59
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
59
A razane Mannir ya k'arasa inda take ya shiga jijjiga ta yana kiran sunanta " Zainab!? ganin bata motsi yasa shi mik'ewa da sauri ya nufi fridge, da sauri ya d'auko ruwa, yana zuwa ya zuba mata, sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi,
sannan ta fara tari, da sauri Mannir ya ajiye ruwan a gefe ya rungumo ta jikinsa.
A hankali - a hankali Zainab ta fara bud'e idanuwanta, da farko dishi-dishi ta fara gani kafin daga baya idanuwanta su washe tarwai,
ganin ta akan k'irjinsa yasa ta saurin zabura ta mik'ewa daga jikinsa had'i da ja baya.
K'ara motsowa jikinta Mannir yayi yana niyyar rungume ta,
da sauri Zainab ta k'ara ja da baya, hawaye na zubo mata ta kalle shi ido cikin ido tace " karka sake ka soma k'ok'arin tab'a ni, bakin Mannir a bud'e cike da matsanancin mamaki ya k'ara matsowa yana cewa " Zainab lafiyar ki kuwa?
Da sauri Zainab ta buge hannun Mannir daga jikinta tace " karka sake ka soma tab'a ni na gaya maka,
matuk'ar kana san ci gaba da gani na cikin farin ciki da walwala gami da annaashuwa kamar da ka kawo min Na'eem.
Tsaye kawai Mannir yayi yana kallanta ya kasa cewa komai,
harta gama ta shige bedroom, sai da yayi wajen 10 minutes yana tunane-tunane gami da sak'e -sak'e,
sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yabi bayanta zuwa bedroom d'in,
kwance ya iske ta tayi rub da ciki tana ta faman kuka kamar ranta zai fice.
Cikin mutuwar jiki Mannir ya zauna a kusa da ita a gefen gadon,
ido ya k'ura mata na wani lokaci sannan yayi numfashi mai k'arfi yace " Zainab wallahi nafi ki buk'atar san kasancewa a kusa da Na'e...............
Kai ta d'ago a d'an zafafe tace ' idan ka fini san kasancewa dashi mai yasa ka kasa bin duk wata hanya dan ganin ka kawo shi gidan nan?
" Zainab ya kamata ki gane Naseer yana da matsananciyar zuciya da kafiya gami da taurin kai tun yana yaro, kuma a wannan zamanin ko d'anka na cikinka yak'in soja bayayi sai dai mulkin farar hula da campain da komai dan matuk'ar kace zakayiwa yaranka dole a wannan zamanin zaka ba dai-dai ba.
" Dole sai dai mu biyo mishi ta bayan gida ta inda bai tab'a tsammani ba.
" Kamar yaya kenan kake nufi?
" Sai dai mu sace Na'eem!!!
Da sauri Zainab ta mik'e zaune tana murmushi had'i da goge hawayenta " yawwa this is a good idea, amma ta yaya kake ganin zamu iya sace shi tunda kasan akwai securities da yawa?
" Duk yawan securities sun isa su hanani shiga gidan,
tunda gidan ubana ne, tare da Ikram, Na'eem yake kwana a bedroom d'in ta, zanje gidan da sassafe around 6:00am duk suna bacci sai na d'auko shi, idan na dawo gida sai nayiwa securities d'ina kyakykyawan warning akan kar su sake su bar kowa ya shigo min gida kai tsaye.
Cikin zak'uwa Zainab tace " yaushe zaka je ka d'auko shin?
Shiru yayi yana tunani wajen 10 minutes sannan yace " dole sai dai jibi.
Fuska ta b'ata tace " mai yasa bazaka je gobe ba,
har sai jibi?
" Dole muyi komai cikin tsari da tunani saboda,
kar muyi gaggawa mu lalata komai,kinga yau naje gidan har munyi cacar baki dashi,
idan aka ga babu Na'eem yau, dole ni za'a zarga,
amma idan muka tsara komai cikin tsari, batare da mun bar wata shaida ba babu wanda ya isa ya fito gar da gar yace mune ko da sa hannunmu.
Rungume Mannir Zainab tayi cike da murna da matsanancin farin ciki tace " thank you so much my love,
light kiss yayi mata a kumatunta yace " don't mind my heart make you happy is my duty.
BAYAN KWANA BIYU
Yau ta kama ranar tafiyar su Naseer k'asar Holland ce shida Na'eem,
tun dare ya gama shirinsa tsaf dan k'arfe 6:00am na safe jirgin su zai d'aga,
ya shirya kayansu tsaf tun dare ya saka duk wani abu da zai tafi dashi a boot d'in mota,
a daren ya cewa Ikram ta shirya Na'eem around 5:00am na safe, dan baya son yayi late kuma gashi yana san ya biya ta kabarin Zarah yayi mata addu'a,
dan bai sai ranar dawowar shi Nigeria ba.
