...08...
by @sadisakhna
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:***
________________________________
*Book 1*
Chp[08]
Washagari da safe da sanyin jiki na tashi da kuma bacci,saboda jiya da daddare vansan lokacin da baccin wahala ya ɗaukeni ba.
Hamma tayi tareda yin mika,uhm yanzu shikenan nagama kwanan gidanmu sai kuma na kabari dazan tafi kwanannan koh.
Nafaɗa a raina..
Yunƙura nayi zan tashi sai naji ƙarar keda,kayan da ammi tavani jiya ne wai inji innar goje,ni ma manta dasu sai yanzu,saboda lokacin data bani ko buɗewa banyi ba.
Ledar na kunce domin naga menene a ciki. Kaya ne kala uku,biyu riga da skirt ɗaya kuma doguwar riga,dukkansu atampar roba ce amma sabi ne,saikuma hijabi ɗaya da kuma takalmi na roba.
Duk da cewar nasan matsayin auren da kuma wa zan aura ɗin,amma banyi tsammanin haka rayuwar aurena zata kasance ba,nayi zaton kodah bansamu kaman yanda nake tunani ba amma dai zai fi haka,saidai kashsh tsugunne bata ƙare min ba,don da alama akwai sauran rina a kaba.
Jikina na kalla bayan na ajiye kayan akan katifah ta,babu lalle babu kurkur irinna amare dasuke,haka nake a koɗe kaman amaryar mutuwa.
Katifah ta nasake duba,ita ɗin ma ƴan matan gidanne suka gama da itah na karba,to ko kuma a wacce zan cigaba da kwanciyah oho,koma tabarma ce duk Allah ne kaɗan yasani. Dan banji kodah wasa wani yace an siyamin wani abun ba. Nice ma na bawa indo ƙawata kuɗi ta siyamin kayan aikin gida,tunda daga nan gidansu babu nisa saita kaimin idan suka kaini.
Guntun hawayen da bansan dalilin zubarsa ba na share kana na fita waje.
Da ubaidu nayi turuss a hanya zai shiga ƙofar mu. Wani tsayayyen kallo yayi min kafin yace.
"Farar mace(yanda yaka ƙirana) ke kuma yanzu wannan gazagin zaki aura?.......wai ai ta ƙaremiki farar mace danni ma lokacin daya sauƙemin allon kafaɗa na daɗe banyi motsiba,wannan inaga ba mutum vane inaga"
"Kai menene haka ka tsayar ta kana ƙara rikirkitata bayan wanda take ciki,kaima ai shirginsa ka shiga shiyasa yayi maka haka,idan tayi duk abinda yace indai ba shine magajin fir'auna ba ai bazai yi mata komai ba. "
"Hmmm ammi zakice haka,to har aka gama abin ɗaura auren fah baya nan,ance ma wai tun jiya yana jeji"
"Oh an ɗaura aurenne"
"Eh an ɗaura yanzu,wani ƙanin babansa ne yayi masa wali,mai anguwa ne yabada dubu goma sadakin gojen"
"In kuɗin toh yake"
"Vaba ya karba,tacan ma ya wuce wai zaije ya siyo dawa dashi,dama jarinsa ya karye"
"Kutt wai nikam Baban yara ina zaije da wannan halinne,yarinyar nan ya bayarta saboda abinda ya aikata,bai siya mata komai ba irin wanda uba ke yiwa ƴar sa,sannan kuma bayan haka wani maga Allah yabada sadaki wanda haƙƙinta ne shima kuma ya karbeshi?"
Cikeda takaici take magana,kanaji kasan ranta ya baci,itama kenan daba ita akayiwa ba,inaga kuma ni,yazanji kenan.
Kallon su kawai nake a nutse,amma cikin raina a dagule yake.
Kallona ammi tayi da sigar rarrashi zatayi magana. Inaa banason wannna rarrashin da babu abinda yake ƙaramin sai raunin zuciya,a barni kawai da daɗin bakinnan,lokaci ne kuma daya kamata nayi jarumta,tareda tarar duk abinda yake shirin tunkarata. Aurene burin kowa yacika an riga an ɗaura shikenan,Allah yabani ikon ɗaukar duk abinda zai biyo baya. Dan haka saurin katseta nayi tun kafin tace wani abun.
