GADAR ZARE…

28

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*




28




Barrister ya kalle ta yace " ya sunanki " Lubnah Muhammad Bature, "meye alak'arki da wanda ake tuhuma? " miji na ne, " ok kiji tsoran Allah ki fad'awa kotu gaskiyar abinda kika sani game da wannan kissan, d'an shiru tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya had'i da share hawayen dake zubo mata a hankali ta kuma kai idonta kan Zaid taga shima ita yake kallo sosai ya kafe ta da idon shi, Barrister yace " kiji tsoran Allah ki dubi girman Allah ki sanar damu gaskiya karki duba alak'arki da wanda ake tuhuma, ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na biyu sannan ta fara magana cikin kuka " a ranar da abin ya faru bayan ya dawo gida yayi wanka ya shigo part d'ina yaci abinci, har muka gama cin abincin amma banga Aunty Teemah ta zo ba alhalin tare muke cin abinci, danaga bata shigo sai na zuba mata nata a food flask nace ya kai mata, da farko kin zuwa yayi sai da na k'ara yi masa magana sannan ya d'auki abincin ya fita dukda ransa bai so ba. 



"Ranar kwanki ne? da sauri Zaid ya d'auko kai suka had'a ido, haka nan Lubnah taji kawai bazata iya bayyawa duniya sirrin zamantakewar auren ta ba, dan idan tayi hakan kamar ta nunuwa duniya mijinta ba adali ba bane, babu wanda zayyi masa adalci a take za'ayi masa mummunar fassara, dan haka tace " eh tana kallan fuskarsa da k'arfi Zaid ya sauke ajiyar zuciya game da runtse idonsa, Barrister yace " daga nan fa? 



"D'aki na koma na kwanta sama-sama na rink'a jiyo ihunta da sauri na mik'e nayi parlor, a parlon muka ci karo da Teemah ta shigo da gudu a firgice tana kuka ganin yanayin da Teemah ta shigo ne yayi mugun tsora ta ni, da  gudu nayi bedroom Teemah ma tabi bayana, daga ni har ita muka koma can k'uryar gado muka b'oye yayinda ni na k'urawa k'ofa ido ina sauraren ganin abinda ya firgita Teemah haka, da sauri naga Zaid ya shigo hannunsa rik'e da wuk'a tsirara, k'ara k'ank'ame ni Teemah tayi tana cewa wallahi kashe ni zayyi Lubnah please ki taimake ni karya kashe ni, shi kuma sai huci yake yana cewa wallahi sai na kashe ki, dakyar na lallab'e shi na bashi hak'uri ya hak'ura ta k'arasa maganar cikin azababben kuka. 



Barrister yace " iyakar abinda kika sani kenan? 


"Eh cewar Lubnah, "ok koma wajenki ki zauna, tunda Lubnah ta fara magana Zaid ya k'ura mata ido cike da matsanancin mamaki had'i da mummunan tsoro, shi dai a saninsa hakan bata faru ba, iyakar abinda ya sani kawai ya biyo ta parlor kuma hannunsa ba wuk'a, take ya fara yiwa kansa tamayar ya akayi hakan ta kasance, shin meke faruwa dashi, meke damun shi, kodai bashi bane, meke shirin faruwa dashi ne, tabbas yasan akwai wani b'oyayyen al'amari a k'asa. 



Barrister yace " da wannan shaidu nake kira da wanna kotu mai adalci data yankewa wanda ake zargi hukunci domin duk wata hujja da ake nema an samu an kuna tabbatar da shine wanda ya kashe matarsa da kansa, da sauri Mukhtar ya mik'e domin tuni jikinsa ya gama yin mugun sanyi shi kansa tsoro da firgici sun shige shi, cikin mutuwar jiki ya fara magana " ina rok'on kotu ta bani dama nayiwa Lubnah, Baba mai aiki, Baba mai gadi tambayoyi, bayan an bashi ya kira su duka gaban kotu ya kalle su yace " ko a cikin ku akwai wanda wata matsala ta tab'a shiga tsakanin shi da Zaid ko Teemah?



