GADAR ZARE…

60

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*






60






ZARAH!!!!, 

bayanta ta juya taga ba kowa, dan haka tayi tsammanin ko ba da ita yake ba, 

hannu ta kuma kaiwa zata d'auki turaren Dior, aiko caraf Naseer ya rik'e hannu ta, yana zubar da hawaye yace " dama kina raye Zarah? , 

kina raye amma kika b'oye kanki? 

kin san irin wahalhalun da faman dana sha, ya k'arasa maganar hawaye na zubo masa. 



Hannunta ta kwace had'i da cewa " who are you please? 



Tsaida kukansa cak Naseer yayi yana kallanta yace "Do you mean baki sanni ba? 



"Ok naji kamar kai ma d'an Nigeria ne, kuma bahaushe ko? 



Da hanzari Naseer ya rik'o hannun Na'eem yana nuna mata a gigice duk ya rud'e ya fita daga hankalinsa yace " kinga Na'eem d'in mu, ya kalli Na'eem yana nuna masa ita yace " ga Momynka, 

ya fad'a yana k'ok'arin rungume ta. 



Hankad'a shi baya tayi a fusace tace " how dare you? 



" Don't ever try to touch my body, Useless man ta fad'a tana jan tsaki mtwwwwwwwww, 

had'i da k'ok'arin barin gurin. 




Da sauri Naseer yasha gabanta yace " me kike nufi Zarah? 



A fusace tace " wai wacce banzar ce Zarah? 

 da zaka dame ni akanta, ni sunana LISAH, kuma ban san ka ban kuma tab'a ganin ka ba, kai ni ko me kama dakai ma ban sani ba!. 



Naseer na kuka ya nuna ta yace " yanzu nine baki sani ba Zarah? 

to idan ni baki sanni ba, I am sure you know him ya fad'a yana nuna Na'eem, 

tunda shi ke kika d'auki cikinsa har tsawon 9 months sannan kika haife shi kika kuma shayar dashi. 



Tsaki tayi gami da cewa Mad man, ta kuma zagaye shi zata bar wajen, 

da k'arfi Naseer ya fizgo ta jikinsa a fusace yace " ke kin isa ki k'ara tafiya ki barni, banza marar alk'awari, 

tauuuuuuu ta d'auke shi da mari ranta a tsananin b'ace tace " banza d'an iska kai yanzu ko kunya baka ji ba, 

kana Hausa Fulani kuma Muslim amma ka rungumi macen daba muharramar ka ba a bainar jama'a. 



Shima ransa a b'ace yace Ni kike cewa banza d'an iska Zarah? 

ni kike cewa ba muharraminki ba? 

to ki sani koda zaki canja komai a rayuwarki, baki isa ki canja zuciyar ki da kuma igiyoyin aure na dake kanki ba. 



Kasancewar k'asar Holland akwai security take jama'ar dake wajen suka kira police suka sanar dasu halin da ake ciki, 

Lisah nata k'ok'arin kwace kanta daga rik'on da Naseer yayi mata amma ta kasa, 

ana haka police suka shigo. 



Naseer ganin za'a kwace Lisah daga hannunsa yasa shi rik'e ta gammmmm yak'i sakinta, 

take ya birkice ya zama cikekken mahaukaci tuburan ya zage yayi ta hauka yana tik'ar uban dambe da police d'in, 

dakyar aka kwaci Lisah daga hannun Naseer, ganin an kwace ta yasa Naseer bud'e baki yana gunjin kuka yana cewa " she is mine, please don't let her go. 



Ganin Lisah ta shiga mota zata tabi su yasa Naseer sakin rikitaccen kuka da tsananin k'arfi yana cewa " please Zarah karki barni, karki kuma tafiya a karo na biyu ki barni, 

idan a baya na iya jurewa yanzu bazan iya ba, 

please don't leave me Zarah I love you please Zarah, 

amma ina ita Lisah ma gaba d'aya tsoransa ya gama kamata, gaba d'aya jikinta kerrrrrma yake. 



