27
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
27
Da k'arfi ya rungume ta a k'irjinsa tare da sakin mahaukacin kuka mai rikitar da ma'abocin sauraro, " i love you Teemah, wallahi ina mugun sanki duk abinda kika ga ina yi miki ina yi ne dan ki gyaru, ke ce rayuwata wallahi koda zan mutu bazan tab'a barin wanda ya kashe ki ya rayu cikin farin cikin rayuwa da walwala ba, ya k'arasa maganar yana k'ara sakin mahaucin kuka, zama police d'in yayi ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallonsa tare da sakin gutun murmushi, yakai 10mnt a haka sannan ya kalli Zaid yace " I arrest you for killing ur wife a razane Zaid ya d'ago kai yana kallon sa, ya kalli yaran sa yace " oya arrest him, da sauri suka nufi Zaid dake rungume da Teemah yana sakin kuka, dakyar suka b'anb'are shi daga jikinta suka saka mishi ankwa tare da tusa k'eyarsa zuwa harabar gidan inda suka yi parking motocinsu, police d'in ya kuma bada umarnin a fito da gawar Teemah harabar gidan.
Jin magana k'asa-k'asa yasa Lubnah surar zumbulelen hijabinta tayi waje turus Lubnah tayi dan ganin dandazon 'yan sanda a hankali takai idonta inda mijinta ke zaune hannayensa sanye da ankwa yana kuka, cikin sanyi idonta ya sauka akan gawar Teemah dake rufe da farin yadi, da sauri ta k'ara wajen ta durk'usa agaban gawar Teemah tana kuka marar sauti hannunta na rawa tasa bud'e fuskar Teemah da sauri ta kawar da kanta gefe, cikin dakewar zuciya ta mik'e ta nufi inda Zaid yake ta tsaya a gabansa tana kallonshi ido cikin ido cikin kuka ta fara magana " yanzu duk irin hak'urin da muka baka ni da ma'aikatan gidan nan ashe daman baka hak'ura ba.
"sai da ka kashe ta Zaid wacce irin zuciya Allah yayi maka kai wanne irin mutum ne marar yafiya, mai yasa ka kasance mai taurin kan tsira, da k'arfi taci kwalar rigarsa " haba Zaid mai yasa zaka aikata laifin da kai kanka kasan makomarka wallahi nayi danasanin aurenka nayi nadamar kasancewa ta matarka kai mugu ne azzalumi, mai tayi maka haka dazaka kashe ta a hankali ta sake shi ta zube a gaban k'afafuwansa tana ci gaba da kukan ta "mai yasa Zaid mai yasa kayi haka mai yasa bakayi tunanin halin da Ammi da Abba zasu shiga ba, kasan halin da Abba fa yake ci ta k'asara maganar tana fashe da mahaukacin kuka, cikin rashin fahimta Zaid yake kallan Lubnah ya bud'e baki zayyi magana yaga Baba mai gadi ya rugu da gudu yana salati da sauri Baba mai gadi yace " ya kashe ta ko?
Baba mai aiki ma ta fita daga d'akinta had'i da d'ora hannu aka ta fasa kuka had'i kallon Zaid " kai yanzu yaron nan duk rok'onka da mukayi amma sai da ka kashe ta, Baba mai gadi ya share hawayen dake zubo masa yace " wallahi dama sai da tace bazata koma cikin gidan ba idan ta koma kashe ta zayyi, har nan waje na ta gudu Ya biyo ta wuk'a, sai da muka rok'oshi muka bashi hak'uri ya nuna ya kyale ta, ashe kwanton b'auna yayi, shiru police d'in yayi yana binsu da kallo fuskarshi d'auke da murmushi, Zaid ko komawa yayi kamar mutum mutumi binsu kawai yake da kallo yayinda da mamaki ya gama ciki masa rai da zuciyar sa take yaji tsoro da fargaba sunyi masa dirar mikiya, nan take yaji ya fara zargin kansa, ya shiga tunanin bayan baya biyo Teemah daga d'aki mai ya faru amma ya kasa tunawa, yana cikin wannan mummunan hali yaji police sunce " kai shiga mota had'i da hankad'a shi cikin motar.
