GADAR ZARE…

52

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*






52





Cikin tsananin firgici had'i da kid'ima Naseer ya mik'e had'i da karb'ar yaron daga hannun Dady yana dubawa, kallo d'aya ya yiwa yaron ya kau dai yana ambaton " Innalillaihi wa'inna ilaihirraji'un, tabbas shi kanshi yasan yana tsananin kama da yaron, a fili yace " ta ya haka ta faru? 



Da k'arfi ya runtse idansa jikinsa na tsuma, had'i da muguwar kerrrma duk ilahirin jikinsa rawa yake, yayinda zuciyar ta tsinke, zuciyar sa ta shiga bugawa da tsananin gaske, yayinda k'irjinsa ya shiga yi masa soya, mak'ogwaran sa ya fara d'aci yana yi masa mak'ak'i, yayinda zuciyar sa ta ci gaba da harbawa da tsananin gaske tana tsalle kamar zata tsaga k'irjinsa ta fito, gaba d'aya jikinsa ya d'auki mugun zafi lokaci d'aya , shi kansa yanzu ya fara zargin kansa yana mamakin taya hakan ta faru, had'i tuhumar kansa, shi dai a iya sanin sa bai tab'a kusantar Zarah ba, iyakacinsa d'an shan minti (romance) take yaji ya tsani kansa da kansa, ashe duk wannan abu daya samu Zarah shine sanadi, a hankali ya share hawayen dake zubo masa, ya kasa koda motsa hannunsa dan yasan yanzu bashi da bakin magana balle ya samu abin cewa, dan yasan shi kowa zai zarga. 



Shi babban tashin hankali ma ita kanta Zarah, tayaya zai kuma had'a ido da ita bayan tarin yardar daya mishi, d'azu-d'azun nan ta gama fad'ar yadda matsayinsa yake a gunta, yanzu idan ta farka taga yaron nan ya zayyi mai kuma zai ce mata, Alhaji Abdullahi ya mik'e a hankali gami da d'aukar yaron ya k'ura masa ido cike da tsananin tausayawa take hawaye suka fara zuba daga idanuwansa, a hankali ya shiga furta " kai kuma taga k'addarar kenan, haka Allah ya tsara maka, ta wannan hanyar zaka zo duniya, amma Allah yafi mu sanin dalilin dayasa yayi haka, dan Ubangiji baya tab'a yin abu babu dalili, duk abinda kaga Allah yayi to akwai dalilin yinsa, sai dai muyi addu'ar Allah ya kiyaye gaba, kallan Naseer yayi daya zama kamar wani tab'abb'e yace " wanne suna za'a saka masa, idansa ya k'ara runtsewa da k'arfin gaske had'i da furta "Innalillaihi wa'inna ilaihirraji'un, shikenan mai afkuwa ta auko ya yanzu kowa shi yake zargi, bashi da wata mafita, maganar Aunty Zainab ta tabbata. 



Sake maimaita masa tambayar Alhaji Abdullahi yayi, kasa magana Naseer, a hankali ya d'ago kai ya kalli Dadynsa yaga shima shi yake kallo yana watsa masa wata uwar harara gami da kallan tuhuma, da sauri ya sunkuyar da kansa k'asa, Dady yace " baka ji ana yi maka magana ne?




Cikin rawar murya Naseer yace " wallahi Dady yaron nan ba d'ana bane, ni bama Zarah kad'ai ba, ni da kowacce mace ma ban tab'a aikata ZINA ba, wallahi Dady ban tab'a sanin wata 'ya mace ba, a matuk'ar hasale Dady yace " to d'an ubanka ne idan ba d'an ka bane? da uban wa yake kama? sannan duk wasu shaidu sun nuna tabbacin yaro nan d'anka ne, ga CINDO sannan ga MARK, kuma kace zaka zo mana da maganar banza, ko akwai wanda kaji ya tuhume, koya yayi maka fad'a? "Dady aje ayi NDA test amma wallahil azim yaron nan ba d'ana bane dan ban tab'a yin zina a rayuwata ba, ran Dady ab'ace ya wanka Naseer kyawawan marika guda hud'u a jere, da sauri Abban Zarah ya rik'e Dady yana cewa " a'a Alhaji duk abin bai kai ga haka ba, shima yana da dama gami da hak'k'in gare kansa, daga b'acin rai yasa ka yanke hukunci cikin fushi wanda daga baya kazo kana danasani, " a fusace Dady ya kalli Abban Zarah yace " wanne danasanin zanyi bayan ga hujja da shaida nan Allah da kansa ya bayyana GASKIYAR AL'AMARI, sannan zaka d'aure masa gindi, dai-dai lokacin da Zarah ta farka tana tari had'i da salati, a hankali ta fara kiran sunan Naseer. 