"Bakomai ammi tunda an ɗaura auren zance ya ƙare,Allah yabani ikon cinye jarrabawata"
Daga Min kai kawai tayi,da alama tausayina ne ya kamata,ni yanzu banason mutane suna nunamin wannan tausayin ma,don ba komai zai kawomin ba bace karyar zuciya.
Shigesu nayi nakoma ɗakinmu don bansan mai zanyi a cikin gidna ba,babu wani taro sosai har yanzu,da alama kosai yamma ƴaƴan gidan zasu zo.
Ban daɗe da shiga dakin ba najiyo sallamar indo itada shareefah,ita Shareefah ƙawata ce ta hadda,ita kuma indo a wajen abinci muka haɗu da ita,dukkansu sunada mutunci sosai,don sune ma masuyimin siyayyar dazan bukata,duk da nasan a yanwancin abin sun Cikaminne da kuɗinsu,godiya nayi musu har bansan adadin ta ba.
Kaman yanda na faɗa kuwa sai wajen la'asar kafin mutane suka fara shigowa gidan,inda tani za'a biye to bazan so kowa yazo ba,dan ba komai yake kawosu ba face gulma da ganin ƙwaƙwaff.
Fitowa ta daga banɗaki kenan na iyo wanka,da cewa nayi ma bazanyi ba,Shareefah ce ta tursasa min,ita kam indo inna ce shikenan,tunda aka fara zancennan koyaushe mita take wai an cuceni,nice ma nake tarar numfashinta wani lokacin.
Murya Aisha naji tashigo gidan ƴar inna rammah suna gaisawa da matan gidan dasuke tsakar gida.
Wani mai chemist take aure a can tsallekenmu Abdullahi,saurayine yayi karatunsa,dani muka fara soyayya dashi muna haɗuwa dashi a hanyar makaranta,harna fara sonsa kuwa saboda barkwancinsa,zuwansa gidannan na farko Aisha taɗora ido a akansa. Nan duniya kuwa tace shi take so kaman zata mutu,ta shirya ƙarya da gaskiya wai ai saurayinta ne nice na ƙwaceshi.
Ko ya akayi rana tsaka mun fara soyayya yace nan duniya aisha yake so,abinnan ya ƙonamin rai har kwana nayi ina kuka. Haka ina gani akayi aurenta dashi waccar shekarar,suna nan zaune itada shi,tana ma da yaron ciki.
Har yanzu wannan abin yana ƙonamin zuciya,musamman yanzu idan ya ganni yayi ta bani haƙuri yana cewa ba laifinsa bane,duk da nasan ba laifinsa bane amma kuma yanda yake tunanin muyi mutunci hakan bai kasance ba. Kowa a gidan yasan babu wanda yayi wannan aikin sai inna rammah,amma haka aka zama makafi akan lamarin.
Ido muka hada da itah na kawar da kaina zan wuce.
"Amarya ykk,tun ɗazu naga kina ta kallona,kinga yanda na sanja nayi kyau koh,to ina samun cima da kuma kulawa yanda ya kamata,tunda na auri mai hankali da nutsuwa,ba ɗan daba mai suffar mahaukata ba"
Ɗan murmushi nayi mata,dan wlh har raina ta bani dariyah,wai fah ita a hakan dani take.
"Mashaallah kam aisha kinyi kyau abinki ina miki murna,amma kuma nai hasken ciki kika yi koh,jiki kuma dama haka na sanki baki ƙaru ba,inmiki fatan Allah ya raba,ni barina tafi ko"
Na zaga ta gefenta na wuce,ita kanta tasani inaga mantawa tayi,inada sanyin rai amma kuma bana ɗauka irin wannan maganar sam.
Duk inda na baza kunnena maganganu kawai nake ji suna shigomin,wasu na jijjiga kai wasu kuma kawai na basar.
Su Shareefah sai baki suke bani,a tunanin su hakan yana damuna,basu san an shani na warke ba.
Zuwa yanzu dare yafarayi,mutanen da suka zo kowa ya fara tafiyah gidansa.
Riga da skirt ɗin daya fi ɗan kyau a cikin kayan na saka,dan har an fara shirye shiyen kaini gidana.
Ba laifi kayan yayi min kyau anyo masa ɗinkin zamani,kuma ya ɗan kama jikina kaɗan.
