63
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
63
Tarrrr Jennifer ke kallan Naseer ido cikin ido ba tare da wani tsoro ko shakkar komai ba,,
cikin mamaki yake binta da kallo bakinsa a bud'e, a hankali ya nunata da d'an tsansa cikin rawar baki yace " you?
Takowa Jennifer ta fara yi tana nufar Zarah a hankali,batare data kalli inda yake ba tace " yes Naseer it's me,,
tsaye kawai Naseer yayi yana kallanta cike da matsanancin mamaki,,
yama rasa abin yi ko abin cewa,gaba d'aya al'amarin ya d'aure masa kansa ya kulle masa kwakwalwar sa,,
sun rikita masa lissafi, had'i da sanya shi a cikin duhu,a hankali Jennifer tasa hannu ta d'aga Zarah daga durkushen data ke,juyawa ta kumayi tayi tattaki zuwa wajen tissue ta d'auko had'i da mik'ewa tace " wipe up your tears and stop crying,karb'ar tissue d'in Zarah tayi ba tare data iya tsaida kukan datake yi ba.
D'an zaman da Jennifer tayi da Zarah na 4yrs, da kuma zaman da tayi a Nigeria na 3 yrs yasa ta jin hausa sosai kamar yarenta,,Naseer dai kallanta kawai yake cike da mamaki.
Dakyar ya bud'e bakinsa cikin rawar murya yace " you create all this drama and scenes?
Tsayawa tayi had'i da hard'e hannayenta a k'irjinta tace " yes Mr Naseer for sure its me, are U're shock and surprised?
Kallanta kawai Naseer ya cigaba dayi batare daya ce komai ba.
Sai can yace " but why?
Murmushi Jennifer tayi had'i da cewa " now you come to the point,
and now you do the right things and good question,
abinda ya kamata ka fara tambaya kenan tun da farko tayi maganar cikin harshen Hausa,,
cike da wani mamakin ya k'ara ci gaba da kallanta,,
murmushi ta kuma sannan tace " yes, Naseer ina jin Hausa tun a Nigeria,,
kuma cikin harshen Hausa zan baka labarin abinda ya faru.
Gyaran murya tayi sannan ta fara,
ASALIN LABARIN MUTUWAR ZARAH
" Tun lokacin da aka kawo Zarah bata da lafiya, sanda ta karye,,
naji a raina ina matsanancin tausayin yarinyar duk da tun a lokacin ni na fahimci cewa ba accident bane,
saboda yadda take kuka had'i da sambatu a cikin sambatun da take yi na fahimci cewa duka ne,,
a lokacin na k'ara jin tausayin ta sosai, musamman dana duba k'ananan shekarunta, da kuma juna biyun dake jikinta,,
na duba girman Family irin naku, wanda your father is former Nigerian president,amma naga yadda yarinya k'arama daga Familyn El-mustapha tana cikin irin wannan mawuyacin halin,,
sai nayi tunanen ko she is a house maid,
sai kuma naga yadda ka rude ka gigice ka fita hayyacinka akanta,
sannan naga kyanta da softy skin d'inta,,
sai na tabbatar she is among da Family's.
"Babu yadda banyi da Zarah akan ta sanar da ni ainahin abinda ke damunta ba amma fir tak'i,at the end dana dameta da tambaya ma sai ta daina min magana,tun a lokacin ta samu hawan jini jininta ya hau sosai, har yakai tun abin na bani mamaki har ya dawo bani tsoro,
na kuma k'ara jin mugun tausayin ta a rai na,
na rasa meye matsalar yarinya k'arama kamarta 'yar 17yrs,naga dai ku baku da matsalar kud'i, ko wani nakasu ta wajen jin dad'in rayuwa ko kayan alatun morewa duniya, da jin dad'in ta,,
dan nasan ko mafi k'ask'anci daga cikin ma'aikatan gidan ku yafi k'arfin babu da talauci har k'arshen rayuwarsa,,
saboda El-Mustapha mutum ne na mutane, yana da matuk'ar kirki, da alheri, ga tausayi, jin k'ai da kuma taimakon al'umma, nayi tunnani mai zurfi na kasa gano ainahin matsalarta a lokacin gashi kuma kwata-kwata ta daina bani fuska balle nasa ran jin damuwarta.
