GADAR ZARE…

55

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*






55






A haukace Naseer ya mik'e yace " waye ya mutum? please karku ce min Zarah, dafa shi Doctor d'in yayi had'i da cewa " am sorry, zuciyarta ce ta buga, cikin tashin hankali Momy ta kalli Doctor, batare datace komai ba, tun daga nan Naseer bai kuma cewa komai ba, ya koma ya zauna kamar wani sakarai, ganin an fito da Zarah daga emergency room fuskarta da jikinta rufe da farin k'yalle yasa Ikram d'ora hannu aka had'i da karma uban ihu ta sulale k'asa sumammiya, da sauri nursing sukayi kanta suka shiga bata taimakon gaggawa, Dady na hawaye ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi murya Dady na rawa yace " Assalamu Alaikum, jin yanayin muryarsa yasa Alhaji Abdullahi dake kishingid'e saurin tashi zaune, ba tare daya amsa sallmar ba yace. 



" El-Mustapha lafiya kuwa naji ka haka? 



Da kyar Dady ya daure yace " Allah ya yiywa Zarah rasuwa, cikin mummunan tashin hankali ya mik'e tsaye yana cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, cikin rawar murya yace " kuna ina yanzu? 



" Muna asibiti amma yanzu zamu karb'i gawarta mu koma gida, "ka sanar da iyayen nata? 



" No ban sanarwa da kowa illa kai dana sanar yanzu, " to shikenan mu had'u a gidan, a rud'e Alhaji Abdullahi ya mik'e yana sanarwa da Kakar Zarah, tana jin rasuwar Zarah ta fasa kuka, yana fituwa harabar gidan ya fara kwalawa driver kira kamar zai tashi sama, ana tafiya yana yiwa driver magana akan ya k'ara taka motar dan shi gani yake kamar ba tuk'in yake ba, a d'imauce Alhaji Abdullahi ya kira Abban Zarah yace su had'u yanzu a gidan El-Mustapha. 



Duk wasu k'adoji da ake bi wajen karb'ar gawa Dady ne yayi aka basu gawar Zarah suka nufi gida da ita, har lokacin Naseer yayi jigum kamar wani tab'ab'b'e koda za'a shiga mota sai Momy ta rik'o hannunsa ta shigar dashi. 



Haka kawai Abban Zarah yaci gabansa na muguwar fad'uwa, kwata-kwata hankacinsa yak'i kwanciya, tsoro da fargaba sun dirar masa a cikin k'ank'anin lokaci, dan haka ya kasa tuk'in yasa driver ya tuk'a shi. 



A mota Dady ya kira Mannir yace masa duk abinda yake yi ya bashi nan da 10 minutes su had'u a gida dashi da Zainab su zo yanzu, a tare Dady da Alhaji Abdullahi, Abban Zarah suka isa gidan, ana yin parking Naseer ya fito sukuku ya shige bedroom d'insa ya rufe, yayi zaman dirshan a k'asa, ya kasa yin komai dan kwakwalwarsa ta daina aiki, shi bai ma san waye shi ba, da gudu Ikram ta fito ta fad'a jikin Alhaji Abdullahi tana gunjin kuka, fito da gawar Zarah akayi daga cikin mota aka shigar da ita main parlor gidan, shi dai Abban Zarah tsaye yayi cikin mutuwar dan har yanzu bai san takamai-mai abinda ke faruwa ba. 



Cike da matsanancin farin ciki Mannir ya shigo gidan yana d'okin ganin Na'eem, Zainab ko sai cika take matsewa, tun daga harabar gidan take jiyo ihuuuu Ikram tana kuka, da sauri Mannir da Zainab suka k'arasa shiga gidan cikin matsanancin firgici, da sauri Ikram ta saki jikin Alhaji Abdullahi tayi wajen Zainab tana kuka tace " shikenan Momy Zarah ta tafi ta barmu, Momy ZARAH TA MUTU!!!.



Wai tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, saboda tsabar rud'ewar da Zainab tayi rufe Ikram tayi da duka hannu bibbiyu kamar zata kashe ta tana cewa" uban ki ne ya kashe ta, dakyar aka kwaci Ikram daga hannun duk ta rud'e ta fita hayyacinta. 



