44
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
44
*LABARIN ZARAH!!!*
cikekken sunana Fatima Muhammad, ana kira da ZARAH ne kasancewar sunan mahaifiyata aka mayarmin, mu 'yan asalin garin Daura, amma ni haifaffiyar garin kano ce, mahaifina Alhaji Muhammad Daura cikekken mutum ne kamili mai ingantacciyar nutsuwa da kamala dattijo ne mai nagarta, wanda asali kasuwanci da neman nakai ne yasa ya baro tushensa, danginsa da iyayensa ya shigo garin kano, a lokacin yana d'an matashin sauri dan bazai wuce shekaru sha takwas ba, dan a lokacin yana ji k'arfi na samartaka da k'uruciya ya shigo garin kano, cikin ikon Allah yasa ya shigo garin kano da k'afar dama dan Allah ya had'ashi da wani attajirin mai kud'i d'an kasuwa Alhaji Abdullahi, d'an kasuwa ne shahararre a zamanin sa, mahaifina ya fara zama yaron gidan Alhaji Abdullahi kamar Almajiri, yana yi musu aikace-aikace gami da aike, a hankali Mahaifina ya fara shiga ran mutanan gidan yana k'ara samun kusanci dasu kasancewarsa mutum mai gaskiya da amana.
Dan duk aiken da zakayiwa mahaifina ko aikin da zaka sakashi zayyi maka shine bisa gaskiya da amana, hakan yasa lokaci d'aya ya samu shiga sosai a gidan da zuciyar Alhaji Abdullahi, ya wuce duk sauran ma'aikatan gidan, Alhaji Abdullahi ya kasance mutum ne nagari kamili mai yawan kyauta gami da adalci gashi kwata-kwata bashi da mugunta balle bak'in ciki hakan yasa Allah yake k'ara bashi nasara akan dukkan harkok'insa, Alhaji Abdullahi yana da matar aure d'aya tal tunta ladan noma, suna yara biyar biyu mata uku maza, Fatima wacce itace 'ya ta biyu a cikin yaransa jininsu ya had'u sosai da mahaifina dukda tana k'aramar yarinya sosai a lokacin da bazata wuce shekaru biyar ba, gaskiya da amanar da mahaifina ya rik'e itace silar d'aukakarshi zuwa babban matsayi a rayuwa, nagartarsa da Alhaji Abdullahi ya gani ne yasa ya mayarda dashi kasuwa wajen kasuwacinsa, lokaci d'aya kasuwanci ya k'ara hab'aka yana ci gaba hakan bak'aramin k'ara d'aukaka darajar mahaifina yayi a wajen Alhaji Abdullahi ba har zuwa wajen abokansa da jama'ar gari dan duk inda Alhaji Abdullahi ya zauna bashi da wata magana sai ta gaskiya da amaar yaronsa Muhammad, sosai Alhaji Abdullahi ya aminta da mahaifina harta kai daya d'orashi akan harkokin kasuwancin sa sosai saboda babu kyashi a zuciyar Alhaji Abdullahi ko takurawa, sosai ya d'agawa mahaifina k'afa ta yadda idan aka fita saro kaya shima zai samu nashi.
Bayan kamar shekaru bakwai kasuwanci ya hab'aka sosai dan yanzu idan aka saro kaya zama akeyi ayi lissafi a raba ribar duk yawanta gida uku anan take Alhaji Abdullahi zai d'auki kaso biyu cikin uku ya bawa mahaifina kaso d'ayan, kafin wani lokaci mahaifina ya fara amsa sunansa shima da kansa ya soma shahara, bai tsaya wasa da almubazaranci ba ya soma tanadarwa kansa kadarori da k'ara fad'ad'a kasuwancimsa, duk wata harkar kasuwanci data samu koda badaga b'angaren Alhaji Abdullahi bane sai mahaifina ya sanar dashi yayi masa tayinta, saboda mahaifina mai sa'a ne, idan kuma akayi harkar sai Allah yasa a dace a samu riba mai tsoka, hakan ya kuma k'arawa Alhaji Abdullahi so da k'aunar mahaifina a zuciyar sa, babu wanda Alhaji Abdullahi ya yarda dash gida da waj sama da mahaifina.
