GADAR ZARE…

56

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*






56






Ya fara janta a k'asa har bedroom d'in Zarah inda tayi aman jini ya nuna mata cikin kuka yace " kin gani ko? saboda tsabar takaici da bak'in cikin ki, ji yadda ta rink'a aman jini, tana kokawa da ranta dan tanaso taci gaba da rayuwa damu, amma kika sata dole ta barmu badan ranta na so ba ya k'ara fashewa da fitinannan kuka. 



A razane kamar an tsikare shi ya mik'e tsaye ya kuma damk'ar kanta yayi waje da ita, yana isa parlor yayi jifa da ita a k'asa ya durk'uso da fuskarsa dai-dai fuskarta yace " kin san menene magana ta ta k'arshe da ita, batayi magana ba illa kansa dake tayi, yace wasiyya akan ku keda wancan lusarin mijin naki, ya d'ago da kansa ya k'ara kurma ihuuuuuun mutuwa gaba d'aya idanuwansa sun canja launi, sun tashi daga farare zuwa ja, sai da yayi mai isarsa sannan ya kuma juyowa wajen Zainab a haukace yace " maganar ta ta k'arshe shine in kulan mata da Momynta, in yafewa Dadynta ko d'anta data haifa wanda shine k'arami bata fara ambatan sunanshi ba, sunanki ta fara ambata , dan haka ZAINAB KECE AJALIN ZARAH, ya fad'a da k'arfi. 



A haukace Zainab tayi harabar gidan ba d'an kwalli ba takalmi balle hijab, tana ihuuu kamar zararriya, babu wanda ya iya motsi balle ya taro ta sai Mannir da shima jikinsa ya gama yin mugun sanyi, ya bita a rud'e yana kiran sunanta tana gaf da fita daga get d'in gidan ya cimmata, cak ya d'auke ta, tana ihuuuu da zille-zille a parlor ya direta, dai-dai lokacin da Abban Zarah yace " lokacin sallar juma'a yana neman ya wuce, mu hanzarta mu kai ta makwancinta, ba musu duk suka mik'e suna shirin d'aukar gawar Zarah, fitinannan ihuuuu Naseer yayi had'i da rik'e gawar gam. 



Yana ihuuuu yana gunji yana kuka, had'i da sambatu, " wallahi babu inda zaku kai min Zarah ta, bata mutu ba, nasan bazata tab'a tafiya tabarni ba, munyiwa junan mu alk'awarurka da dama, kuma nasan Zarah akwai amana da gaskiya bazata tab'a karya min alk'awari na ba, dan Allah Dady ku tausaya min karku rabani da Zarah please, wallahi ina santa ina mata mugun so, wallahi bata mutu ba, dan Allah karku raba mu muna matuk'ar k'aunar junan mu da gaske da kuma zuciya d'aya ya k'arasa maganar cikin mahaukacin kuka. 



Sosai aka kama kokawa tuburan muraran da Naseer ya rik'e Zarah gam ya hana a tafi da ita, ya zage ya rink'a tikar hauka muraran, ya zama cikekken mahaucin tuburan,  sai da kyar Dady da Abban Zarah da Mannir suka taran masa suka danne shi suka jashi, aka danna shi a d'aki aka rufe, buga k'ofar Naseer ya shiga yi yana ihuuuu kamar zai b'alla k'ofar, ana zuwa za'a kuma d'aukar gawar Zainab ta rik'e gawar gam tana kurma ihu, gaba d'aya jikinta rawa yake yana muguwar tsuma kamar wacce ake kad'awa ganga. 



Itama dakyar Mannir ya jata ya danna a d'aki tana ta turjewa tana tik'ar hauka, tana ihuuuu gami da fisge-fisge, Abban Zarah Naseer ya shiga kwalawa kira yana rok'onsa " dan girman Allah Abba ka bud'e naje na bunne Zarah da kai na, ko zuciya ta ta huta, wallahi Abba matuk'ar bani na binne Zarah da kai na, na saka ta a kabari da hannu ba zuciya ta bazata tab'a barin rayuwa ta ta huta ba, bazan tab'a yarda Zarah ta mutu da gaske, kun sanya min kokonto kennan har k'arshen rayuwa ta, dan Allah ku bani wannan damar dan in rayu cikin salama batare da kokonton komai ba, yana bubbuga k'ofar kamar zai b'allata yake maganar.