Shiko Mannir k'amewa yayi a tsaye ya kasa kwakkwaran motsi, a hankali Alhaji Abdullahi ya kama hannun Zainab ya kai ta har gaban gawar Zarah dake kwance yace " gata nan ki bud'eta ki gani da idonki dan ki tabbatarwa da kanki, hannun Zainab na kerrrrrrma idanta na duk ya firfito waje tasa hannunta dake rawa ta yaye farin k'yallen da aka rufe fuskar Zarah dashi, da sauri ta runtse idanuwanta had'i da had'iyar yawu k'uttttttt. 



A hankali ta sauke idanta akan gawar Zarah, a haukace Zainab tayi baya da sauri had'i dayin zaman dab'aro a k'asa ta d'ora hannu aka ta kurrrrrrma uban ihuuu, a d'imauce take girgiza kanta hawaye na zuba tana cewa " wallahi k'arya ne Zarah bata mutu ba, duk wanda yace min Zarah ta ta mutu sai na kashe shi. 



A kid'ime ta mik'e ta nufi wajen Dady tace " Dady please ka dawo min Zarah ta, ina tsananin buk'atar ta, idan ta mutu ta barni nima mutuwa zanyi, wallahi ina matuk'ar san Zarah sosai, har cikin rai na da zuciya ta kullum sai nayi kukan bak'in cikinta a kusa dani, dan girman Allah ku tashe ta, ganin Dady bayyi magana bane tasa ta nufar Alhaji Abdullahi tana k'ugin mutuwa tace " please Abba ka taimaki rayuwa ta ka dawomin da Zarah ta da.......... 



Wani gigitaccen mari Alhaji Abdullahi ya kifawa Zainab, cikin k'onar zuciya yana zubar hawaye ya kalle ta yace ", kina san nata ne kika yi watsi da ita da lamuranta, dan Allah ya d'ura mata k'addara, wacce ke kanki yaki fi k'arfin Allah ya jarrabeki da irinta ba, wanda nasan idan ke Allah ya jarraba da irin k'addarar daya jarrabi Zarah da ita Fatima mahaifiyar Zarah bazata tab'a yin watsi dake da rayuwarki ki ba. 



" Wallahi nasan mahaifiyar zata bazata tab'a yi miki abinda kikayiwa tilon 'yarta ba, nasan koda duk duniya zata juya miki baya ta k'i ki Fatima bazata tab'a juya miki baya tak'i ba, koda za'a zare mata rai, zata iya rabuwa da kowa akanki, tasha hawala akanki, tayi wahala dake iya rayuwarta tayi miki duk abinda uwa take yiwa 'yarta, ko sau d'aya bata tab'a kallan ki a matsayi k'anwarta ba, tana d'aukarki ne a matsayin 'yar cikinta, amma ke tilon 'yarta guda d'aya tak data mutu ta bari bari in kasa yi mata irin rik'on data yi miki, kin wulak'antar da ita da rayuwarta, alhalin nasan da Ikram Allah yayiwa wannan jarabawar dabaki mata abinda kikayiwa Zarah ba. 



"Mahaifinta cikekken mutum ne wanda ya isa a kira shi d'an halak, kuma asalin bafulatani na kwarai, tun da ake abin nan yayi muku kara ke da mijinki bai tab'a yin ko tari ba, bayan nasan yana jin abin har cikin ransa da k'ok'on zuciyar sa, yana dai d'auke kai ne kawai, har dukan mutuwa kukayiwa 'yarsa , da karaya biyu, amma ko kallan banza bayyi muku ba, bayan kema a matsayin 'ya kike a wajensa, yana da ikon hukunta kamar yadda kuka hukunta Zarah, tak'amarku dai kun rik'e Zarah kuke ganin kuna da k'arfin iko akan ta, to kamar yadda kuka rik'e masa 'yarsa haka shima ya rik'e ki, duk gata da so da kike tak'amar kinyiwa Zarah haka shima yayi miki, kuma bashine ya baki rik'on Zarah da kansa ba, ke da kanki kika nema wanda a lokacin ma kara yayi miki kawai ya baki dan bai so rabuwa da 'yar sa a lokacin ba, amma haka ya daure ya baki ita.