Duk suka ce a'a,ya kuma cewa acikin ku akwai wanda yaga sanda Zaid ya kashe Teemah da idonsa? nan ma suka ce a'a, "to ya akayi kuka tabbatar shi ya kashe ta, ko kuna da hujjar hakan? cikin sanyin jiki suka ce a'a, "to mai yasa kuka bada shaidar shiya kashe ta? Baba mai gadi yace " ai bamu ce shiya kashe ta ba, " ok to idan bashi bane waye? cewar Mukhtar "wani ne, cewar Baba mai aiki, "wani wa? "zai iya yiyiwa wani ne ya kashe ta dan ya d'orawa Zaid dan ya b'ata masa suna, " gud cewar Mukhtar, ku koma ku zauna, ya juya wajen Alkali yace " su wad'anda aka gabatar a matsayin shaida sunce basu tabbatar da cewa Zaid ne ya kashe Teemah ba, sannan sun k'arawa kotu haske akan ko wani ne ya kashe ta dan ya b'atawa Bature Family suna, da wannan nake rok'on kotu data sake bada damar bincike, bayan kowa ya zauna an nutsu ana jiran abinda Alkali zaice ne ya d'ago kai yace " kotu ta d'age k'ara nan da ranar 21 ga watan nan, kuma a ranar ne kotu zata yanke hukunci. 



Ranar 21 ga wata, bayan kuwa ya hallara a kotun an gabar da komai Lawyer gomnati ya mik'e yace " yau ina da manyan shaidu biyu wanda sun isa su tabbatar da cewa Zaid ne yayi wannan kisan kan, yana gama fad'a ya kalli DSP yace " kawo call recording d'in nan, DSP ya mik'e ya d'auko call recording ya kunna a kotu kowa naji, bayan nan ya kuma kallan Alkali yace " shaida ta biyu CTV Camera gidan sa d'auki sanda yake bin Teemah da gudu rik'e da wuk'a tana ihu, ya juya tare da bawa wani police umarnin ya kunnan, d'an sandan ya mik'e had'i da kunna babban TV dake kotun ya jona, take Zaid ya bayya yayinda yake bin Teemah da gudu hannunsa rik'e da wuk'a, yana cewa wallahi sai na kashe ki, itama kuma tana gudu tana ihu, ta shige d'aki, daga nan video ya katse.



Ai Zaid suman tsaye yayi kawai ya kasa koda kwakkwaran motsi, sosai ya k'urawa TV idon dan yana son tabbatar da abinda yake gani, tabbas shine babu ko tantama, shi kansa ya gaskata abinda yake gani a gabansa, ya kuma yarda da cewa hotansa ne ke bayyana a kwatin TV hannunsa rik'e da wuk'a abu d'aya ne ya kasa yarda dashi har yanzu cewa shine ya kashe Teemah, yak'i tabbatar wa da kansa hakan, har a lokacin yak'i gaskatawa zuciyar sa tak'i yarda akan shine wanda yayi kisan, sosai tsoro, fargaba sukayi nasarar yimasa dirar mikiya had'i dayi masa k'awanya a kowacce gab'a dake gangar jikinsa tuni zuciyar sa ta tsinke gudun jinin dake jikinsa ya k'aru, bayan an gama gabatar da shaida Mukhtar ya mik'e yace " idan har gaskiya ne abinda cameran ta d'auka meyasa bata d'auki inda ya kashe ta ba, haka kuma ya akayi Teemah ta shiga duk d'akin wad'anda suke gidan a lokaci d'aya bayan kowanne yace lokacin da suka shiga d'akinsa sai da ya bawa Mr Zaid hak'uri ya hak'ura, haka ma ai a call recording din cewa tayi mijin tane zai zai zai bata karasa abinda take son fad'a ba, kuka sani ko cewa zatayi mijin tane zai kare ta, ko mijin ne zai kwace ta akwai abubuwan da dama da hakan ke nufi ba lalle tana nufin zai kasheta ba. 




"Kum.. d'ago jajayen idonsa da Zaid yayi suka had'a idone ya hana shi k'arasawa, a hankali Zaid ya shiga girgizawa Mukhtar kai, yana cewa " Friend kayi shiru kawai duk abinda zaka fad'a musu baza su tab'a yarda ba, dan ko ni na fara zargin kai na, ni kaina na rasa meye gaskiyar al'amarin nan balle kuma wani, ka barshi kawai Friend nagode sosai Allah yabar zumunci ni dai fatana ko bayan rai na Allah bayyana gaskiya, "amma friend... da sauri Zaid ya d'aga mishi hannu yace " kabar shi nagode, shiru Mukhtar yayi cikin mutuwar jiki yana share hawaye ya koma ya zauna. 



