GADAR ZARE…

58

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*






58






Ta k'araashe maganar cikin matsanancin kuka, kanta ya shiga shafawa kawai batare dayace mata komai ba, dan shi kad'ai yasan irin abinda yake ji a zuciyarsa zuwa k'irjinsa, dan wani irin mugun tafasa jinin jikinsa keyi, ga k'unar da rad'ad'in da zuciyarsa keyi masa, k'irjinsa ko jinsa yake kamar yana ci da wuta, mak'ogwaronsa kuwa ko yawu ya had'iya ji yake kamar mad'aci. 



Idanuwansa ya runtse da k'arfi yana sauraran yadda zuciyarsa ke bugawa da tsananin k'arfi kamar zata fasa k'irjinsa ta fito, shima yasan matuk'ar aka raba shi da Na'eem to kwanakinsa na duniya sun k'are, yasan raba shi da yaron dai-dai yake da tsinkewar numfashinsa, domin yasan lokacin mutuwarsa yayi, Allah kad'ai yasan irin mugun son da yake yiwa Na'eem, wanda shi kansa yasan Allah ne ya jarrabeshe da tsananin sansa, wanda shi kansa yana mugun mamakin yadda yake jin yaron a ransa. 



Ko bacci idan ya farka babu abinda yake fara fad'o masa sai Na'eem, idan sallah yana ransa, kai komai Mannir yake da tsananin tunanin Na'eem yake yin sa, baya iya yin ko da 1 second batare daya tunashi ba, tun da Mannir yake a duniya bai tab'a san wani abu kamar Na'eem ba, bai tab'a sanin haka zafin so da rad'ad'in sa yake ba sai akan Na'eem, kwata-kwata baya cikin farin ciki da kwanciyar hankali gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa, duk ya d'imauce ya fita daga kamanninsa, duk 1 minute yana jin yadda san yaron yake shigarsa yana ratsa duk wani b'argo da tsoka had'i da jijiyoyin jikinsa zuwa magudanar jininsa, take ya fara zubar da hawaye yana tausayawa kansa da rayuwarsa, a hankali hawayen dake zuba daga idanuwan Mannir ya fara d'iga akan kuncin Zainab. 



A hankali Zainab ta d'ago kai tana kallan fuskarsa, taga yadda hawaye ke zubowa da gudu, a tunanin Zainab ta d'auka hawayen tausayinta ne bata san hawayen tausayawa kansa da halin da zai shiga muddin aka raba shi da Na'eem bane, a hankali Zainab tasa hannu tana goge masa hawayen dake bin faskarsa itama tana zubar da hawayen ta shiga girgiza mishi kai alamar yabar kuka, kasa dainawa yayi dan bai isa ya tsaida hawayen dake zuba ba dan baga Idanuwansa suke ba daga zuciyarsa suke.



Dakyar Zainab tace " please kayi shiru, idan kaima kana kuka nima inayi tsakanin mu wazai bawa wani hak'uri, wazai rarrashi wani? 



"Dan Allah ka daina kuka idan kana kuka sai na karaya, kukan ka zai hana zuciyata sakat, zai hanani nutsuwa da farin ciki, kuma zai k'ara saka ni rauni, naji kamar mun rasa Na'eem ne, please control your emotions , ta fad'i maganar tana goge masa hawayen dake zubo masa. 



Ajiyar zuciya Mannir ya kuma saukewa yana kallan ta batare dayace mata komai ba, a hankali ta kuma kwantar da kanta akan k'irjinsa tana ci gaba da kukan ta, shiko Mannir ya kasa furta koda kalma d'aya ce saboda halin bak'in cikin dayake ci, kanta kawai yake shafawa yana fidda numfashi da sauri-sauri, yayinda zuciyarsa ke harbawa tana ci gaba da bugawa da tsananin k'arfi. 