Bayan nasaka kayan hijabin na ɗauka na saka,ta gefen idona naga Shareefah sai kallona take.
Kallonta nayi dauke da murmushin ƙarfin hali akan fuskata.
"Menene yafaru Shareefah kike kallona haka kaman wadda zan tafi inda bazamu sake haɗuwa ba"
"Uhmm ba wai tafiyarki ne yasakani kallonki ba,abubuwane da yawa acikin kaina na gameda yanda rayuwarki da sauyah Sumaimah,a islamiyyah kinfi kowa ilimi,haka ma a makarantar safe da mukayi JSS,ke kikemana na daya,amma haka kika daina zuwa makaranta lokaci ɗaya. Wlh banaso naga mace mai ilimi wacce take son cimma burinta na ilimi kuma hakan bai faru ba. Inama munada ƙungiya masu irin wannan aikin,da sun hana wannan aurennanku saboda cutarwa ne.
Amma kuma tunda ya riga ya faru yanzu abinda zakiyi shine yin abinda Allah yace a gidan aurenki Sumaimah,wannan mutumin da muten ke ƙira da dodo kokuma ɗan daba,kefah yanzu ya tashi daga wannan matsayin ya koma mijinki aljannarki kuma duniyarki. Yanzu duk wata ragama na linazamin aurenki yana hannunki. Nasan kina tsoro Sumaimah kuma bazan ce ki daina tsoronsa saboda nasan hakan abune mai wuya,amma ki tuna abu ɗaya ke macece,kinada baiwa a matsayinki na ƴa mace. Duk kwarjinin na miji da wuyar sha'ani kisa a ranki zaki iya dashi,in kikayi hakan sai kiga komai ya tafi a tsari mai ma'ana"
Ƙirjina ne ya buga kana wasu hawaye masu ɗumi suka zubomin,tabbas idan da yana matsayin ɗan daba a wajena to fah yanzu a matsayin mijina yake. Wannan wasu tarin gaskiya ne masu zafi da kuma matuƙar ɗaci Shareefah ta tunamin,wanda kuma komai zanyi hakan suke bazasu canja ba.
A sanyaye na gama shiryawar Ƙanwar babammu Baaba Ladi ta kamo hannuna muka fito..
Dan dama ita ke kai duk wata yarinya da akayi aurenta ɗakinta..
Bayan mun fita su indo ne suka biyo bayanmu muka fito daga ɗakin
Da ammi naci a karo a bakin ɗakin tana kallona.
Wani kukane naji ya ƙwacemin da bansan ta ina ya faro ba,idan nace babu shaƙuwa tsakanina da ammin to nayi babbar karya,dan tun vanni da wayo na tashi na ganta,da daɗi da babu daɗi dai haka ta riƙeni.
Cikin raunanniyar murya nace.
"Ammi .........."
Ban iya cewa komai ba dan babu kalmar dazata sake fitowa bayan wannan ɗin.
"Babu komai Sumaimah,ki daure aure dama shi yaƙin matane,kowacce mace da haka ta girma,balle ke naki da kuma tsoro,dan haka saikin haɗa da haƙuri kinji...bazan samu damar rakaki ɗakin ba dan haka kuje Allah ya ƙare yabada zaman lafiyah....saikuma a yayyafi juna na abinda ya faru"
Ɗaga mata kai nayi kawai,dan narasa ma mai zance.
Hanyar waje muka nufah,baba kam tunda ya karbi sadaki na babu wanda ya sakashi a idonsa,dan haka ba zancen yin sallama dashi,in yana nan ma mai zaice min,shiba wa'azi sai min ba ko nasiha,dan in kura zatayi maganin zawo tafara daga kanta tukunna.
A ƙafa muke tafiya shuru babu wanda yake cewa komai har muka isa anguwar su gojen.
Ohh ni Sumaimatu ina ganin rayuwa,aure a yanzu ko maƙwantanku ne sai anje da mota an zagayo dakai. Amma ni ganida ƴan rakiyar da sayyadarmu mukazo. Kodayake ana ta kai waya ke ta kaya na samu ma na tsira da raina da lafiyata.
Baaba ladi ce a gaba,itakuma tayi sallama da muka shiga gidan.
