62
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
62
Photos suka zubo, jikin Naseer na matsanancin kerrrma had'i da rawa ya durk'usa cikin mutuwar jiki yasa hannunsa dake karkarwa ya d'auki photos din yana dubawa,
take jikin Naseer gaba d'aya yayi collapsing had'e da weak,
ganin picture d'in sa wanda sukayi da Zarah tun kan suyi aure,
jikinsa na tsananin kerrrma yaci gaba da duba pictures din,pictures d'in Na'eem ya gani lokacin yana jariri dai-dai lokacin da Zarah ta mutu,
sai pictures d'in Ikram, Zainab da Mannir.
Jikinsa na muguwar tsuma ya bud'e diary din ya fara karantawa kamar haka....Da fari dai sunana ZARAH MUHAMMAD DAURA,
ni haifaffiyar garin kano ce,ina da yaro d'aya sunansa NA'EEM,,
sai kuma ubana kuma uwata domin shi tamkar mahaifi na dauke shi
ya wuce miji kad'ai a gare ni shi gaba d'aya rayuwa ta ne,
shi kad'ai keda zuciyar Zarah,
NASEER MUSTAPHA!!!
Ai tsayuwar gagarar Naseer tayi, take yaji gwiwoyinsa sun saki,,
k'afafuwansa kuwa kasa d'aukar sa sukayi balle su iya ci gaba da tsayawar saboda tsananin kerrrma da sukeyi,,,
cikin mutuwar jiki Naseer ya zube wanwar a k'asa,,
take numfashinsa ya fara nan d'aukewa,
yayinda Idanuwansa suke neman rufewa dan tuni sun fara gani dishi-dishi,,
lokaci d'aya jin sa ya d'auke kunnensa ya dod'e baya iya jin komai sai shhhhhhhhhhhh,,,
da sauri yasa hannuwansa ya toshe kunnensa dake ta faman yimasa amsa kuwa a cikin dodon kunnensa.
Zube gaba d'aya kayan yayi a k'asa yana bin su da kallon tsoro kamar yaga aljani,,
da sauri ya fara ja da baya yana daga zaunen har yakai ga bango,,
kwata-kwata Naseer baya cikin hankali da nutsuwarsa ya gama fita fit daga hayyacinsa,,
take ya fara tunanin ta yadda akayi hakan ta faru, hannayensa ya d'ago yana kallansa had'i da furta,,
"da wad'annan hannayen na saka ta acikin kabari,
a gaba na akayi mata sutura had'i dayi mata sallah,
ta ya hakan ta faru?
Yayiwa kansa da kansa tambayar,,
shi da kansa ya bawa kansa amsa da cewa lalle akwai wani b'oyayyen abu a k'asa,,
a zabure cikin rashin nutsuwa da hankali Naseer ya mik'e ya dinga neman evidence,,
ko dalilin dayasa Zarah tayi haka,
yana birkita d'akin yana mahaukacin kuka had'i da sambatu shi kad'ai,,
duk yabi d'akin ya hargitsa ya birkita komai,,
had'i da yin jifa da duk abinda yazo hannunsa a matuk'ar haukace Naseer yake yin komai had'i da kukan matuwa kamar za'a zare masa ruhinsa daga gangar jikinsa,,
Gaba d'aya Naseer ya haukace ya zama tantirin mahauci tuburan,,
ya zage ya rink'a tik'ar hauka haik'an,,
ganin ya birkice komai da ko'ina na d'akin amma ya rasa wata hujjar komai yasa Naseer zubewa bisa gwiwoyinsa had'i da sakin uban ihuuuuuuuu da duk gidan sai da ya amsa kuwwa,,
dafe kansa yayi da hannu bibbiyu yana kukan mutuwa tuburan muraran,,
had'i da tsananin mamakin wannan birkitaccen al'amari,,
shi yanzu babban burinsa na farko yana so ya fara gano dalilin dayasa Zarah tayi haka,,
tayi masa wannan mummunan hukuncin akan laifin wasu, laifin daba shi ya aikata ba,,
laifin da kwata-kwata bai kamata ya samu hukuci akansa ba,,
ya rasa dalilin da yasa Zarah tayi masa wannan mugun butulcin.
A kanta babu abinda bayyi ba, babu irin wulak'anci da k'ask'ancin da bayyiwa jama'a ba,,
shi yana san Zarah tsakani da Allah ne badan komai nata da kowa nata ba,,
true love yake mata, wanda shi da kansa ya rasa wanne irin makahon so yake mata,,
wanda akan ta zai iya rufe ido ya tatawa kowa tijara,amma shi Zarah zata guda, shi zata yiwa haka,
akan me tayi masa?
akan wanne dalili?
Hannu Naseer yasa ya dafe kansa had'i da d'aga kansa sama cikin d'aga murya yace " why Zarah? I don't deserve all this punishment from you!!!
I didn't cheat on you, and I didn't hurt you,,
but why do you cheat me?
why do you hurt me and betrayed me?
" why all this?
" why do you create this drama and scene?
"Why Zarah?