Tun k'arfe 4:30am na safe Naseer ya tashi yayi wanka ya shirya cikin wani tsaddaden d'anyan boyel sky blue mai shegen kyau,
ya saka takalmi, hula, agogo ash color, kallo d'aya zaka yiwa kayan jikinsa ka hango tsadar kayan,
Naseer yana bala'in san manyan kaya, dan shi kwata-kwata k'ananan kaya basu dame shi ba, bama shi dasu in dai ba irin simple d'innan na zaman gida ba,
shi dai yasaka Shadda, Boyel, Material na maza, d'an yan yadi sannan zai san ya saka kaya.
Lokacin da yana karatu a Holland abokanansa har tsukanarsa suke sosai suna ce masa sarkin k'abilanci,
k'arfe 5:00am Naseer ya fito bayan ya gama shirinsa, kasancewar ya sanar dasu Momy lokacin tafiyar yasa yana saukowa ya iske su gaba d'ayan su a parlor,
da murmushi a fuskarsa ya k'arasa inda mahaifan suke zaune suna jiransa,
har k'asa Naseer ya durk'usa ya gaida su, suka amsa cike da fara'a.
Bayan ya gama gaida su Ikram dake tsaye rik'e da Na'eem tana ta faman kuka, cikin muryar kuka tace " good morning Uncle,
murmushi yayi yana shafa kanta yana amsa gaisuwar, cikin muryar kuka ta kuma cewa " yanzu Uncle da gaske tafiyar zakuyi ku barni ni kad'ai ba Zarah, ba Na'eem?
Sosai tausayin Ikram yayi masifar kama Naseer, dan yasan dama dole kewa tayi mata yawa, duk duniya babu wanda tafi sabawa dashi sama da Zarah, gashi yanzu babu ita,
tayi tafiya mai nisan nisa ta har abada, daga baya kuma tayi sabo da Na'eem shima gashi yanzu za'a raba ta dashi kuma Allah kad'ai yasan ranar dawowar su,
kuma yarinyar tayi masifar sanin ya kamata, dan duk wannan hargitsin dayake faruwa a tsakanin shi da iyayenta bata tab'a shiga ba,
ba kuma ta tab'a nuna masa komai ko a fuskarta bane,
dan haka yake mugun santa da tausayinta.
Kasa ce mata komai yayi, ci gaba da kukan ta tayi, a hankali ya jawo ta jikinsa ya rungume ta sosai, take shima ya fara zubar da hawaye, gaba d'aya jikin kowa a wajen yayi mugun yin sanyi, a hankali ya zame jikinsa daga Ikram ya karb'i Na'eem,
juyawa wajen su Momy yayi yana hawaye muryarsa na rawa yace " Momy, Dady zan tafi lokaci na k'urewa kar nayi late,
rungume shi suka yi su duka suna hawaye " Allah yayi maka albarka, ya tsareka ya kuma baka kariya, dan Allah ka kula da kanka, da Na'eem, da kuma addininka, al'adarka ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka.
Hawayen dake zubowa daga idan Momy ya goge mata,
shima yana hawaye muryarsa na rawa yace " in sha Allah Momy zan kula sosai,
kan Naseer Dady ya shafa yana murmushi hawaye na zuba yace " Allah ya baka sa'a ya d'oraka akan mak'iyanka.
Dakyar Naseer ya iya cewa " Amin ya Allah nagode sosai Momy,& Dady, ya fad'a yana goge hawayen dake zubo masa, yayi saurin fita,
ai Ikram na ganin ya fita da Na'eem ta durk'ushe a wajen had'i da fasa rikitaccen kuka,
dakyar Mamy ta rarrashe ta ta kaita bedroom d'inta, sannan suma suka wuce nasu bedroom d'in.
Naseer na fita ya shiga mota driver yaja, direct kabarin Zarah ya fara nufa,
yakai wajen 15 minutes a kabarinta yana kuka had'i dayi mata addu'a,
sannan suka nufi Aminu kano international airport,
driver ya ajeshi ya shiga ciki d'auke da Na'eem a kafad'arsa.
Misalin k'arfe 6:00am na safe Mannir yazo gidan,
ganin ba kowa a parlor ne yasa shi zama akan sofa yana san ya gani ko akwai wanda idansa biyu,
ganin yakai wajen 15 minutes amma bai ji motsin kowa bane ya sashi mik'ewa cikin sand'a ya nufi bedroom d'in Ikram.