Su Mannir na fita Naseer ya fito hannunsa d'auke da Na'eem ya iske Momy da Dady zaune a parlor kusa da Momy ya nufa directly, a gefenta ya zauna yana duban k'asa batare dayace komai ba, ganin hakan da yayi ne ya tabbatar wa Momy akwai magana a bakin Naseer dan haka ta karkarta gaba d'aya hankalinta ta maidashi kansa, tana kallan sa, ganin wajen 10 minutes amma Naseer bashi da alamar ko motsa bakinsa balle yace k'ala yasa Momy kallan Dady, shima ita yake kallo, a hankali Dady ya mik'e ya koma kusa dashi ya zauna yana fuskantarsa, yasa hannu yana shafa suman kansa zuwa gadon bayan sa, Momy ma matsowa tayi kusa dashi sosai tasa hannu ta d'auki Na'eem dake kan cinyar Naseer, ba musu Na'eem ya yarda da Momyn had'i da kwanciya luuuuuf a jikinta, Ikram Momy ta kwalawa kira. 



Wacce tun mutuwar Zarah ta mayar da kanta zaman d'aki, ta mayar da kanta, shiru-shiru duk ta rame ta koje ta zama kamar ba ita ba dan magana ma ita yanzu ba'a san ranta take yinta ba akan dole ake sawa tayi magana, mika mata Na'eem Momy tayi tace " kiyi masa wanka ki had'a masa madararsa ki bashi yasha, batare data ce komai ba ta d'auki Na'eem dake ta mik'o mata hannu tun fitowarta daga bedroom. 



Mai da hankalinta Momy tayi kan Naseer tace " meke faruwa ne Naseer? 



Shiru yayi yana tunanin ta inda zai fara b'ullo musu da maganar barin Nigeria, dan yasan ba lalle ne su amince masa ya tafi can shi kad'ai ya koma can da zama ba, amma shi hakan shine kad'ai kwanciyar hankalinsa da nutsuwar sa, dan kwata-kwata Nigeria ta gama fice masa a rai, yadda kasan akan wuta yake zaune haka yake ji. 




Tun mutuwar Zarah ya gama ayyanawa a ransa shida Nigeria haihata-haihata matsawar yana san ko kwatankwacin farin ciki da walwalar sa na baya zasu dawo masa, amma matsawar yana cikin Nigeria, ko yaci gaba da zama a cikin ta, rayuwarsa ta baya bazata tab'a barin zuciyarsa ba, 

ya kuma san muddin hakan zata ci gaba da faruwa barazana ce ga lafiyarsa dama rayuwarsa gaba d'aya, 

dan haka ya gama yanke hukuncin barin k'asar nan kota halin k'ak'a inko ba haka ba za'a waye gari aga gawarsa shima zuciyarsa ta buga. 



Shi kad'ai yasan halin dayake ciki, dauriya kawai yake yana k'ok'arin danne damuwarsa, dan kar hakan ya haifarwa da rayuwar iyayensa matsala ya gusar musu da farin cikin su kamar yadda nashi ya gama gushewa ya kuma tarwatse, 

a kullum kwanan duniya idan ya waye gari ya ganshi a cikin gidan, bak'in cikinsa tsananin k'aruwa yake, kewar Zarah da mugun santa na k'ara harbar zuciyarsa, yana k'ara tsintar kansa da rayuwarsa cikin matsanancin bak'in ciki da damuwa mai d'auke da zafi da k'una. 



A hankali ya lumshe idansa hawaye na zubo masa, sai da yayi wajen 10 minutes a haka sannan ya bud'e idan nasa da suka gama rikid'ewa zuwa launin ja!!!!,

ya sauke su akan iyyen nasa, kansa Momy ta shafa tana dukan sa cike da tausayawa, ji take kamar ta d'ora hannu aka ta fasa kuka saboda tsananin rad'ad'in da take ji na ganin Naseer a cikin muguwar damuwa, mai tsananin yawa, 

dan kallo d'aya zakayi masa ka fahimci halin daya ke ciki. 



Kansa Dady ya shafa yana kallansa yace " Son kayi magana mana dan alamunka sun nuna kasan magantuwa. 



Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi sannan yace " please ina san barin k'asar nan d..... 



Bai k'arasa ba Momy tace " kamar yaya ban fahimci ka ba, me kake nufi da kana san barin Nigeria? 



Fuska ya b'ata kamar zayyi kuka cikin rawar murya yace " please Momy & Dady allow me to leave this country please I beg you in the name of almighty Allah ,

 wallahi nayi mugun tsanar k'asar nan yadda kuka san akan k'aya nake haka nake ji na. 



A zabure Momy tace " kana nufin tafiya zakayi ka bar mu ko me kake nufi Naseer? 