Wani irin razananniyar fad'uwa gaban Naseer yayi jin Zarah ta farka kuma sunansa ta fara kira, da hanzari Naseer ya mik'e ya nufi bakin gadan, a fusace Dady ya ka mishi tsawa yace " karka sake ka k'arasa inda take, a hankali Zarah ta yunk'ura ta mik'e zaune, cikin sanyin murya irin ta marasa lafiya tace " Dady please let him come to me? ido Dady ya runtse gami da yin tsaki da k'arfi ya kawar da kansa gefe, Naseer na ganin haka da sauri ya nufi Zarah, cikin kuka yace " please Zarah ki sanar dasu bani ne baban yaron nan ba, ki fad'a waye ainahin mahaifin sa, ki gaya musu MEKE B'OYE, dan Allah ki sanar dasu GASKIYAR AL'AMARI da SIRRIN B'OYE please kona fita daga zargi, ke kad'aice kawai duk duniyar zata iya kub'utar dani daga zargi. 



Hannunsa ta rik'o cikin nata tana zubar hawaye, tace "wallahi Naseer nima kai na ban san waye uban yaro nan ba, ban ya akayi na samu cikinsa ba, amma ni dai abu d'aya na sani shine nasan bazaka tab'a yimin haka ba, nasan bazaka tab'a iya cutar dani ba, Naseer koda duk duniya zata yarda kai ne mahaifin yaron nan ni bazan tab'a yarda ba, ta rasa mai yasa zuciya ta tak'i yarda da aminta akan cewar kai ne kayi min ciki. 



Amma nasan komai daren dad'ewa gaskiya zata bayyana kanta koda bama rai raye mun bar duniya ne, Allah ne ya jarrabe mu daga ni har kai sai dai mu karb'i jarabawarsa hannu bibbiyu muyi addu'a Allah ya bayyana GASKIYAR AL'AMARI, ajiyar zuciya Naseer ya sake da k'arfi gami da k'ara damk'e hannunta cikin nashi yace " Alhamdulillah tunda baki yarda da hakan ba, dama ni tsoro na da fargaba ta d'aya kema karki yarda da abinda mutane suka yarda dashi, sannan karki aminta da abinda duniya zata ce, dan bana san kema ki rink'a yi min wani irin kallo kamar yadda sauran mutane zasu rink'a yimin, karki rink'a yi min kallan mugu, azzalumi wanda ya cuci rayuwarki ya gurb'ata miki daniyaki, ya musanya miki farin ciki da walwalar ki izuwa bak'in ciki da damuwa kuma ya..... jin an banko k'ofar d'akin da k'arfi yasa Naseer yin shiru batare daya k'arasa maganarsa ba. 



Zainab ta shigo cikin d'aurewar fuska ta had'e rai sasoi tace " Alhamdulillah, Masha Allah, yau dai anyi walk'iya munga gaskiya, kuma anyi iska munga d'uwawon kaza, GASKIYA AL'AMARI ya fito fili, ABU A DUHU ya bayyana kansa da kansa, yau kuma Naseer me zaka ce? da wanne kalar wasan kwaykwayon zaka kuma rainawa mutane hankali, ga yaro yayi kama da ubansa sak, sannan ga CINDO & MARK, Allah ne ya kawo k'arshen dramar ka Naseer, dubunka ta cika munafuki mak'iyin Allah, mik'ewa Naseer yayi duk da Zarah na k'ok'arin hana shi, amma zuciyar sa taje sama bazai controlling kan sa, daf da daf yaje kusa da ita ta yadda suna ina jiyo bugun zuciyar junan su ya kalle ta ido cikin ido ransa a matuk'ar b'ace zuciyar sa nayi masa ambaliyar wuta gami da k'una yace.



" Yes Zainab yaron can d'ana ne, jini nane halak malak na kuma karb'e shi hannu bibbiyu, babban abin takaicin shine ace ba'a san ubansa ba, to yanzu an san waye ubansa tunda gashi tsaye a gaban ki, kuma ubansa yakai uban daza'a iya nunawa duniya, saboda yakai duk inda wani namiji yakai, kyau, kud'i, ilimi, gata duk ina dasu, mu kalar tamu k'addarar kenan, ke ko ku an san kalar taku k'addarar da zata zo muku a nan gaba, kuma sannan ina miki albishi a yau d'in nan zan auri Zarah, kuma yanzu-yanzu anan ba'a wani waje ba, sannan na karb'i d'anta daga yau ya zama d'ana kuma na saka masa sunan uban rik'on ta mijinki wato MANNIR, hannu yasa a aljihu ya ciro kud'in dashi kansa bai san konawa bane ya risina ya mik'ewa Alhaji Abdullahi yace " ka dubi girman Allah ya aura min Zarah yanzu kuma anan take, da sauri ta d'ago kai ta kalle shi tana hawaye, kallan ta yayi yace " eh Zarah yanzu zan aure ki, in ga wanne d'an iska ko shege ne zai kuma nuna min iko da gadara a kanki, naga wanda ya isa ya kuma tab'aki matuk'ar ina raye, ya juya ka d'auki jaririn yace " daga yau sunansa MANNIR NASEER MUSTAPHA. 



