48
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
48
Dariya Aunty Zainab tayi had'i da cewa " kai badai ciki ba, duba dai da kyau ka ganin, murmushi yayi had'i da cewa " ciki ne da ita mana harna wata hud'u, tsaki tayi cikin fishi ta mik'e tana magana " baka san aikinka ba wallahi, ban san mahaukacin daya baka aiki ba, a baya Doctor ya biyo ta yana mata magana amma ko kallansa bata yi ba, direct wajen Zarah ta wuce, da taimakon nursing suka saka ta a mota ta, tana driving tana mita ita kad'ai harta k'arasa k'ofar wani private hospital.
Da gudu nursing suka fito, cikin girmamawa suka gaida ita had'i da d'aukar Zarah suka wuce ciki da ita, nan ma gwajin farko Doctor ya shaidawa Aunty Zainab tana da shigar ciki na 4 months, nan ma tijara ta zazzagawa Doctor d'in sannan ta d'auki Zarah tayi ficewarta, wasa-wasa dai sai da Aunty Zainab taje hospital har biyar amma duk maganar d'aya ce shine ZARAH TANA DA CIKI, har government hospital taje amma duk haka ake ci mata, sosai jikin Zainab yayi mugun yin sanyi amma har a lokacin bata yarda Zarah nada ciki ba, zaune tayi a cikin mota ta kasa yin komai jikinta sai kerrrrrma, a hankali ta juya ta kalli Zarah, takai wajen 10 minutes bata d'auke idanta daga kanta, tana san gano wani abu amma ta kasa, rasa abinyi tayi, ta jima tana tunani kafin daga k'arshe ta yanke shawarar kiran Family doctor su, ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi sannan ta ciro wayarta daga cikin jaka tayi dialing.
Ringing d'aya yayi picking cikin girmamawa, yace " Hajiya ya gidan? bata samu damar amsa masa ba illa cewa da tayi " kana ina yanzu? "ina asibiti ya bata amsa cikin kulawa, "ok ina san ganin ka right now, ok bani nan da 30 minutes zan zo in sha Allah, "no badamuwa bari nazo kawai ina kan hanya, cikin mamaki abinda take so da sauri haka yace " ok sai kin k'araso, batayi magana ba ta kashe wayar had'i da yiwa motarta key, dayake ba tazara sosai in 15 minutes ta k'arasa, waya tayi masa ta sanar dashi ta k'araso, da saurin sa yazo yana murmushi, martanin murmushi ta mayar masa cikin yak'e, ganin yanayin datake ciki bak'aramin bashi mamaki yayi ba, yace " Hajiya baki da lafiya ne?
" No Zarah ce bata d'an jin dad'i ta fad'a tana kallan cikin motar inda Zarah ke kwance, bin inda ta kalla yayi da kallo shima, da sauri yace " subhanallah bari nayiwa nursing magana, yana tafiya yana magana a ransa "wanne irin so Zainab takeyiwa yarinyar nan ne haka, daga bata da lafiya duk ta rud'e ta canja gaba d'aya ta fita daga hayyacin ta, yana maganar harya k'arasa inda nursing suke ya shaida musu akwai mara lafiya a waje, tare da Aunty Zainab suka shigo, office d'insa ya kai ta yace ta zauna kafin su gama duba Zarah ba musu ta zauna.
Direct d'akin duba marasa lafiya aka wuce da ita, bayan ya gama yi mata duk abinda ya kamata ya bata taimakon gaggawa ta farfad'o, sai da yayi test yakai 5 tyms amma sakamakon dai d'aya ne, sai da yayi test kala-kala a k'alla shida amma duk dai ciki yake gani.
Yayi masifar mamaki da shiga mummunan tashin hankali dan shi a iya saninsa yasan Zarah bata da aure, jiya ma Naseer ke sanar dashi cewar jibi auran su, a tunanin ta yadda zai sanar da Zainab wannan maganar ya farayi dan yasan akwai babbar matsala, amma yasan ya zama dole ya sanar da ita gaskiya, dan haka cikin sanyin jikiya nufi office d'in, cikin rashin kuzari ya zauna a kujerar zaman sa yana fuskantar ta, a hankali ya kira real name d'inta abinda bai tab'a yi ba dan ta d'au magarsa mahimmnci " Zainab!, gabanta ne yayi mummunar fad'uwa jin ya kira ainahin sunta, bata iya amsawa ba illa ido data zuba masa a matuk'ar tsorace.