" A haka har Allah yasa Zarah ta samu lafiya karayarta ta warke sumul har aka sallameku daga asibitin,
tun daga nan ban k'ara jin labarin Zarah ko na kuma ganinta ba sai ranar da aka kawo ta haihuwa,,
a lokacin da aka kawo ta haihuwa na ganta a galabaice, ta gama fita daga hayyacin ta sosai,,
kuma jininta yayi mugun hawa,,
sannan a lokacin abinda ya hana Zarah haihuwa da kanta zuciyar ta ce ta kumbura, zuciyar ta a kumbure shine dalilin da yasa ta kasa haihuwa da kanta,
a wannan lokacin ne na k'ara tabbatar wa there's something wrong,
tun daga nan nayi tunanin akwai wani mummunan al'amari dayake faruwa da yarinyar,
na bak'in ciki, ko k'uncin rayuwa to dan haka na sakawa rai na kota halin yaya sai naji labarinta na kuma taimake ta,
a lokacin nayi iya yi na
amma tak'i gaya min komai, haka a wannan lokacin na hak'ura akan dole batare da na samun abinda nake san samu ba.
Haka a wannan lokacin ma aka kuma sallamarku,
har zuwa lokacin da aka kuma kawo Zarah hospital a karo na uku,,
a wannan lokacin zuciyar Zarah ta riga da ta gama tab'uwa sosai dan 60% ta lalace,,
al'amarin da yayi mummunan tsora tani kenan ya d'aga min hankali na,
ganin mummunan halin da yarinya k'arama ke ciki,,
sai lokacin a wannan lokacin naci nasara Zarah ta sanar dani halin da take ciki,
bayan kun kawo Zarah asibiti an shigar da ita emergency.
EMERGENCY ROOM
Ajiyar zuciya Doctor Jennifer ta sauke bayan ta gama kallan scanning report d'in da akayiwa Zarah,,
a hankali Doctor Jennifer ta jawo kujerar ta zauna had'i da zubawa Zarah ido kawai batare data ce mata komai ba,,
sai da tayi kusan 10 minutes sannan ta kuma sauke ajiyar zuciya had'i da kiran sunanta " Zarah,,
kai Zarah ta juyar daga kallan Doctor Jennifer dan tasan maganar da Doctor Jennifer kesan yi mata,,
bata kula da yadda Zarah tayi mata ba taci gaba da magana.
" Zarah ki taimaki kanki da rayuwarki ki fitar da abinda ke ranki yana damun rayuwarki,
wanda har ya kai ga yiwa rayuwarki mummunar illa haka,
ya jawo miki ciwon zuciya,
a matuk'ar razane Zarah ta juyo tana kallan Doctor Jennifer,,
"Yes Zarah kalli kiga kiga yadda kaso 60 cikin 100 na zuciyar ki ya lalace,,
cewar Doctor Jennifer tana nunawa Zarah scanning d'in, sannan gaki da ciki, duka-duka yaushe kika haihu amma gaki nan da wani cikin har na 3 months,,
cikin mummunan kid'ima Zarah ta mik'e zaune had'i da cewa ciki?
Kai Doctor Jennifer ta d'aga mata alamar eh,
a razane Zarah taci gaba da kallanta tana hawaye,,
mik'ewa daga kan kujerar Doctor Jennifer tayi ta koma kan bed d'in ta zauna a gefen Zarah had'i da dafa kafad'arta,
cikin sanyin murya Doctor Jennifer tace " ki daure ki amaryar da abinda ke cikinki ko kya samawa kanki cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali,ki yarda dani zan taimaka miki da abinda nasan zan iya, dan Allah ki daure ki sanar dani damuwarki.
Runtse ido Zarah tayi tana zubar da hawaye,,
a hankali tace " haka kawai na yarda dake har naji zan iya sanar dake damuwa ta,
na kuma ji lokaci d'aya na aminta dana gaya maki sirri na, daga nan Zarah ta sanar da Doctor Jennifer komai na rayuwarta, tun daga zuwan mahaifinta kano, har zuwa auren shi da mamanta,
har zuwa labarin cikin Na'eem, da auren su da Naseer, da labarin Zainab da Mannir,
babu abinda Zarah ta iya b'oye mata, tana maganar tana kuka harta gama.