Alhaji Abdullahi da kansa ya fara sh'awar mahaifina ya zauna kusa dashi har abada, dan haka da kansa yayiwa mahaifina maganar ya kamata ya samu gida ya siya ya dawo da iyayensa da k'annansa kusa dashi suma ya bud'a musu su samu na kansu dan nan gaba da zarar an k'ara wasu shekaru nauyin zayyi mishi yawa, kuma shim ya kamata ya fara k'ok'arin mallakar mallakar gidan zama nashi na kansa, ba musu mahaifina ya amince,kasancewar akwai kud'i a kasa yasa batare da b'ata wani lokaci ba aka fara neman fili anan kusa da Alhaji Abdullahi, cikin sa'a a kasamu wani makekken fili gari guda zan za'ayi iyayin primary school, take aka siyi filin aka fara gina matafaren estate, dan so yake yayi family hause babba sosai.
Yayinda daga b'angaren d'aya sabo da shak'uwa ya fara kid'ewa yana komawa soyayya mai k'arfi tsakanin mahaifina da kuma Fatima 'yar Alhaji Abdullahi, ana cikin haka Allah ya k'ara bawa matar Alhaji Abdullahi k'aruwar haihuwar d'iya mace aka saka mata suna ZAINAB, yayinda tuni an fara gina katafaren filin mahaifina harma an kusa gamawa dan sosai ake yin ginin ba wani b'ata lokaci, b'angaren iyayensa aka fara gamawa dan haka yaje har Daura ya sanar dasu cewa nan da sati d'aya zasu koma kano da zama gaba , kin amincewa sukayi da farko, sai dakyar Abban mu ya shawo kansu suka amince, sati na zagayowa shi da kanshi yazo ya z'auke, sunyi murna da farin ciki sosai ganin makeken gidan ga kyau da had'uwa.
Bayan iyayensa sun dawo ba'a jima ba aka gama ginin gidan kaf kusan part 16 ne a gidan banda filin ball da filin wasa dana motsa jiki, ganin an gama gidan yasa yiwa Alhaji Abdullahi maganar Fatima wanda dama shi tuni yasan da maganar ba tare da wani b'ata lokaci ba akayi biki aka kai mahaifiyata gidan ta.
Duk wani burin duniya mahaifina ya d'auka ya d'ora shi akan matarsa Fatima bashi da wani burin dayafi ya faranta mata ranta duk wani da take so matuk'ar baifi k'arfinsa ba yana yi mata shi, sosai yake bata kulawa, shekara biyu da auren su amma ko b'ari Mamana bata tab'a abin ya dame su sosai amma Abba na ya danne tashi damuwar yana rarrashin Mama na, sunje asibitoci da dama amma duk inda sukaje maganar d'aya ce lafiya lau Allah ne dai bai kawo lokaci ba, ganin halin da Mama na ke ciki yasa Abba na rok'ar sirikinsa Alhaji Abdullahi akan a basu Zainab , ba musu Alhaji Abdullahi ya amince dan babu abinda Abba na zai tambaya a hannunsa ya iya hana shi matuk'ar yana dashi, Zainab nada 2yrs ta koma hannun yayarta mahaifiyata, tun daga ranar Mamana bata k'ara bak'in ciki ko damuwa akan rashin haihuwa ba, dan ta d'auki Zainab k'anwarta kamar 'yarta ta cikinta.
Ana cikin haka Fatima da kakata mahaifiyar Mamana da Alhaji Abdullahi suka dame Abba na akan dole sai ya k'ara aure dan kar ganin Fatima 'yar su ce yasa shi kuma ya cuci kansa, amma fir yak'i ganin haka yasa Fatima fara yi masa akan dole sai ya k'ara aure amma fafur yak'i dole suka hak'ura suka kyale shi.
BAYAN SHEKARU 14
Duk wanna tsayin shekarun Allah bai bawa Mama na haihuwa ba kai ko b'ari bata tab'a yi ba, hakan yasa Alhaji Abdullahi da Kakata suka matsawa mahaifiya akan dole fa wannan lokacin yayi aure ko yak'i ko yasa, dole tasa Abba nah ya yarda badan yaso ba dan shima iyayensa sun matsa masa akan dole sai yayi auren, ba'a san ranshi ba ya fara k'ok'arin neman aure a lokacin Zainab nada shekaru 16,kasancewarshi mai hannu da shuni yasa bai d'auki lokaci yana neman aure ba ya samu, duk da nan cikin kano ya auri yarinyar mai suna Zuwairat, Zuwairat ba budurwa bace bazarawa ce dan ta tab'a aure.
