NIDA UWAR MIJINA

Page 1&2

by @jameey

*⚜️NIDA UWAR MIJINA⚜️*


      _By_


*'Yar mutan kankia ❣️*


_It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via ***_



🆓🅿️0️⃣1️⃣▶️0️⃣2️⃣





Tsaye take bakin tati ta rasa yanda zatayi dan motarta ta tsaya gashi ita mace ce bata san yanda zatayi ba ta gyara motar ga yau titin ba abubuwan hawa da yawa saboda ba wajen da mutane ke bi ba ne sosai. 

Tun tana dubu agogo har takai ga ta daina dubawa, gashi ta manto wayarta gida balle ta kira gida a turo drive ya tafi da ita, haka take tsaye bata ga tsuntsu bata ga tarko. 

Tafiya yake cikin kwanciyar hankali yana jin wakar part scatter wakar fireboy, driving yake cikin natsuwa dan sai kace ba tuka motar ake ba, cikin kwarewa yake driving ɗin wakar a silently take fita dan bai ka volume was ba dan bai cika san hayaniya ba, wakace yake bi amman hankalinshi yana bisa titi. 

Tun daga nisa ya hangota tsaye, yayi mamaki da yaganta nan duk da bai santa ba amman yaga hanyar ba mutane sosai gata kuma mace har mangariba ta matso amman tana waje bisa titi, da har ya wuce ta sai yaga rashin dacewar haka sai yayi reverse ya dawo ya tsaya gaban ta yana zuge glass ɗin motar shi sannan ya fara magana. 


"Sannu ko."


Wani farinciki ne ya lalube kasan zuciyarta, ta samu wanda ya kulata yaji matsalarta dan tafi awa nawa a tsaye sai dai azo a wuceta ba ko tausayi, murmushi dauke a fuskarta tace... "Yauwa sannu bawan Allah."


Iskan bakinshi ya furzar yana cewa.."mai kikeyi haka kan tati ke ɗaya".? 

"Wallahi mota nane ya tsaya man ina cikin driving". Tace tana nuna mashi motar da hannunta wanda yasha zanen kunshi mai bala'in kyau...Fitowa yayi ya fara checking ɗin motar sannan ya dawo wajenta ya fara cewa..."gaskiya motarki tana bukatar ganin bakanike amman ga motana ki tafi gida dashi ni kuma zan samu machine na hau na ɗauko bakanike ya gyara sai na kowa maki taki." dan shiru tayi tana kallonshi sai tace..."Taya haka zata kasance bayan bansanka ba."? Murmushi yayi yana ɗage kafaɗunshi yana cewa..."Nima ban san ki ba, amman ai kina da waya ko."? 


"Yes of course."


"That good, sai muyi exchange din number idan aka gyara sai na kawo maki taki motar sai ki bani tawa."

"Ok shikenan, nagode sosai Allah ya saka maka da alkhari."


"karki damu yima kai ne."

Nan suka yi exchange numbers, kallonshi tayi tana kauda kai gefe dan yayi mata kwarjini da yawa, idanunwanshi wani irin abu suka haifan mata lokaci guda dakyal ta bude bakinta tace.."suna fa."? 

"Kamal, and you."? 



"Zainab."


ansar key din yayi ya nufi motar tata dan ya kulle ko ina yace..."ok nice name."


"thank you."


Nan Kamal ya ba Zainab key ɗin motarshi, shin kuma ya samu machine ya tafi taho da bakanike, sosai taji dadin taimaka mata da Kamal tayi kallon cikin motar tayi komai tsab yake kamar ba'a using da ita murmushi kawai tayi ta cigaba da driving dinta har ta iso gida, da gudu ta shiga cikin parlorn tana cewa.


"Anani na dawo."


Wata dattijuwace zaune tana bisa laulausar kujeruta royal, kallo daya zakayi mata ka gane hutu da jindadi sun wadatu a taitare da ita zata kai shekara 65 zuwa da shidda a duniya, amman ba sai kace bata wuce 50 ba saboda kyaun jiki da Allah ya wadata dashi, murmushi shimfiɗe a fuskarta tace..."Zainaba ina kika tsaya haka? Kin tadaman hankali gashi wayarki kin barta gida balle na kiraki, na Kira duk inda nasan zaki biya amman sunce baki zo ba." faɗawa tayi jikin Anani tana cewa. 

 

"Anani mota tace ta samu problem wallahi nafi karfin two hours tsaye amman ba wanda ya tsaya ya kulani sai wani bawan Allah, kinga key ɗin motarshi nan ya bani na taho gida shi kuma ya tafi ya samo masu gyara." ajiyar zuciya Anani ta sauke tana cewa.. "Allah dai ya biyashi, amman yayi koƙari kin san yanzun zamani ya lalace baki ɗaya shiyasa ba'a tsayawa taimako dan daga taimako sai ka jama kanka mashifa shidai ya tsaya gaskiya wanann mutunmin kirkine da baiyi maki komai ba". 