Kuka ya fara sannan yace " please still I beg your permission, wallahi Momy matuk'ar kuka ce dole sai naci gaba da rayuwa anan tabbas wata rana za'a wayI gari bana nan duniyar ma gaba d'aya sai dai kuga tawa gawar nima dan nima zuciyata gaf take da tarwatsewa,, Momy k'ok'ari kawai nake ina danne damuwa da halin bak'in cikin danake ciki dan karna jefaku a halin damuwa. 



"Momy Allah ne kad'ai yasan gaskiyar abinda ke raina, shi yasan me nake ji a cikin rai na da zuciya ta, so please Momy allow me to go, please don't say no ya k'ara maganar yana zubewa a gaban su bisa gwiwowinsa yana had'a hannayen shi biyu alamar rok'o (magiya). 



Momy zatayi magana Dady yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'ora hannunsa akan nata ya danna, hannun tabi da kallo tana sauke ajiyar zuciya dan ta fahimci abinda yake nufi, dole yasa ta yin shiru badan ta so ba, shi ko Dady gaba d'aya jikinsa ne ya gama yin mugun sanyi, take zuciyarsa tayi la'asar tausayin Naseer yayi mugun kamashi, 

sai da ya faki idan Naseer da Momy ya goge hawayen tausayin Naseer dake zubo masa had'i da sauke ajiyar zuciya sannan yace. 




" Wacce k'asa zaka? 


Sai da Naseer ya lumshe ido hawaye na ci gaba da zubo masa sannan yace " HOLLAND. 



murmushi Dady yayi had'i da shafa kansa yana kallansa cike da tausayawa yace " bakomai Naseer mun yarje maka ka tafi mun baka izini ko yau ma kana iya tafiya, 

amma kayi min alk'awarin zaka cire damuwa a ranka zaka ci gaba da rayuwarka cikin farin ciki da nishad'i, 

sannan ka kula da addininka, al'adarka da kuma mutuncinka dana addininka da namu mutunci. 



"Alhamdulillah shine abinda Naseer ya fara furtawa kafin yace " in sha Allah I will try my best, karka damu Dady ko wannan ma daya faru akan Zarah Allah ya riga ya tsara akwai rabon Na'eem sannan kwanakinta na duniya ba masu tsawo bane. 



Kansa Momy ta shafa tana murmushi tace " Allah yayi maka albarka ya albarkaci rayuwarka, Ubangiji ya tsare min kai da tsarewarsa ya kare min kai da kariyarsa, duk abinda zai fi k'arfinka ko ya zame maka matsala Allah yayi maka maganinsa, sosai Momy tayi ta kwararo masa addu'o'i haka ma Dady shima sosai yayi masa addu'a wanda haka ba k'aramin dad'i da sanya shi cikin farin ciki suka yi ba. 



Kallan Momy yayi yace " Momy a shirya kayan Na'eem dan dashi zan tafi, ya fad'a yana duk'ar da kansa k'asa. 



A fusace tace " kamar ya dashi zaka tafi? 



"Eh Momy bazan iya barin shi anan bane, ni ina can hankali na bazai kwanta ba. 



"Saboda cinye shi zamuyi, kafin ka dawo mun kanya shi munyi farfesun shi ko? 



" A'a Momy ba haka nake nufi ba, Momy kona bar miki shi su Mannir bazasu barshi anan gidan ba, sai sun rabaki dashi nasani, ni kuma babu abinda nafi tsana a doran duniya sama dasu, 

ko dabba ta bazan tab'a bari ta k'ara taka gidan ba balle kuma d'ana na ciki na, please Momy ki barni na tafi dashi, ya fad'a cike da ladabi, 

dan idan baki barni na tafi dashi ba an bar baya da k'ura dan konaje can d'in ma hankalina ba kwanciya zayyi ba. 



Murmushi Dady yayi yace " oh my son an zama Baba Naseer kana da san d'a da yawa son, yanzu in banda rigima irin taka ya zakayi da shi acan idan an baka? 



"Nanny zan d'auka daga hospital sannan zan saka shi a day care, kaga zai samu kulawa. 



Ajiyar zuciya Dady ya kuma saukewa sannan yace " ok badamuwa Allah ya tsare ku baki d'aya, Ubangiji ya baka damar kula da shi. 