Saboda kara irin ta shi, dan ko a mutanen da ba kowa ne zayyi irin karar da yayi ba, kuma tunda ya baki ita bai tab'a nuna miki komai ko a fuskarsa ba, amma ku kun taru kun azabtar mishi da 'ya, daga k'arshe ma kunyi sanadin barinta duniya, kina tsammanin Fatima zatayi farin ciki da muguwar sakayyar da kika mata ya k'arasa maganar yana hawaye, cikin muryar kuka yace " na zuba muku ido ne dan naga ko zaku gane abinda kukeyi ba dai-dai ne kuskure ne, ku gane kuranku amma ina kun riga da kunyi nisa, ni wallahi kunyar Muhammad nake ji, da sauri Abban dake kuka tun lokacin da Ikram tace Zarah ta mutu, sosai yake kukan bak'in ciki da takaicin karar da yayiwa wad'anda kwata-kwata basu san kara da kawai ba yace. 



" A'a Alhaji har abada babu wannan a tsakanin mu, kuskure ne mu duka munyi sai dai a kiyaye gaba, Zainab dake tsaye ta zube akan gawarar Zarah had'i da d'ora hannu aka ta zunduma iban ihuuuu ta na birgima tana cewa " wayyyyyyyo ni Zainab na shiga uku naga ta kaina ina zan sa rai da rayuwata, naga taskon rayuwa gami k'angin duniya, sosai Zainab take bori had'i da zunduma uban ihuuuu. 



Cikin rawar murya Dady yace " duk mai faruwa dai ta riga da ta faru aikin gama ya gama, yanzu muyi gaggawa kamar yadda Allah yace mu kaita makwancinta, Alhaji Abdullahi yace " a shirya ta kafin sallar juma'a sai ayi jana'izarta a masallacin juma'a bayan an idar da sallar juma'a, cikin k'anganin lokaci akayi mata wanka aka shirya ta tsaf cikin likkafani a bisa koyarwar sunnah, Alhaji Abdullahi yace " a kira mijinta, d'an jummmm Dady yayi dan yasan akwai tashin a kiran Naseer shi inda san ranshi ne a barshi kawai a yadda yayi hocking d'inan, k'ara maimaita maganar Alhaji Abdullahi yayi a karo na biyu, cikin mutuwar jiki ya nufi bedroom d'in Naseer, acan k'uryar gado ya had'a kai da gwiwa kawai ya rasa meke faruwa. 



Hannunsa Dady ya rik'o batare dayace masa komai ba, aiko ba musu Naseer ya biyo Dady kamar sakarai ko dolo, haka suka isa parlor kamar rak'umi da akala, Alhaji Abdullahi ya nuna masa gawar Zarah dake rungume a jikin Zainab yace " kayiwa matarka addu'a.



A hankali Naseer yabi inda Alhaji Abdullahi ya nuna masa da kallo, maganganun da Zainab keyi rungume da Zarah ne suka dawo dashi cikin hayyacinsa, Zainab cikin kuka ke cewa " ina sanki Zarah, dan Allah ki dawo karki tafi ki barmu please, wallahi ina miki mugun so, meye zakiyi nesa damu, meyasa ta har abada ba dawowa Zarah meyasa zaki MUTU!!!. 



Sai a lokacin Naseer ya tuna abinda Doctor yace masa " ALLAH YAYIWA ZARAH MUHAMMAD RASUWA, a hankali ya juya inda inda yake jiyo gunjin kuka Ikram ya juya kalli Abban Zarah yaga shima kukun yake, a hankali ya rink'a bin jama'ar wajen yana kallonsu, yaga kowa kuka yake ya juya ya kalli gawar Zarah dake kwance cikin linkafani tab!!!! tashin hankali wanda ba'a sa mara rana, wani irin mahaukacin gigitaccen fitinannan uban ihuuuuu Naseer ya baki iya iya k'arfinsa ya kurma had'i da dafe fuskarsa da tafin hannusa ya durk'ushe wajen yana kurma gigitaccen Ihuuuuuuuuuuuuu kamar ransa zai fita.




