GADAR ZARE…

57

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*






57






Kukan kura tayi,tayi kan Naseer a fusace, murmushi Naseer yayi had'i da gyara tsaiwarshi yana jiran k'arasowarta, cikin zafin nama, Mannir yayi wuf ya tare ta dan yaga shirin da Naseer yayi yana jiran k'arasowarta, fisge-fisge ta fara yi tana son kwace kanta daga rik'on da Mannir yayi mata, amma inaaa yayi mata mugun rik'on da bazata iya kwacewa ba. 



K'ara tayi mai k'arfi ta fisge kanta daga jikin Mannir ta durk'ushe k'asa had'i da fasa kuka mai k'arfi, hawaye na zubowa Naseer yace " Zainab kin cuce mu, akan cikin yaron da kike so abaki ki rik'e kikayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa, saboda rashin yadda da k'addara, kuka zage ke da mijinki kukayi mata dukan mutuwa, harda karaya biyu tsabar rashin imani da tausayi, tsabar babu tsoran Allah kwata-kwata a zuciyar ku. 



Cikin kuka Zainab ta mik'e ta nufi wajen Momy da Dady duk ta rud'e ta fita daga hayyacinta kwata-kwata babu ko d'igon nutsuwa a tattare da ita, gaba d'aya a kid'ime take, ta zube a gaban su Dady tace "Dan girman Allah Momy kusa baki Naseer ya bar min Na'eem, wallahi nayi mugun yin nadama jikina yayi mugun sanyi, wallahi nayi danasanin abubuwan danayi, kuma Allah zan rik'e shi da amana bisa gaskiya da tsoran Allah, duk duniyar nan babu wanda yafi ni cancanta dana rik'e Na'e........... 



"Ke awa? cewar Nasir, a zafafe ya yarfa hannayensa da k'arfi zuciyarsa nayi masa suya gami da rad'ad'i mai zafi, ya kalle ta ido cikin ido yana hawaye yace " ko ke a makashiyar mahaifiyar sa, idan har na bawa wacce tayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa ta rik'e shi banyi masa adalci ba, banyi masa gata ba, nasan idan ya girma sai yaji ya tsane ni, ko ma yasani acikin jerin wad'anda zayyi hukunci. 



Tana kuka ta mik'e ta nufi inda Naseer yake cikin matsanancin kuka tace " please Naseer ka bar min Na'eem kona ji sassaucin abinda nake ji a zuciyata, walahi ji nake kamar na mutu dan mutuwar zata fiye min sauk'i da salama akan bak'in halin bak'in cikin danake ciki. 



" To ki mutu mana, da uban waye ya hana ki mutuwar, in kin mutu waye zayyi bak'in cikin mutuwarki, mun ma rage mugun iri a doron k'asa, banza wofi kawai. 



A hankali ta zube a gabansa bisa kan gwiwowinta (ta durk'usa) tana kuka kamar ranta zai fita, zuciyarta nayi mata suya had'i da k'una tana jin k'irjinta kamar zai tsage zuciyarta ta fito saboda tsabar tsananin zafin take ji a k'irjinta, tace " dan girman Allah Naseer ka bani Na'eem bazan tab'a sawa kayi dana sani ko nadamar bani rik'on shi, please ka bani dama ta k'arshe na gyara kurakurai na, in sha Allah zan sa kayi alfahari da hakan, na nuna mashi so da tsantsar soyayyar kamar yadda kowacce uwa take bawa d'anta, please Naseer. 



A matuk'ar fusace Naseer yace " soyayarki ta banza da wofi, Allah yayi wadaran soyayya irin taki, soyayyar mara amfani, wacce da zarar mutum yayi kuskure d'aya kuma koda akan rashin sani ne, bakya bashi uzuri, nan take zaki manta da tarin soyayyar kiyi watsi dashi da lamuransa, daga k'arshe ma ki zama sanadiyyar salwantar rayuwarsa, me za'ayi da irin soyayyarki. 



K'ara k'arfin kukanta tayi ta zube a gaban shi tana rok'onshi tana yi mishi magiyar ya bar mata Na'eem, " please Naseer kaji tausayi wallahi ina buk'atar a tausaya min. 



Murmushin takaici Naseer yayi yace " Allah ko? 



"Ashe ke kina buk'atar a tausaya maki? 



