31
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
31
Idris driver na zuwa uncompleted building d'in da ita ya tsaya cikin alamar tsoro da firgici had'i da mummunan tashin hankali ya fara magana " Hajiya kin tab'a taimako na dan haka bazan tab'a bari ina gani wani mummunan abu ya same ki ba, da sauri yasa hannu a aljihu ya zaro memory card ya mik'a mata yace " gashi idan kinje gida ki nutsu ki gani kinji duk shirin da Mukhtar keyi a kanki yana ciki, sannan ya k'ara da cewa " a kowanne lokaci kina iya jin ance maki na mutu to ba mutuwar Allah da Annabi bace dan Mukhtar yana neman rayuwata akan wannan memory, yana kaiwa nan bai tsaya ya jira abinda zata ce ba ya fita da gudu a matuk'ar firgice, a tsaye ya barta tana ta zancen zuci yayinda da hawaye sai ambaliya yake yi a fuskarta, dakyar ta iya jan k'afarta zuwa inda mota take ta shiga, koda suka isa gida a parlor ta iske Mukhtar bata tsaya bin ta kansa ba ta shige d'aki had'i da danna key.
Jikinta na rawa ta saka memory a wayarta ta kunna ta fara kallon abinda ke cikin, iyakar tashin hankali kan Teemah ta shige shi, jikinta ya shiga rawa had'i da kerrma cikin tsoro da mummunan tashin hankali taci gaba da kallon video, Mukhtar ta gani tsirarar Allah yana aikata zina da wata zankad'ed'iyar budurwa bayan sun gama aikata masha'arsu budurwar ta kwanta a saman k'irjinsa tana shafo fuskarsa a hankali ta d'aga kai tana duban sa, ido d'aya Mukhtar ya kanne mata yace " ''yan mata ya akayi ne?
Murmushi tayi had'i da yin wani farrr da ido sannan tace " yanzu duk irin soyayyar nan da mukeyi amma bazaka aure ne ba? "Inji wa yace bazan aure ki ba? "gani nayi da ido na ai ba sai an fad'a min Teemah zaka aura ba, "what Mukhtar yace had'i da mik'ewa zaune yana kallanta yace " God forbid na aure ni wallahi ko mata sun k'are a duniya ni kuwa mezanyi da ita, wanne dare ne jemage bai gani ba, tun Teemah tana 14yrs nake kusantarta, haba ke ko abinci ne ai yaci ace ka gaji dashi haka, nayi amfani da ita ne dan cikar burina, dan ni babu abinda bazan iya akan kud'i ba, ke ni in tak'aice miki magana idan ta kama ma na kashe Teemah to tabbas zan kawar da ita daga doran duniya abu mai sauk'in ne na tsinke mata numfashin ta matuk'ar naga zata bani ciwon kai, " a firgice budurwar ta d'ago tana kallan Mukhtar tace " kai my dear yanzu zaka iya kashe Teemah?
Murmushi yayi irin nasu na cikakkun 'yan bariki sannan yace "ke nifa tunda nake a duniya ban tab'a ganin mace irin Teemah, shegiya mahaukaciya kawai ita in banda bata da cikekken hankali yama za'ayi tayi tunanin zan aure ta bayan naga irin abinda tayiwa Zaid ni karan hauka ne ya cije ni zan aure ta, ni ma idan ta samu wani wanda tafi sanshi akayi na abu mafi sauk'i ne tayi min irin abinda tayiwa tsohon mijinta.
"To yanzu meye target d'inka akanta? shiru Mukhtar ya d'anyi sannan ya kalli busurwar yace " kinga dai har yanzu ban bata kasonta ba, ina lallab'a ne dan mu rabu lafiya kin san fa halin karuwai, idan ta gane mai nake nufi da ita komai yana iya faruwa, dan haka nake son tsara komai a hankali, ta yadda bazata tab'a fahimtar komai ba, wani mahaukacin kuka Teemah ta saki had'i da buga wayar da bango aiko take wayar ta tarwatse, durk'ushewa tayi a wajen tana wani irin mahaukacin kuka mai cin rai, sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e ta shiga bathroom ta watsa ruwa, ta canja kaya, ta zube a gado ta fara tunanin neman mafita, dan yau Teemah ko parlor bata fito ba balle tabi takan abinci.