Doctor Jennifer tun da Zarah ta fara bata labarin rayuwarta take kuka,
sannan matsanancin tausayin Zarah ya k'ara ratsa zuciyar ta da gangar jikinta,
hawayen ta share had'i da janyo Zarah jikinta ta rungume batare data iya furta koda kalma d'aya bace,, taci gaba da kukanta kawai,,
daga ita har Zarah kukan suke babu mai rarrashi wani,,
sai da sukayi kukan su har suka gaji sannan Doctor Jennifer ta d'ago kai ta kalli Zarah,
a hankali ta share mata hawayen ta had'i da cewa,
" kiyi hak'uri duk abinda kika ga ya samu bawa muk'addari ne daga Allah, sannan kuma jarabawarsa ce haka,
dan Allah baya tab'a barin bawa batare da ya jarrabi imanin sa ba,
ki godiya ga Allah abisa jarrabawar da yayi miki,
ki kuma yi addu'ar Allah ya baki ikon cinye jarabawarki,
ke taki kalar jarabawar kenen baki san kalar ta wasu ba,
ina da shawara da mafita d'aya idan zaki yarda da ita.
Da sauri ta tsaida kukanta had'i da k'urawa Doctor Jennifer ido, batare datace komai ba.
Doctor Jennifer taci gaba da magana " ban sani ba ko zaki yarda ba ki amince da hakan ba,
dan bani da tabbacin zaki yarda,
amma wannan ita kad'ai ce mafita,
da sauri Zarah tace " fad'i muji ina jinki.
Ajiyar zuciya Doctor Jennifer ta sauke had'i da cewa " mutuwar k'arya zakiyi,
"Kamar ya? cewar Zarah cikin rashin fahimta,
" kinga yanzu kina da shigar ciki har na 3 months, sannan ga ciwon zuciya,,
to matuk'ar kina san tsira da lafiyarki da kuma rayuwarki dole ne kiyi nesa da Familyn ki,,
har na wani lokaci ta yadda gaba d'ayan su zasu san darajarki da kuma k'imarki,,
ki koyawa kowa hankali,
sannan kiyi nesa da su, ki dage ki nemarwa kanki damarki,,
sannan ki kwatarwa kanki 'yanci,
kuma ki...........
Zarah ce ta dakatar da ita ta hanyar cewa " ni fa ban gane abinda kike nufi ba, ki fito sak a mutum kiyi min bayani.
Murmushi Doctor Jennifer ta yi sannan tace " ai ina kan magana ta ne, kamar yadda kika ji nace kiyi mutuwar k'arya tun farko to haka nake nufi,,
allura zanyi miki wacce take saka mutum suman 24hrs,
idan nayi miki allurar sai na fita na shaidawa Family ki cewar kin mutu,,
bayan anyi miki sutura da jana'iza sai ni kuma naje na tuno ki,
yau dama saura na just 2 weeks na koma Holland,
idan zan tafi sai na tafi dake can ayi miki ingantaccen magani sannan a baki kulawa ta musamman,
hope kin fahimci abinda nake nufi yanzu?
Zarah wacce tunda Doctor Jennifer ta fara magana ta saki baki kawai tana kallanta sororo kamar wata tab'abb'iya cike da mamaki,,
har ta dasa aya, murmushi Zarah tayi had'i da cewa " ke a tunaninki yanzu nabar yaro na d'an 6 months da mijina, dangina da iyaye na na biki ko me kike nufi?
"Yes of course cewar Doctor Jennifer,
murmushi Zarah ta kuma sannan tace " laifi na ne dana biyeki na sanar dake sirrina,
ke yanzu a ganinki da tunanin ki wannan adalci ne nayiwa kaina,
nabar kowa nawa na biki, ke da ban sanki ba, ban San ainahin wacece ke ba,
ban san k'asarku, yaranki, addinin ki ba, kawai sai na biki,
to wai ma duk ba haka ba tayya ma zan yarda dake?