Murmushin farin ciki Zarah ta rink'a yi yayinda hawaye ke zubo mata daga idanunta, sosai Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suka ji mugun dad'i da tsananin farin ciki ya gauraye musu duka zukatan su, Alhaji Abdullahi ya kalli Abban Zarah yace " kaje waje ka nemo mutane biyar suyi shaidu, sannan ni zanyiwa Naseer waliyyanci, ya kalli Dady dake tsaye yace " kai kuma sai kayiwa 'yar waliyyanci, ba musu Abban Zarah ya mik'e ya fita, zuciyar Aunty Zainab kamar zata fashe saboda tsananin bak'in ciki da takaici, kallan Zainab Naseer yaci gaba dayi ido cikin ido yayi tsaye kawai yana aika mata da silent killer smile, bak'in ciki ya k'ara turnik'e ta, AbbanZarah bai jima ba ya dawo da mutane wajen guda 10,nan take ranar a lokacin aka d'aura auren NASEER MUSTAPHA & FATIMA MUHAMMAD ZARAH.



Cikin nishad'i da fara'a gami da tsananin farin ciki Naseer ya kuma takawa har gaban Aunty Zainab yana murmushi yace " Alhamdulillah suruka ta tunda kinga k'arshen wason kwoykwayo na, kin san sai cikekken namiji mai kafin basira da tunani ne kad'ai dai iya tsara irin wannan wasan kwaykwayon, sannan GASKIYA AL'AMARI, da kike yawan fad'a gashi Allah da kansa ya bayyanar dashi cewar NASEER MUSTAPHA shine mijin Zarah, ABU A DUHU shima ya fito fili cewar NASEER MUSTAPHA shine mahaifin d'an ZARAH MUHAMMAD, sai me kuma kike cewa? ya fad'a yana karkata kai sama alamar tunani, sai kuma yayi murmushi yace " yawwa SIRRIN B'OYE da kuma MEKE B'OYE, hmmmmm suna duk ga sunan kin gani yanzu a gabanki sai kuma idan yaro ya girma yazo gidan kakaninsa cin tuwo ya k'arasa maganar idansa tarrrr cikin nasa yana silent

 smile. 



Cikin muryar kuka Zarah tace " please Uncle stop is, she is still my Mom like no other, wata gigitacciyar tsawa Zainab ta dakawa Zarah " dallah can rufewa mutane baki, sai bayan da kika bari ya gama fad'ar duk abinda zai fad'a yakai inda yake san kai, ya dasa aya sannan zaki yiwa mutane bariki da hanzari Naseer yasha gabanta yana girgiza mata kai had'i da cewa " no! no! Zainab, shi is now Mrs NASEER not miss Zarah, you have to be understand Mrs Mannir, dai-dai lokacin Mannir ya shigo cikin matsanancin farin ciki da walwala mara misaltuwa had'i da annushuwa direct wajen Zarah ya zarce bai ma lura da wad'anda ke wajen ba, sannu ya shiga yi mata yana shafa kanta had'i da k'ok'arin rungume ta, cak yaji an d'auke hannunsa daga jikin Zarah had'i da cewa " sorry Mr man, wannan ba Zarah'n daka sani da bace, wannan Zarah matar aure ce yanzu, kuma mijinta yana da tsananin kishin matarsa, dan haka don't ever touch her again if not, ya cije lab'ensa na k'asa da k'arfi. 



"What cewar Mannir a kid'ime, "yes she is Mrs Naseer, a matuk'ar firgice ya juya yana yiwa mutanen wajen kallan tambaya, sai a sannan Dady yayi magana " yanzu muka d'aura auren Naseer da Zarah, a hargitse Mannir yace " what kamar yaya Dady, "eh kamar dai yadda kake ji, kamar Mannir zayyi kuka yace " but why Dady? 