Takai 3hrs tana tunanin ta inda zata b'ullowa Mukhtar inda daga k'arshe tunaninta ya tsaya akan ta nemi ABRAHAM, batare da sake tunanin komai ko wani kokonto ba ta mik'e ta nufi parlor inda Mukhtar ke zaune, a zaune ta iske shi a gaban system, k'ok'arin saita kanta ta fara yi kafin ta isa inda yake fuskarta a sake, a hankali ta rungumo shi ta baya ta d'ora hab'arta akan kafad'arsa ta shiga hura masa iska a kunne tana yi masa wani irin salo mai wuyar basarwa, a hankali yasa hannuwansa ya juyo da ita, a d'an firgice ya zaro idonsa waje yace " my life ya haka kuka kikayi meya sameki? Murmushi tayi masa had'i da d'an yamutsa fuska tace " kai na ne kemin mugun ciwo, amma karka damu nasha magani ma, mik'ewa yayi tsaye da ita a hannunsa ya koma kan sofa 3 sitter ya zauna yana kallan cikin kwayar idonta yayinda wutar k'aunarta yake sake roruwa a zuciyar sa, take yaji zai iyayin komai akan Teemah zai kuma rabuwa da kowa akanta, babu koma abinda bazai iya yi ba matuk'ar zai sanya ta cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
A hankali ya had'e bakin su ya fara tsotsar bakin ta cikin kwarewa, bakinsa ya zame daga cikin nata yace " dear ince dai bani na saka miki ciwon kan ba ko? murmushi tayi masa batare data ce komai ba, ganin duk ya rikice mata yasa ta mik'ewa da sauri ya k'ara mai da ita jikinsa ya cigaba da rod'a mata jiki, tasan idan ta tsaya bazai tab'a kyale taba sai yayi koda damba ne yasa cewa " please my heart ka kyale ni wallahi bana jin dad'i yau, yanzu ma aran wayarka nazo ka bani in kira layi na, na rasa inda waya ta ta fad'a na nema harma gaji, rinannun idanunsa ya d'ago ya kalle wanda dama idan jarabarsa ta tashi haka yake komawa in few minutes, murya can k'asan mak'ogwaro yace " please ki taimake ni my life wallahi nakai mak'ura wajen buk'atar ki, kin san daga wajen ki ne kad'ai nake samun nutsuwa, ke ce duniya ta, ina sanki fiye da kowa da komai aduniyar nan ta mu, wallahi zan iya yin komai matuk'ar zai saki farin ciki, ido kawai ta k'ura masa a ranta kuma tana jinjina girman munafurci irin na d'a namiji, kai maza munafukai ne duk zaman da zakayi dasu baka isa ka gane inda suka dosa ba, sai dai muyi ta addu'a.
Ganin ta k'ura masa ido kuma da gani zancen zuci take yasa shi hura mata iskar bakinsa a fuska yace " ko ba ki yarda bane ki gwada yanzu ki gani, murmushi yak'e tayi masa, sannan tace "ya za'ayi nak'i yarda bayan na gani da ido na ni ganau ce ba jiyau ba, ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa tsaye, yasa hannuwansa ya sake maida ita jikinsa ya rungume ta tsam a jikinsa yana mai da numfashi sama-sama.
Fuska ta b'ata tace " nace maka fa bani da lafiya kuma ai sai da lafiya ake komai ko? kayi hak'uri man na d'an wani lokaci na ji sauk'i mana, ido ya k'ura mata yana aiyana wani abu a ransa sai kuma yace " ok badamuwa, ya sake ta da sauri ta mik'e had'i da d'aukar wayarsa dake kan center table, tana shiga bedroom d'inta ta danne key sannan ta zauna a bakin gado ta shiga neman number Abraham tana yin searching taga number hannunta na rawa da d'auki number tayi serving sannan tayi delete number daga wayarsa sannan ta mik'e ta mayar mishi da wayar bata ko kalli inda yake ba ta dawo bedroom ta shirya tayi ficewarta.
Sai da ta samu wani k'ayataccen garden ta zauna ta nutsu sannan tayi dialing number Abraham, su Abraham na zaune suna tsara next target d'in su, su basu tab'a tunanin Teemah zata nemi Abraham ba, wayar sa ta fara ringing, ido ya k'urawa number na d'an wani lokaci sannan ya kalli Zaid da Lubnah da su Idris yace " bak'uwar number da sauri Zaid ya zaro ido yana kallo wayar, ya kalli Abraham yace " pick it, wayar na gaf da tsinkewa ya d'auka Teemah najin anyi picking ta d'auke ajiyar zuciya had'i da cewa " hello Teemah ce matar Zaid da sauri Abraham yasa wayar a hand free yayi musu nuni da hannunsa da suyi shiru yace " bana ji wake magana please, kamar a mafarki Zaid yaji muryar Teemah tace " Teemah ce matar Zaid, please ka tsaya muyi magana dakai, yanzu kana ina?
