GADAR ZARE…

49

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_


      ~NA~


*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 


*GARGAD'I*


'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 


~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*


*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*



49



A haukace Naseer ya k'asa wajen yasa hannu ya fisge Zarah daga hannun Mannir ya kalle shi ido cikin ido yace " wallahi duk abinda ya same ta bazan tab'a yarda ba sai nayi shari'a dakai, tsabar baka da imani ka zage iya k'arfinka da Allah ya baka a matsayinka na namiji kayiwa mutum wannan mummunan dukan sai kace ka samu dabba. 


Murmushi Mannir had'i da cewa " ai dole kaci haka tunda ka lallab'a ka d'urwa 'yar mutane ciki, shege munafuki mazinaci, masik'i kawai, abinda dama damai bak'ar zuciya, gadan-gadan Naseer yayi kan Mannir dai-dai lokacin da iyayen nasu ke k'arasowa, tsawa Dady ya dakawa Naseer had'i cewa " stop! Karka soma ina ruwanka da shiga tsakanin su ba tare ka gansu ba, yayi mata duk abinda zai iya, idan ma kashe ta zayyi gashi nan gata, tunda bashi da hankali yaga idan hukuma zata kyale shi, yayi maganar yana kallan Mannir dake ta faman huci. 


Aunty Zainab dake tsaye tunda aka fara abin bata motsa ba sai taga Naseer ya sumgumi Zarah yana niyyar yin waje da ita, da sauri tasha gabansa tana jefansa da kallan tsana tace " ina kuma zaka kaita? bayan ka riga da ka gama lalata, kallanta yayi ido cikin ido yace " kamar yayafa? 


"Ni zaka kalli ido na kace min kamar yayafa? sau nawa ina kama da ita, a zabure Dady ya juyo yana kallan ta yace " Zainab mekike kice? 


Hawayen fuskarta ta fara sharewa sannan tace " eh Dady gashi nan ku tambaye shi idan k'arya nake masa, wallahi sau uku ina kamashi yana romancing d'inta, kafin Dady yayi magana Naseer yace " da kika ganni ina romancing d'inta, kin ganni a kanta ne? ko kuma kin tab'a kamani akan ruwan cikinta ina sex da ita ya fad'a idansa cikin nata, dama Naseer akwai bak'ar zuciya, ganin ransa yayi masifar b'aci kuma sun san idan ransa ya b'aci haka idonsa rufewa yake yana iyayin komai yasa kuwa yin shiru, a hankali ya sunkuya ya sab'i Zarah a kafad'a yayi waje, Dady da Momy suka bi bayansa. 


Amma kafin su iske shi ya figi motar a 360, da sauri suka shiga mota suka bi bayansa, a k'ofar wani had'add'e private hospital yayi parking, da hanzarinsa ya fito ya shiga cikin hospital d'in bai jima suka fito da Doctor da nursing, kai tsaye emergency aka wuce da Zarah, tsaye Naseer yayi a k'ofar emergency room d'in yana safa da marwa, a haka su Dady suka k'araso, da sauri suka nufe shi, Dady yace " ya ake ciki ne? 


Naseer ya bud'e baki zayyi magana Doctor ya fito a gigice da sauri Naseer ya tare shi, Doctor yace " ina mijinta? batare da fargabar komai ba Naseer yace " nine? 


" accident d'in data samu gaskiya ya munana dan harda karaya biyu, a razane Naseer yace " what!!! KARAYA!!! a d'an tsorace doctor yace " eh k'afa da hannu, zaman dirshan Naseer yayi a wajen a k'asa ya fasa gigitaccen kuka, Kallan sa Doctor kawai yake yana mamakin namiji kamar Naseer amma da karyayyar. 