"Gaskiya nima nayi mamaki, bari nayi wanka sai nazo naci abinci Dady bai shigo ba kenan".? 

"Eh bai shigo ba yana hanya nasani yanzun maza kije kiyi wankan kafin ya shigo".

"Ok Anani, ni na shiga sai na fito".

Kamal kuwa yana zuwa cikin gari ya samo masu gyara suka taho tare, gyara motar sukayi ya basu kuɗinsu sannan ya shiga mota direct gidansu ya wuce dan ya gaji yana bukatar hutu zuwa gobe yaje ya bata motarta. 


"Momy sannu da hutawa."


"Kamal ina ka tsaya baka dawo ba."? Turo baki gaba yayi yana cewa..."Momy sai kace wani ƙaramin yaro tsakani ga Allah ni banda ikon da zani kai dare waje sai ki tambayata kamar su Husna ai ko su Lamrat baki yi masu haka sai ni sai kace nine macen sune mazan." kama baki tayi tana kallonshi daure fuska tayi tana cewa..."Gidanku Kamal, ba dole na tambayeka idan kake zuwa ba, ni bansan wannan yawan banza salan kaje kaga yar'asirin tayi maka asiri ta aureka."murmushi kawai yayi yana kallon Momy, yana kuma mamakin halin Momy wai sai yaushe zai zama babba a wajen Momy? Kullum maganarta karda ya kula mata suyi mashi wayau kamarshi ace mace zatayi ma wayau, furzar da iska mai zafi yayi yana goge gefen idonshi yace..."Wai maiyasa Momy baki san nayi budurwa bayan duk abokaina suna da mata wasunsu ma harda masu ya'ya amman ni kin hanani yin budurwa baki so baki ɗaya kiji nayi maki maganar mace."? Murmushi tayi tana kamo hannunshi ta zauna dashi tana cewa.."Ai baka isa aure ba Kamal duka duka yanzun kake 35yrs ina ka isa aure salan kayi auren matar tayi maka wayau ta cinye maka kudi, kuma duk wanda ta aureka ba dan Allah zata aureka ba dan kudinka zata aureka tunda baka isa aure ba." duƙar da kanshi kasa tayi dan jin maganar yayi wata iri wai bai isa aure ba, to sai yaushe ne zai isa aure a idon momy? Kallonta yayi yana cewa.."Momy ban isa aure ba."? 



Daga mashi kai tayi tana cewa.."Ehmana, kaga bansan yawan surutu tashi ka ban waje, inba yaran zamani da bakuda kunya ba, ina ka isa aure haka mukayi da Usman ya matsaman sai yayi aure yanzun da yayi auren ya riƙe matar tashi? Yanzun har yayi mata biyar duk suna fita."



Tashi yayi yana cewa.. "Hmmm! Shikenan Momy mubar maganar kawai ni zan shiga wanka akawo man abincina part ɗin na bansan fitowa yau parlour."

"Ok shikenan."

 

Haka Kamal ya shiga part ɗin shi yana mamakin halin mahaifiyar tashi itadai kishi take dasu shiyasa bata san suyi aure da take cewa Usman ya gaza riƙe mata ai itake kashe mashi auren ba kowa ba tunda duk matar da ya auro sai tace batayi mata ba, kudinshi zata kwashe haka ya kama tunaninshi sannan ya shiga wanka, bayan ya fito wanka yaga Husna ta kawo mashi abinci bayan ya gama shiryawa ya kwanta bacci tunda shi ba fitar dare yake ba balle ya kaima Zainaba motarta Momy bata bari yana fita wai ita karda yayi budurwa... 




Washe gari bayan Kamal ya gama abunda yake ya wace wajen aiki dan ko tsayawa baiyi ba yayi breakfast gaisawa kawai yayi da Momy sannan ya wucewarshi dan shi yana jin haushin yanda Momynshi take hanashi yin maganar auren bayan shi mutune mubuƙaci. 


       *×××××*


"Anani ni zani wuce wajen aiki."kallonta Anani tayi tana cewa.."ok Amman Zainaba har yanzun wanann mutunmin bai kawo maki motar ki ba." tashi tayi tana goge bakinta da tissue tace..."Wallahi Anani nima abun yaba ni mamaki, may be bai samu masu gyaran bane shiyasa."

"Eh kuma haka, nima nayi tunanin haka to nima yanzun zani office sai ki shigo nayi droping ɗinki a office ɗinki ko."? 

"Aa Anani moto ɗinshi zani yi using da ita ni yau bani daɗewa ina zuwa zan dawo."

"Ok shikenan, Zainaba please ki kula bansan wanann driving ɗin da kikeyi kamar baki san ranki." dariya tayi tana cewa..."to Anani ai nadaina nayi hankali tunda jiya mota ta tsayaman a kan hanya, bye."