Kallan Zaid yayi, Zaid yayi masa nuna dayace yana America, da sauri yace " ina America, "ok please idan zaka samu dama kazo Holland ina so muyi magana dakai, " wacce irin magana ce wacce bazamu iya yinta a waya ba?
"Maganar tana da mahimmanci sosai "ok ki fara sanar da ni idan naga takai nazo sai nazo, cikin rawar murya tace "akan Zaid da Mukhtar ne, kafin Zaid ya mutu ya mallakawa Mukhtar gaba d'aya dukiyar ku, shine nake so mu d'ana k'arfi da k'arfe mu k'ato duniyar, da sauri Abraham ya dawo cikekken d'an barikinsa kamar da yace " wow kin san ni fa akwai san kud'i sai dai ni duk san kud'i na ina da rok'on amana, inda magana ce ta kud'i yauma ina biyo jirgin dare, kin ni mayen naira ne, murmushin farin ciki tayi sannan tace masa " amma ina da sharad'i, cikin k'aguwa yace " fad'e shi komaye zan yi, "ok da farko raba dai-dai zamuyi ma'ana 50/50.
"Ah indai wannan ne ai mai sauk'i ne, kefa kika zo mana da business d'in ya za'ayi nak'i, karki damu indai wannan na yarda na kuma amince, " ka bari mana na gama sanar dakai sharud'an, "ok ina jinki, sai da tad'anyi jimmm sannan tace " sharad'i na biyu shine bayan komai ya kammala dole ka aure ni, ta fad'i maganar batare da wani tsoro ko fargaba ba, duk iskancin Abraham sai da gabansa yayi mummunan fad'uwa da sauri ya kalli Zaid, shima Zaid kallo d'aya zakayi masa kasan ya shiga firgici amma duk da haka ya daure yayiwa Abraham alama daya ce eh cikin rawar murya Abraham yace " gud idea kinga sai muyi tacin duniyar mu da tsinke ko?
Murmushi jin dad'in amincewarsa tayi sannan tace " ok yanzu yaushe zaka zo, "yanzu ma zan tashi na yanke ticket, "ok to idan ka isa ka kirani sai nazo Airport na d'auke, "ok badamuwa gani nan, yana aje wayar ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfin gaske yana kallan su Zaid, Zaid yace " ba bata lokaci idan kun had'a ka gaya mata ta san yadda zatayi ta had'a gaba d'ayan takardun sannan tabugar dashi ta bashi yayi singing da zarar yayi singing shikenan duniya ta dawo hannun masu ita, sai kuma musan meye abinyi a gaba.
Kamar yadda suka tsaka haka ce ta kasance, wajen 3:00am yayi mata waya yace gashi a Airport ya k'araso, da sauri taje ta d'auke takai shi wani tsadadden hotel, suka d'anyi hira, acikin hirar ne Abraham ya fada mata tasa Mukhtar yayi singing akan takardun, dan baya son su bata lokaci so yake kawai ya mallake ta, murmushi tayi masa tace "karka damu gobe da safe zan zo maka da su, tana fita ya kira su Zaid ya sanar musu yadda sukayi da ita, washe gari Teemah ta bugar da Mukhtar da giya ta saka shi gaba ta rink'a yi masa kwarkwasa tana d'auke masa hankali had'i da rod'a masa jiki da salonta irin na 'yan bariki, aiko take ya rud'e ya zauce, ganin haka yasa ta fito masa da duk takardun ta cikin wata irin murya tace "yi singing ba musu ya rink'a yi singing a duk inda ta umarce shi, har ya gama yana gamawa ta hankad'e shi gefe ta mik'e, wayarta ta ciro tana sanarwa da Abraham cewar komai ya kammala da sauri yace tazo hotel din data sauke shi.