'''Ni ko nace hmmmmm Doctor baka san so bane'''


Sosai zuciyar Dady da Momy ta karaya, a hankali Dady ya cewa Doctor " kuyi duk abinda ya kamata kawai, ku d'orata, "ok doctor kawai yace ya juya ya koma cikin Emergency room, a hankali Dady ya durk'usa a gaban Naseer ya rungumo shi jikinsa yana lallashi yayinda Momy ke shafa kansa, a zuciyar Dady yana jinjina tsantsan rashin imani irin na Mannir, cikin kuka Naseer yace " Dady kana jin Doctor ma cewa had'ari ta samu dan shi a tunanin sa accident ne, babu wanda zayyi tsammanin wannan duka ne, Dady Mannir kwata-kwata bashi da imani, baya ganin akwai ciki a jikinta idan wani abu ya same ta fa, wallahi Momy bazan yarda ba sai nayi shari'a dashi kona rama mata, daga Momy har Dady babu wanda yace k'ala. 


Wayar Dady ya ciro daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ya sanar dasu halin da ake ciki, basu jima ba suka k'araso tare, cikin mummunan tashin hankali, anan Dadyn Naseer yayi musu bayanin duk abinda ya faru batare daya b'oye musu komai ba, sosai zuciyar Abban Zarah ta sosu, amman ya daure ya b'oye bai bari ko fuskarsa ta nuna ba, balle a gane yaji zafin abin, Alhaji Abdullahi ne ya harzuk'a ya rufe idonsa yayi ta zazzaga ruwan bala'i san ransa. 


Sai da akayi a k'alla 5 hrs sannan aka fito da Zarah jiki duk nad'e da bandeji, da hanzari su Naseer suka mik'e suka bayan su, wani shegen d'aki aka kaita mai shegen kyau da k'ayatuwa babu abinda babu harda kitchen da bathroom & toilet, a bakin gadon kusa da ita Naseer ya zauna had'i da k'ura mata ido hawaye na zuba, sosai al'amarin ya bawa duk jama'ar dake wajen tausayi, wajen 11:00pm na dare Dady ya kalli Momy da Naseer yace su fito su tafi, amma bud'ar bakin Naseer yace " in tafi ina?


Juyowa Dady yayi yana kallansa dan yasan dama za'a rina, fuska d'aure had'i cewa amma kasan dai bazai yiyu ka kwana nan ba ko? "ni fa Dady babu inda zani nabar Zarah, haba sai kace dai marar gata da galihu bayan wannan mahaucin dukan sannan atafi a barta babu wanda ya lura da halin datake ciki ga ciki a jikinta, a hasale Dady yace " to idan ma za'ayi jinyar tata kasan dai baka d'aya daga cikin jerin wad'anda suka dace ko? 


" please Dady kayi hak'uri amma babu inda zani, babu yadda Dady, Momy, Alhaji Abdullahi da Abban Zarah basuyi akan Naseer ya tashi ya tafi ba amma fafur yak'i ko motsi, dayaga an dame shi ma sai cewa yayi " wai me kuke gudu ne bayan mai afkuwa ta afku duk abinda kuke tsoran karrya faru ya rigada ya faru, dan ni babu inda zani, sanin Naseer na kafiya tun yana yaro yasa Momy cewa " shikenan kuje ni zan kwana dasu, sosai Abban Zarah da Alhaji Abdullahi sukaji dad'in karar da Momy tayi, dan haka suka shiga yi musu godiya " lah bakomai an riga an zama d'aya, Momy tacewa Dady " ka bawa driver barguna da pillows ya kawo min, Dady yace " to muje mana ki d'auko duk abinda ya kamata inyaso sai na dawo dake, ba musu ta mik'e tabi bayansa. 


Zarah najin k'arar rufe k'ofa ta bud'e idanta dan ta dad'e da farkawa kunya ce kawai ta hana ta bud'e idanta, duk budurin da akayi da Naseer akan kunanta, hawaye na zubo mata ta k'ura masa ido had'i da kiran sunansa a hankali " Uncle!!, a hanzarce ya juya yana kanta shima hawaye na zubo masa, dakyar ta bud'i baki tace " wallahi Allah Uncle ban san yadda akayi na samu ciki ba, please ka yarda dani, Allah yadda kuka  ga cikin nan a jikina haka nima na ganshi, wallahi Allah Uncle ban tab'a sanin wani d'a namiji ba, ban tab'a aikata zina ba, har rantsewa su Momy da Dady da Qur'an nayi amma sunk'i yarda dani ta fashe da matsanancin kuka. 