" Nasan dama dole kiyi tantama akan maganata,
kasancewar yanzu kwata-kwata duniya ba yarda da amana ta zama abin tsoro,
dole kiyi shakku akaina,
sannan ni 'yar k'asar America ce,
cikin garin Holland,
sannan ni musulma ce kamar ki, ana dai kira na ne da Jennifer ko Janny saboda shine ainahin sunana,
a hankali Doctor Jennifer ta rik'o hannun Zarah cikin nata, had'i da kwantar da murya tace " tun ranar dana fara ganin ki naji ina sanki, with no reasons,
naji kuma ina tsananin tauyawa rayuwar ki, har naji ina san na taimaka miki,
Zarah ki yarda da ni bazan tab'a cutar ki ba,
bazan kuma tab'a cin amanar ki ba,,
kawai dai ina san nayi miki gata ne,
na zame miki uwa kuma ya,,
Zarah ki rufawa kanki asiri ki nisanci wannan family tun kafin su kashe ki ko su illata rayuwar ki,,
wallahi wallahi wallahi Allah, na rantse miki da girman Allah bazan tab'a cutar dake kona ci amanarki ba,
Allah ya sani zanyi miki haka ne dan nayi maki gata sannan na kwatar miki 'yan cinki.
Haka Doctor Jennifer taita kwad'aitawa Zarah zuwanta Holland da kuma amfanin zuwan nata,,
da kuma fa'idar nisantar ahalinta,
sai da Doctor Jennifer tasha wuya sosai kafin daga k'arshe dakyar Zarah ta yarda ta amince da shirin Doctor Jennifer.
Sai da tayi mata allurar da 10 minutes sannan ta shaidawa su Naseer cewar ta mutu,
bayan an kai Zarah kabarinta an binne Doctor Jennifer tabi dare taje ta hak'o ta,
takai ta gidan ta, ta kwanta, sai da akayi good 7hrs da hak'o Zarah sannan ta farka daga doga dogon suman datayi tana ambaton sunan Naseer.
Da sauri Doctor Jennifer ta isa gare ta,
had'i da bata ruwa tasha, sannan takai ta bathroom tayi wanka ta shirya taci abinci.
Washe garin ranar Doctor Jennifer ta fara yiwa Zarah shirye-shiryen tafiya,,
da neman visa,
bayan sati biyu suka d'aga zuwa Holland,
bayan 2 weeks da zuwan su Doctor Jennifer ta samarwa Zarah Admission a University of Holland ta fara karantar gynecology (likitan mata).
Bayan Doctor Jennifer ta gama bashi labari ta juya ta kuma kallan shi tace " yanzu Zarah she is gynecologist Doctor dan yanzu haka ma tana aiki a hospital d'in danake aiki,
sannan tana wani course ne a halin yanzu.
Murmushi Naseer yayi had'i da cewa " you leave me with no reasons Zarah,
anan kwata-kwata babu wani babban dalilin da zai saka ki barni har tsawon 4yrs,,
duk soyayyar danake miki ta tashi a banza kenan,
Zarah you cheat me,
you hurt me and you disappointed me,
Zubewa Zarah tayi a gabansa had'i da fasa rikitaccen kuka tace,
" wallahi nima ina sanka, ban kuma yi haka da nufin na cutar dakai kona ci amanar ka ba,
nayi haka ne danna nemana mafita, dan Allah kayi hak'uri nasan nayi maka laifi mai girma,
but please forgive me, please Naseer ta fad'a tana rik'o k'afafuwansa.
Wancakalar da ita yayi gefe had'i da matsawa baya da sauri,
cikin b'acin rai yace " karki kuskura ki k'ara tab'a ni,
Zarah kwata-kwata bana buk'atar ki a rayuwata ta gaba,
baki da wani abu da zaki gaya min da zai sa na saurare ki,
baki da abinda zaki kare kanki dashi,
babu wani abu da zai sa na saurare ki,
baki da abin cewa Zarah ya fad'a yana share hawayen dake zubo masa,
yace " abin da matuk'ar ciwo idan makusancinka ya cutar da kai,
amma ba komai.
Yana kaiwa nan ya juya ya nufi hanyar fita,
ya kai bakin k'ofa yana gaf da fita cikin matsanancin kuka da rawar murya Zarah tace " bazaka saurare ni ba koda nace na haifa maka cikin dana taho dashi, bazaka yafe min ba koda na sanar dakai ina tare da YARANKA ('YA'YANKA)?..................
Don't forget to vote and comments
MOMYN ZARAH