Zuwairat mace ce mai tarin munayen halaye, dan gaba d'aya 'yan gidan su anyi musu tambarin rashin tarbiyya had'i tsaface-tsaface (asiri), auren ta hud'u duk inda taje mugayen halayenta kesawa a sake ta, amma akayiwa Abba na rufa-rufa akan aurenta d'aya mijinta mutuwa yayi, tun bayan auren Abba nah da Zuwairat komai ya lalace ya tab'arb'are,wacce tana shigowa ta canja komai, ta mallake Abba nah, ta canja masa halayensa da asiri yamana baya ji baya gani a kanta, ita kad'ai kawai yake sauraro, kowa yasan a al'adalce komai yana hannun uwar gida amma ina banda a gidan Abba dan komai yana hannun Zuwairat shi kanshi bai isa yayi wani abu ba sai da saninta ba, tuni ta raba shi da iyayensa da danginsa, ko d'akin Mama na bashi da ikon shiga saboda bai isa ba, matuk'ar ya sake ya shiga kuwa ya shiga uka dan ranar mak'iyinsa ma sai ya tausaya masa, duk kyawawan halaye irin na Abba na sai da aka wayi gari babu ko d'aya, ya zama marar adalci a tsakanin matansa, dan gaba d'aya hankalin sa ya karkata akan Zuwairat, duk wani abu na nashi na hannunta cikin kuwa harda kadarorinta, idan kana so kaga rashin mutunci to ka tab'a masa Zuwairat yanzu zai rufe ido yayi ta zazzaga tujara, hakan da Alhaji Abdullahi ya gani ne yasa shi mamaki, ya tabbatar da ba haka Zuwairat ta barshi ba, duk irin nagarta mahaifina Allah ya jarrabeshi da hatsabibiyar mace mara imani da tausayi.
Kasancewar Fatima baya da d'a bata jika sai Zainab yasa ta d'auki da gatan duniya ta d'orawa Zainab duk wani abu data gani burinta ta sai mata musamman yanzu data zama budurwa take da 16yrs, sosai Fatima take mugun son Zainab take nuna mata gata, dan duk abinda zakayiwa Fatima zata jure amma banda ka tab'a mata Zainab yanzu zakaga gishinta, duk wannan son da takeyiwa mata bai hana ta bata cikekkiyar tarbiyya ba.
BAYAN SHEKARA BIYU
Haka rayuwa tayi ta tafiya tsakanin Mamana da kishiyarta babu wani sausauci sai ma k'aruwa da ake samu dan kusan kullum sai Zuwairat da Abba na sun fito mata da sabon salan wulak'anci hak'uri kawai Mama na keyi, duk da wannan halin datake ciki bata tab'a zuwa takai k'ararsa wajen iyayenta ba, haka suma iayen dayake dattawan da ne akwai kara babu wanda ya tab'a yin magana, sai dai kullum suyi ta bawa Mama na hak'uri suna cewa ta dage da addu'a dan Allah ya jarrabi mijinta da masifa, Zainab ta zama cikekkiyar budurwa 'yar shekara 18, tun shekarar data wuce ta gama secondary school, manema tako'ina sai fito mata suke amma bak'i kulasu, ana haka Allah ya had'a ta da MANNIR d'an babban aminin Abbanta Alhaji Abdullahi, suma manyan masu kud'i ne dan Abban su Mannir yayi president a Nigeria, ana kiran Family su da EL-MUSTAPHA FAMILY dan family babban family ne, Mannir su biyar ne a wajen iyayensu shine babba sai k'annensa mata sannan k'anin NASEER wanda a lokacin yake JSS 1,kasancewar Alhaji Abdullahi kakana da El-Mustapha akwai amintaka mai k'arfi yasa ba'a wani b'ata lokaci ba akayi bikin MANNIR & ZAINAB k'anwar mahaifiya ta.
El-mustapha family gaba d'ayansu manyan 'yan boko wayayyo ne,, masu ji da kud'i da aji, ga kyau kamar su sukayi kansu, akwai baiwar da Allah yayi ta duk d'an da aka haifa a family su yana da CINDO, gaba d'aya familyn babba da yaro babu Wanda bashi da cindo matuk'ar kai jinin su ne, koyaya kuka had'a jini to kana da wannan cindon, Mannir mijin Aunty Zainab ba k'aramin kyakykyawan gaske bane, amma duk kyansa Naseer ya gishi dan Naseer kamar su d'aya sak da salman khan sanda yana matashin sauri ba yanzu daya tsufa ba, ana auren Aunty Zainab ta samu ciki, murna a wajen Mama na da Familyn El-mustapha ba'a magana, cikin Aunty Zainab yana da wata biyu, tafiya ta kama Zuwairat ba k'aramin kashedi tayi masa akan karya sake ya kwana da Mama na ba.
