GADAR ZARE…

64

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*







64





Cak Naseer ya tsaya batare daya juya ba,, 

ganin ya tsaya ne yasa Zarah cikin muryar kuka cewa " eh Naseer na haifa maka cikin dana taho dashi,, 

kuma twins Allah ya bamu mace da namiji,, 

na sawa namijin sunan Dadynka MUSTAPHA ana kiransa da NAWAF,, 

ita kuma macen na sa mata sunan Momynka MARYAM, ana kiranta da NURR,, 

Naseer Allah ne kad'ai yasan meya b'uye a tsakanin mu,, 

Allah kad'ai yasan dalilin dayasa ya raba mu har tsawon 4yrs,, 

ni dai nasan tabbas Allah baya tab'a yin abu babu dalili,wallahi Naseer nima ba'a san rai na ne, nayi nesa da kai ba sai dan dole, 

ta k'arshe maganar cikin matsanancin kuka. 



A hankali Doctor Jennifer ta tako gaban Naseer ta kalle shi had'i da sauke ajiyar zuciya kana tace,, 

"" Naseer kai kanka kad'ai ka sani, Ita kasan halin bak'in ciki da mawuyacin halin data shiga akan nesa datayi dakai? 



" garin Allah bai tab'a wayewa dare ya kuma yi ba tare da Zarah tayi matsanancin kuka akan Ka ba,tun ina rarrashinta har na gaji na hak'ura na dai na,na saka mata ido dan na fuskanci abin nata ya wuce so, so, 

ya zama ciwo,, 

Ni baturiya ce naga soyayya iri daban-daban amma ban tab'a ganin tsananin so, da alk'awari irin na Zarah ba,tasha wuya sosai kafin ta iya saita kanta, 

dan wallahi Allah sai da Zarah ta kusa samun tab'un hankali akan ciwon sanka. 



A hankali Doctor Jennifer ta taka izuwa bakin wata wardrobe ta bud'e ta d'auko wani file tazo gaban Naseer ta mik'a masa,, 

tace " karb'i ka gani da idanta irin halin da itama ta shiga akan mahaukacin son da ta keyi maka, 

ita da tasan ma kana raye kenan, tasan kuma kana nan cikin koshin lafiya,, 

haka ta rink'a bibiyarka. 



"Sannan kai a zatonka kai ka ga Zarah? 



" To idan ma zaton ka kenan ka dai na,, 

domin Zarah ce ta ganka, itace ta kuma bayyanar da kanta a gare ka. 



"A zatonka kai ke bibiyarta? 



"To nan ma idan zato kake ka daina domin ita ce ke bibiyar rayuwarka. 



Kasan ya akayi hakan ta faru? 



Shiru kawai Naseer yayi had'i da hard'e hannayensa a k'irjinsa ya zuba mata ido yana kallanta. 



Doctor Jennifer taci gaba " bayan Zarah ta haifi su Nawaf,, 

sai tayi masifar tada hankalinta akan ita dole sai ta koma Nigeria wajenka, 

babu yadda banyi akan na rarrashe ta na hana ta tafiya amma fafur ta kafe tak'i,, 

haka akan dole na hak'ura na fara k'ok'arin naima mata ticket,, 

Allah bai sa ta kai ga tafiya ba nasamu labari daga wajen abokanan aiki na hospital cewar tun bayan mutuwa Zarah kabar Nigeria kuma baka kuma komawa,bayan na sanar da ita halin da ake ciki,, 

Zarah ta shiga mummunan tashin hankali dan kwata-kwata ta daina ci ta daina sha balle walwala, 

hakan dana gani ne yasani tafiya Nigeria dole dan na gano k'asar daka tafi. 



Bayan na gano kana nan Holland ne yasani dawowa cike da d'oki na sanar Zarah,, 

ranar tayi farin ciki sosai, tun daga ranar ta shiga binciken ka, 

da kuma inda kake zaune, 

sai da tasha bak'ar wahala sosai na wajen 2yrs sannan ta gano ka, gidan ka komai naka. 



" A ranar da Zarah ta fara ganin ka tasha kuka sosai kamar ranta zai fita dan sai da ciwonta ya tashi,

yi tayi kamar zata mutu ta rink'a shid'ewa. 


 

"A lokacin kasan meyasa bata bayyanar maka da kanta ba? 



"Saboda akwai rikici matuk'ar ita ta fara bayyanar maka da ita hakan yasa dole muka shirya maka GADAR ZARE,, 

ya zama na cewar kai ne ka ganta ka kuma fara yi mata magana. 