Muryar wata matace daga wata ƙofa ta amsa,kanajin hayaniyarta tun daga bakin ƙofar gidan da yara. Da alama itace matar ƙanin babannasa,wai dagajin muryar ya kuwa jarababbiyace,danni tsabar zama da masifaffu tun daga muryaru nake ganesu.
Iya amsa sallamar bai isheta ba saida tafito daga ƙofar tana riƙeda kunkumi a gabanmu.ohh dama ba ramammiya bace yanda nake hasashenta,tanada ƴar ƙiba. Magana tafara cikeda isa da gadara.
"Ohh amarya ce ta iso sannu zuwa,gashi ango kuwa tun jiya babu shi babu labarinsa. Sunana gaji matar kawunsa nima nan uwarsa ce da........"
"Dan Allah gaji ya isa haka,yanzu suka shigo maimakon ki tarbesu kibasu wajen zama kuma kin tsaya kina surutun da bashida amfani"
Yanzu wata dattijuwa ce tayi magana,wacce na tabbatar itace kenan innar goje kuma surukata. Ita kam tanada kirki da kamala a ido sabanin matar data ƙira da kanta Gaji. Indai haka innarsa take to albasa batayi halin ruwa ba. Koba komai naji daɗi da innarsa ba masifaffiya bace..
Bin innar gojen mukayi zuwa ƙofarta bayan mun wuce gaji a tsaye tana mita.
Ruwa ta kawomana tareda yimana sannu dazuwa.
Gaisuwar mutunci sukayi da Baaba ladi,alamu ya nuna dama sunsan juna kenan..
Bamu daɗe da zama ba baaba ladi tace zasu tafi,yanda kuka san na jawo ta na zaunar da ita haka naji.
Wasu hawaye ne suka fara zubomin ganin da gaske fah tafiya zasuyi su barni.
"Toh Mairo ga nan amana mun kawo miki na ƴar mu,don Allah a dunga duba zamannasu,mu zamu tafi Allah ya kare tsautsayi"
"Ahh har zaku tafi daga zuwa,kuma bakuga ƙofar inda zata zauna ɗin ba"
Zaro ido nayi wacce ƙofar zan zauna,dama ba anan zan zauna ba a wajenta ɗakin danake hangowa?
Innalillahi kaddai can wani gun za'a kaini wajensa,inda zaiji daɗin kasheni hankali kwance koh"
"Ahah mukam zamu tafi,inyaso saiki rakata da kanki mairo"
"Lahh ya kusa dawowa ma da kun tsaya kun gaisa koh"
Dukkansu zarowa ido sukayi hardani wacce zan zauna dashi ɗin.
"Ahah mairo nikam tafiya zanyi,bansani ba ko su ƙawayennna ta zasu tayata zama kafin yazo"
"Ahah"
Suka bada amsa a tare suna zare ido.
Yau na shigesu ni ɗiyad zinaru,haka zanyi rayuwa dashi ???
Ina gani babu kunya dukkansu suka shuri takalmansu zuwa gidansu a kwanciyar hankali,nikuma inna mairo ta nufi ranaki ɗakin gogan.
Sai wasu kalamai take min da banajin abinda take faɗa.
Ƙofar a kewaye take da ginin bulo,ɗaki ɗayane sai banɗakinsa a gefe . Buɗe ɗakin tayi muka shiga..
Babbar katifa ce a ƙasa sai akwatin kayansa,a dungun ɗakinɗakin akwai fankar ƙasa da kuma wani tsohon rediyo.. Kana ganin ɗakin kasan da bahaka yake ba,gyara yasha na wucin gadi.
Dan ga nan inda aka rurrufe shirgi a gefe.
A kan katifar tayimin nuni dana zauna.. Magana take cikin sanyin murya,amma kaman mutum mutumi haka nake kallonta bana cewa uhmm bare uhmuhm. Kaba ɗaya raina ya fita daga gangar jikina yaje wani gu ya buyah..
Bayan ta fita na daɗe a zauna hakan ban motsa ba,dan ji nake kaman in kan zare.
Can bayan wani lokaci nafara jin alamar sautin sawun mutum yana tahowa,zan iya rantsuwa bana Inna bane,in kuwa banata bane to na waye.
"Na mutuwarki ne"
Wata murya wacce nasan ta ruhina ce ya raɗamin a cikin kunne nah.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
***
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
***
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
***
Share please