Sai da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan yaci gaba " Zainab ko wanne mutum da kika gani a rayuwa yana da k'addararsa da jabarwa dan Allah bazai tab'a barin mutum ba jarabawa abinda nake so dake kiyi k'ok'arin cinye taki jarabawar please, kuma ki fahince k'addara, kar hakan ya zame miki sanadiyyar kamuwa da ciwo, dan duniya tasan irin mugun san da kike wa Za..... hannu ta d'aga masa had'i da cewa " what is going on? just go to straight to the point, cikin sanyin jiki yace " Zainab ina so ne ki fara fahimta kafin na sanar dak....... katse shi tayi ta hanyar cewa " go on Mr Doctor.
Cikin rawar murya yace " she is pregnant, a zabure Aunty Zainab ta mik'e tana huci tace " kai ma haka zakace kenan idan su sauran basu san Zarah kai ai kasanta tun kafin tasan kanta, amma kai ma mayar da kanka kamar sauran, murmushi had'i da mik'ewa yace " zo muje abinda yace kenan ya wuce gaba ta bishi a baya, umarni ya bawa nursing dasu kai Zarah scanning room, a baya suka bi su da Zarah, suna shiga yacewa nursing su fita, bayan sun fita ya kwantar da Zarah, ya fara yi mata scanning ya kalli Zainab yace " kalli kiga, baby Zainab ta gani yana ta wutsil-wutsil har an kusa gama masa halitta, Doctor yace " idan test zayyi k'arya scanning bazayyi k'arya yanzu dai kin gani da idanki.
Ya k'arasa maganar yana juyawa gefenta gabansa ne yayi muguwar fad'uwa ganin halin da take ciki, tsaye take cak kamar mutum-mutumi, idanuwanta kan na'urar scanning d'in, ta kasa koda matsa hannunsa da sauri ya mik'e ya k'arasa inda take yana kiran sunanta cikin tashin hankali " Zainab!!!!, bata ko matsa ba, hannu yakai ya tab'a ta yaga ta tafi luuuuuuu ta fad'i, cikin tashin hankali ya fara kwalawa nursing kira da k'arfi da gudu suka shiga.
Kai tsaye Emergency aka shigar da Aunty Zainab had'i da juna mata Oxygen, Doctors biyar ne akanta suna iya k'ok'arin su amma shiru har wajen 3hrs suna kanta amma babu ko alamar motsi gashi kuma zuciyar ta na bugawa, duk hunhunta yana motsi bare suce kota mutu, sun bata iyakar taimakon su amma babu wani ci gaba, haka suka hak'ura suka fito da ita suka kai ta d'aki had'i da saka mata na'urori kala-kala harda Oxygen d'in.
Itama Zarah an kwantar da ita asibitin kasancewar tana masifar jin jiki, sai bayan komai ya lafa Doctor ya kira El-Mustapha da Naseer ya nasar dasu halin da ake ciki, a rikice Naseer da Momy da Dady suka k'araso asibitin bayan sun sanar da familyn Zainab, kusan lokaci d'aya suka k'araso, a rud'e Naseer yake tambayar Doctor abinda ya faru, cikin in ina Doctor yace " Zarah ce bata da lafiya shine Hajiya ta fad'i, kamar daga sama Doctor yaji Naseer yace " meke damun Zarah!?
A tsorace Doctor ya d'ago ya kalli Naseer, yanayin yadda ya d'ago ya bawa kowa mamaki, kame-kame Doctor ya fara yi ya rasa abin cewa, a zafafe Naseer ya nufi shi yana cewa " baka ji ana maka magana ne? Kayiwa mutane shiru, da sauri el-mustapha ya k'arasa wajen had'i da dakatar da Naseer ya kalli Doctor yace " meke damun Zarah? yayi maganar yana kallansa ido cikin ido, ajiyar zuciya Doctor ya sauke dan yasan maganar kallan da Dadyn yake yi masa.
