13&14
by @jameey
*⚜️NIDA UWAR MIJINA⚜️*
_By_
*'Yar mutan kankia ❣️*
*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
***
_It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via ***_
*🆓🅿️1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣*
Washe gari, tunda safe Anani tazo ta tada Zainaba ta tafi da ita wani waje, can cikin gidansu ne, amman daga karshen gidan ne, dan wani apartment ne ta tafi da ita, ba ma zuwa wajen suke ba.
Suna isowa ta tadda abokan Anninta ne, sun kusa kai goma, zaune suna jiran isowarsu, samun waje Anani tayi ta zaunar da ita a bisa royal din da ke parlourn, bayan ta zauna ta fara gaidasu daya bayan daya sannan ta shiru ta dukar da kanta kasa tana wasa da yatsan hannunta.
Da'ya daga cikin su ta fara yi ma Zainaba magana tana cewa."Zainaba kema lokacinki yayi, masha Allah Alhmdulillah daman shi aure lokacine, abunda mutane basu gane ba kenan, da anga yarinya ta daɗe batayi aure ba sai a kama cewa ta biye ma boko taƙi yin aure, bayan hakan ba yin kanta bane, tunda haka Allah ya ƙaddara ma rayuwarta, mudai abunda zamu fara cewa shine anan Allah ya albarkaci wannan auren naku, ya baku zuri'a ɗaiyaba."
Gaba ɗaya wajen suka ansa da.
"Amin ya Allah."
amman banda Zainaba da ta ansa Amin dinta cikin zuciya, dan daman Zainaba ba daga baya ba wajen kunya, Allah ya azurta Zainaba da kunya, kuma kunyar tana yi mata kyau sosai.
Numfasawa Hajiya Aisha tayi sannan ta cigaba da cewa.
"Zainaba daga gobe kin zama matar wani, nan da wani dan lokaci kuma zaki zama uwar wasu, to wani irin zama zakiyi da mijin naki? Wani irin zama zakiyi da dangin mijinki? Sannan wani irin zama zakiyi da yan unguwar da aka kaiki Zainaba."?
Cigaba da cewa tayi ki tsaya ki saurareni da kyau Zainaba shi aure ya kunshi abubuwa da yawa Zainaba, to maiye wannan aabubuwan Zainaba? Ki bude kunnanki da kyau na gaya maki Zainaba, wannan abubuwan sune suka hada biyaiya dan ita ce kan gaba sai kuma Hakuri, sai kuma tsafta sannan kuma yanda zakiyi ma yaranki tarbiya Zainaba ki nuna masu abunda musulinci ya gudaya mai kyau da marar kyau."
"Biyaiya!, idan akace maka biyaiya Zainaba ba wai ina nufin biyaiya ga iyaye ba ko mu abokan Anninki ko kuma su Annas, Aa muma anaso ayi mana dama sauran mutunen da suka girmai maka suma yana da kyau ayi masu, amman ni a nan zanyi maki bayani ne akan biyaiya ga miji, karki manta Zainaba Aljanarmu tana kasan kafar mazajenmu, dan haka ki bude kunnanki da kyau zan fara yi maki bayanin Zainaba."
"To Zainaba zana fara yi maki bayani daga biyaiya, Zainaba yin biyaiya ga miji sai ansa hakuri gami da jajircewa, dan ba abune mai sauki ba kuma yana da wahala sosai Zainaba,kinsan komai yasa nace maki haka Zainaba? Nasan kina mamaki yanda nace yana da wahala gashi da sauki kuma."
"Eh hakane Zainaba yana da sauki kuma yana da wahala, saboda shaidan zai shiga cikin lamarin dan shi aure bautar ubanjine, shi kuma shaidan bai da guri a duniya ila yaga ya shiga, cikin zuciyoyin dan adam domin ya yana mu yin aikin Allah wato aikin alkhari wanda zai sa ka shiga aljana kayi kyawkyawan karshe."
Numfasawa Hajya Aisha tayi sannan ta cigaba da cewa ma Zainaba."bari na baki wata ruwaya Zainaba, A wata ruwayar da zan baki Zainaba duk da ni ba wata mai ilimi bace, amman zan gaya maki iyakar sani na, ma'ana zanyi iyakar bakin kokarina na gaya maki ƴ'ata Zainaba, idan garin Allah ya wayen shaidan yana aika yan uwanshi shaiɗanu domin su hana mutane aikin lada, idan suka dawo daga aikin da ya aika su zai fara tambayarsu domin ya ji kowa nan su yau wani aiki suka yi mashi, zai fara tambayar daya yace kai yau wani aiki kayi? Wanda ya tambaya zaice ni yau nasa wani ya kashe dan uwanshi mutun, sai yace wannan shine aikin da kayi? To ba laifi, haka dai zai kama tambayarsu har sai da yazo gun wanda ya sa aure ya mutu, nan fa ya kama jinjina mashi, dan shi shaiɗan ya fi son yaga mutuwar aure, kinga kenan yin biyaiya a zaman aure sai mutun ya daure ya cije dan hakuri shine ginshi kin zaman aure."