Driver na jan motar Naseer ya durkushe a wajen had'i da sakin rikitaccen kuka, 

police d'in suka danna shi a mota suka nufi police station dashi, sai da Rose tazo tayi belinsa sannan suka sake shi, 

koda Naseer ya koma gida direct bedroom d'in sa ya wuce Na'eem na tayi masa magana amma ko kallan sa bayyi ba, ya wuce bedroom had'i da dannawa k'ofar key. 



Kan bed Naseer ya zube ya shiga tunani tabbas da hannunsa da kuma kanshi ya saka Zarah a kabari, 

to amma ya akayi haka ta kasance danshi yasan wannan Zarah'n sa ce, 

domin irin bugun da zuciyarsa keyi masa a duk lokacin daya kasance da ita, 

ko kuma take kusa in da yake irin bugawar zuciyara tayi masa a lokacin daya shiga Sharaton, 

sannan irin reactions d'in dayake ji aduk lokacin daya tab'a jikinta kota tab'a nashi irinsa still yaji a lokacin da hannunsa ya sauka akan nata. 



Sannan her best perfume is Dior still yanzu ma shi taje siya, 

yama za'ayi ace masa wannan ba Zarah'n sa bace, 

a fili yace " that is impossible, 

mik'ewa yayi zaune had'i da yin tagumi da duka hannayen sa ya tallabo fuskarsa, 

tunani ya kuma yi, tabbas yasan matuk'ar Zarah ce babu yadda za'ayi ta ganshi ta nuna kamar bata san shi ba, 

yasan ko loosing memory tayi shine mutum na farko wanda idan ta ganshi nan take zata dowa hayyacin ta, 

kuma ma a ganin da yayi mata babu alamar ciwon komai a tattare da ita, 

Cikin cikekken hankali da nutsuwarta ya ganta, 

ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi had'i da tunanin mafita, 

zuciyarsa ce ta bashi amsa da cewa mafita d'aya ce shine ka zama inuwarta, duk inda tasa k'afa ta cire ya zamana kai ka maida taka ta haka ne kad'ai zaka san gaskiyar wacece ita.



Dan tabbas yasan there is something behind, 

dan yasan haka kawai babu yadda za'ayi Zarah ta ganshi amma ta nuna kamar bata tab'a sanin shi a rayuwarta ba, 

tunawa ya kuma yi da marin da tayi masa, 

a fili yace " _Banza d'an iska_

yasan babu yadda za'ayi Zarah ta iya d'aga hannu ta mari koda wani ne balle shi, balle kuma harta iya bod'e baki ta zage shi, 

haka dai Naseer ya kwana yana sak'a da warwara har garin Allah ya waye. 



Washe gari ranar Saturday, around 6:40pm Naseer na kwance Na'eem ya shigo bedroom d'insa da gudu, dan tun jiya da abin ya faru bai kuma fita ko k'ofar parlor ba, balle waje, 

yana bedroom d'in sa yana ta tunane-tunanen abinyi, sai kuka yake ya kasa dainawa, muryarsa harta dishe saboda kukan fitar hankalin dayake, dafa

kansa Na'eem yayi yana cewa " sweet Dad are you okey? 



Da sauri Naseer ya goge hawayensa, dan yasan matuk'ar Na'eem yaga hawayensa to fa ba zaman lafiya, 

dan Na'eem yana tsananin san Naseer, kwata-kwata ya tsani duk wani abu da zai saka Naseer a damuwa, 

idan yana k'aunar mutuwar sa yana san yaga hawayen Naseer, 

wasu lokutan idan Naseer ya tuna Zarah yana kuka, Na'eem zuwa yake yana goge mai hawaye shima yasaka kuka sai dakyar ake iya rarrashinsa, 

idan ko ya ganshi a damuwa ya rink'a tambayar sweet Dad waya b'ata maka rai, 

kowaye bazan barshi ba, 

idan na girma sai na rama maka na b'ata mishi ran shi ma, 

hakan kuwa yana yiwa Naseer masifar dad'i had'i da sashi cikin farin ciki har yaji kamar he is the best father in the whole world. 