Ya k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka mai ban tausayi.
Zarah na school haka kawai taji gabanta yana fad'uwa,kirjinta ya shiga bugawa take tsoro da fargaba suka shigeta lokaci d'aya,,
a hanzarce ta mik'e ta fito da wayar ta kira ta sanar da abokiyar zamanta halin da take ciki,sannan ta kashe wayar, kwata-kwata ji tayi yau bata iya zaman school d'in balle harta iya fahimtar lactures din,
dan haka ta mik'e tayi waje,
direct wajen motarta tayi ta bud'e ta jefa hand bag d'inta sannan ta zagaya ta shiga had'i da yiwa motar key ta nufi gida,,
tana tuk'in gabanta na ci gaba da fad'uwa yayinda zuciyar ta ke bugawa da saurin bala'i,,
tana shiga harabar gidan ta fito,,
ji tayi gabanta yana tsananta bugawa da k'arfi, yayinda matsanancin tsoro da fargabarta suka k'aru.
Cikin mutuwar jiki ta shiga gidan,
tana isa parlor ta tsaya cak, gabanta yayi mummunan fad'uwa ganin duk illahirin gidan an hargitsa shi,,
take zuciyar ta tashiga tsalle tana tsuma kamar zata tsaga k'irjinta ta fito,,
da sauri ta saki hand bag d'inta ta fad'i k'asa,,
da gudu ta nufi secret bedroom d'in ta,
tana ganin k'ofar a bud'e taji mummunan tashin hankali had'i da matsananciyar fargaba,
a kid'ime ta shiga bedroom d'in da gudu, bata lura da Naseer ba, direct ta nufi k'ark'ashin gadon ta durk'usa had'i da lek'awa,,
ganin babu abinda take nema ne yasa ta yin baya da sauri a matuk'ar razane.
Idon Naseer ya sauka akanta,kamar daga sama Zarah taji muryar da ko gigin mutuwa take taji ta zata gane ta,,
dan har abada bazata tab'a mance muryarsa ba.
" Wannan kike nema?
cewar Naseer yana yi mata nuni da diary d'in dake hannunsa.
Iya kid'ima da mummunan razana Zarah tayi,
cikin matsanancin tashin hankali ta kalli inda taji maganar,,
zaune ta ganshi diary da photos d'in a gabansa,,
da k'arfi ta runtse idanuwanta had'i da sauke razananiyar ajiyar zuciya,,
take duk ilahirin jikinta ya d'auki kerrrrrma had'i da tsuma,,
ta zaro gaba d'aya Idanuwanta waje kamar zasu fad'o k'asa,,
tashin hankalin data shiga kuwa bazai tab'a fad'uwa ba,
dan tayi muguwar razana,
a kid'ime ta mik'e tsaye had'i da zuba masa idanuwanta, shi kansa Naseer jikinsa yana rawa ya mik'e tsaye had'i da zuba mata nashi idon,,
wanda yasa ta dole yin k'asa da nata idon,,
hannunshi ya tafa had'i da cewa " wonderful miss...... sai yayi shiru had'i dayin murmushi yace " Lisah ko?
"Ko Zarah zan kira ki?
"Ni na rasa ma da wanne sunan zan kira ki dashi ZARAH KO LISAH?
"Amma tunda naga kinfi san Lisah bari na kira shi dashi,
Miss Lisah ya fad'a idanshi tarrrr akan ta,
" gaskiya Lisah kin cika jarumar gaske, kin cancanci yabo,
kin cancanci a jinjina miki,A kuma tafa miki,
saboda tsananin halaccinki da amanarki sannan da kuma gaskiya da alk'awarin ki.
"Weldon Miss Lisah master planner, ya fad'a yana tafa hannun.
dakewa Zarah tayi had'i da cewa " ni fa Malam ban fahimci abinda kake nufi ba please waye ka..............
Tauuuuuuuuuuuu!!!!!
Kauuuuuuuuuuuu!!!!!
Naseer ya yarfa mata lafiyayyun marika kyawawa guda hud'u wanda suka hana ta k'arasa maganar rainin wayon datayi niyya,,
hannayenta tasa ta tallafe duka kuncinta,,
tana ci gaba da kallansa ido cikin ido,,
duk da itama tasan sanin kanta ne zata iya fuskantar fiye da haka daga gare shi,,,
dan tasan Naseer da shegiyar bak'ar zuciya mai zafi,,
cikin matsanancin b'acin rai ya matso daf da ita yana huci yace,,
" karki sake ki kuma neman raina min hankali ko wayau,,
kinyi wasa da hankali da tunanin na,,
bama iya ni kad'ai ba har iyayen mu Zarah.