Ba'afi 30 minutes ba ta k'ara so hotel d'in, kai tsaye ta danna kai d'akin, tana shiga ta iske shi zaune akan sofa yana busa sigarinsa da sauri ta k'arasa inda yake ta manna masa kiss a fuska tace " burinmu ya cika yanzu saura me? da sauri ya mik'e yace " kai haba, batayi mishi magana ba ta bud'e jakarta ta ciro takardun ta mik'a masa hannunsa na rawa ya karb'a ya fara dubawa sai da yaga komai ya cika sannan ya d'ago yana yi mata murmushi yace " komai ya kammala amma shi Mukhtar fa? "Mukhtar kuma ai ban bar mishi komai ba wallahi dan har takardun account dana kadarorinsa dake Nigeria duk na had'o yanzu dashi da matsiyaci mai kwanan kasuwa duk d'aya dan ban barshi da ko sisi ba, dariya suka saka a tare sai da sukayi mai isar su sannan ya kalle ta yace " ki bar takardun nan a hannuna gobe in sha Allah ni da kai na zanzo har gidan daga nan sai mu sanar masa Komai, "ok badamuwa kawai tace.
Tana fita su Zaid dake lab'e a toilet suka fito, Abraham ya mik'a masa takardun yana murmushi hannun Zaid na rawa ya karb'a ya k'urawa takardun ido, sai hawaye sharrrrr a hankali Abraham ya mik'e daga inda yake zaune ya koma kusa da Zaid ya shiga share masa hawayensa " karka damu Zd ita duniya inda ta halak ce bata tab'a guduwa tabar mai ita har abada kota tafi sai ta dawo, wannan gumin Abban mu ne na halak, wanda yasha fafutuka da tad'i tashi cikin sanyi, zafi, damuna ya tara ta.
Sosai Abraham ya lallashi Zaid ya kuma kwantar mishi da hankali,
Abraham ya kalli shi yace " ya maganar su DSP sun taho "eh sun taso tun jiya yau zasu k'ara so, "ok shida waye zasu zo, "shi da alk'alin daya yanke hukuncin, da lawyer gomnati, sai DSP "ok Allah ya kawo su lafiya "hope dai an tsara komai yadda ya kamata "eh karka ji komai.
_tun lokacin da Teemah ta kira Abraham suka yanke hukuncin jiran DSP da sauran wand'anda case d'in ke hannun su dan suzo su gani da idon su_
Tsakar dare jirgin su DSP yayi landing a Holland, Abraham ne yaje ya d'auko su daga Airport ya sauke a lafiyayyen hotel cikin karamci da girmamawa, Washe gari tun 8:30am Zaid, Abraham, Lubnah, Idris, Ali, suka d'unguma sukayin gidan su Teemah sai wajen 9:30 sannan suka fito, Teemah daga ita sai rigar bacci shi kuma sai boxers direct dinning table suka nufa dan basu lura da su Zaid, Teemah ta d'auki spoon zata zata kai bakin ta idonta ya sauka akan Zaid wanda ke sanyi cikin wani d'anyen farin yadi fari sol, kyansa ya k'ara fitowa sosai yayi so fresh dashi fuakar nan sai kyalli take, ya had'e k'afa, gefansa ga Lubnah wacce kamar zata shige masa cikinsa, d'aya b'arin ga Abraham shima sanye da kaya irin na Zaid sunyi anko, sai su DSP wata mummunan kwarewa tayi, cikin zarana had'i da firgici ta mik'e tsaye da sauri Mukhtar ya mik'e tsaye shima yana tambayar ta "meye?
Kasa yi mishi magana tayi illa nuna kawai da take masa da hannunta da inda su Zaid ke zaune a hankali ya kalli inda take yi masa nuni da hannunta, gaba d'aya idanuwansa ne sukayi yo waje kamar zasu fad'o k'asa saboda tsabar tsoro da razana, ya kasa magana illa jikinsa kawai daya d'auri rawa, take zuciyar sa ta shiga bugawa da k'arfi, a hankali Zaid ya mik'e yayi tattaki har zuwa inda suke yace " friend oh! you ask me to call you my Enemy right?
Ai take fitsarin da Mukhtar ke dannewa ya kufce masa sai zarrrrrr fitsarin Zaid ya bi da kallo had'i dayin murmushi sannan yace " da sauri haka my enemy ai ka bari ma mu gaisa ko, gashi nazo har gidan ka tun safe bako breakfast ya fad'a yana zama akan d'aya daga cikin kujerun dunning d'in ya kalli su Abraham da DSP yace " bissimillah kuzo mu ci abinci........
Don't forget to vote and comments
MOMYN ZARAH