Murmushi Naseer yayi had'i da cewa " I'm absolutely fine son, 

dariya Na'eem yayi had'i da cewa " amma sweet Dad ya baka chirya ba? 



" In shirya kuma, ina zamu? 


Fuska Na'eem ya b'ata cike da shagwab'a yace " sweet Dad ka manta ko? 



Kai Naseer ya d'aga alamar tunani yana murmushi yace " ayiwa Dad afuwa ya manta a taimaka a tuna masa, 



K'afa Na'eem ya d'an shura had'i da cuno baki yace " yau fa Saturday, 

"Ok I'm so sorry Son yau akwai zuwa shan ice cream ko? 


"To har yanzu banyi late ba, bari na shirya sai mu fita, 

dariya Na'eem yayi yana cewa " my best Dad. 



Ba tare da b'ata lokaci ba Naseer ya shirya cikin boyel riga da wando, da hula suka fita, 

diret Hilton garden suka nufa, bayan sun siya sun biya suna fitowa Naseer ya hango Lisah na shigowa, 

take duk ilahirin jikinsa ya d'auke kerrrrrma had'e da tsuma, gaba d'aya jikinsa rawa yake yana shaking, 

take zuciyarsa ta shiga bugawa da tsananin k'arfin tsiya, 

bai san sanda ya saki hannun Na'eem ya nufe ta, 

a baya Na'eem ya biyo shi. 



Gabanta Naseer yasha had'i da k'ura mata ido yana hawaye, 

cikin matsanancin kuka Naseer yace " please Zarah me mukayi miki a rayuwa ni da Na'eem da zakiyi mana haka? 



" Why Zarah, kin san irin mahaukacin son da nake miki, kin san bazan tab'a iya jurewa rashin ki, 

ya zube bisa gwiwoyinsa a gabanta, dai-dai lokacin da Na'eem ya k'araso wajen, ganin Dadynsa yayi kneeling down yasa shi ma yin kneeling down d'in kamar yadda yaga Naseer yayi had'i da rok'on hannun Naseer, shima ya fara kuka dan matuk'ar Na'eem yaga Naseer yana kuka shima sai yayi. 



Cike da tsananin mamakin gaske Lisah ke kallan su, 

Naseer yace " please Zarah ko ba danni ba, kodan Na'eem ki dawo gare mu dan girman Allah, kar laifin wasu ya shafe mu kiyi mana horo abisa laifin mak'iyan mu, ki tuna duk duniya baki da kamar mu, 

wannan d'anki ne ni kuma mijin kin, ya k'arasa maganar yana k'ara fashewa da rikitaccen kuka, 

ita dai Lisah tsayawa tayi sororo tana ganin ikon Allah abu kamar a film, 

cike da tsoro Lisah tace " wallahi Allah bawan Allah ban san ka ban tab'a ganin ka, ban ma san akan me da wa kake magana ba. 



A zuciye Naseer ya mik'e had'i da rik'o ta cikin matsanancin b'acin rai yana zubar hawaye yace " wallahi karya kike yi Zarah, 

kece Zarah ta, bugun da zuciya take min a halin yanzu ba k'arya bane, 

shi kad'ai ya isa ya shaidata min ke Zarah tace ta gaskiya, 

Zarah so ba k'arya bane, san gaskiya na tsakani da Allah har bada baya tab'a canjawa, 

idan ke ba Zarah ta bace babu yadda za'ayi zuciya ta rink'a bugawa a duk sanda na ganki, 

idan ke ba Zarah ta bace babu yadda za'ayi body reaction d'ina ya rink'a' canjawa a duk sanda na tab'a jikinki. 