"Dan haka Zainaba ina mai janyo hankalinki akan yin biyaiya ga miji, dan yi ma miji biyaiya yana ƙara ɗankon soyayya, idan yace daina ki daina, sannan kuma idan kikaga ran mijinki ya ɓaci kisan yanda zakiyi ki sashi farinciki, kisan irin kalaman da zakiyi mashi har ya huce daga fushin da yake, Zainaba ki sani wannan yana ƙara ɗankon soyayya a tsakin miji da mata, sannan magana ta karshe da zan maki, a biyaiya harda hakurin da duk abunda na lissafo maki duk hada maki nayi, duba da lokaci kuma wanda zatayi wa'azi naji ance tana hanya ta kusa ƙarasowa dan haka a gurguje shine karki biye ma shawarae ƙawaye, sannan kuma karki kama yawo kamar kamshi yau baki bikin ƙawa gobe baki gidan suna, A'a ban hanaki cewa zaki fita ba, sai dai karki fiya yawon dai, ki zauna gida kina kula da mijinki da kuma tarbiyar yaranki, karki tona sirrin mijinki, komai zai maki kiyi hakuri dashi Allah yayi maki albarka."
Kuka Zainaba take sosai, dan wa'azin Momy Aisha tayi mata, ba karamin kashe mata jiki yayi, haka sauran suka yi mata wa'azi, sannan suka kamata suka kaita room dinta, daman Sa'adatu ta taho da mai makaup nan tayi ma Zainaba kwaliya, itama Sa'adatu akayi mata, ita Zainaba after address aka samata , masha Allah dan ba ƙaramin kyau Zainaba tayi ba.
Su kuma su Sa'adatu jallabiya suka sa da harami, sunyi kyau sosai.
Haka sukaje akayi wa'azi mai shiga jiki, dan akan zamantakewa akayi wa'azin, yanda mace zatabi ta zama tauraruwa wajen mijinta cikin sauki ba tare da taba kanta wuya ba, taje wajen boka ta kauce hanya.
Bayan angama kowa ya koma ma saukinshi jiki duk a sanyaye.
Wata kaza ce Anani ta dafa ma Zainaba ta kawo mata, tusata gaba tayi sai da ta cinye ta duka kuma ta shanye roman duka shima,wani ruwan wanka mai shigen kamshi Anani ta haɗama Zainaba, sannan ta tasa ta shiga ciki duk da zafin da ruwan yake dashi haka Zainaba ta daure ta zauna ciki, sai da tayi kusan 30min sannan ta fito, wani Anani ta sake haɗama tayi wanka dashi, kafin ta fito ta tadda Anani ta kawo nata lemun dabino da yaji aya da kannumfari sai kamshi yake dan ko sugar bata sa mata a ciki ba zuma tasa mata mai kyau tana tsaye sai da taga Zainaba ta shanye shi tas, sannan tayi mata sai da safe ta tafiyarta.
Waya sukayi da Kamal sannan ta kwanta bacci.
Washe gari tun da safe aka fara shirin biki, dan karfe biyu na rana aka ɗaura Auren *KAMAL ABUBAKAR* da amaryashi *ZAINAB MASA'UD* akan sadaki naira dubu ɗari, sannan aka ɗaura auren *MUHISIN MASA'UD* da Amaryashi *FATIMA HABIB* suma akan sadaki naira dubu ɗari, daga nan suka tafi abuja aka ɗaura auren *USMAN ABUBAKAR* da Amaryashi *MARYAM AHMAD* suma akan sadaki naira dubu ɗari.
Bayan sun dawo daga abuja suka tafi reception nan fa akaci aka sha masha Allah tubarakalla.
Tunda Momy taji an daura ma yaranta aure, ta shiga wani room tana kuka, dan ita gani take ba'ayi mata adalci ba da akayi ma Kamal aure, duka nawa Kamal yake da har za'ayi mashi aure, sai da tayi kukanta mai isarta sannan tace."wallahi idan na ansa suna na Saudatu sai na raba wannan tsananan auren, wanda baida albarkar uwa a cikin shi, natsaneki Zainaba bani sonki kuma bani bukatar ganinki da ɗ'ana dan haka wallahi akan Kamal ba abunda ba zan aika taba."
Tana cikin maganar taji ance."wallahi Yaya Saude, mundun kikayi wasa, to Kamal sai ya zama mijinta ce, dan ni naga yanda yake rawar jiki akan wannan auren, kuma wallahi ba a banza, wannan yarinyar asiri tayi mashi har ya aureta, sauran kuma idan ta shigo tayi mashi asiri ya manta daku keda ƙannanshi Yaya Saude."
Kallonta Hajiya Jalila Momy take sannan tace."Jalila mudun ina numfashi ba wanda ta isa ta raba ni da yarona, ai tayi asirin farko taci riba ko? To wallahi bazatayi nasara a karo na biyu, mundun ko tayi nasara to kisani ni Saudatu bani numfashi a dorar kasa."
Murmushin mugunta Jalila tayi, daman tana zargin yayai tata bata son auren Kamal gashi kuma ta gani da idonta, ta wannan hanyar zasu cika burinsu ita da ƴ'arta Wasila ta auri Kamal kuma su mallaka gida suci kararsu babu banbaka.
_wata sabuwa kuma a wajen Hajiya Jalila🤔_
Cewa tayi."gwara ma ki tashi tsaye Yaya, ni zan koma na cigaba da kula da baƙi."
Bata ce mata komai ba, sai ma kwanciya da ta yi tana tunanin abunda zatayi ma Zainaba, dan a duniya nan ba wanda ya tsana kamar Zainaba gani take asiri tayi ma Kamal har yace zai aure ta wannan kenan.
Hidima akeyi sosai, shiri ko Anani ta fidda kunya ta shirya ɗiyarta yanda ta dace, kuma ta gaya mata shirin zama da miji da abubuwa da dama.
Sai da aka fara kawo matar Auta Muhisin sanan akayi ma Zainaba wa'azi aka tafi kai ta gidan mijinta....
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽 👇🏽👇🏽
*🪀****
*Muje Zuwa..... 🖤*
*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share domin Allah