Cikin rawar baki yace " she is pregnant, "wad'in cewar Naseer da k'arfi, kan Doctor a k'asa yace " Zarah tana da shigar ciki na wata hud'u.
A razane Naseer ya shak'i wuyan Doctor yana cewa "ubanka ne yayi mata ciki?
Dakyar El-Mustapha ya k'ace Doctor daga hannun Naseer, ya kalli Doctor a firgice yace " wake da cikin Zarah ko Zainab?
A tsorace Doctor yace " Zarah ce keda cikin 4 months, ai Abban Zarah da Alhaji Abdullahi kasa motsawa sukayi jin maganar da Doctor ke fad'a, a razane Naseer yayi baya had'i da kurma mahaukaciyar k'ara da k'arfi wacce tayi sanadiyyar farkawar Aunty Zainab, cikin kuka ta fara magana " Zarah kin cuce ni duk irin tarbiyyar danayi muku, da tsarewar danake yi muku, duk abinda kuke so shi nake yi muku dame har namiji zai rud'e ki, yanzu da wanne idan zan kalli Abbanki da mahaifiyarki da k'arasa cikin mahaukacin kuka.
Naseer ma kukan yake yi sosai kamar ransa zai fita, kamar k'aramin yaro, kai Abban Zarah ya dafe had'i da zaman dirshen a k'asa ya kasa cewa komai, El-Mustapha da Momy tsaye sukayi kamar an dasa su, a hankali idan Aunty Zainab ya sauka akan Naseer dake kuka tuburan yana yarfe hannu.
A zuciye ta mik'e ta nufe shi tana tangad'i, cakumar kwalar rigarsa taci cikin matsanancin kuka tace " Naseer ka cuce ni, ka lalata min abinda na dad'e ina b'oyansa, cak ya tsaida kukansa jin abinda Aunty Zainab ke cewa, da wani irin kallan mamaki yake binta, dukan k'irjinsa ta farayi tana cewa " Naseer meyasa, meyasa zakayi min haka, akan me, menayi maka, lokacin daka tsaya a gaba na kake min bayanin irin sanda kake yiwa Zarah da irin ingantacciyar kulawar dazaka bata, na yarda da kai sosai da zuciya d'aya, na aminta ko bana raye zaka rik'e min Zarah hannu bibbiyu bisa amana da gaskiya.
" Ashe ba haka bane, na yaudari kai na danayi saurin yarda dakai Naseer, ta k'ara fashewa da matsanancin kuka, idansa Naseer ya runtse da k'arfi yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, k'irjinsa nayi masa wanirin zafi, mak'ogwaronsa yayi masa mugun d'aci, gaba d'aya jikinsa rawa yake yana tsuma, shi kansa yasan babu abinda zai fitar dashi daga zargin yiwa Zarah ciki har sai idan ita Zarah ta farka ta fad'i wanda yayi mata cikin sannan zai fita daga zargi daga wajen kowa dan yasan a halin yanzu bashi da mafita ko abincewa, da gudu Zainab tayi hanyar fita cikin zafin nama Abba ya rik'o ta, kallo d'aya zakayi mata kasan kwata-kwata bata cikin hayyacin ta.
A firgice tace " Abba ka kyale ni taje wajenta ta fad'a min wani tsinannan ne yayi mata ciki please Abba, tayi magana tana k'ok'arin kwacewa, kanta Abban ya shafa had'i da had'iye abinda yake ji yace " a'a Zainab ki bari sai kin ji sauk'in jikinki tukunna, "Abba babu abinda yake damuwa na lafiya k'alau, kwanciyar hankali na d'aya ku kai ni wajen Zarah, kanta ya shafa ba tare daya ce komai ba, sai ya lallab'a ta Doctor yasa mata drip da yaya mata allurar bacci.
Ana ranar Dady ya kira Mannir yace duk abinda yake yi ya dawo gida, dan ba lafiya, washe gari jirginsu yayi landing a airport d'in AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT, hankalinsa a tashe yayi gidan inda ya tarar da Ikram kawai, ya tambaye ta abinda ke faruwa, kasancewar batasan abinda k'e faruwa ba tace masa Zarah ce ba lafiya dan iya abinda ta sani kenan, sai da yaje asibiti yaga Zainab ma ba lafiya.
