimated demand 4 higher paper...
Kanta da sunkuyar k'asa tana kanne dariyar dake shirin kufce mata, a hankali ta mik'e tace " mayi magana latter bata jira amsar saba tafita, yabi bayanta da kallo, bayan antashi daga office wajen 8:00pm ya shigo office d'inta ya iske ta zaune sai faman aiki take kallon ta yayi yace "you still there? kai ta d'ago ta kalle shi tana murmushi dan bama tasan ya shigo ba tace " you haven't either sir, murmushi yayi yace " for me home & office mean d same thing, ido kawai ta zuba masa bata ce komai ba yaci gaba " a home is where someone wait 4 u, murmushi tayi tace " I don't hv anyone waiting 4 me either, sir, murmushi ya kuma yi mata yace " tashi mu tafi ko? ba musu ta mik'e suka jera.
A gida kowa Zaid zaune gaban Mukhtar suna magana akan Teemah Zaid yace " I decided to spend all m life with Teemah & I wanted 2 start dis new life as soon as possible, murmushi Mukhtar yayi yace " gaskiya to ya kamata kaje ka tunkare ta ka fad'a mata kana santa kawai ka cire tsoro da fargabar komai, nan dai Mukhtar yayi ta k'ara masa k'arfin gwiwa, harya yarda akan gobe zai sanar da ita.
Washe gari ta kasance ranar Saturday dan haka babu aiki kasancewar duk ranar weekend Zaid da Teemah suna tare a wajejen shak'atawa, yau ma haka ce ta kasance, zaune suke a wani garden mai kyau sai kamshen flowers ke tashi, kallonta Zaid yayi a hankali ya kira sunanta "Teemah yanayin yadda ya kira sunan nata da wata irin kasalalliyar murya kuma ya kafe ta da ido ne yasa ta kasa amsawa sai ido kawai data zuba masa, sun kai wajen 30 minutes a haka amma ya kasa cewa komai kuma ya kasa d'auke idonsa daga kanta itace data gaji da kallon ta sunkuyar da kanta k'asa.
Jikinta ne ya kuma bata ana kallonta dan haka ta kuma k'ara d'ago kai ta kalle shi aiko suka had'a ido murmushi suka sakarwa juna a lokaci d'aya a hankali Teemah tace " you've been practicing about 4 d last 1:30 hrs , will u say something now? " what do I say Teemah? 4 d first tym I've fallen in love, 4 d first tym I'm meeting someone lyk dis, 4 d first tym I've done shopping 4 someone & sai kuma yayi shiru ya kuma sauke ajiyar zuciya, kallansa tayi cikin rashin fahimta tace " what!? what are you talking, murmushi ya kuma yace " 4d first time I set my eyes on you I fall in love with you Teemah you come into my life and make it meaningful " kaga ni fa ban gane abinda kake nufi ba dan haka I don't follow a thing , stay here i may go ta fad'a tana k'ok'arin barin wurin mik'ewa da sauri Zaid yayi ya rik'ota dan yasan yau ne kawai damarsa a hankali shima ya mik'e tsaye ya fuskance ta yadda kowanne su yana iya jiyo numfashin juna yayi gaf da ita sosai yace " I want 2 say something Teemah, I'm businessman as u already know , honestly Teemah I'm in love with u, pls accept my loving hands Teemah, ya fada cikin wata irin kasalalliyar muryar.