Dan duk yadda kake tunanin Zuwairat ta mallake Abba na abin ya wuce nan, cikin ladabi da biyayya ya amsa mata, tana tafiya ya koma part din Mama na dan har a lokacin yana jin santa da tausayin ta a ranshi dan dai babu yadda zayyi da Zuwairat ne, cikin ikon Allah Mama na ta samu ciki na, Zuwairat bata dad'e da dawowa ba ciki na ya bayya a lokacin cikin Aunty Zainab yana da wata uku na mama kuka wata d'aya, duk da an gama mallake Abba hakan bai hana shi nuna murna da farin cikinsa a fili ba, dan kamar zayyi hauka, fad'ar halin da Zuwairat ta shiga b'ata lokaci ne take hankalinta yayi mummunan tashi ta shiga damuwa, ta kuma k'ara zage dantse da d'ammarar asiri ta dage ta ko'ina bankawa Abba asiri take baji ba gani, dan taso a zubar da cikin amma duk bokan data jewa da wannan maganar sai yayi ihuuuu sannan yayi mata kashedin matuk'ar tana san ranta tabar maganar zubar cikin, ganin gaba d'aya komai ya k'ara jagulewa ne yasa iyyen Abba na da Mama na tashi ttsaye da addu'a bani ba gani dare da rana, kullum aciki neman taimakon Allah suke suna bayar da sadaka.
Sannu bata hana zuwa, yau Aunty Zainab ta tashi matsananciyar nak'uda ana kaita asibiti bata fi 1hr ba ta haifi d'iyarta mace, wacce akayi niyyar sawa sunan Mama na amma ta hana tace " a sunan kaka ta tawajen uba HAFSAT ana kiranta da IKRAM, bayan wata d'aya Mama ta tashi da matsananciyar nak'uda itama takai wajen kwana biyar tana nak'udar a asubiti, amma haihuwa shiru hakan yasa aka yanke shawarar yi mata CS bayan ta gama shan bak'ar wuya ta fita a haiyacinta ko mutane bata iya ganewa, ana ahirin shiga da ita theater room ta haifeni, tunda ta haifeni cewa ya k'ara tsananta sosai, cikin haka Abba na ya shigo d'akin dakyar Mama na ta neme shi shafiya yana kuka yace ya yafe mata itama cikin kuka tace ta yafe masa, Mama tana jikin Abba ta mutu bakinta yana furta kallamar shahada.
Fad'ar tashin hankalin da zuri'ar mu tashi ma b'ata lokaci ne musamman Zainab da Abba nah, dan Zainab hauka ta rink'ayi tuburan tana sambatu kamar mahukaciya dan sai rufeta akayi a d'aki dan sosai take mahaukacin ihuuuu, Abba na kuwa tun da akayi mutuwar ya rufe kanshi a d'aki yana aikin rusgar kuka dare da rana ba ji ba gani, tun da aka haifeni Aunty Zainab ke rungume dani ta hana kowa d'aukata, bayan sati d'aya da rasuwar Mama aka had'a Family meeting har lokacin Abba yana d'aki yak'i fitowa, sai dakyar kakana Alhaji Abdullahi ya matsa masa ya fito, duk ya rame ya k'ek'ashe ya fita kamanninsa.
Aunty Zainab na rungume dani tana aikin rusgar kuka, Kakana Alhaji Abdulahi wanda muke kira da Alhajin sama yayi gyaran murya yara magana da nasiha sosai, sannan ya cewa Abba na yayi min hud'uba amma Abba ko tari bayyi ba, Alhjin Sama ne yayi min hud'uba da sunan Mama na FATIMA ana kira na ZARAH, yin duniya Abba yayi magana amma yak'i babu abinda yake sai rusa kuka, Zuwairat na hakince akan kujera hard'e da k'afa tana ta fama girgiza tana yiwa duk jama'ar dake wajen kallan banza ciki kuwa harda kakanni duka hud'u, cikin tak'amar ta gama gamawa da Abba nah, sai da Alhajin Sama ya had'a shi girman Allah yayi magana, maganar ta farko a lokacin itace Zuwairat na sake ki uku.