Bayan Zainaba ta wuce office, da yake a waterboard kaduna take aiki, kuma tana ɗaya daga cikin manya shiyasa singing kawai tayi taɗan gaisa da abokan aikinta sanann ta wutowarta gida. 

Tunda ta dawo gida ta fara aiki duk da suna da yan-aiki ga kuɗin da Allah ya azurtasu dasu hakan bai hana Anani ta koyama yaranta aiki ba, dan su biyar ne ta haifa hudu maza Zainaba ce mace sauran duk maza ne kuma manya ne dan namiji ɗaya Zainaba ta girma. 

Bayan ta gama aiki ta ɗaura abinci, bayan ta gama abinci ta shiga wanka ta shirya ta dawo parlour ta kunna kallo HijiraTv ta kunna dan tana san program ɗinsu. 



     *××××*



Kamal Abuja yake aiki a N. N. P. C  amman Momy ta hanashi kwana tace duk rintsi ya dawo kaduna ya kwana shiyasa two nayi yake tashi idan ko ya kwana Abuja to meeting zaiyi da president, amman duk meeting ɗin dazaiyi bai kwana Abuja jet yake biyowa ya dawo kaduna duk rana idan ya sauka a airport yake hawa moto ɗinshi sai ya iso gida haka yake kullun. 

Wanann abun yana bashi mamaki wai Momy bata barinshi ya wataya kamar shi wai shi mace zatayi ma wayau kuma yace ta fidda mai mata ita da kanta amman tace sai yayi hankali zata yi mashi aure, kullun case ɗinsu kenan shida Momy tun yana ɓoye mata har ya kai da yace mata shi gana bukatar aure amman tayi burus dashi danshi Kamal bai da shi'awar bin matan banza nan ne Allah ya tsare dan ko matan kala-kala suna yi mashi tallar kansu amman bai kallonsu idan ko ta isheshi zai wulakanta yarinya. 

Bayan ya tashi daga office direct airport drive dinshi yakai ya hau jet ya wuto Kaduna, jet din na sauka ya hau moto din Zainaba sanann yayi darling din number Zainaba yake shida mata zuwa shi ta bashi address din gidansu dan gidansu ba boyaiye bane a Kaduna dan unguwarsu daya malali suke amman ba road dinsu daya ba, kuma Babanta sunanshi ba boyaiye bane dan shi dan siyasa ne, shiryawa kawai yayi ya fito. 

Nan ya dauki hanyar gidansu Zainaba, as usual waka yake ji amman yau wakar hausa yake ji.. 

Tafiya yake cikin kwanciyar hankali dan shi Kamal bai san yana gudu da mota kuma baisan yana kure volume komai nashi silent yake haka Allah yayi Kamal, yana isowa gate din gidansu ya dauko waya ya kirata..."Hello Zainab gani a bakin gate dinku, sai ki taho ki shigo dani."


"Ok Kamal am coming."


Haka Zainaba ta fito ta shigo da Kamal cikin gida, bayan sun shigo take zuwa cikin gida ta dauko mashi drinks da fruits ta ajiye mashi dan kallonshi tayi tana cewa..."Bissimillah Kamal ga lemo nan kasha please."dan murmushi shima yayi yana cewa.."Ok shikenan, Zainab nagode amman ni ruwa kawai zansha."


Shagwaɓe fuska tayi tana turo dan karamin bakinta gaba tace..."Aa please nidai komai sai kasha ba ruwa kawai ba."zuba mata ido yayi yana kallonta dan hakan da tayi mashi sai ya kara mata kyau sosai kuma wani abu yaji ya shukar mashi zuciya take a kanta, duk da ya lura bata san tayi ba alamu sun nuna ita yar shagwaba ce maybe auta ce yace a zuciyarshi, kallon tray din yayi yana cewa..."To naji zuba man, amman idan kika cika man ciki kece zance ma Momy na."



Dariya tayi tana rufe fuskarta da tafin hannunta tace..."uhmm! Tunda kace haka bari na kawo maka abinci kaga sai ka hadani da Momy da hujja ko."? Dasauri ya dauko kanshi ya kalleta baki sake yaga da gaske tashi zatayi baisan sanda yace mata.."Rufaman asiri bani nasha ko na tashi na tafi gida kinga dare ya soma yi ok."


Suna cikin haka su Anani suka dawo daga aiki nan suka gaisa Daddy yayi mashi godiya sanann suka wuce ciki suka barsu suna gaisawa bayan Kamal ya gama shan su ruwa da juice sannan ya wuce yace sai sun hadu online. 

Tunda Kamal yafi yake tunanin Zainaba dan shi tayi mashi kuma in bai aureta ba akwai matsala dan baisan ko wace mace inba Zainaba ba dan haka bazaiyi wasa ba, dan ya samu dama dan haka zai gaya mata manufarshi dan yana sonta da aure haka ya isa gida cikin farin ciki dan shi gani yake kamar anbashi ita ma.... 




*Muje Zuwa.... 🖤*



*Yar'mutan kankia ce❣️*


Share domin Allah