"Amma ke kwata-kwata baki jin tausayin wasu, baki jin rok'on su ko kukan su, baki da saurin yafiya, baki tab'a manta laifin ke da akayi miki, amma ke kin iya magiya, kin iya rok'on a tausaya miki, bayan ke baki aikata d'aya daga cikin abinda kike rok'on ayi miki, haka Zarah tayi ta kuka tana baki hak'uri tana neman yafiyarki, tana tsananin buk'atar tausayawa daga wajenki amma kika k'i sauraranta balle ki tausaya mata, ga abinda kikayi ya janyo nan, sai kema ki d'and'ani bak'in cikin inda gaske kikeyi.



"Naseer duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik'e Na'eem sama dan........ 



Tun kafin ta k'arasa ya katseta da cewa " sai ni, Zainab sai ni ubansa kuma mahaifinsa na fiki cancanta dana rik'e d'ana, ke kin isa ma ki kalli tsabar ido na kice min duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik'e min d'ana sama dake bayan ina nan a raye. 



Da sauri ta mik'e ta nufi wajen Abban Zarah dake tsaye tace " dan Allah kasa baki Naseer yabar min Na'eem naga yana matuk'ar jin maganarka, kafin Abban Zarah yayi magana Naseer yayi saurin cewa. 



" Banda a wannan b'angaren, Zainab dama kin hak'ura kin dai na wahalar da kanki wajen rok'on na, da bin mutane akan su sani nabar miki Na'eem, dan wallahi tallahi duk duniya babu wani mahaluk'i daya isa yasani nabar miki ruk'on Na'eem, wallahi ko waye shi, idan ma mutum yasan ina ganin girman sa da mutuncinsa karya sake ya soma saka baki a maganar nan, dan zan iya shafawa ido na toka na zage na tsula rashin mutunci, ke dai dayake kwata-kwata baki data ido sai kiyi tayi. 



" Wallahi tallahi, wallahil azim, na rantse miki da girman Allah Zainab ko zaki mutu, bazan tab'a baki Na'eem ba koda zakiyi mushe a gaba na, zan sa k'afa na tsallake mushenki nayi gaba da d'ana, ya juya ya d'auki Na'eem daya ajiye akan sofa, ya nufi bedroom d'in sa. 



Cikin kuka Zainab tace " ni ban san me nayi maka a rayuwarka ba, na rasa me nayi maka haka, cak ya tsaya had'i da juyowa ya tako har gabanta ya sunkuyo da fuskarsa saitin tata fuskar yana kallanta ido cikin ido yace " Au tambaya ta ma kike yi, kina nufin baki san abinda ki kayi man ba, lalle Zainab kwakwalwar ki bata aiki, ta samu matsala tunda har kike cewa kin rasa abinda kika yi man, Na'eem dake rungume a k'irjin Naseer ganin ya sunkuyo saitin Zainab ya juyar da fuskarsa daga kallan Zainab ya cusa kansa cikin k'irjin Naseer ya k'ara k'ank'ame Naseer had'i da tsandara kuka. 



Ganin abinda Na'eem yayi yasa Naseer dakatar da maganarsa batare daya gama fad'ar abinda yake san fad'a ba, ya mik'e tsaye yana kallan Na'eem, duk ya rud'e ya fita hankalinsa, murmushi Naseer yayi yace " Alhamdulillah Masha Allah, nagodewa Allah, ya kalli Zainab yace " kinga tsantsar k'iyayyar da Na'eem yake miki ko, ko k'aunar kallan fuskar ki baya san yi, ji yadda ya fita daga hayyacinsa saboda kawai na sunkuyo dashi sai tin ki, kin dai gani da idanki, bai girma ba balle kice ni na koya mishi yadda zai tsane ki. 



Gaba d'aya jama'ar wajen cike da matsanancin mamaki suke kallan Na'eem suna al'ajabin abinda yaro d'an 6 months yayi, hannu Zainab ta d'ora aka had'i da fashewa da matsanancin kukan bak'in ciki.




K'ara rungume Na'eem Naseer yayi tsam a k'irjinsa yana murmushi hawaye na zuba daga idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya, batare dayace komai ba, ya shige bedroom d'in sa ya rufo k'ofa, anan Zainab ta durkushe tana matsanancin kukan bak'in cikin rayuwa, anan kowa ya barta Alhaji Abdullahi, da Abban Zarah sukayi tafiyar su, Dady da Momy suka haye samansu, sai da dakyar Mannir ya lallab'e ta ta yarda suka tafi gidan su suma. 