Hannu yasa yana cizgar gashin kansa yana yakushin fuskarsa, yana ci gaba da sakin fitinannan ihuuuu, a haukace yaje wajen gawar Zarah ya d'aga ta ya rungume gam a k'irjinsa yana kuka yake cewa " mai yasa zakiyi min mai yasa zaki tafi ki barni, bayan kin yi min alk'awarin kasancewa dani har rai da mutuwa, mun gama tsara rayuwarmu, mun tsara yadda zamu rayu da yaran mu cikin farin ciki, mai yasa Zarah ya k'ara fashewa da mahaukacin kuka, dai-dai lokacin Na'eem ya tashi daga bacci had'i da tsandara k'ara, a kid'eme Naseer ya nufe shi ya d'aushi ya kawo shi kan gawar Zarah yana nuna masa yace " please Na'eem kacewa Momynka ta tashi karta tafi tabar mu cikin maraici da kad'ai, gaba d'aya Naseer ya fita fit daga hayyacinsa ya koma cikekken mahauci, cikin rashin nutsuwa yake yin komai, sai a lokacin hankalin Mannir dake tsaye kamar mutum mutumi dan ya gazayin komai, tsaye kawai yake yana zubar da hawayen bak'in ciki daka kallan shi kasan yana cikin tsantsan nadamar rayuwa, hankalinsa ya kai ga Na'eem dake ta faman rusa kuka yana laluben nonon Zarah. 



Cikin tsananin bak'in cikin rayuwa Mannir ya fasa kuka dan ya kasa controlling kansa, gaba d'aya wajen tausayin Naseer da Na'emm ya mamaye musu zuciya da duk ilahirin jikinsu, tuni Zainab ta yada hijab da d'an kwalli babu abinda ya rage a jikinta sai doguwar riga, duk ta zare ta d'imauce ta fita daga hayyacinta, a firgice ta mik'e ta nufi Naseer tasa hannu tana k'ok'arin kwace Na'eem daga gareshi, d'ago jajayen idanuwansa da suka gama rinewa yayi ya kalle ta, ganin Zainab ce tsaye a gabansa tana k'ok'arin kwace Na'eem yasa shi tuna duk abubuwan data yiwa Zarah. 



Aiko cikin zafin rai ya mik'e ya kifa mata lafiyayyen marika guda biyu kyawawan masu k'arfin gaske wanda sai da suka sakata bajewa wanwar a k'asa,, ya damk' i wuyanta yace " kinsan me yayi sanadiyyar mutuwar Zarah? 




A haukace yace " mata ciwon zuciya, ya nuna saitin zuciyarsa yace mata " zuciyarta ce ta buga, wanda kece sanadiyyar faruwar hakan, Zainab, Zarah bata da wata matsala ko damuwa balle bak'in ciki sai naki, kullum sai tayi kukan rashinki a kusa da ita da kuma kewarki, kallo d'aya zaga yiwa Zarah kasan tana cikin matsananciyar damuwa, duk iya k'ok'arin dake nake naga na sanya ta cikin farin ciki da walwala amma a banza saboda tunaninki, duk iya k'ok'ari na akan naga Zarah ta rayu cikin farin ciki amma sai da kika wargaza min burina KIKA YI AJALIN ZARAH. 



A firgice ta kalle shi cikin alamun tambaya amma ta kasa furta koda kalma d'aya, kallanta yake shima yace " yes ZAINAB KECE SANADIYYAR MUTUWAR ZARAH, saboda da bakiyi abinda kika yi ba da bata mutu ba, da kin yarda da k'addara, kin kuma d'auki k'addara kin fauwalawa Allah komai da hakan bata faruwa ba, da kin rungume ta kin saurare ta, kinyi mata gata kin zame mata uwa ta gari da batayi kukan bak'in ciki har ciwon zuciya ya kamata ba, da kin yarda da rantsuwar data miki da Qur'an da kin jata ajikinki kin nuna mata so da kulawa Zainab kin cuce mu. 



 Wani mahaucin kukan ya kuma saki, cikin rashin nutsuwa Naseer yasa hannu ya damk'i k'afarta ya fara janta a k'asa............. 






Don't forget to vote and comment 




MOMYN ZARAH