A babban division d'in su sukayi parking, suka fito dashi, a wani babban d'aki mai cike da na'urori suka suka saka shi a d'akiyar d'akin akwai table had'i da kujerun zama babban jami'in da kes d'in ke hannu shi ne zaune a d'ayan daga cikin kujerun had'i da wasu 'yan sanda 5 sai Zaid shima dake zaune akan kujera, babban jami'in ya kalle Zaid fuskarsa d'auke da murmushi yace " ni sunana DSP Lawan Hassan ko zan iya sanin sunanka " sunana Zaharaddeen Muhammad Bature, murmushi DSP yayi yace " Muhammad Bature, sannan yace " kasan zargin da akeyi maka? "Eh nasani " ok wanne kenan cewar DSP, " kuna zargin ni ne na kashe matata Fatima wacce akafi sani da Teemah, " good to ya abin yake ko zamu iya sanin gaskiyar al'amari? shiru Zaid yayi yana tunani " ka taimaki sharia ka fad'a mana gaskiya ta yadda sharia ma zata taimake ka, a hankali Zaid ya d'ago kai yace " na kasa tuna komai ne, "what! DSP ya fad'a a zafafe sai kuma ya taso yaje kusa da Zaid yayi k'asa-k'asa da murya yace " please Zaid kar muyi haka dakai, kayi k'ok'arin tuna koda abu d'aya ne.
Shiru Zaid yayi ya shiga tunani " yawwa tuna, yi tunani abinda DSP ke cewa kenan, amma ina Zaid ya kasa tunana komai a hankali ya d'ago kai yace " I cant, table d'in DSP ya buka da k'arfi had'i da juya baya yana shafa kansa, da hanzari ya juyo ya kalli yaransa yace " ku kawo min phone recording "ok Sir d'aga daga cikin su ya fad'a had'i da fita, baifi minti 5 ba sai gashi ya dawo, umarni ya bayar da a had'a na'urar da sauran na'urorin, kwatsam Zaid yayi muryar Teemah cikin firgici da mummunan tsoro gami da mugun tashin hankali cikin kuka take cewa " nice Fatima Muhammad Bature matar Zaid Muhammad Bature miji na ne zai zai zai sai kuma matsananciyar k'arar data saki da sauri Zaid ya mik'e daga zaunen dayake cikin mugun tashin hankali kansa ya dafe da duka hannuwansa wanda barazanar tsagewa gida biyu.
A hankali DSP ya mik'a masa ruwan sanyi ya hard'e hannuwansa a k'irjinsa ya k'urawa Zaid ido yana murmushi, hannun Zaid na rawa ya karb'i ruwan, "na baka 2hrs ka huta, ya fad'a had'i fita, zaman dirshan Zaid yayi a k'asa yasa hannuwansa duka biyun ya dafe kansa, bayan 2hrs DSP ya dawo ya zauna a gaban Zaid da tunda ya zauna ya kasa motsawa DSP ya kalli Zaid yace " All the evidence goes against you, as for ur wife, dat ur wife's call 2 the control room at 12:20am, if not ur wife's voice, say dat no 1 tried 2 kill her, or say dat u know nothing at all.
Ido Zaid na kallon gefe yace " yes, it is Teemah, but I don't know how it happened & when, DPS, if dat's true we must find Teemah killer first, some 1 must've attacked her when I was out, but u can grill me if you want to, da k'arfi DSP ya buga table d'in ya durk'uso da fuskarsa dai-dai ta Zaid ta yadda zuna iya jiyo numfashin juna yace " skip d act, Mr Zaid, ur wife has clearly mentioned ur name, another thing the call was being taped & u had no idea about it, da k'arfi Mukhtar ya bango k'ofar cikin zafin rai yace " waye in charge d'in ces d'in nan, " DSP Hassan Lawan yaji an fad'a daga bayan sa ciki tak'ama Mukhtar ya juya yana facing DSP , DSP yaci gaba " I'm in charge of did case, all dis is happening as per my wish wish, murmushi gefen baki Mukhtar yayi yace " ur wish?
_Kun san dama Mukhtar lawyer ne, kuma shine Lawyer d'in Muhammad Bature Family_
Mukhtar yaci gaba " d law doesn't allow u to act according 2 ur whims & fancies, if you want to grill him, you should have a remain order from the court, murmushi DSP yayi idonsa nakan Mukhtar yake yiwa yaran sa magana " Isma'il " yes Sir " Barrister fa yayi magana mai kyau, kuma gaskiya ya fad'a ko? shiru yaron nasa yayi dan ya gano so yake ya rainawa Mukhtar hankali, ya fuskanci Mukhtar yace " if you think you will get him bail tomorrow morning then you are wrong, murmushi Mukhtar ya k'arayi masa yace " ok that'll be decided tomorrow morning, as of now, ya sauke ajiyar zuciya ya kuma cewa " I want to talk my client in private if don't mind ya k'arasa maganar yana yi masa murmushi, kallonsa DSP ido cikin ido yace " sure, it's all your ya fad'a had'i da juyawa yayiwa sauran yaransa inkiya da su fita suma.