Alkali ya d'ago kai yace " duba da irin tarin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu, kotu ta yankewa Zaid Muhammad Bature hukunci d'aurin rai da rai had'i da horo mai tsanani a baban gidan yarin dake garin Bauchi, wata mahaukaciyar k'ara Lubnah ta saki had'i zubewa k'asa, da sauri Zaid ya yunkura zaije wajen ta police suka tare shi, sukayi caa akanshi suka rik'e shi, yana ji yana gani aka danna shi a mota akayi gidan yari dashi yana ihun mutuwa, ita kuma Lubnah akayi asibiti da ita.



Tunda aka kaishi prison ya shiga tunanin wanda zai iya had'a masa wannan GADAR ZARE, ran shi ya tsaya akan Abraham saboda shi a sanin sa duk duniya bashi da wani abokin gadawa ko gaba, shi dai yasan Abraham ne kad'ai ya fito ya nunawa duniya baya k'aunarsa akan dukiya, kuma yasan babu abinda Abraham bazai iya akan kud'i ba, kuka ya fashe da shi saboda tsabar bak'in ciki da takaicin wai d'an uwansa uwa d'aya uba d'aya ne yayi masa haka akan dukiya, a cikin gida yarin yake ihu yana kuka, sai da Lubnah tayi kwana 3 a hospital sannan ta wartsake ta koma normal, tun daga ranar da aka sallamota daga asibiti kullum sai ta kaiwa Zaid abinci kuma sai ta tsaya ta tabbatar da yaci, yauma kamar kullum ta shirya ta d'auki abincin ta kai masa, bayan yaci ya d'ago kai ya kalle ta yace " Lubnah ni dai kinga yadda Allah yayi dani da rayuwa ta dan haka k'addarar mu bazata tab'a zuwa iri d'aya ba, bazan bari kema rayuwarki ta salwanta kamar yadda tawa tayi ba, dan haka na yanke hukuncin sauwak'e miki aure na dake kanki dan kar in barki da nauyin aure na a kanki, a firgice ta mik'e ta shiga girgiza mishi kai hawaye suka shiga zubo mata ido kawai ta k'ura masa ta kasa cewa komai, da gudu ta wuya ta fice daga prison din yayinda Zaid keta kwala mata kira amma kota juyo. 



A hankali Mukhtar ya tako har bakin k'ofar d'akin da Zaid ke tsare ya tsaya idonsa yana zubar da hawaye daga ganinsa kasan yana cikin mummunan tashin hankali game da firgici, a hankali yasa hannu ya share hawayen dake zubo masa ya kalli Zaid yace " har abada bazan tab'a daina kukan bak'in ciki ba Friend, murmushi Zaid yayi yace " ka cika aboki na kwarai da ako'ina zan iya alfari dakai, nagode sosai dan kayi iya k'ok'arin ka, ni yanzu rayuwata ta k'are, please Friend kayi min wani abu d'aya, da sauri Mukhtar yace " meye shi ka fad'i ko meye nayi maka alk'awarin zanyi maka shi duk wahalarsa, " murmushi Zaid ya kuma yi a karo na biyu sannan yace " so nake kafin na mutu na fara kashe wanda ya kashe Teemah tukunna, bani da wani buri daya wuce wannan a rayuwata, dan girman Allah Friend kayi min wannnan k'ok'arin.



"Ina bakin cikin yadda zan mutu nabar makashin Teemah a raye yaci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, murmushi Mukhtar yayi yace " indai wannan ne burinka zan cika maka shi a satin nan, Zaid yace " yawwa friend please ka taimake ni, sannan gobe kazo da gaba d'aya takardun companies d'in mu had'i da takardar kotu ta yarjejeniya dan zan bar maka amanar dukiyar mu, dan bazan tab'a bari burin Abraham na mallakar dukiyar mu ya cika ba, bazan tab'a barin dukiyar da Abba yasha wuya wajen tara ta salwanta ta ba, shiru Mukhtar yayi sai can kuma ya sauke ajiyar zuciya yace " gaskiya Friend bazan iya d'aukar maka wannan amanar ba, dan amana tana da matuk'ar wuya zan dayyi k'ok'arin fitar dakai daga nan, hawaye ne suka shiga zubowa Zaid da sauri Mukhtar yace " haba Friend kukan kuma na meye ko so kake ka tada min hankali? 