Tunda Naseer ya koma gida ya shige bedroom d'in sa ya rufe yake ta rusa kuka, yak'i bud'ewa yak'i ci yak'i sha babu yadda Dady da Momy basuyi akan ya bud'e k'ofar ba amma yak'i, kuka kawai yake tuburan baji ba gani, babban bak'insa yadda aka lalatawa Zarah rayuwarta.
Duk budurin da akeyi Zarah batasa ni ba, dan bata san wainar da ake toyawa ba.
Sai da su Aunty Zainab sukayi sati d'aya a sabitin sannan aka sallame su, Zarah ta warke sumul babu abinda yake damunta , haka ma Zainab ta warke sai da batayiwa kowa magana tun da abin ya faru burinta kawai taga Zarah.
Suna shiga gidan ita da Mannir suka tarar da Zarah da Ikram a parlor da gudu Zarah ta nufu Aunty Zainab tana" Momy I really misses you so much, Mannir shima dabe san meke faruwa ba yayi tsaye yana murmushi, a zabure Aunty Zainab tayi kan Zarah ta shak'e ta, wani irin mugun duka ta ko'ina ta shiga yi mata tana kuka, da sauri Mannir ya k'arasa inda take ya kwace Zarah.
"Lafiyarki kuwa Zainab kike mata irin wannan dukan me tayi miki?
Cikin kuka tace " Mannir ka bani ita ta sanar dani uban da yayi mata cikin jikinta, a kid'ime Mannir yace " what! Ciki Zarahn? "Eh mannir Zarah CIKIN SHEGE TAYI ta d'auko mana magana da abin kunya.
"Kin san abinda kike cewa kuwa?
Jakarta ta bud'e ta ciro d'auko gaba d'aya test d'in asibitin dataje, ta had'a da scanning duka ta mik'a masa hannunsa na rawa ya karb'a ya zauna akan kujera yana dubawa, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yake ta maimaitawa bai san sanda takardun suka zube k'asa ba, Zarah da tunda taji maganar ciki jikinta ke kerrrrrrma ta durk'usa had'i da d'aukar takardun tana dubawa, wani irin mahaukacin ihu ta saki had'i da zubewa k'asa a sume, a matuk'ar zuciye Mannir ya mik'e ya zage iyakar k'arfinsa ya shiga kasar mata mahaukatan naushi da duka tako'ina, take ya had'a mahangurb'a, dukan dayake mata ne ya farfad'o da ita daga suman datayi.
Sosai Mannir ke dukan Zarah, amma Zainab na tsaye ko gezau batayi, ita Zarah tama kasa kuka saboda gaba d'aya ba'a cikin hayyacinta take ba, ba zafin dukan tafi ji ba, zafin da zuciyar ta take yi mata shi tafi ji, kanta Mannir ya kama ya gwara da bango wanda sai da yayi sanadiyyar d'aukewa numfashinta.
Fad'uwa a k'asa a sume jini na zuba ta bakinta da hanvinta, fuskarta ta kumbura sumtum, gaba d'aya Mannir ya gaba sab'a mata kamanni, duk da suman datayi amma hakan baisa Mannir tausaya mata ya kyaleta ba, dukan nata yaci gaba dayi kamar mahaukacin zaki, dukan daya sumar da Zarah haka dukan ne ya farfad'o da ita.
Sai ya gaji dan kansa sannan ya kyale ta, anan ta zube tana mayar da numfashi sama-sama saboda wahala ta kasa tashi, jikinta duk a fashe, cikin kuka Ikram tazo ta ja ta bedroom taKaita kan bed ta kwantar ta sata gaba tana kuka.
A hankali Zarah ta d'ago kumburar kanta ta da jajayen idanta ta kalli Ikram dakyar ta iya bud'e bakin tace " Ikram da gaske ciki ne dani?