Tun a parlor Zainab ta zube tana ci gaba da kukanta, shiko Mannir dayake yafi Zainab shiga matsanancin halin damuwa da bak'in ciki shiru kawai yayi ya shige bedroom d'in sa ya fad'a bathroom ya sakarwa kansa shower had'i da dafa bango yana tunanin mafita dan shi kansa yasan bazai tab'a iya ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da walwala muddin ba Na'eem a kusa dashi ba, zaman lafiyar sa d'aya, da kwanciyar hankalinsa shine yaga Na'eem a tare dashi, dan shi da kansa yasan tunda yake a duniya bai tab'a san wani abu kamar yadda yake mugun san Na'eem ba, dan idan ya ganshi jikinsa har rawa yake, ga yaron kyakykyawan gaske fari fat kub'ul-kub'ul dashi kamar yaron turawa, muddin aka raba shi da Na'eem dai-dai yake da raba shi da duk wani farin ciki, jin dad'i, walwala, nishad'in sa. 



Dan duk duniya a halin yanzu babu abinda Mannir yake so yake kuma k'auna kamar Na'eem yafi san shi fiye da kowa da komai, akan yaron babu abinda bazai iya ba, muddin zai dawo masa da yaron kusa dashi ko meye shi zai iya yin abun komai wahalarsa, tsaki yayi had'i da kaiwa bangon bathroom d'in naushi da hannunsa, take yaji ciwo jini ya fara zuba amma shi ko kad'an bai ji zaifin ciwon ba, dan zafin da zuciyarsa take masa yafi ciwon yi mishi rad'ad'in, babu abinda zuciyar sa keyi masa sai rad'ad'in zafi da k'una, ga wani mahaukacin suya da k'irjinsa keyi masa kamar an zazzaga petroleum an kunna ashana. 



Duk iya tunaninsa ya rasa wata mafitar kamawa, yayi-yayi amma babu wani kwakkwaran abin kamawa balle ya samu hanyar da zai kasance da Na'eem farin cikin rayuwarsa,, ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi, sannan ya kashe shower ya fita daga bathroom d'in, kan bed ya fad'a yana ci gaba da tunanin naimarwa kansa mafitar da zata fishe shi, ganin har lokacin bai samo mafita bane yasa shi mik'ewa ya nufi parlor. 



Bai iske kowa a parlor ba, dan haka tunanin shi ya bashi tana bedroom, kai tsaye ya nufi bedroom d'in Zainab, a hankali ya tura k'ofar ya shiga, akan bed ya iske ta tayi rud da ciki tana ta faman rusa uban kuka kamar ranta zai fita har shid'ewa take yi amma tak'i yin shiru, hannayen shi ya harde a kafad'arsa ya zuba mata ido yana magana shi kad'ai a ransa " hmmmmmm Zainab kenan ke kin ma samu damar yin kuka kin gusar da naki bak'in cikin rayuwar, idan damuwa da bak'in ciki sukayi ma mutum yawa baya iya yin kukan fili sai na zuci, duk abinda kikaga ana yi masa kuka yana da sausauci ne, amma ni dayake nafi tsananin san kasancewa da Na'eem kwata-kwata na kasa kukan, ni so nake ma nayi kukan hawaye ya zuba kona samu sausaucin rad'ad'in da zuciya ta keyi min. 



A fili kuma yace " subhanallah yana sauri ya k'arasa inda take had'i da d'ago ta ya rungume a k'irjinsa, yana cewa " kai haba Zainab mai yasa kike irin haka ne kwata-kwata kin k'i ki yarda da k'addara ki mik'a dukkan lamuranki da Allah, k'ara sautin kukan nata tayi tana k'ok'arin kwace jikinta daga nashi, shi kuma ya k'ara matseta da k'arfi yadda bazata iya kwace kanta ba, hak'ura tayi ta kwantar da kanta akan k'irjinsa tayi luf tana ci gaba da kukan nata.




Cikin rashin nutsuwa Zainab ta d'aga kanta tana kallan fuskar Mannir tana shashshekar kuka tace " idan har kana sona, kuma san da kake yi min gaskiya ne, ta nuna sai tin zuciyar sa tace " idan har zuciyar ka tana bugawa da tawa bugun zuciyar, idan har kana san naci gaba da rayuwa a duniya, idan har kana k'aunar ci gaba da ganina a duniya, kasan duk hanyar daza kabi ka kawo min Na'eem cikin gidan nan, matuk'ar kana k'aunar ganin farin ciki da walwala ta ka kawo min Na'eem, duk hanyar daza kabi, kabi kowacce irin hanya ce, kuma komai zaka aikata koma meye kayi ka kawo min Na'eem............ 






Don't forget to vote and comment 




MOMYN ZARAH