Ganin maganar da yake tana da matuk'ar mahimmanci da amfani yasa Abba tsayawa a bakin k'ofar d'akin yace " kayi min alk'awarin idan na bud'eka bazaka tab'a yimin hauka ba, da sauri Naseer yace " nayi maka alk'awari Abba, batare da Abba yace komai ba ya bud'e shi, yace " kaje bedroom d'inka ka shirya kazo mutafi muna jiranka a waje, "a shirye nake Abba muje kawai, Abba bai k'ara cewa komai ba ya wuce Naseer yabi bayansa, tunawa da Naseer yayi a daren jiya ya kashe arna kuma bayyi wankan tsarki bane yasa shi cewa Abba bari na dawo, kallansa kawai Abba yayi. 



Naseer yana wankan yana kukan bak'in ciki mai sauti, harya gama wankan ya zura kaya ya fito, sanin komai yana iya cakud'ewa ne idan Naseer ya fito yaga gawar Zarah yasa akayi saurin sata a mota kafin ya fito, yana kukan ya shiga mota suka tafi, suka bar Momy da Ikram na kuka, yayinda Zainab ke cikin d'aki kulle tana hauka, a babban masallacin juma'an gidan sarki akayi sallar gawar Zarah Naseer nata kuka har a lokacin yak'i yin shiru, daga nan sukace mak'abartar d'an agungi dake wajen k'ofar Na'isa, kafin suje har anyi ginin kabari, sai da akayi mata addu'a sannan Naseer da Abba suka kama gawar Zarah suka sakata a makwacinta na k'arshe, Dady, Abba na zubar hawaye amma Naseer kuka yake sosai dan ya kasa dannar zuciyar sa, da hannunsa yau yasa Zarahn sa a kabari, dole babu yadda zayyi da kanshi ya mayar da k'asa ya bunne ta. 




_Am so sorry fans, da mutuwar Zarah, ina san nayi muku tuni da كل نفس ذائقه الموت, duk mai rai dole mamaci ne, bawai ayita karatun novel na zallar soyayya, hot romance and sex ba, ya kamata a rink'a sirkawa da abinda ya riga ya zama dole kuma yana kan kowa, mu dai fatan mu Allah yayi mana rahama yajik'an mu, ya yafe mana yasa mucika da imani muna masu ambaton  اشهد ان لا اله الا الله واشهد ان محمدا عبده ورسوله_



~Wannan kenan~



Tunda aka fito daga mak'abartar Naseer ya d'ora hannu aka ya zunduma ihuuuuuuuuu had'i da rugawa a guje,, ya zage ya zama cikekken mahaukaci ya rink'a hauka tuburan muraran, a kid'ime Dady yayiwa mutanen dake tare dasu magana akan su taimaka masa su kamo Naseer, da gudu wajen mutane 10 suka bi bayansa ciki kuwa harda Mannir, dakyar da jib'in goshi suka samu nasarar kamo Naseer, sai da suka ci uwar dambe sannan yayi matuk'ar basu wahala sannan suka samu nasarar danna shi a mota suka danne shi driver yaja motar. 



Koda aka je gida sai da akayi fama sosai sannan aka samu aka saka shi a d'aki aka kulle, fashe-fashe Naseer ya shiga yi a bedroom d'in nasa, duk wani abu daya danganci glass sai da yayi rugu-rugu dashi ya fashe komai dake d'akin, ya rink'a ihuuuuuuu yana hauka gami da matsanancin kuka mai tsananin cin rai, kowa a gidan jikinsa yayi matuk'ar yin sanyi kowa ka gani cikin matsanancin bak'in ciki da damuwa yake baka jin komai sai sheshshekar kuka, Zainab kuwa itama sai hauka take a d'akin da aka kulle ta tana kuka kamar ranta zai fita tana dukan k'ofar. 




Bayan kwana akwai da rasuwar Zarah aka share makoki, kuma tunda aka rufe Zainab da Naseer ba'a bud'e su ba saboda haukan da suke, sai ranar da akayi sharar makoki sannan Alhaji Abdullahi yace a fito da su, ba musu aka bud'e su, duk sun rame sun fita hayyacin su sunyi bak'i sosai kamar ba su ba, Zainab da sauri ta fad'a jikin Abban Zarah ta k'ara sakin hargitsatstsan kuka cike da tsananin nadama cikin kuka tace.