K'ara matso ta yayi sosai ya k'ura mata ido, itama shi take kallo dan haka idonsu cikin na juna yake kallanta fuskarsa d'auke da kwantaccen murmushi yace " My heart, my life, my everything I gv u, in fact Teemah you're my everything !! idonta ta lumshe tana murmushi dan ta dad'e da kamuwa da mugun son Zaid, a hankali ta bud'e idonta ta sauke su akan na Zaid, kallansa kawai take ta kasa da furta kalma d'aya, ya kuma cewa " will u belong 2 me in dis lifetime & all d lifetime? Murmushi kawai Teemah keyi ta kasa cewa komai, hakan ne ya tabbatarwa da Zaid ya karb'u
Sannu a hankali soyayya mai k'arfi ta rink'a shiga tsakanin Teemah da Zaid, kusan kullum suna tare da dare kuwa kusan kwana suke suna waya, sosai Teemah ta gama shiga jikin Zaid haka ma Zaid ya gama mamaye every part na Teemah, amma tunda Zaid yake bai tab'a zuwa gidan su Teemah ba, yayi juyin duniya amma tak'i kai shi koda unguwar su balle gidan su, yauma kamar kullum ya gama shirin tsaf dan sunyi zasu had'u a wani park, yana sauri ya shiga b'angaren su Ammi a zaune ya iske Ammi da Abba sai Mukhtar dake zaune gefe, har k'asa ya durk'usa ya gaida iyayen nasa, da fara'a suka amsa masa.
Ganin yadda yake ta faman sauri da rawar jiki yasa Ammi mamaki, " kai kuma ina zaka haka naga sai rawar jiki kake, kai ya shafa sannan yace " meeting ne dani, dariya Mukhtar ya tuntsure da ita har yana k'ok'arin kwarewa gaba d'aya suka kalli Mukhtar, Ammi tace " kai lafiyar ka kuwa?
Dariya yayi yace " bakomai Ammi yakai dubansa kan Zaid dake ta faman raba idanu dan yasan abinda Mukhtar ke shirin yi masa, kuma kallon Zaid Ammi tayi tace " ga abinci can kaci sannan ka fita, kai ya langwab'ar yace " please Ammi ana jira na, ban san na b'ata musu lokaci idan na dawo sai naci, kallonsa Abba dake gefe yayi yace " wanne meeting ne dakai around 5:00pm yanzu ya fad'a yana kallon agogon hannunsa, shiru Zaid yayi ya rasa abincewa dariya Mukhtar ya kuma yi yace " a dai rink'a fad'ar gaskiya.
Abba da Ammi suka kalli Mukhtar suka ce "to da magana kenan? da sauri Zaid ya kalli Mukhtar ya k'ifta masa ido ya girgiza masa alamar karya fad'a aiko karaf akan idon Abba, dariya yayi yace " meye kake k'ifta masa ido, " Abba ba ido na k'ifta masa ba wani abu ne ya fad'a min a idon, murmushi Mukhtar yayi yace " kyale shi Abba ba ido zai kanne min ba idan ma hanci ne sai na fad'i, aiko da gudu Zaid ya nufe shi, shima Mukhtar mik'ewa yayi aiko suka shiga zaga parlor'n, Abba da Ammi dai sun kasa fahimtar komai da ido kawai suke binsu, cikin zafin nama Zaid ya rik'o Mukhtar yasa duka hannunsa ya rufe masa baki, yayi ta k'ok'arin kwacewa amma ya kasa.
Cikin dabara Mukhtar ya samu ya gantsarawa Zaid cizo a hannun aiko da sauri ya sake shi yana yarfa hannun, da sauri Mukhtar yace " zance zashi, da sauri Ammi da Abba suka had'a baki "zance!!!? "Eh wallahi Ammi ai an samo muku suruka, sunanta Fatima amma ana kiranta da Teemah, zama Zaid yayi akan kujerar yasa hannunsa duka biyun ya rufe fuakarsa alamar jin kunya, "oh! wato shine kake ta rawar jiki ko, kuma ko ka bamu labarin ta, Ammi ta fad'a tana zama kusa dashi, Abba kusa dashi ya zauna ya dafa kafad'arsa yace " bamu labarin ta, hannu Ammi tasa ta cire masa hannuwansa daya rufe fuskarsa yace " who is she?
Murmushi yayi yana mik'ewa yace " she is beautiful, intelligent, loving, caring & she had walked into my life, she had everything, she's just kinda different Ammi,I really love her, " uhnnn Zaid manyan gari duk wannan bayani haka, so who is her parent cewar Abba, fuskarsa ya langwab'e da alamar tausayi yace " I think they are poor, but I don't know, " u wat, u mean u don't knew her parents, " yes Ammi, " ok to ina kuke zance?