Da sauri Mukhtar ya k'arasa wajen Zaid da tun shigowar sa yake bin su da kallo, a kusa dashi ya zauna had'i da dafa kafad'arsa ya kalle shi ido cikin ido yace " Friend wai ya akayi ne mai ya faru tsakanin ka da Teemah me kayi mata? Wani irin kallo Zaid yayiwa Mukhtar "ok kai ma kana zargi na kenan? kaima ka yarda da cewar ni na kashe Teemah? "haba Zaid tambayar ka fa kawai nayi wallahi na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kai na, kawai ina son jin gaskiya abinda ya faru ne saboda mu samu mafita a kota saboda nine lawyer ka, kuma ko ba wannan a matsayi na na babban abokin ka dole ne nasan komai, Zaid na yarda da kai sosai fiye da tunani saboda na tabbatar da bazaka tab'a aikata mummunan abu ba, murmushi Zaid yayi yace " thank you friend, " you are welcome, babu godiya a tsakanin mu dan haka daga yau kar ka kuma yi min godiya, jiya ai ba yau ba you are my childwood friend, family ku sunyi man komai matsayin nan ma danake ciki dan ku ne, murmushi kawai Zaid yayi sannan ya bawa Mukhtar labarin komai tun daga farko har k'arshe.
Ajiyar zuciya Mukhtar ya sauke da k'arfi cikin mutuwar jiki ya dafa Zaid yace " karka damu Friend Allah yana bayan mai gaskiya kaji, kuma in sha Allah mu zamuyi narasa, murmushi kawai Zaid yayi, Mukhtar ya mik'e ya fita, Mukhtar na fita DSP ya shigo yaci gaba da gudanar da bincike kasancewar gobe ne za'a fara zaman kotu.
Lubnah kuwa ana fita da Zaid da gudu ta koma d'aki ta fad'a gado ta saki kuka mai cin rai, tana kukan tana magana " maiyasa Zaid me tayi maka, akan me zaka kashe ta, sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e ta shiga bathroom tayi wanka, doguwar riga kawai ta zira a jikinta sannan ta kira iyayenta ta sanar da su halin da ake ciki, cikin tashin hankali Mama da Baban ta suka ce gasu nan, aiko ba jimawa suka k'asaro Lubnah na ganin su ta rungume su had'i da fashewa da gigitaccen kuka, sosai Mamanta ta lallab'a tayi shiru ta basu labarin komai, a hankali Lubnah ta d'ago kai ta kalli iyayen nata cikin kuka tace " please karku sanar da iyayensa dan a halin yanzu Abba bashi da lafiya sosai nan ta sanar dasu halin da Abban ke ciki, ran Baban ta ne ya b'aci sosai yace " amma Lubnah baki kyauta min ba ace Abba yayi rashin har a fitar dashi waje amma koki sanar da ni?
Cikin kuka ta basu hak'uri, rungume ta Dady yayi yace " bakomai daughter in sha Allah mu zamu zame masa iyaye zamu yi masa gata za kuma mu tsaya mishi amma dole a gayawa Hassan d'insa (Abraham) ya kalle ta yace " kina da number Abraham? "A'a amma wayar Zaid na hannuna " ok duba nasan zaki ga number sa, ba musu ta mik'e ta d'auko wayar tako ci sa'a babu pin, tana dubawa taga number ta bawa Dady, bugu d'aya ya d'aga Dady ya sanar dashi duk halin da ake ciki, a firgice Abraham yace " what!! da sauri Dady ya rok'e shi akan karya sanar da su Ammi, "ok in sha bazan sanar dasu ba amma ni gani nan gobe.
Washe gari a kotu
A babban kotun dake garin Bauchi motar police ta faka d'auke da Zaid wanda hannuwansa ke d'auke ankwa, yana fitowa dubban jama'a tare da 'yan jarida sukayo kan shi dakyar da taimakon hukuma aka samu aka shigar dashi kotun, bayan kowa ya zauna lawyer gomnati ya fito ya gabatar da kansa had'i da cewa " ya mai girma duk wata shaida da ake nema akan kisan da Mr Zaid yayi na kashe matarsa Teemah an riga an samu an kuma tabbatar domin da kanta ta kira police station ta sanar dasu cewa mijinta yana san kashe ta, bayan haka kuma duk ma'aikatan gidan sun tabbatar da faruwar hakan, ina mai neman alfarmar kar wannan koto mai adalci ta bada bailing Mr Zaid akan kud'i ko nawa, yana kaiwa nan ya koma mazaunin su, da sauri Mukhtar ya mik'e ya gabatar da kansa yace " my load kamar dai yadda kowa ya sani Mr Zaid sanannan d'an kasuwa ne a wannan k'asar kuma yana da tarin dukiya had'i dama a hannunsa ta yadda idan yaga damar kashe mutum abu me mafi sauk'i a wajen sa, zayyi abinsa ne cikin tsari ta yadda babu wanda zai zarge shi balle har a sani kuma zai iya d'aukar killers suyi masa kisan ba tare da sanin kowa ba da wannan jawabin nake rok'on wannan kotu mai adalci data bada bailing Mr Zaid dan har yanzu zarginsa ake ba'a tabbatar ba, da sauri lawyer gomnati ya mik'e yace " ina rok'on wannan kotu da kada ta sake ta bada bailing shi saboda zai iya amfani da kud'i da kuma hanyar da yake da ita yayi wasa da hankalin shari'a, ajiyar zuciya alk'ali yayi sannan ya d'ago kai yace " za'a dawo zaman kotu na biyu a ranar 14 ga wannan watan sannan hukumar 'yan sanda zataci gaba da tsare shi a hannun su, yana kaiwa nan ya buga table alamar an tashi, gaban Mukhtar DSP yazo ya kalle shi ido cikin yana murmushi.