"Banza d'an iska, kalmar da kika jefe ni da ita kenen,
Zarah na yarda dake amma kin cuce ni, kin ha'ince ni kinci amanata,
kin yaudare ni, lokacin da kika kira ni da BANZA D'AN ISKA sai na tabbatar wa da kai na cewar bake bace,,
saboda nasan Zarah ta kwata-kwata bazata tab'a iya bud'ar baki ko da mutumin daya girmeta da sati d'aya bane,,
amma zuciyata ta tak'i yarda cewar bake ce Zarah ta ba,
ya k'arasa maganar cikin matsanancin kuka,,
sosai itama Zarah ke kuka kamar ranta zai fita,
a hankali ta durk'usa a gabansa bisa gwiwoyinta taci gaba da rusgar kukanta batare data iya cewa komai ba.
" A lokacin da zuciya ta ci gaba da gaskata min cewa ke Zarah ta ce kin san me nayi?
Ajiyar zuciya ya sauke had'i da share hawayensa yace " kyautata miki zato nayi,
na kuma yi miki uzuri,,
sannan nace nasan tabbas kina da kwakkwaran dalilin dayasa kika aikata haka Zarah,saboda tsananin son da nake miki yasa na kasa ganin laifinki ko sau d'aya,na kasa kallan ki a matsayi wacce ta munafurce ni,
maimakon hakan ma sai nayi miki uzuri na kuma kyautata miki zato,,
Zarah son da nake miki bai tab'a bari ko sau d'aya na tab'a ganin ki da laifi ba a iya tsayin rayuwa ta,
Zarah san da nake miki yasa na kasa kallan ki a matsayin wacce taci amana ko ta gujeni ba,,
a kullum kwanan duniya ina miki kallan mutuniyar kirki wacce tafi kowacce mace a duniya kyawawan halaye na gari,,
kinsan duk mai ya jawo hakan?
"Saboda sanda nake miki na gaskiya ne,
My love for you is a pure and true love,,
Zarah k'arfin soyayyar gaskiyar danake miki ne ya kawo ni Holland,
dan nazo na iskeki,
soyayyar gaskiyar danake miki ne yasa Allah ya bani ikon zuwa Sharaton ranar,
soyayyar gaskiyar danake miki ne yasa duk sanda na ganki zuciya ta ke bugawa da k'arfi,
bugun zuciyata ya k'aru wanda tun asali yana yi ne dan ke kad'ai,,
Zarah kin san halin dana shiga lokacin da kika barni?
"Haukacewa nayi, na rink'a hauka tuburan,,
akanki nabar k'asa ta, garin mu, tushe na, mahaifa ta, dangi na, 'yan uwa na, ahalina, da kuma iyaye na,,
Zarah akanki babu irin abin da ban yi ba,
amma saboda ke ba mutum bace kika rasa da abinda zaki saka min sai haka,,
har d'anki na tura miki saboda nasan k'arfin soyayya irin ta d'a da mahaifi am........
Kasa k'arasa maganar yayi saboda matsanancin kukan daya ci k'arfinsa,,
yana kukan yaci gaba,
"amma saboda tsabar rashin imani kika watsar dashi,
kika gaya masa ke ba Momyn sa bace,
ki duba irin maganganun da Na'eem ya fad'a miki wanda duk uwar da d'anta kamar Na'eem ya fad'a haka dole zuciyar ta ta karye,,
ta tausaya masa, duk girman laifin da akayi mata,,
balle ke da ba laifin zaune bana tsaye, ba'ayi miki laifin komai ba,
amma kika zab'i kibar yaronki d'an 6 months, da mijinki,
duba da k'ananan shekarunsa, ya sanar dake matsalarsa wanda ni danake tare dashi bai tab'a fad'a min ba,,
amma kasancewar ki na uwa rana d'aya ya sanar dake,
amma saboda tsantsar rashin tausayi haka kika juya masa baya,
kika yi tafiyar ki kika barshi a wajen yana kuka,,
har kika cusa k'in ki da k'iyayyarki a zuciyarsa,,
duk da cewar shi yaro ne amma har ya fuskanci kwata-kwata baki san sa, baki k'aunarsa,,
shima yace baya sanki ( he hate you), ya k'arasa maganar hawaye na bin kuncinsa.
Ita dai Zarah tana durkushe ta kasa cewa komai sai tsananin kuka da take yi,,
bata iya furta koda kalma d'aya ba, illa kukan fitar ran da take yi.
Tsananin bak'in ciki ne yasa Naseer durkushewa had'i da fasa ihuuuun mutuwa,,
yana kukan tsananin bak'in ciki da takaicin rayuwa,,
cikin kukan yace cewa.
"Why Zarah?
" mai yasa, menayi miki?
"Why, ya k'ara fashewa da azababban kuka mai cin rai.
Kamar an zabure shi ya mik'e zambur ya shak'i wuyanta,,
had'i da damk'ar gashin kanta,,
kamar zararren mahaukaci,,
a fusace yace " meyasa Zarah?
" Zarah why?
Daga bayansa Naseer yaji an ce " leave her, I'm the one that suppose to told you, what is hide in darkness, It's me that deserve to told you the real secret, and what was happened .
A rikice Naseer ya juya yana kallan inda maganar ke fitowa,
sosai ya kid'ime ganin Doctor JENNIFER a gabansa hard'e da hannuwanta a k'irjinta .................
Don't forget to vote and comments
MOMYN ZARAH