Shiru yayi kamar bazaiyi magana sai yace " babu yadda banyi da ita akan ta kaini gidan su ba amma tak'i, kullum sai dai mu rink'a had'uwa a park "what! Ammi tace a fusace irin wannan matar kake shirin aure irin wannan uwar zaka zab'awa yaranka? to bari kaji wannan shirmen badai a family mu ba, wannan ai zance banza ne daga ji wannan ba 'yar mutunci bace "no haba Ammi meyasa zaki yankewa 'yar mutane hukunci tun kafin ki ganta, kamata yayi kisa shi ya kawo miki kiga tarbiyya da nutsuwa sannan ki yanke hukunci, cewar Abba a hankali Zaid ya sauke ajiyar zuciya dan ji yayi kamar Ammi na watsa masa ruwan zafi, a hankali Abba ya kalli Zaid da hankalinsa yakai k'ololuwar tashi yace " gobe ka kawu ta, kanshi a k'asa yace " ok Abba in sha Allah, tashi kaje, a hankali ya mik'e ya kalli Ammi yayi murmushi yace " Ammi zan tafi ya fad'a yana yi mata kiss a kumatu murmushi tayi tace " ka gaida ta wani irin sanyin dad'i yaji ya ratsa shi dukda dama yasan Ammi mai sauk'i hali ce, " ok zata ji, ya juya inda Mukhtar ke tsaye yace " adayyi zuciya dan ni na kusa wuce gorin Ammi ya fad'a sigar tsokana, dariya shima yayi yace " oho dai ka sani ma kona riga ka angoncewar "ah ai banga alamar hakan ba ya fad'a yana k'ok'arin barin parlor " ok shine kokace nazo na raka ka?
"Ka raka ni ina, tab sha zamanka bana gayya, Teemah tafi 1hr zaune a park tana jiran Zaid, dan haka koda yazo bak'aramin rarrashi ba kafin ya shawo kanta asha love, nan ya shayda mata maganar iyayensa suna san ganin ta dan haka ta shirya gobe zai kaita.
Washe gari wajen 5:00pm Zaid yakai Teemah gidan su, a falo ya ajiye ta yace " ina zuwa tunda Teemah ta shigo gidan su Zaid kanta ya buga dan ganin girma da kuma tsaruwar gidan, aranta tace "Allah kad'ai yasan mak'udan kud'in da aka kashe wajen tsara gidan, tana cikin wannan tunanin taji Zaid yace " Teemah meet my parents, ya fad'a yana nuna mata Ammi da Abba, a hankali ta d'ago kai ta kalli Ammi da Abba ganin mutumin da take gani a gidajen TV tsaya a gabanta yasa k'irjinta bugawa da k'arfi, murmushi tayi tana gaida Ammi da Abba tana daga zaunen akan kujera faran-faran Ammi ta amsa bata nuna mata alamar komai ba, ta karb'e ta hannu bibbiyu, Ammi ta umarci 'yan aiki dasu kawo mata kayan motsa baki aiko aka cika mata gabanta da kayan ciye-ciye fal, wani abun ma bata tab'a ganin sa a rayuwarta ba, babu kunyar komai cike da wayewa taci ta k'oshi ta cika cikinta fam, a hankali Ammi ta kalli Zaid da Abba, shi kanshi Zaid sai da yaji baiji dad'in abinda Teemah tayi ba, murmushi Ammi tayi tace " ya sunanki? kai tsaye tace " Teemah, "ok Teemah a wacce unguwa kike sannan suwaye iyayen ki? da k'arfi gaban Teemah ya buga zuciyar ta ta shiga lugude gami da harbawa, kafin ta gama nutsuwa taji Abba yace " ke 'yar asalin wanne gari ce?