Tun daga wannan rana kullum Zarah sai taje gidan ka,, 

wani lokaci ma acan take kwana, 

makarantar daka saka Na'eem can ta saka su Nawaf da Nurr, sannan ta had'a su friendship a tsakanin su,, 

kuma kullum sai taje taga Na'eem kuma daga nan take had'a masa lunch box d'in sa,, 

kuma ita ke bashi abincin kullum a baki. 



Kasan me yasa bai gane ta ba? 



Shi dai Naseer ba baka sai kunne, 



" Saboda b'adda kama take (basaja) canja kama take,, 

sannan taje masa. 



" Kasan me yasa take canja kama kafin taje masa? 



Ta kuma tambayar Naseer, batare data jira amsarsa ba taci gaba. 



" Saboda ta tabbatar da cewa Na'eem yasanta a photos, 

ta kuma san Na'eem yana da wayo sosai da shegen surutu matuk'ar ya ganta a kamanninta na gaskiya sai ya gane ta. 



" Kana tsammanin duk mafarkin Zarah ko gizonta dakake gani ba itace a zahiri ba? 



" To ba mafarki bane ba kuma gizo take yi maka ba, 

itace a zahiri take zuwar maka cikin barci,

bayan mutuwar Zarah a Nigeria baka ganta ba? 



"Tazo maka kamar gizo, ranar da akayi rigima akan Na'eem,, 

to a lokacin ma ba gizo bane ita ce a zahiri, 

ranar da jirgin mu zai tashi zuwa Holland ne, 

ta tubure akan bazata tab'a iya tafiya batare data je ta ganka ba, 

kuma tana san ta d'auko Diary d'inta da photos d'in familyn ta,, 

babu yadda banyi na hanata zuwa ba, saboda ina tsoran kar asiri ya tonu amma ta nace dole sai da taje ta ganka.



Haka ma a gidan ka na nan Holland kusan kullum Zarah sai taje ta kwana acan,, 

kota kwana a bedroom d'in ka kota kwana da Na'eem. 



 "Ranar da Na'eem ya kai mata gift ranar Mother's day nasha wuya sosai kafin na samu kanta dan kusan mutuwa tayi saboda tsananin kuka,, 

Naseer Zarah na tsananin sanka, da k'aunarka, 

itama tana sanka da zuciya d'aya, 

her love to you it's pure and true love, 

she really love you so much Naseer, 

Wallahi Zarah zata iya sadaukar da komai akanka da kuma farin cikinka Naseer. 



Shiru Naseer yayi kawai yana sauraren Doctor Jennifer dan shi kwata-kwata wannan surutun nata ba shigar shi suke ba, 

dan wannan bai isa hujjar da Zarah zata iya kare kanta dashi ba,, 

sai lokacin Naseer ya tuna abubuwa da dama, wannan dalilin ne yake sa kullum Na'eem baya cin abincin lunch box d'insa kenan,, 

kenan duk mafarkan da yake yi da Zarah a gaske suke faruwa, 

zahiri ne, shiru yayi yana tunani sosai sai can ya sauke ajiyar zuciya, 

Batare daya kalli ko d'aya daga cikin su ba, 

Naseer yace " ina 'ya'yana (yara na)? 



Kafin d'aya daga cikin su ta bud'i baki tayi magana ta bashi amsa,, 

su Nawaf da Nourr sun shigo da gudu,, 

ganin yanayin Doctor Jennifer da Momyn su yasa su yin turussss,, 

a hankali suka nufi wajen Zarah, 

Nawaf yace " Momy what wrong with you? 



Nourr tace " Sweet Mom who make you cry? 



Bata basu amsoshin tambayoyin su ba, illa nuna musu Naseer da tun shigowar su yayi kneeling down yana kallan su,, 

gaba d'aya yaran da Cindo a hannayen su suma, 

sannan ga tsananin kamar da macen (Nourr) keyi da Momynsa,, 

Namijin ma (Nawaf) kamar an tsaga kara shi da El-Mustapha Dadynsa, sosai yaran ke tsananin kama da iyayensa. 



Cikin muryar kuka Zarah ta nuna musu NASEER tace " This is your Father, 

da sauri Nawaf yace " what Sweet Mom u mean he is our Dad? 



Kai ta gyad'a musu kawai, batare data iya furta koda kalma d'aya ba, Nour tace " I know him, he's our Father's friend Na'eem . 



" Yes, and I'm Na'eem's mother, 

I'm his Mom like you, 

he's my blood son. 



"What, but Sweet Mom are you kidding and us? 