"Zarah ana kama sak da sak a duniya sosai har murya har movements d'in ku ya zama iri d'aya da mutum amma banda bugawar zuciya da kuma soyayya, 

hannu ya d'ora akan saiti zuciyarsa yace " wannan bugawar da zuciya ta keyi yana yi ne domin ke kad'ai Zarah, bayan ke babu wata 'ya mace da zuciya ta ta tab'a bugawa akanta kamar haka, 

sannan ya d'ora hannunsa a saitin zuciyarta yace " wannan bugun da zuciyar ki keyi kad'ai ya isa ya shaidamin ke Zarah ta ce, 

domin zuciyar mu d'aya ni dake, a take suke bugawa, matuk'ar tawa tana bugawa da k'arfi haka kema taki zata kasance tana bugawa da k'arfin. 



Hannu Lisah tasa ta hankad'a Naseer baya a zafafe tace " waye kai,  daga ina kake, ina ka sanni? da kake neman shigowa rayuwata kake neman matsa min,

wallahi ban san ka ba, ban kuma tab'a ganin ka ba, 

tana kai nan ta watsar da ice cream d'in had'i da ture shi tayi waje da gudu. 



Sunkuyawa Naseer yayi had'i da duba ice cream, 

a fili Naseer yace " vanilla flavour , Zarah's best flavor, 

har lokacin Na'eem bai daina kuka, 

har suka koma gida kuka yake, sai da kyar Naseer ya samu ya rarrashe shi, yasha ice cream d'in sannan yayi bacci.



Washe gari kwata-kwata bayyi niyyar fita ba, 

yana kwance akan bed yajiyo Rose na fama da Na'eem, sai daru yake akan bazai je school ba sai yaga Dadynsa, 

sanin halin Na'eem da tsinanniyar kafiya da shegen taurin kai yasa shi mik'ewa dole ya zura jallabiya ya fita zuwa parlor, 

Na'eem na ganinsa ya tafi da gudu ya fad'a jikinsa, 

cikin maganar sa ta yara yace " Sweet Dad, kaji Mom wai na tafi school ban gan ka ba, 

kansa ya shafa had'i da k'ak'aro murmushin dole, 

dan yasan Na'eem da shegiyar tambayar tsiya idan ya ganshi a haka ya rink'a damunsa kenan da tambayar abinda yake damunsa, 

yace " yauwa my son, gara daka tsaya kaga Dadynka, 

dariya Na'eem yayi yace " Dady gayi min alkawayi tiya jaka kai ni school yau, 

murmushi Naseer yayi yace " kayi hak'uri son, ka bari sai gobe na kai ka, 

k'afa Na'eem ya shiga diddirawa a k'asa had'i da tab'a fuska zayyi kuka. 



Da sauri Naseer yace " ya haka kuma son? 



"Ni dai gacciya Dady cai ka kai ni, 

kai ne fa kace babu cau cab'a alkawayi. 



" Ni na fad'a Son amma yau ayi min uzuri please son, kuka Na'eem ya fara had'i da ajiye school bag d'in akan sofa yace " to ni ma na faca zuwa, 

dariya Naseer yayi yace " ayi haka kuwa son? 



"cocai ma, cewar Na'eem, bayi ka gayi ma bacci zanyi, sosai Na'eem ya bawa Naseer dariya, ganin yadda ya rufe ido yana jan mun shari wai shi bacci yake, 

har da sakin hannu,

 d'aukarsa cak Naseer yayi yana cewa " oh my son, Dad d'in naka zaka yima wayau, to muje na kai ka, 

dariya Na'eem yayi had'i da yiwa Naseer peck a kumatu yace " thank you sweet Dad. 