" Abba Zarah ta tafi ta barni, Abba meyasa Zarah tayi min irin wannan hukuncin mai tsananin gaske, dan Allah ka taimake ni ka bata hak'uri kace ta dawo ina tsananin k'aunar ta, duk abinda nayi, nayi ne bisa zafin zuciya, amma yanzu nayi matuk'ar nadama, da danasani, na tuba ya Allah استغفر الله و اتوب اليك na shiga uku ina zan saka kaina da rayuwata, idan laifi nayiwa Allah ya hure ni da irin wannan masifar mai zafi, Allah na tuba, ka yafe min ya Allah, ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai tab'a zuciya, take jikin kowa yayi mugun yin sanyi zuciyar kowa ta karye, kowa ya shiga zubar da hawaye, Naseer ko tunda ya fito ya koma gefe ya rakub'e bai kuma cewa k'ala ba, gaba d'aya ya koma miskini kalar tausayi. 



Hawaye na zuba daga fuskar Abban Zarah ya shafa kan Zainab yace " wanda ya bamu ita ya kuma fi mu santa ya karb'i abarsa dan alk'awarin Allah baya tashi, babu abinda Zarah tafi buk'ata daga gare mu yanzu sama da addu'a shine kad'ai hanyar da zamu nuna mata tsantsan so da k'aunar da muke mata, muna nan duk zaman jiran namu lokacin komawa ga Allah muke, domin gaba d'ayan mu matafiya ne, komai dad'ewar dazakayi a duniya dole akwai ranar da zaka barta ka amsa kiran mahaliccinka. 



" Dan mutuwa bata kwankwasa k'ofa, kuma Allah baya tab'a barin wani dan wani yaji dad'i, idan lokacin mutum yayi ko 1 second baza'a tab'a k'ara masa, a koyaushe, a ko'ina idan lokaci yayi tafiya zamuyi batare da wani b'ata lokaci ba, shin kana ina, me kake aikatawa a dai-dai lokaci nan, wallahi idan tazo aduk yadda kake tafiya zakayi, shiyasa ake san a koyaushe, a ko wanne lokacin mutum ya kasance yana aikata alkhari, ana san d'an Adam ya kasance mai tsoran Allah, mai aikata alkhari a kowacce rana dan yanzu mutuwar bazata ake yi, sai a kwanta dakai ba'a tashi da kai ba, ko'a tashi dakai ba'a kwanta dakai ba, dan haka mu kasance masu tsoran Allah da tunawa da ranar sakamako, mu kyautata mu'amular a tsakaninmu, mu kyautatawa junnanmu zato, mu zamo masu yafiya da afuwa, mu zamo masu zumunci, mu zamo masu duban laifukan kan mu, bana wasunmu ba, mu zamo masu yiwa kanmu hisabi. 



Sosai Abban Zarah yayi musu nasiha mai ratsa zuciya, daga k'arshe Alhaji Abdullahi ma ya k'arba yayi iya yinsa akan yadda da k'addara da jarawar Ubangiji, haka ma Dady yayi iya yinsa, dan gaba d'aya jikin su yayi mugun yin sanyi, sun saduda, cikin ikon Allah sosai zuciyar Naseer tayi sanyi, ya ji sauk'in abinda yake ji, zugi, da rad'ad'in da k'irjinsa yake masa yaji ya ragu sosai, haka ma tafasa, k'ona, azalzala, zafi, k'unci, da zuciyarsa ke masa yaji duk sun gushe, a hankali Naseer ya mik'e ya d'auki Na'eem dake cinyar Mannir ya mik'awa Momy batare dayayi magana ba ya juya ya nufi bedroom d'in sa, kiran sunansa Alhaji Abdullahi yayi " Naseer! tsayawa yayi cak batare daya jiyo ba, " ka yawaita fad'ar 


انا لله و انا اليه راجعون

اللهم اجرني في مصيبتي واخلفلي خيرا منها

 استغفر الله

سبحان الله والحمد لله والله اكبر

حسبنا الله و نعم الوكيل الحمد لله


" in sha Allah, Allah zaya yaye maka damuwar ka yayi maka maganin damuwar da kake cki, ya ya gusar maka da bak'in cikin dakake ciki, murmushi Naseer yayi masa batare dayace komai ba ya shige bedroom d'in sa, ya kulle.