Kafin Zarah ta kuma cewa wani abu,, 

Doctor Jennifer tayi saurin cewa " its not kidding or joke, 

he is your real Dad, let me show you evidence, 

ta fad'a tana d'auko Diary da photos d'in da Naseer ya zubar, tana nuna musu pictures d'in Naseer da Zarah a tare, sannan ta nuna musu Diary d'in, 

shiko Naseer kukan bak'in ciki da takaici ya saka, wai ace 'ya'yansa na cikinsa halak malak, 

amma basu san shi ba, suna doubting akan cewar he is there real blood Father,, 

ai suna gama gani da gudu suka nufi Naseer suka fad'a jikinsa suna murna,, 

tsam-tsam Naseer ya rungume su a jikinsa kamar za'a kwace masa su yana kuka. 



Nourr tace " Dad ina Na'eem? 



Kanta ya shafa yana zubar da kwalla had'i da kallanta yace " yana gida, 

"Dad ka kaimu wajen sa please Nouwaf ya fad'a cike da shagwab'a yana langwab'ar da kai gefe, 

shafa kansa Naseer yayi yana murmushi yace " dama ai kun gama zama a nan, dan bazan barku ku k'ara koda 1 second ba nan, a razane Zarah ta d'ago kai had'i da tsaida kukanta ta kalle shi, 

dan tasan halin Naseer da kafiya, taurin kai da kuma bak'ar zuciya,, 

kenan duk abinda Doctor Jennifer ta fad'a masa bai sa zuciyar sa tayi sanyi ba. 



Ganin Naseer ya mik'e yana k'ok'arin fita rik'e da hannun yaran yasa Doctor Jennifer cewa,, 

" wai ku maza mai yasa kwata-kwata baku da adalci da tausayi ne kanku kawai kuka sani? 



" Naseer yadda fa kake tak'amar kana san Zarah itama haka take sanka,, 

haka yadda kake tak'amar kasha wuya a kanta haka itama tasha bak'ar wuya akanka, 

yadda kake tak'amar tabar ku kai da Na'eem, kuma kayi rainansa,, 

haka itama ta zauna ta haifa maka twins ta kuma yi maka rainan su, 

amma dan rashin tausayi da imani da tsabar rashin adalc................



Kauuuuuuuuuuuu!!!!!!!!!!!!!! 

Tauuuuuuuuuuuu!!!!!!!!!!!!!! 



Naseer ya watsawa Doctor Jennifer gigitattun marika kyawawan gaske,, 

 a zuciye cikin matsanancin b'acin rai ya nuna ta da yatsansa yace " tunda na shigo gidan nan kinji nayi miki magana kona kulaki? 



"Ko kinji na tanka miki? 



" Jennifer babu wanda ke da alhalin duk wannan laifin sai ke,duk ke ce kika ja komai, kika kuma k'irk'iri komai,, 

saboda badan ke ba nasan babu yaddan za'ayi kwakwalwar Zarah, ko tunaninta ya bata ta barni,ke kika jawo komai, duk wannan tarin d'umbin laifin da kika yi min amma ki zo gaba na ki tsaya min kina min surutan banza,, 

har ke zakiyin maganar adalci, da san kai? 



" Ke kina da bakin da zaki maganar rashin imani da tausayi? 



"Ke ki duba girman laifin da kikayi,, 

kin raba ma'aurata, kin raba uwa da d'anta, kin raba uba da 'ya'yansa, sannan ita kanta Zarah kin rabata da kowa nata harna tsayin 4yrs,, 

duk wanda yaji maganar nan ke zai d'orawa laifi, 

saboda kin haifi Zarah, 

kuma sannan kin fita wayo, hankali da tunani.



" Duk da cewar ita ma da laifinta tunda ba zarga mata igiya kikayi kika jawo ta ba,, 

ba kuma rufe mata bakin dazata sanar da wanda ya cancanci hakan kikayi ba,sannan ba rufe mata tunani da kwakwalwar ta da zatayi tunani kikayi ba, 

ya k'arsa maganar yana kallan Zarah datayi tsaye sororo had'i da rufe bakinta da hannayenta dan ganin marin da yayiwa Doctor Jennifer, 

yaci gaba " Jennifer you're behind of all this drama, 

and you are the one who was created the scenes, 

wallahi sa'a ma kika ci daban ci ubanki nayi miki mugun duka ba, 

kuma zan tafi da yara na naga uban daya isa ya hanani tafiya dasu. 