Ido Zaid ya k'ura masa kawai yana zubar da hawaye, sosai hankalin Mukhtar yayi matuk'ar tashi, cikin tashin hankali ya shiga tambayar Zaid abinda ke damunsa, dakyar Zaid yayi magana " yanzu ina ji ina gani zan bar dukiyar mu ta salwanta, yanzu a hannun Abraham zan mutu nabar dukiyar mu? dakyar Mukhtar ya lallashi Zaid yayi shiru, shima Zaid ya shiga rok'on sa akan ya karb'i amanar dukiyar, dakyar dai Mukhtar ya karb'a badan yaso ba. 



Washe gari Mukhtar yazo da takardun companies dana yarjejeniya, ya mik'ewa Zaid had'i da cewa kayi tunani dai Friend, tsaki Zaid yayi tare dayin sigh a takardun , ya mik'ewa Mukhtar yace " na baka amana, murmushi Mukhtar yayi yace " bakomai Friend, sai da ya juya gefe da gefe sannan ya ciro magani daga aljihunsa ya bawa Zaid yace " kasha maganin nan, idan kasha zakaji kamar heart attack amma bashi bane, daga nan za'a saka a ambulance dan akaika asibiti idan kunje tsakiyar daji sai kayi k'ok'ari ka gudu, ni kuma zan jira ka da mota a dajin daka fito sai mu gudu, da sauri Zaid ya warci maganin yace " kaje yanzu ka jira ni, " Ok kawai Mukhtar ya fad'a. 



Kamar yadda ta saba yauma haka ta dafa abinci ta shirya ta fito, driver ya taso ta dakatar dashi had'i cewa Baba ka barshi ba damuwa yau da kaina zanyi driving, "Allah ya tsare, "Amin tace sannan ta shiga motar ta nufi gidan yarin. 



Bayan tafiyar Mukhtar Zaid ya sha maganin aiko take k'irjinsa ya rik'e ya fara ganin bibbiyu juwa ta d'ebe shi yayi baya luuuu, da sauri aka sanar da police suka zo,a gigice aka kawo ambulance aka nufi asibiti dashi, ana saka shi a ambulance Lubnah na kawo kai, amma kafin ta fito har sun tafi, motor ta k'ara yiwa key tabi bayan su, sai da ya bari anzo tsakiyar dajin dai-dai wajen da Mukhtar yace masa sannan ya buga tsalle ya duro daga cikin motar yayi daji da gudu, da sauri Lubnah tayi parking tabi bayan Zaid amma kafin ta k'arasa har ya shiga motar Mukhtar, da sauri ta koma inda tayi parking, ta shiga mota ta rufa musu baya.



A wani k'aton fili Mukhtar yayi parking ya fito da sauri Zaid ma ya fito ya dafe k'irjinsa, glass d'in dake fuskarsa ya cire sannan ya yar gefe, a hankali ya tafa hannunsa sai ga Teemah ta fito daga bayan mota, fuskarta d'auke da murmushi direct ta nufi Mukhtar ta rungume shi ta manna masa hot kiss had'i da sakar masa k'ayataccen murmushi, a hankali ta juya ta kalli Zaid ta fashe da dariya had'i da cewa my heart, my Cweet husband ya kake kwana biyu bamu had'u ba ko? 



Iya mummunan tashin hankali Zaid ya shiga take k'irjinsa ya shiga bugawa da k'arfi zuciyar sa ta shiga yi masa zafi had'i da k'ona, jinin sa ya tsinke, tsoro da fargaba suka shige shi, zuciyar ta harba had'i dayi masa tsalle kamar zata tsaga k'irjinsa ta fito, mak'ogwaronsa ya fara soya had'i da tuk'uk'in bak'in ciki bakinsa ya shiga fitar da tiriri, nan da nan gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa gami da kyarrrrma, a hankali ya d'ago kai ya kalle shi yace " ya akayi ne best friend for ever, are you surprise? 




MOMYN ZARAH