Kai Ikram ta d'aga mata hawaye na zubo mata alamar "eh, ido Zarah ta lumshe tana ambaton " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, had'i da shafo cikin ta, aiko wutsil taji ya motsa, a hankali ta bud'e idanta tana sauraran yadda Babyn ke motsawa sosai a cikinta, hakan ne ya k'ara tabbatar mata akwai d'a acikin cikinta, ita dai tasan ba'a tab'a samun ciki sai an kwanta da d'a namiji (sex) dan ta karanta a addini da kuma biology, ita kuma a iya saninta babu wani namiji daya tab'a saninta 'ya mace ko ya kusance ta, balle harta samu ciki, sai dai idan saka mata akayi dan ta tabbatar bata tab'a samun ciki haka nan ba, haka Zarah ya kwana cur bako gyangyad'i balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare, har gari waye, haka ma Aunty Zainab da Mannir babu wanda ya iya runtsa, balle kuma Oga Naseer.
Da sassafe Aunty Zainab ta shiga d'akin Zarah ta tarar da kwance cikin bargo tana ta kakkarwar sanyi, Ikram na gefenta, tsaye tayi a kanta tana kallanta cike da muguwar tsana dan yanzu kwata-kwata bata k'aunar ganin Zarah tace " Zarah ki sanar dani uban da yayi miki cikin nan, cikin kusa Zarah tace " wallahi Allah Momy ban san waye ba, nima ganin cikin kawai nayi a jiki na, wasu fitunannun marika ta watsawa Zarah wanda yasata hantsilawa cikin fushi tace " karki k'ara kirana Momy ni ban haifi MAZINACIYA ba, tsayar da kukanta Zarah tayi ta k'ura mata ido kawai, had'i da maimaita sunan da Momy ta kira ta MAZINACIYA!!! , a hankali tace " Momy wallahi nima ba mazinaciya bace, na rantse da girman Allah ban tab'a aikata laifin ZINA ba, K'ADDARA TAH ce haka.
Cikin zafin rai Aunty Zainab tace "cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, dakyar Zarah ta yunk'ura ta mik'e, dakyar ta take taka k'afarta, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa na rantse da girman Qur'an dake kai na bansan wanda yayi min ciki nan ba, ban kuma tab'a aikata zina ba.
Jikin Aunty Zainab yayi mugu mugun yin sanyi, gaba d'aya jikinta ya saki, zuciyar ta daina yi mata zafi da tafarsa dake ji, tasan Zarah tana da cikekken ilimin addinin islama, tana kuma da nutuwa da hankali tasan bazata tab'a rantse mata da Qur'an akan k'arya ba, a harzuk'u Mannir ya k'arasa shigowa d'akin dan dama yana tsaye yana kallan duk abinda ke faruwa, bai jira wata-wata ba hau dukanta tak'o ina baji ba gani, ya zage yadda zai daki k'aton gardi namiji d'an uwansa yayi ta kai mata naushi da kutufo a ko'ina, cikin rashin imani da tausayawa.
Ya rink'a gwara kanta da bango, yana d'aga ta sama yana jefarwa har sai da ta daina numfashi da motsi amma bai dai na dukanta ba, wata irin razananniyar k'ara Ikram ta fasa had'i da fita da gudu tayi wajen wayar Zarah, da sauri dayi dialing number Naseer, da kamar bazai d'aga sai kuma yayi picking ganin number Zarah ce, a gigice tace " Uncle kazo da sauri Momy da Dady zasu kashe Zarah, kayi sauri please karta mutu, a gigice ya fito da gudu yayi habar gidan dai-dai lokacin da Momy da Dadynsa ke yin parking sun dawo daga unguwa, ganin yadda Naseer ya fisgi motar a haukace sun san ba lafiya ba, dan haka suka rufa mishi baya.
Yana yin parking bai jira motar ta gama tsayawa ba ya fito yayi cikin gidan a haukace, a gefen motar sa su Dady sukayi parking suma suka fito suka nufi cikin gidan.
Naseer na shiga gidan ya jiyo ihun Ikram a bedroom d'in Zarah a hanzarce ya nufi can ya shaga kai tsaye dai-dai lokacin da Mannir ya shak'eta yana cewa " mu zaki rainawa hankali, kin tab'a ganin inda akayi cikin haka nan ko a ruwa ake sha, idanuwanta suka firfitu waje gaba d'ayansu suka kakke numfashinta ya tsaya..........
Don't forget to vote and comment
MOMYN ZARAH