Shima kukan yake ya kasa cewa komai, "Uncle jibi irin dukan da Dady yayi min, Momy har kira na da MAZINACIYA (My up coming novel) tayi, kowa yak'i ya yarda dani, babu mai yi min uzuri, laifi na kowa yake dabuwa, nasan kai kowa yake zargi amma ni ban tab'a ji a raina ko sau d'aya zakayi min haka ba, na rasa mai yasa kwata-kwata zuciya ta tak'i zarginka, Uncle karka d'ai kawai a rage min a masu so na, na baya dan Allah Uncle karka guje ni, please ka yarda dani wannan ABU A DUHU (Next novel d'ina in sha Allah) yake, daga ni har kai babu wanda yasan MEKE B'OYE (shi kuma upper novel d'ina) har yanzu babu wanda yasan GASKIYAR AL'AMARI (Next upper novel d'ina) balle kuma duniya tasan SIRRIN B'OYE (My new novel). 


A hankali yasa hannu yana share mata hawayen dake zubo mata yace " karki damu Zarah, nima na rasa me yasa har yanzu zuciya tak'i ganin laifinki ko sau d'aya ba, wallahi na yarda dake 100% kuma ina tare dake d'ari bisa d'ari, cikin rawar murya tace " thank you Uncle, thank you so much, duk duniya a halin yanzu bani da sama dakai, bani da masoyi na gaskiya mai k'aunata tsakani da Allah sama dakai. 


_Ni ko nace hmmmmm Zarah kenan baki daddara ba kenan har yanzu_


Goshinsa ya d'ora akan nata suna kuka babu mai lallashin wani, Momy dake tsaye tana kallansu tun d'azu batare dasun sani ba, ta share hawayenta sai a lokacin ta samu sausauci a zuciyarta, d'an gyaran murya sannan tayi sallama, da sauri Zarah ta rufe idanta. 


Cikin tausayawa Momy ta k'arasa inda suke ta zauna a kusa da had'i cewa " ki bud'e idanki Fatima dan duk naji mai kuka ce, banbi Dady ba ganin dare yayi yace zai bawa driver ya kawo min, dan haka naji maganarki tun daga farko har k'arshe, a hankali Zarah ta bud'e idanta ta sauke su akan Momy yayinda hawaye keta faman ambaliya a fuskarta tace " wallahi Allah Momy ban san yadda akayi cikin nan ya shiga jikina ba, ban san mafarin abun ba illa BAK'IN GANI (still my novel) danayi, hawayen Momy ta goge mata karki damu Zarah, na yarda dake kuma nayi miki alk'awarin ina tare dake akoyaushe ko'ina, murmushin yak'e wanda yafi kuka ciwo Zarah tayi, Momy tace " karki sake ki damu karki saka komai a ranki balle ki jawowa kanki ciwo kinji, kiyi hak'uri kowanne d'an Adam da irin k'addararsa, sosai Momy ta kwantarwa da Zarah hankali sannan ta kira doctor ya dubata aka bata magungunanta.


Sannan Momy ta bata light food tad'anci d'an mitsitsi shima ba'a san ranta sai da Momy da Naseer suka matsa mata dakyar taci, , a b'angaren Aunty Zainab kuwa kwata-kwata bata runtsa ba, yadda taga rana haka taga dare dan bacci k'aurace mata yayi, haka ma Mannir dan shi safa da marwa ma yayi tayi a d'akin har gari ya waye. 