Kasa magana tayi ta shiga in'ina sake kallon Zaid da Abba Ammi ta kuma a karo na biyu tayi murmushi, cikin rawar murya Teemah tace " ni mareniyya ce ni kai na ban san iyaye na ko garin ba, a gidan marayu na taso, ta fad'a tana share kwallar dake zubo mata, take tausayin Teemah ya cika zuciyar Zaid da Abba amma Ammi murmushi tayi irin nasu na manya tace " ikon Allah wanne gidan marayu kenan, cikin rawar baki Teemah ta fad'a musu gidan marayun data taso, daga Abba har Ammi sai da gaban su ya fad'i dan gidan marayun da aka d'auko Abraham ne, cikin rawar baki Abba yace " ok badamuwa, zamu bincika,sai bayan magrib Teemah tabar gidan su Zaid cike da kayayyaki da kud'i da Ammi da Abba suka bata.
A motar Zaid da Teemah zaune babu mai yiwa wani magana kowa da abinda yake sak'awa a ransa, ajiyar zuciya Zaid ya sauke a hankali ya kalli Teemah yace " mai yasa baki tab'a gayamin ke marainiyya bace, a hankali tasa hannu tana goge hawayen fuskarta tace " ina gudun karna rasa kane, ina mugun sanka Zaid idan ka barni wallahi mutuwa zanyi murmushi Zaid yayi yace " ke! ya kike irin wannan maganar ne, waya ce miki ni zan iya rabuwa dake? "Ni dai please ta fad'a tana rik'o hannunsa gam cikin nata yayin da hawaye ke zubo mata, wani mugun shocking Zaid yaji kasancewar yau ne rana ta farko da mace ta tab'a shi, taci gaba da cewa " dan naga kamar iyayenka bazasu karb'e ni ba, " saboda ya tambaye ta? "alama na gani kuma kaga ku masu arzik...... hannu ya d'aga mata yace " ni iyaye na ba haka suke ba, ba irin masu kud'in yanzu bane dan suna da fahimta da kuma adalci, abinda kikayi ne kawai bai kamata ba, " kasan ni ban san komai akan rayuwa ba, dan ban san gatan iyaye ba dole wani abun sai ana yin min uziri tunda kaga ba'a hannun kiyaye na ta taso ba basu suka yi min tarbiyya ba, jikin Zaid yayi sanyi, a hankali ya shiga kwantar mata da hankali, harya kaita ya ajiye.
Zaid yana komawa gida Ammi ta tada falli bata son Teemah wai ta waye da yawa kuma bata da tarbiyya, kayi ta lallashen amma fir tak'i babu yadda Mukhtar da Abba da Zaid basu ba amma ta rufe idonta tace " ya daina nemo wata amma banda Teemah akayi ta abu kusan wata d'aya amma tak'i yarda Zaid duk ya rame ya shiga damuwa da takura amma Ammi ko a kanta da ta kafe ta k'ek'ashe k'asa akan ita bata son Teemah, dakyar Abba ya shawo kanta ta yarda akan tana da sharad'i, Abba yace " bakomai sunji sun yarda, da safe Abba ya kira Mukhtar da Zaid duk suka zauna bayan sun gaida iyayen nasu, a hankali Ammi ta k'arewa Zaid kallo taga mugun ramar da yayi take tausayinsa ya shige ta, a hankali ta kalle shi ta kira sunansa "Zaid! cikin nutsuwa ya d'ago kai yana kallon ta had'i da amsawa, "na yarda ka auri yarinyar nan Teem.... ai kafin ta k'arasa ya nufe ta ya rungume ta "thank you, Ammi thank you so much, a hankali ta zame jikinta ta b'ata fuska tace bisa sharad'in d'aya gaban Zaid ne yayi muguwar fad'uwa k'irjinsa ya shiga bugawa dan yasan tunda Ammi ta had'e rai maganar babba ce, maganar sa na cracking yace " wanne irin sharad'i Ammi.............!
MOMYN ZARAH