"Amin Naseer yace, kafin yayi jummmm ko suna da wata maganar dashi, ganin basu da abin cewa ne yasa Naseer mik'ewa har ya kai bakin stairs Dady ya kira sunansa " Naseer 

a hankali Naseer ya juyo yana kallon Dady had'i cewa " na'am.



Cikin sanyin murya Dady yace " ka tuna duk lalacewar Mannir da Zainab naka ne su, kuma duk lalacewar naka, 

naka ne, dan hausawa sunce naka sai naka, dad'in zama sai bare, kuma d'an uwa rigar k'aya ka saka ya soke ka, ka cire ka tafi tsirara, murmushi kawai Naseer yayi ba tare daya ce komai ba ya haye samansa. 



Washe gari tun da safe Naseer ya tashi domin maganar tafiyar sa, ya kama shirye-shiryen haik'an dan yana san nan da kwana biyu ya d'aga, cikin sa'a ya gama duk wasu shirye-shiryen sa kasancewar akwai kud'i a hannu, bai dawo gida ba sai yamma sosai. 



A parlor ya iske Dady da Momy, Mannir dake gefen su rai b'ace, bayyiwa kowa magana ba ya fara k'ok'arin hayewa sama, ganin su Dady basu da niyyar yi masa magana yasa Mannir mik'ewa a fusace cikin fushi yace " Naseer wajenka nazo, magana nake san yi dakai. 



Ba tare daya jiyo ba yace " duk maganar da zakayi dani ka fara yi da magabata na tunda kasan ina da iyaye kuma har yanzu suna nan a raye, 

a hasale Mannir yace " wannan maganar kace, dan maganar Na'eem ce. 



Har Naseer ya d'aga k'afarsa zai taka next step jin Mannir yace maganar Na'eem ce ya sashi, 

mayar da k'afarsa baya, a hankali ya juya yana taka step d'in one by one har ya isa inda Mannir yake, 

ya tsaya daf dashi yana kallansa ido cikin ido yace " uhnnnn ina jinka. 



Ido Naseer ya d'aga ya fara kallansa duk daga k'asa har sama baki bud'e, sannan yace " izini kake nema ko kuma kazo sanar min ne? 



"Ni dai na gaya maka nazo tafiya da Na'eem ne, 


"Shine ai na tambaye ka izini kake nema ko kuma kana sanar min ne? 



" A fusace Mannir yace " ina sanar maka ne, 



Murmushi Naseer yayi sannan yace " kai a matsayinka wa, a wajensa? 



Shiru Mannir yayi ya rasa abin cewa, ya kama kame-kame, ganin haka yasa Naseer motsi da bakin yayi sauti yace " ayya ashe kai ba kowa bane a wajensa, tun baka da wani matsayi a wajensa,

 sai ka koma wajen wacce ta aiko ka, kace mata hak'onta bai cimma ruwa ba, dan karrrrrr nake kallan ku, kuma ka sanar da ita Naseer dattijo ne dan magana d'aya kawai yake, baya tab'a canja maganarsa, sannan kace mata Naseer cikekken namiji ne ba irin lusarin mijinta wanda sai abinda tace yake ba. 



Cikin tsananin fushi Mannir ya d'aga hannu zai mari Naseer, da sauri Naseer ya rik'e hannunsa had'i da cewa karka soma inba so kake yanzu jikinka ya gaya maka ba, dan daga wa baka kau ba, banza sakarai, hotiho,lusari, sauna, shashasha.




Naseer na kaiwa nan yayi hayewarsa sama yabar Mannir nan tsaye yana cizon yatsa. 



A parlor ya tadda Zainab tana ta faman safa da marwa tana jiran dawowarsa, tana ganin shi ta nufe shi da tsananin sauri tana murmushi had'i da waiwayen bayan sa tana san hango Ikram d'auke da Na'eem, ganin babu kowa a bayansa yasata ja da baya da sauri, 

tana girgiza kanta wahaye na zubo mata. 



Duk abinda ya faru tsakaninsa da Naseer ya kwashe tasssss ya fad'a mata bai b'oye mata komai ba, ai yana gama gaya mata ta sulale k'asa sumammiya...............!!!!!! 





Don't forget to vote and comment 





MOMYN ZARAH