Daga bakin k'ofar bedroom d'in nata ya rink'a jiyo kamar motsi,
tsayawa yayi ya d'an saurara had'i da kasa kunnensa ajikin k'ofar,
sheshshekar kukan Ikram yaji yo daga cikin bedroom d'in,
da sauri ya tura k'ofar ya shiga, a k'asa ya ganta a zaune ta d'ora kanta akan bed tana ta faman kuka,
da hanzarinsa ya k'arasa gare ta.
Hannu yasa ya d'ago ta yana kiran sunanta " Ikram lafiya kuwa, meke damunki?
Cikin kuka ta fad'a jikinsa tana cewa " Dady na shiga uku, ba Zarah ba Na'eem,
gaban Mannir ne yayi wani irin razanannan fad'uwa a kid'ime yace
" meya same Na'eem d'in?
"Dady sun tafi sun bar ni,
Iya tashin hankali Mannir ya shige shi, dan a tsammaninsa wani mummunan abu ne ya samu Na'eem d'in,
take zuciyasa ta shiga bugawa da tsananin k'arfi,
kirjinsa ya d'auki dokawa, yayinda yake jin kamar k'irji sa zai tsage,
gaba d'aya jikinsa ya d'auki kerrrrrrma da tsananin rawa,
jikinsa na b'ari gami da tsuma, cikin rawar murya yace " me ya same shi?
cikin muryar kuka tace " Na'eem da Uncle sun tafi Holland, a zabure ya saki Ikram ya mik'e tsaye,
Muryarsa na cracking yace " yaushe suka tafi?
" Yau zasu tafi, d'azu suka tafi airport, bai k'ara bi takan Ikram ba ya fito a kid'ime ya shiga mota had'i da figarta a 360 yayi Airport,
da mahaukacin gudu ya shiga Airport d'in, yana yin parking ya fito a rud'e ko tsayawa rufe motar bayyi ba ya fito ya nufi reception,
amma ina ya riga da ya makara,
yana zuwa jirginsu Naseer na d'agawa zuwa k'asar Holland.
Wata ma'aikaciya dake aiki a Airport d'in ya tambaya " please yau she jirgin Holland zai d'aga?
Murmushi tayi had'i da cewa sun riga da sun tashi yanzu 5 minutes ago, hannu Mannir ya d'ora aka ya durk'ushe a wajen gami da fasa rikitaccen ihuuuuuu da kuka,
gaba d'aya hankalin jama'ar dake gurin yayo kansa, take ma'aikatan wajen suka zo wajensa suna tambayar shi abinda ke damusa,
amma ko kallan inda suke bayyi ba,
, sai da yayi kuka iya san ransa sannan ya tashi ya shiga mota ya wuce gida jikinsa a matuk'ar sanyaye,
shi ko tunanin Zainab bayyi ba ta kansa kawai yake,
baima tsaya tunanin abinda zai ce mata ko halin da zata shiga ba,
saboda kwata-kwata baya cikin hankalin sa da nutsuwarsa.
Yana yin parking ya fito baima tsaya rufe motar ba, Zainab na bedroom akan bed a kwance sai juyi take cike da farin ciki,
tana jiran dawowar Mannir da Na'eem,
tana jin tsayawar motarsa ta fita da gudu,
a parlor sukayi kicib'us dashi,
tana murmushi ta tare shi dan ita tsammaninta tare da Na'eem zata gansu,
ganin yanayin dayake ciki,
kwata-kwata babu alamar nutsuwa a tattare dashi, kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin mummunan tashin hankali.
Cikin rawar baki tace "Mannir lafiya,
ya banganka da Na'eem d'in ba?
Bai ko kalli inda take ba yana ci gaba da tafiya yace " sun tafi Holland shi da Naseer,
ya fad'a yana shigewa bedroom d'in sa,
anan Zainab ta zube a k'asa had'i da fasa rikitaccen kuka mai tsuma zuciya, ta rink'a ihuuuuuu tana kuka kamar ranta zai fita.
Mannir na shiga d'aki ya fad'a kan bed had'i da fasa kuka, yana jin kamar zuciyarsa zata fashe,
saboda tsananin zafi da zugin da take yi masa, dan ji yake tamkar an raba shi da ransa ne,
sai da taci kuka sosai harta fara shid'ewa sannan ta mik'e dakyar tana had'a hanya ta nufi bedroom d'in Mannir,
tsaye ta iske shi ya dafa bango yana ta faman zubar hawaye,
a fusace ta k'arasa inda yake taci kwalar rigarsa tace.
" wallahi ka shirya ka tafi Holland yau ka kawo min Na'eem idan ba haka ba mutuwa zanyi,
saboda tsananin b'acin ran da Mannir yake ciki, kuma kwata-kwata baya cikin hankali da nutsuwarsa rufe Zainab da duka yayi haik'an kamar zai kashe ta.