Addu'a Dady yayi aka shafa, Dady ya kalli Zainab yace " yaushe zaki koma gidan ki? cikin muryar kuka tace " sai anyi sadakar bakwai, "ok kawai Dady yace, Momy dai batace komai ba illa rungume Na'eem datayi a k'irjinta tana hawaye, tana k'ara jin tsananin tausayin yaron a ranta, ranar da daddare Naseer na kwance wajen karfe 1:00am na dare ya kashe gaba d'aya light d'in dake bedroom, ya kwanta rigingine yana kallan sama ya tsunduma duniyar tunani yayinda hawaye ke zubo masa. 



A hankali yaji motsi a gefensa, cikin mutuwar jiki ya juya b'angaren dayaji motsin, Zarah ya gani zaune a gefensa sanye da doguwar riga ta atamfa ta saka hijab tana yi mishi murmushi hawaye na zuba daga idanunta zuwa kuncinta, a hankali tasa hannunta, ta shafo fuskarsa, zuwa sajensa, ta cusa hannunta cikin sumar kansa cikin muryar kuka tace " Uncle bakayi min adalci ba, da ma wannan ce irin soyayyar da kake min, kasan bana san b'acin ranka balle har yakai ga kayi kuka, Uncle matuk'ar kana san na kwanta a kabarina cikin salama kayi min alk'awarin baka k'arayin kuka, yana hawaye ya girgiza mata kai, "a'a kayi min magana kace kayi alk'awarin baka k'ara kuka cikin rawar murya yace " nayi miki alk'awarin ban kuma kuka, amma me yasa kika tafi kika barni, murmushi tayi takai masa kiss, lumshe ido Naseer yayi, jin shiru yasa Naseer saurin bud'e ido, ganin wajen yayi ba kowa mik'ewa yayi ya kunna light yaga kwata-kwata ba alamun Zarah, hannu ya d'ora akansa yana shirin kurma ihuuuuuuu sai ya tuna da alk'awarin daya yiwa Zarah, dan haka yayi saurin maida kukan sa ya shiga kukan zuci, ya tabbatarwa da kansa Zarah ta fara yi masa gizo, mik'ewa yayi ya shiga bathroom ya d'auro alwala, yazo ya tada sallah, tun daga ranar Naseer ya daina haukan kuka da ihuuuuuuu ya koma kukan zuci kawai. 



Ya zama so silent kamar bashine Naseer d'in da, mai yawan wasa da dariya, mai yawan san barkwanci da yawan tsokana ba, duk ya zama wani iri dashi kwata-kwata baya magana, kullum yana d'akinsa rufe idan kaga ya fito to masallaci zashi, dan ko abinci baya ci, sai Momy ta matsa masa dakyar yake shan tea ko coffee. 



Ranar sadakar bakwai Naseer yana kwance a bedroom d'in sa ya rink'a jiyo magana sama-sama, kasancewar baya san hayani ko yawan magana yasa Naseer mik'ewa dan ya sawa kofarsa key, yana kaiwa dai-dai k'ofar ya jiyo maganar Zainab na cewa " Momy duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik'e Na'eem sama dani, dan Allah Momy ki bani shi, tab!!!! Wata irin muguwar zabura Naseer yayi a sukwane yayi waje bibbiyu yake taka step d'in saboda tsananin sauri..................... 




A zafafe ya fisge Na'eem daga hannun Zainab a matuk'ar fusace ya kalleta ido cikin ido yace " lalle Zainab ke cikekkiyar mara kunya ce, fitsararriyar zamani ce, ke yanzu idan kina da kunya da cikekkiyar nutsuwa ko bana raye kyama soma tab'a Na'eem? 



"Ko an gaya maki na manta abubuwan da kika yi akan shi, tun kan yazo duniya tun yana cikin mahaifiyarsa, sai yanzu ne zaki nuna so da damuwarki akan sai yanzu zaki kula dashi, ko shima kina san na bak'i rok'onsa ne ki salwantar da rayuwar sa kamar yadda kika salwaantar da rayuwar mahaifiyarsa? 



"Ko ke a zantan ki bazai samu labarin kashe masa uwa da kika yi ba? 



"Ko kina san wanke laifin ki ne a wajensa dan kar ya girma ya d'au fansa? 



"To bari kiji matuk'ar mahaifinsa Naseer Mustapha yana raye sai ya d'au fansa, kuma karki d'auka kinci banza ko rayuwar Zarah ta tafi a banza, dan wallahil azim bazan tab'a barin makasan Zarah su rayu cikin farin ciki da walwala ba....... 



Ihuuuunn kuka Zainab ta zunduma had'i dayin kukan kura tayi kan Naseer.........





Don't forget to vote and comment 



MOMYN ZARAH