37
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
37
Hajiya Lailah na gam gaf da k'arasawa inda Kausar take su Ni'ima suka shigo d'akin "sai kace mai canja fata kin wani yi zamanki, murmushi Kausar tayi dayasa dimples d'inta suka lotsa had'i da cewa " I'm really sorry k'awata, jin sassanyar muryar Kausar ya sake zauta Hajiya Lailah dake tsaye cak ta kasa gaba ko baya, take ta fara hango ta kwance ita da Kausar kwance akan gado suna soyewa, tana cikin wannan tunanin taji k'ara rufe k'ofa da sauri ta kai idonta kan k'ofar taga su Kausar ne suka fita, wani irin yawo ne ya wucewa Hajiya Lailah ta mak'ogwaronta ba shiri, a hankali ta zauna a gefen gadon, a hankali ta furta " kota halin yaya sai na kwanta da yarinyar na, koda zan k'arar da abinda na mallaka na rabu da kowa a duniya sai na cika burina akanta.
Cikin mutuwar jiki ta fita batare data shiga bathroom d'in ba, tana isa parlor'n gidan ta hango Kausar a tsakiyar k'awayen ta tana da murmushi yayinda dimples d'inta ke lotsawa, tsayawa Hajiya Lailah tayi cak ta k'urawa Kausar ido k'em batare datasan me take yi ba, dan gaba hankalinta yana wajen Kausar, Umman su Ni'ima ta k'araso inda Hajiya Lailah ke tsaye kamar mutum mutumi , tace " Hajiya har kin fito, shiru Hajiya Lailah bata amsa ba dan bama tasan Umman na tsaye ba balle tasan abinda takeyi, k'ara yi mata magana Umman tayi amma shiru ba amsa, a hankali Umma tabi inda Hajiya Lailah take kallo, da kallo ta kalli wajen itama, ganin su Ni'ima zaune sunata harkar gabansu bama susan da ita ba yasa tace " ikon Allah.
A hankali Umma ta dafa kafad'ar Hajiya Lailah had'i girgiza ta tace" lafiya Hajiya? firgigit Hajiya Lailah ta dawo hayyacinta, ganin Umma a gabanta yasa ta fara kame-kame a kunya ce tace " hmmmm hmmmm uhnnnnn wallahi yaran ne masu hankali da nutsuwa, murmushin jin dad'i Umma tayi, Hajiya Lailah ta nuna Kausar da hannunta tace " ya sunan wacce? "KAUSAR Umma ta bata amsa, a hankali Hajiya Lailah ta maimaita sunan " KAUSAR, Ok wacece ita, ko itama 'yarki ce? "A'a 'Yar mak'otan muce Mamanta ma k'awata ce sosai, kinga ma mamanta ta can, Umma ta fad'a tana nuna mata Maman su Kausar, a hankali tabi inda Umma ta nuna mata da kallo, Murmushi Hajiya Lailah tayi had'i cewa " kai masha Allah.
Wasu mata ne suka kira Umma ta tafi tabar Hajiya Lailah anan a tsaye tana cewa " Hajiya ki shiga d'aki ki zauna ina zuwa, Hajiya Lailah bata samu damar amsawa Umma ba, saboda ganin Kausar ta mik'e ta nufi d'akin Ni'ima, aiko da sauri Hajiya Lailah tabi bayan ta, a d'akin ta iske ta tana k'ok'arin fitowa, da sauri Hajiya Lailah ta k'arasa inda take, cikin nutsuwa Kausar ta kalli Hajiya Lailah ta d'an risuna tace " ina yini?
Hannu Hajiya Lailah tasa ta dafa Kausar tana murmushi tace " lafiya lau, ya sunan ki? " Kausar ta bata amsa, " nice name ta fad'a tana kallan Kausar ido cikin ido, Kausar kina da aure? da sauri ta sunkuyar da kanta had'i da girgiza kai alamar a'a, hannunta data dafa kafad'arta ta dafa had'i mammatsa mata kafad'ar cikin wata irin murya tace " you are very beautiful Kausar, a hankali Kausar ta zame jikinta ta d'an matsa baya kad'an had'i dayin murmushin yak'e, k'ara matsowa gaf da ita Hajiya Lailah tayi ta mik'a hannu zata rik'ota Ni'ima ta shigo tana cewa " to shekarau d'anko hand bag d'in kenan? murmushi had'i fita batare datayiwa kowa magana ba, Ni'ima ma tabi bayan ta.