Dan gani yake kamar ita ta jawo komai, kuma gashi tazo tana neman k'ara mishi zafi bayan wanda yake ciki,
dakyar Zainab ta kwaci kanta ta gudu bedroom d'in ta,
sai dare sannan Mannir yaje bedroom d'inta ya rarrashe ta sosai, daga k'arshe suka rungume juna suna kuka.
HOLLAND 🇳🇱
Da misalin k'arfe 3:30am jirgin su Naseer yayi landing a k'asar Holland ,
dayake Naseer ya riga yasan k'asar sosai kasancewar acan yayi karatunsa na wajen 7yrs,
shiyasa sai da yayi booking komai, har gidan da zai zaune ya rigada ya gama dashi,
Dayake su ranting (haya) gidajensu ba irin namu bane, idan kayi hayar gida zaka samu akwai komai na gida babu abinda babu dai-dai da cokali akwai,
duk wani abu na gida akwai, everything.
Yana fitowa yaga taxi driver sa d'auke da sunansa a board NASEER MUSTAPHA,
direct wajensa ya nufa, tafiyar 40 minutes sukayi daga Airport kafin su isa gidan Naseer, a k'ofar gidan an rubuta NASEER MUSTAPHA 128A,
gidan mai kyau dan an k'ayata shi da kayan alatu na more rayuwar duniya,
gidan 3 bedroom maka-maka, kowanne bedroom akwai toilet & bathroom, sai makeken parlor da kitchen, dinning area, daga waje kuma akwai swimming pool, da garden, irin dai gidajen nan da kuke gani a films d'in turawa, gidan ya had'u iya had'uwa.
Dama tun daga Nigeria ya riga da yayi booking nursing nanny da zata rink'a kula da Na'eem 24hrs, dan haka a gidan yazo ya iske baturiyar mai suna Rose wacce a k'alla zata kai 45yrs ba,
da sauri ta mik'e ganin Naseer ta gabatar da kanta, simple smile yayi mata,
had'i da mik'a mata Na'eem, da bedroom d'aya yace ta d'auke shi, ya kai mata kayan Na'eem can.
Washe gari da ya fita siyayya, ya jibgowa Na'eem iyayen kayan wasa dana sawa, da motoci, machine na yara irin masu amfani da battery, banda lilina daya kwaso, da Teddy's d'aki guda ya ware ya shiryawa Na'eem kayan wasa.
Sosai Na'eem yayi b'ul-b'ul yayi kyau, dayake yana samun ingantacciyar kulawa, dai-dai da swimming pool sai dai Naseer ya zubawa Na'eem kayan a ciki dayake kullum da yamma sai sunyi wanka a ciki.
BAYAN SHEKARA UKU
Sosai Na'eem ya girma yayi wayo ga shegen surutun tsiya kamar aku dan yanzu ya kusan 4yrs,
har lokacin Naseer bai kuma waiwayar Nigeria ba, sau uku su Momy, Dady, Ikram na zuwa Holland wajen Naseer,
duk k'arshen shekara sai sun zo, duk sanda suka zo sai sun so tafiya da Naseer da Na'eem amma yak'i dan a cewarsa shida aure da Nigeria har abada.
Sosai Na'eem ya saba da Rose dan Momy ma yake ce mata shi a tsammanin shi itace Momyn shi,
tare suke komai da ita sun saba sosai.
Duk ranar Friday Naseer da Na'eem ke zuwa shopping,
yau ta kama Friday wajen 7:30pm suka tafi Sharaton dake birnin Holland,
tun da suka shiga gaban Naseer ke muguwar fad'uwa, tsoro da fargaba suka shige shi lokaci d'aya
Na'eem nata zuba mata surutu da unnnnnnn hmmmmmm un'un kawai yake binsa,
bayan sun gama siyayyar da zasuyi kaf har sun tafi wajen biyan kudi Naseer ya tuna bai sai perfumes ba,
dan haka ya juya wajen dake d'auke da perfumes,
Dior wanda tun bayan rasuwar Zarah ya koma amfani dashi ya shiga nema,
idansa ne ya sauka akan wani guda d'aya daya rage a wajen.
Da sauri Naseer ya mik'a hannu zai d'auka,
hannunsa ya d'ora akan na wata mace da itama Dior d'in tazo siya,
jin electric shock ta jashi yasa Naseer saurin d'auke hannunsa daga kan nata had'i da d'aga kai ya kalle ta.
Take zuciyarsa ta buga da tsananin k'arfin gaske, gabansa yayi mugun razanannan fad'uwa, yawon bakinsa ya k'afe ganin ZARAH tsaye a gaban sa,
cikin rawar baki Naseer yace " ZARAH!!!!.......
Don't forget to vote and comments
MOMYN ZARAH