Naseer na driving amma gaba d'aya Na'eem ya isheshi da surutun sa, 

wani ya bashi amsa wani kuma ya kyale shi, har suka k'arasa school d'in, light kiss Na'eem ya k'ara yiwa Naseer a kumatunsa yana cewa " I love you Dad, 

murmushi Naseer yayi had'i da cewa " I love you too Son, 

tsayawa Naseer yayi yana kallan Na'eem har ya shige school d'in, 

murmushi yayi had'i da girgiza kansa yana mamakin tsananin wayon Na'eem, 

zai ja motar kenan ya hango Lisah na fitowa daga cikin motar ta tare daya wasu cuties baby's boy & girl. 



Tsayawa Naseer yayi cak had'i da k'ura mata ido, magana suka tsaya suna yi da yaran amma baya iya jiyo abinda suke cewa, 

dariya yaga tayi had'i dayi musu kiss, tsayawa tayi har suka shige cikin school d'in sannan tayi murmushi ta shiga motar ta taja, 

Naseer na ganin taja motar ya rufa mata baya, yana binta batare data sani ba.



Binta Naseer ya rink'a yi a baya batare data sani ba har suka isa gidan su, Naseer na gani tayi parking ta shiga gidan ya fito ya zagaya k'ofar gidan sannan ya shiga motarsa ya tafi. 



Tun daga ranar ya zama inuwarta ya zama duk inda take yana wajen, duk inda k'arta ta taka k'afar Naseer na wajen, data saka k'afarta a waje ta cire Naseer zai mayar da tasa, ya rink'a bibiyar da bibiyar lamuranta, 

sosai Naseer yake nazarinta yana karantar halayyarta amma kwata-kwata ya rasa makama balle hanyar dazai b'ullo mata. 



Naseer na haka ranar Mother's day tazo, dan haka Naseer ya shirya wani plan, 

ya shirya Na'eem sosai yayi masa kwalliya, d'aukar shi yayi yaje wajen siyan gift ya sai duk wani abu da yasan best choice's d'in Zarah ne har da Dior da chocolate da ice cream , 

sannan ya had'a pics d'inta ita da Zainab da Ikram da Mannir dashi Naseer d'in, 

ya siyi wani gift na love wanda akayi bututu kamar haka jiki _don't cheat, betray, in true love, love your husband madly, & true love never end_



Ya sa aka saka masa pics d'insu wanda dauka suna dariya su biyu, 

sannan ya siyi wani gift wanda uwa ke d'auke da babynta ta k'ura masa ido tana hawaye shima anyi rubutu kamar haka a jiki _no one loves you like the way your mother do! She is ur First Love, when she knows she is pregnant she cry because of happiness, and when you come to the world she is going to do the same , when you get pain she will cry, when you get sick she feel like she is sick too that is mother's true love...._


_So why dont you love me Mom?_


_I love you sweet Mom NA'EEM_


*HAPPY MOTHER'S DAY*



Naseer ya had'a gift d'in waje d'aya sannan ya saka mota ya kai shi har wajen da take a paradise island ya nuna mishi ita daga nesa ya bashi flower yace " idan kaje ka durk'usa a gabanta ka mik'e mata flower da gift d'innan kace I LOVE YOU SO MUCH MOM,

sannan kace mata come back home Mom kana kuka kaji son Naseer ya fad'a yana share hawayen idonsa, yayi kukan ne dan ya saka Na'eem dan yasan matuk'ar yayi kuka shima sai yayi, 

aiko take Na'eem ya fara kuka, had'i da nufar wajenta. 



Na'eem sarkin wayau beyi mistake ko d'aya acikin abinda Naseer ya koya masa ba, 

yana zuwa gabanta yayi kneel down yana kuka yace " I LOVE YOU SO MUCH MOM, please come back home, 

ya fad'a yana mik'e mata flower da gift d'in. 



Zumbur ta mik'e tsaye had'i da...........




Don't forget to vote and comments 




MOMYN ZARAH