Bayan sallar ishsha aka kai amarya Ni'ima gidanta, bayan iyayenta da abokanan arziki sunyi mata nasiha mai ratsa jiki, sosai Ni'ima da Kausar ke kuka kamar ransu zai fita daga jikinsu, koda suka isa gidan suna rungume da juna, koda Hajiya Lailah ta shigo d'akin taga yadda Kausar ke ta faman ji tayi kamar ta d'ora hannu aka ta kura ihu dan jin kuka Kausar d'in take yi har cikin ranta da ruhinta, ganin yadda kuma suka ruk'unk'ume juna ita da Ni'ima ne yasa ta jin wani irin mugun kishi ya taso mata, take taji zuciyar ta tayi bak'i k'irjinta yayi mata zafi yayinda mak'ogwaronta ya fara yi mata d'aci.
Da kyar Hajiya Lailah ta iya controlling kanta saboda tsananin kishin dataji na taso mata, a hankali ta mik'e ta koma gefen Kausar ta zauna had'i da jawo ta jikinta ta rungume tana d'an bubbuga mata bayanta tare da lallashinta, dakyar Kausar ta iya rabuwa Ni'ima ta fito domin mutocin abokanan ango da zasu maida su gida sunzo, Hajiya Lailah na rungume da Kausar da sunan lallashinta take domin daga Kausar har jama'ar dake wajen basu san halayyar Hajiya Lailah ba balle su ankara da abinda take nufi da Kausar, Hajiya Lailah kuwa yak'e kawai take dan jin zuciyar ta take kamar zata kama da wuta saboda tsananin kishi, ko da aka je shiga mota Hajiya Lailah tace su tafi kawai ita zata mai da Kausar gida, amma fir tak'i yadda, babu yadda batayi ba amma tak'i yarda, haka Hajiya Lailah ta hak'ura dole ba dan taso ba.
Tun da Hajiya Lailah ta koma gida ta kwanta take ta faman juyi akan bed ta kasa bacci saboda tunanin Kausar da kuma tsananin santa datake ji yana ratsa duk wata jijiya da b'argo dake jikinta yana bin magudanar jinin jikinta, tun da take a duniya bata tab'a kamuwa da son wani abu a duniya kamar yadda take jin son Kausar ba, jinta take yi kamar ranta, bata tab'a jin sha'awar wata halitta a iya rayuwarta kamar Kausar ba, ganin ta rasa mafita ne yasa ta kiran Jimrau bokan su " yana d'agawa yace " hala an gano wata 'yar shilan ne dan ba'a jinku sai idan da aiki, dariya tace " kamar ka sani, Boka mai duniya, amma wannan yarinya ba kamar sauran matan dana saba kawo maka bace dan tasha bam bam dasu ita ta daban ce.
Wata irin gigitacciyar dariya yayi sannan yace " ba KAUSAR ba? cikin mamaki Hajiya Lailah ta mik'e zaune daga kwancen datake duk tasan wannan ba abin mamaki bane dan kad'an daga cikin hatsabibancinsa tace " ya akay..... da sauri ya katse ta had'i "kin san bana san yawan tambaya ko?
Ayi min afuwa ya bokan duniya, ajiyar zuciya boka jimrau yayi sannan yace " ki bani nan da gobe saboda ina so nayi duba (bincike) akan al'amarin sosai, "ok shikenan badamuwa Allah ya kai mu gobe, Hajiya Rabi kuwa sai dai muce Allah ya kyauta dan abu yaci tura kullum bata da wani aiki sai na tunanin Kausar, dan har gizo Kausar d'in keyi mata, duk ta rame tasa kanta uku duk wanda zata ambaci sunansa sai ta kira shi da Kausar ko bacci ta iyawa, kusan kullum yadda taga rana haka take ganin dare, a b'angaren Hajiya Lailah ma haka abin yake da kwata-kwata kasa runtsuwa tayi Allah Allah take gari ya waye ta kira Boka jibrau.