Washe gari da sassafe Zainab da Mannir, Ikram suka tafi gidan su Momy dan jin yadda Zarah ta kwana, dan ita Zainab tun da Zarah ta rantse mata da Qur'an kwata-kwata ta daina ganin laifinta ta karkata gaba d'aya laifin ta d'orawa Naseer dan tasan idan ba shi babu mai d'urkawa Zarah ciki, shine suke kullum kuma koyaushe, Mannir dai baya nan balle ta zarge shi dan yanzu 4 months 2 weeks kenan baya k'asar. 


Suna isa harabar gidan Dady na fitowa d'auke da kwandon breakfast, ya gansu sarai amma ya d'auke kansa ya shiga mota had'i da yiwa driver alamar ya taho, da sauri Mannir ya nufe shi yana yi masa magana amma Dady ko kallan inda suke bayyi ba balle ya amsa masa ya bawa driver umarni daja motar. 


Da hanzari Mannir ya koma cikin motar yana yiwa Zainab alama data shiga, ya figi motar ya rufawa Dady baya, acan Dady ya iske Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ana ta drama da Naseer ya tafi gida yayi wanka ya shirya ya dawo amman yak'i, su Dady suna gaisawa Mannir da Zainab shigo d'akin, a hasale Naseer ya mik'e zai zuba tijara Dady yayi saurin hanashi, Mannir na niyyar nufar gadan Zarah Dady yayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu, Zainab tsaye tayi k'em ganin mummunan halin da Zarah ke ciki duk jikinta nad'e da bandeji har fuskarta ga k'afarta da hannunta d'aya a sak'ale duk da k'arafa alamar d'ori , sosai Zainab ke kuka cike da tsananin tausayin Zarah. 


Mannir yace " please Dady ka barni na ganta wallahi tun jiya muke neman asubitin da kuke, daga ni har Zainab hankalin mu a matuk'ar tashi yake dukkan mu babu wanda ya runtsa. 


A hasale Dady yace " kuna san nata ne kai da matarka zaku had'a kai kuyi mata wannan mugun dukan da har Doctors suna tsammanin accident ne, babu wanda yayi tunanin wannan duka ne harda karaya biyu. 


"Karaya fa Dady Mannir ya fad'a a razane yana zaro ido, " baka da gani ne ko baka da ido ne ko dazaka shiko part d'in bakaga an saka Orthopedic ba, " dan Allah kayi hak'uri wallahi ban.... bai kai ga k'arasa maganar ba suka jiyo ihun Naseer, duk suka kalle shi,, da gudu ya nufi gadan Zarah yana kwala mata kira Zarah!!! gaba d'ayan suka kalli wajen, jini ne fitowa Zarah ta baki ta hanci data kunnenta, idanuwanta gaba d'aya sun kakkafe bak'in ya d'auke sai iya farin kawai, jikinta ya sandare, sai kaf-kaf datake kamar mai farfad'iya. 


A haukace Naseer ya shiga jijjiga ta yana kiran sunan Doctor da k'arfi duk ya fita daga cikin hayyacinsa, nutsuwarsa ta gushi ihuuuu kawai yake yana kuka, hannunsa Zarah ta rik'o da d'ayan hannunta mai lafiya dakyar tace " Naseer, yau ne rana ta farko data ambaci real name d'insa a razane ya d'ago yana kallanta ido cikin ido yana kuka kamar ransa zai fita, murmushin k'arfin hali tayi masa tace " nagode sosai da soyyayyar daka nuna min, dazan rayu dana yi maka..... bata k'arasa ba ta fara aman jini gunduwa-gunduwa dakyar ta tallafo fuskarsa tana murmushi tace " uncle mutuwa zanyi, please ka daina kuka, na baka amanar Momy na Ikram ka kular min dasu yadda zaka kula da kanka, ka yafewa Dady na please karka rik'e shi a ransa. 


Hannunsa da rik'e tana zabure-zabure can kusan tayi salati jikinta ya saki........ 


Don't forget to vote and comment 


MOMYN ZARAH