Hannu ta d'ora aka tana ihuuu da kuka ta durk'usa a gabansa tana bashi hak'uri amma ko kallanta bayyi haka taje gaban kakanni na tana basu hak'uri amma babu wanda ya saurare ta, kaka ta taso k'arb'a ta tarik'e ni amma fafur Zainab ta hana kowa ni, tace zata had'a ni da Ikram ta shayar dani, da wannan uzurin kowa ya yarda, tun daga lokacin rik'o na ya koma hannun Aunty Zainab k'anwar Mama, ta had'ani da Ikram take shayar damu.
Tun rasuwar Mama Abba ya koma so silent ba ruwanshi da kowa, ba ruwanshi da mata kwata-kwata ma shi tsoran su yake ji, tunda rik'o na ya koma hannun Aunty Zainab wacce muke kira da Momy take yi min mugun so fiye da Ikram dan ko kuke mukeyi ni take fara d'aura, kai komai zatayi nice akan gaba, har Allah yasa muka fara girma mukayi wayo sosai, bayan Aunty Zainab ta yaye mu babu yadda Mannir bayyi akan ta raba d'aki damu ba amma taki tace yarda dole ya hak'ura, muna 4yrs aka saka mu a primary school nida Ikram dan komai namu tare ne kamar 'yan biyu babu wani banbanci a tsakani, dan bak'aramin so Aunty Zainab keyi min ba akaina babu abinda bazata iyayi ba, yayinda shak'uwa mai k'arfi ke shiga tsakanina da NASEER k'anin Dady mijin Aunty Zainab, sosai Naseer ke ji dani dan kusan kullum yana gidan, daga k'arshe ma kwaso kayansa yayi ya dawo gidan mu da zama, yayinda Dady ke ji damu kamar ransa, dan tun daga kan Ikram haihuwar Aunty ta tsaya cak, a haka muka yi ta girma har muka kai JSS 3 a lokacin duk wasu halittu na 'yan matanci sun fara fito mana, yayinda muke wasa ko wanne iri da Naseer, wata rana Aunty Zainab bata nan ta fita unguwa ta dawo ta iske Naseer yana min wasa da nono, iya tashin hanakali Momy ta shige shi, tunda nake bata tab'a ko harara ta ba amma ranar nasha duka, sannan ta mayarda Naseer gidan su dan a lokacin shi ya girma sosai Naseer bai dad'e da komawa gida ba ya tafi Halland dan k'arasa karatunsa, tun daga lokacin Momy ta sa mana ido sosai ni da Ikram
Lokacin d'aya muka gama secondary school da saukar Alqur'an a laocin duk wata halitta ta mace ta gama bayyana a jikin mu, dan muna da 17yrs mukayi Candy, a lokacin Abba nah yana da yara shida mu uka mata maza hud'u idan aka had'a mu bakwai kenan, wanda dakyar da jibin koshi aka aura masa NA'IMA k'anwar Mama wacce daga ita sai Aunty Zainab.
Bayan mun kammala secondary school da sati d'aya Naseer ya dawo bayan ya gama masters d'in shi, wanda har a lokacin ban san Dady da Momy ba sune suka haifeni ba, amma muna yawan zuwa gidan Abba da Alhajin sama sosai, bayan Naseer ya dawo ya fara nuna min wasu abubuwa wanda na kasa gane masa, daga k'arshe na yameni ya sanar dani yana so, nayi masifar shiga tashin hankali dan ni nasan Naseer ganin Dady ne kuma a iya sani na ba aure a tsakanin mu, hakan yasa na naje na samu Momy a parlor ina yi mata tambayoyi.
"Momy dama akwai tsakanin k'anin mahaika da kai,? abin ya bawa Momy mamaki cikin mamaki tace " a'a, yawwa Momy kenan ba aure a tsakani na da Uncle Naseer ko? gaban Momy yayi masifar fad'uwa, cikin rawar baki tace " eh a babu, ya akayi? " to amma Momy Uncle Naseer yace " yana so na zai aure ni?
Cikin firgice Zainab ta juyo yayiwa Zarah wani irin kallo, a tsorace tace " cewa yayi yana sanki? "Eh Momy wai aure na yake san yi, nan da nan gaban Momy ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku dan bazata tab'a manta ranar data kama Naseer yana wasa da nonon Zarah ba.......
Don't forget to vote and comment
MOMYN ZARAH