Tun k'arfe 7:00 na safe ta kira boka dan ta kasa hak'uri, yana d'aga wayar ya tuntsure mata da dariya sai da yayi mai isar sa sannan ya tsagaita, itako Hajiya Lailah ta kawo iya wuya ta shak'a iya shak'a, dan dai ba yadda zatayi dashi ne, Boka Jimrau yace " Hajiya a gaskiya akwai matsala, da sauri tace " wacce irin matsala ce? "Eh to gaskiya a halin yanzu bazamu tab'a iya cin narasa akan yarinyar nan ba, saboda yarinyar tana da k'arfin addu'a sannan ma'abociyar ibada ce, wata irin mummunar fad'uwar gaba Hajiya Lailah taji, yadda kasan saukar aradu, rikin in'ina tace " to .... to ya.. nz.. u.. ba.. bu...wata... mafitar... kenan? "to ni dai mafita d'aga na gano, da sauri tace " wacce? "sai dai idan zaku kasance a gida tsaya har na tsawon wata uku kuna cin abin iri d'aya kuna shan ruwa iri d'aya sannan zan baki wani magani dazaki rink'a zuba mata a abincinta tana ci, zan baki wani turare da zaki rink'a shafawa a jikinki kullum da daddare duk sanda kika shafa ki tabbatar data shak'a har na tsawon wata d'aya, zan baki wanda zaki rink'a turara gidan kullum da safe kafin ta tashi daga bacci shima wata d'aya zakiyi kina amfani dashi, da wanda zan baki kullum ki tabbatar kin shafe mata jikinta dashi, har tsawon wata d'aya, duk aiyukan da zan baki idan aka fara su ba'a tab'a bashi har a gama gidan kika kuskura kika yi fashi to aikin ya lalace koda kin kai kwana 29, sannan ba'a had'a su lokaci d'aya duka sai dai gidan kin gama wani ki fara wani, kin shi zai baki wata uku kenan.
Tunda ya fara magana Hajiya Lailah tayi shiru dan bata san ta yadda zata kasance da Kausar har na tsawon wata uku ba, Hajiya Lailah ta karaya sosai jikinta yayi sanyi, tana dai sauraran sa ne har sai da ya dasa aya yakai k'arshen maganarsa, cikin fidda tsammani tace " to yanzu ta wacce hanya zan kasance da itan harna tsawon wata uku? wallahi boka bani da wata mafita, murmushi Boka Jibrau yayi had'e da cewa " akwai mafita d'aya tak, amma tana da matuk'ar wahalar gaske ba lalle ne ki iya ba, a hanzarce tace " boka fad'i komaye zanyi duk muninshi duk had'aranshi kuma duk wahalar shi matuk'ar zan mallaki Kausar, cike da isa boka Jibrau yace " sai dai idan zaki aura mata d'aya daga cikin 'ya'yanki maza, da sauri Hajiya Lailah ta mik'e tsaye had'e cewa " what?
" kai ma kasan hakan bazata tab'a yiyuwa ba, ni da nake son nakance da ita shine kuma zan aura mata d'a kasan yadda nake tsananin kishin Kausar kuwa? ina matuk'ar san ta sosai sanda ban tab'a yiwa wani d'an Adam arayuwa ta ba, bana kuma tunanin zan k'ara yiwa wani irin bayan ita, yama za'ayi ni da kai na da hannu na aurar da Kausar ga wani d'a namiji?