"Saboda Allah ya rigada ya tsara cewar Zarah matar Naseer ce, sannan ka d'auki matarka kubar wajen nan yanzu, tun kafin ran ku ya b'aci, wajen Baby ya nufa yasa hannu ya d'auke shi yayi hanyar fita dashi, tsawa Dady ya daka masa had'i da cewa " ina zaka kai yaron? "zan tabi dashi inda ya dace ne, dan ya samu ingantacciyar tarbiyyar gami da kulawa ta musamman ne, " baka da hankali ne, ya zaka raba yaro da uwarsa, d'ayen jaririn zaka raba da nonon mahaifiyarsa? 



"Eh Dady bazan bari su lalata shi kamar yadda suka lalace, murmushi Naseer yayi had'i da nufar inda Mannir yake, cikin tsananin fitsara yake kallan shi k'uri, murmushi yayi masa had'i mik'a masa hannu yace " bani d'a na, k'in bawa Naseer Baby Mannir yayi, da k'arfi Nasser yasa ya b'anb'are hannun Mannir daga jikin Baby ya kwace yaro, cikin tsananin b'acin rai yana ta faman huci kamar zaki, yayi hanyar fita yana cewa " Zainab zo mu tafi, har sun kai bakin k'ofa suka jiyo muryar Alhaji Abdullahi na cewa " Mannir daga yau mun din kasan ba alkhairi zai kawo ka kai da fitsararriyar matarka wajen mu ba karku kiskura ku k'ara zuwa inda muke, bai jiyo ba yayi ficewarsa Zainab ma ta rufa masa baya. 



Alhaji Abdullahi ya yiwa yaro hud'uba da sunan da ubansa ya rad'a masa MANNIR, yace a rink'a kiransa da Na'eem, ranar aka sallame su suka koma gida, da farko k'in Zarah k'in shayar da yaron tayi sai da Naseer ya nuna b'acin ransa a fili sannan ta fara Breastfeeding baby, sosai Momy ke kula da Zarah tana yi mata duk abinda ake yiwa wata 'ya mace 'yar gata idan ta haihuwa, kulawa ta musamman Momy ke bawata tana kuma gyara mata jikinta sosai had'i da tsumata da ingantattun magungunan mata, dan tasan muddin ta gama bik'i Naseer bazai tab'a d'aga mata k'afa ba, musamman yadda yake rawar kan nan.



_Hmmmmmm Ashe k'addara ta rigayi fata_



BAYAN WATA BIYU




Sosai Na'eem nake samun kulawa a wajen Momy, yaron yayi kyau yayi b'ul-b'ul dashi kamar d'an larabawa, gwanin ban sha'awa, yayinda Zarah ta tsane tayi kyau, tayi wani so fresh da ita, sai dai kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin matsananciyar damuwa, kwata-kwata Zarah bata cikin kwanciyar hankali tunda ta rabu da Zainab take cikin tunani da bak'in ciki akan rashin ganinta, gashi yanzu ko wayar bata kiran su, ta had'asu daga ita har Ikram tayi watsi dasu, dan ma Ikram tana matuk'ar k'ok'arin kwantar mata da hankali, haka ma Momy duk wani abu datasan zai faranta ran Zarah shi takeyi dan tana jin mugun tausayinta, tasha zama tayi mata kuka akan k'addarar da Allah ya jarrabe da ita gata yarinyar k'arama wacce har yanzu bata cika 18yr ba, kullum Momy sai ta markad'awa Zarah fruits ta zuba mata pick milk da honey aciki ta had'e ta bata tasha, sannan ga tsumi kala-kala da ingantattun magungunan mata data ta mafan d'irka mata, dana gyaran jiki, fata, breast, aiko cikin k'ank'anin lokaci tayi d'au da ita, tayi mugun kyau da shek'e duk da matsananciyar ramar datayi, dan tana cikin matsananciyar damuwa. 



Wajen k'arfe 12:00am na dare Naseer kwance akan bed d'insa sai juyi yake ya kasa runtsawa, haka kawai yaji yana san ganin Zarah dan haka ya mik'e a hankali cikin sand'a ya nufi d'akinta, dama tunda Zarah ta gama 40 ta mayar da ita bedroom d'in dake kusa da Naseer, sosai Momy ta gyara bedroom d'in, aka saka komai sabo, kamar a k'asar waje, cikin sand'a ya shiga bedroom d'in had'i da mayar da k'ofar d'akin ya rufe da key, a hankali ya lalubi makunnin light d'in ya kunna haske ya gauraye bedroom d'in, cak ya tsaya yayinda gabansa yayi muguwa fad'uwa, gaba d'aya jikinsa ya d'auke kerrrrrma a kid'ime bakinsa na rawa yace "............. 




Don't forget to vote and comment 



MOMYN ZARAH