Bayan sun koma police station ne DSP tare da yaran sa suka sake taruwa a d'akin binciken, DSP ya kalle Zaid yace " ko za iya bamu labarin farkon had'uwar ku, a hankali Zaid ya d'ago kai ya kalli DSP sannan ya shiga bashi labarin had'uwar shi da Teemah har zuwa ranar da abin ya faru daga k'arshe ya kuma kallon DSP yace "That's it, I don't know what happened afterwards, when I regained consciousness, you folk were before me, whatever Teemah was, whoever she was I love her dearly, I could never kill her, murmushi DSP yayi yace " the court will decide that.
Bayan an gama duk binciken da za'ayi da gawar Teemah ne aka kaita gidan ta na gaskiya aka binneta a makwancinta,
Ranar 14 ga wata aka koma kotu kamar yadda Alk'ali yace " bayan kowa ya zauna an nutsu ne lawyer gomnati ya mik'e ya kuma gabatar da kansa sannan ya kalli Alk'ali yace " hujjoji game da shaidu duk sun bayyana akan Mr Zaid ne ya kashe matarsa Teemah, ina rok'on kotu ta bani dama na gabatar da shaidata ta farko, alk'ali yace " an baka, risina kai yayi yace nagode, juyawa yayi ya kalli jama'ar dake zaune a kotu yace " kotu tana san ganin Baba mai gadi a gaban kotu, a d'an tsorace Baba mai gadi ya fito ya tsaya, gabansa lawyer gomnati yace " ko zaka iya sanar da kotu ainahin sunana? " cikin rawar murya yace " Malam Mamman " Malam Mamman shin shekarar ka nawa kana aiki Zaid?
" tunda yayi aure na tare dashi a gidan sa amma nakai sharaka 15 ina aiki a k'ark'ashen mahaifin sa, " ok shin menene gaskiya abinda ya sani akan tuhumar da ake yiwa mai gidanka? "Eh to ni dai ina daga d'aki na dake bakin get na rink'a jiyo ihun matarsa tana cewa " dan Allah karka kashe ni wallahi bazan kuma ba, ni dai ina nan zaune sai naga ta shigo d'aki na da gudu tana ihu tana cewa Baba ka taimake ni wallahi kashe ni zayyi, ana haka sai gashi shima ya shigo d'akin hannuwansa rik'e da wuk'a yana cewa wallahi sai na kashe ki, da sauri Zaid ya d'ago ido yana kallon Baba mai gadi, Baba mai gadi yaci gaba " dakyar na rok'eshi ya hak'ura ya kyale ta, lawyer gomnati yayi murmushi yace " ina kar abinda ka sani kenan? yace " eh " ok koma ka zauna, ya juya wajen alkali yace " ina rok'on kotu ta bani dama na gabatar da shaida ta biyu kai kawai alkali ya d'aga masa, ya juya yakira baba mai aiki, itama ta fito yayi mata irin tambayar da yayiwa Baba mai gadi tace " nima ina daga d'aki na na rink'a jiyo ihunta daga k'arshe sai gata ta shigo d'aki na da gudu ta b'oya a baya na sai gashi ya shigo hannuwansa rik'e da wuk'a yana haki yana cewa wallahi sai na kashe ki, dakyar nima na bashi hak'uri ya kyale ta, in banda mamaki, tsoro had'i da muguwar fargaba babu abinda Zaid ke ciki duk ya tsorata yana cikin wannan hali yaji lawyer gomnati yace " bashi dama ya gabatar da shaida ta k'arshe, bayan an bashi damar ne yace " LUBNAH da sauri Zaid ya d'ago kai cikin Firgici da tashin hankali.
A hankali take takowa harta k'araso wajen tsayawar shaida ta tsaya, ido Zaid ya k'ura mata gani yayi tayi muguwar rama da gani tana cikin mugun tashin hankali, a hankali ta d'ago kai tana zubar da hawaye ta kalle shi aiko karaf suka had'a ido, aiko take gabansa yayi muguwar fad'uwa k'irjinsa ya shiga bugawa da k'arfi............
MOMYN ZARAH