"Kai ma kasan bazan iya yin hakan ba, dariya Boka Jimrau yayi yace " to ruwanki kuma sharawa ta rage gamai shiga rijiya, ni dai na gaya miki wannan ne kad'ai mafita matuk'ar kina san kasancewa da Kausar, kuma kiji wajen duk wani boka a duniyar nan kiga idan yana da wani abunyi bayan wannan, haba sai kace ba mace 'yar bariki ba, ke kika san yadda zaki b'ulluwa al'amarin, ki tsara shi yadda zai tafi akan tsari, a cikin yaran naki sai ki aurawa nutsatstsen danshi ba lalle ne yabi ta kanta ba balle harya nemi wani abu daga gare ta ba, kuma zamu iya yin asiri mu kawar da hankalinshi daga kanta yaji kwata-kwata baya ko san ganinta, amma idan kika aurawa wancan d'an iskan kin ba asiri ba kome zamuyi sai yayi amfani da ita saboda shi na banza ma nema yake balle wannan, sosai Boka Jimrau ya d'auki lokaci yana fahimtar da Hajiya Lailah ya kuma nuna mata wannan ce kad'ai mafita, akayi sa'a Hajiya Lailah ta fahimta sosai ta kuma yarda ta amince.
Har sunyi sallama zata aje wayar sai kuma ta tuno da iyayen Kausar d'in aiko da sauri tace " Boka to iyayen Kausar d'in fa? cikin dariya yace " karki damu da wannan kibar komai a hannuna zanyi musu aiki dukkansu daga yaron har yarinyar da kuma iyayenta duk zan rufe musu bakin su ta yadda dakinje neman auren ba musu zasu amince miki, haka shima yaron dakin je mishi da maganar bazai yi miki musu ba zai yarda, cike da jin dad'i da matsanancin farin ciki tayiwa Boka Jimrau godiya sannan sukayi sallama.
Bayan Boka Jibrau ya gama aikin ya sanar da Hajiya Lailah akan ta taje wajen iyayen yarinyar ta nemi auren, sannan bayan komai ya kammala sai ta sanar da yaron nata cike da farin ciki ta kashe wayar, da sauri ta kira layin Momyn Bashir mijin Ni'ima take ce mata tana so ta rakata wajen nemarwa Fahad aure, nan tayi mata bayanin taga k'awar matar Bashir mai hankali da tarbiyya shine take son aurawa Fahad ita, Momy dayake bata san dawar garin na, cikin farin ciki tace bakomai sai ta k'araso, koda suka isa unguwar basu wuce gidan su Kausar kai tsaye ba sai da sukaje gidan su Ni'ima suka yiwa Umma da Baban Ni'ima bayanin komai, cike da farin ciki yayi musu jagora har zuwa wajen Malam Baban Kausar, a falon gidan aka sauke cikin mutantawa da girmamawa, Malam na zaune Baban Ni'ima na gefensa yayinda duka matan GE zaune daga gefe, Baban Ni'ima ne yayiwa su Malam bayanin komai, dayake Boka Jimrau ya gama aiki a kansu gaba d'aya, shima ba musu ya amince cike da farin ciki, Hajiya Lailah tace bata son bikin ya d'au lokaci idan ita asan ranta ne karya wuce sani biyu, ba musu kowa ya amince da hakan, suka rabu akan nan da kwana biyu yaran da Baban shi zasu zo.
A ranar Hajiya Lailah ta samu Fahad da maganar auren sai da yayi d'an jimmmmm sannan daga bisani ya amince shima ba musu duk da bai san wacece matar daza'a aura mishin ba, washe gari Friday Alhaji Sambo yazo gida weekend , sai da Hajiya Lailah ta bari ya gama cin abinci yayi wanka ya nutsu a bedroom d'insa sannan ta shirya tsaf ta nufi bedroom d'in nasa cike da kissa ta ta zauna a gefensa take k'arshin turaren da Boka Jimrau ya bata yace " ta rink'a amfani dashi a dun lokacin da take ta buk'ata a wajensa take zai amsa koda bai shirya, k'arshin turaren ya bugi Sanata Sambo, a hankali ya d'ago kai ya kalle ta tayi masa wani irin rikitaccen kallo gami da cewa " sweetheart dama wata magana nake son muyi dakai aje duk abinda yakeyi yayi ya funkance had'i da jawo ta jikinsa yace " ina jinki.............
Don't forget to vote and comment
MOMYN ZARAH