Doctor Jennifer data saki baki tana kallan Naseer saboda tsabar mamaki tace 

" I think you knew this country is not your selfish, rubbish, jobless, homeless craters country bane, 

inaga ka d'auka yadda wannan k'azamar wulak'antancciyar k'asar taku (Nigeria) take haka ko'ina ma yake,, 

to ka sani mu nan bama sonkai, bama karb'ar cin hanci da rashawa kuma bama a fusace Naseer yayi kan Doctor Jennifer,, 

sanin halin Naseer yasa Zarah saurin shiga tsakiyar su, dan tasan ba k'aramin aikin Naseer bane yayi mata mugun duka ba. 



Cikin daga murya yace ma Zarah " stop it please, 

I'm Nigerian, so I won't tolerate any disrespect or disgrace my nation,, 

sannan ta kalli Naseer tace " ni ya kamata ka daka Naseer ba ita ba,, 

a kaina ya kamata ka huce fushinka ba'a kanta ba, saboda nice taka, nice kuma wacce nayi maka laifin ba ita,, 

tsananin bak'in ciki ne yasa Naseer nausar mirror d'in dake gefensa ya tarwatse batare daya kuma cewa komai ba yaja hannun yaransa suka fita, durk'ushewa Zarah tayi a wajen had'i da fasa mahaukacin kuka, da sauri Doctor Jennifer ta k'arasa inda take had'i da d'agota tace " yi sauri kibi mijinki, 

kiyi fighting akan rayuwarki Zarah yanzu da da yanzu ba d'aya bane, 

kin san duk takness d'in da zakibi wajen karkato da hankalinsa shi gareki. 



"Nasan kin san lagwansa, kiyi yak'i ki karkato da hankalinsa gare ki,, nasan Naseer yana tsananin sanki kuma da bak'ar zuciya, kuma zuciyar sa tana iya sawa ya hak'ura dake duk tsananin san daya yake miki, ki dage ki kula da mijinki da yaranki, 

ki tuna yaranku uku ke dashi dan haka ya zama ke kema kin zama shi, 

kin zama dolensa shima ya zama dolenki, 

ki bi shi, kije kiyi yak'i akan rayuwarki da farinki, 

gobe in sha Allah zanzo na kawo muku kayan ku keda su Nourrr, zanyi missing d'inku sosai Zarah, mun saba 4yrs ba wasa ba, 

ta fad'a hawaye na gangaro mata, 

itama Zarah kuka take, cikin kukan tace " nima zanyi kewarki sosai, 

murmushi kawai Doctor Jennifer tayi had'i da saurin juya bayanta, 

Zarah zata kuma magana Doctor Jennifer tace " just go, 

batare data kuma magana ba ta juya ta fita da gudu tabi bayan Naseer. 



Tana zuwa harabar gidan ma ya dad'e da tafiya dan haka tayiwa motarta key tabi bayan sa,,

a gefen motar Naseer tayi parking ta fito da sauri, 

a tsaye ta hangoshi a bakin k'ofa yana yin nocking,, 

da sauri ta k'arasa wajensa har tana yin tuntub'e,, 

dai-dai lokacin da Na'eem ya fito da gudu daga cikin gidan yana kiran,, 

" you are welcome sweet Dad yana dariya,, 

ganin Zarah yasa shi yin turuss had'i da b'ata rai take. 



Yace " you again? 



Durk'usawa Zarah tayi had'i dakai hannu zata tab'a shi, 

da sauri Na'eem yaja baya had'i da cewa, 


"Ok you come and make my Sweet Dad cry again. 



Kai Zarah ta girgiza masa batare data iya cewa komai ba sai hawaye da ke zubo mata, 

cikin kuka tace " no, I Won't make your Dad cry forever, na dawo nan da zama ne nima,, 

" what cewar Na'eem yana kallan Naseer,, 

tsaye Naseer yayi hard'e da hannuwa a k'irjinsa yana kallan su, 



Na'eem ya kalli Naseer yace " Sweet Dad is she not the one that made you cry last time?

and she is the one said you are lied to me, 

so Dad I really hate her, impact if she is going to stay here I'm leaving now, 

ya fad'a yana hankad'a Zarah waje da k'arfi yace " I really hate you so much, get out from our home, 

ta bud'e baki zatayi magana. 



Da sauri Na'eem yace " I don't want here anything from you, and I said get lost, I hate you I don't want see you again in my life, 

ya k'ara hankad'a ta waje, 

ganin bata da niyyar fita ne yasa Na'eem kallan Naseer yace " sweet Dad if she won't leave I'm leaving............ 




Don't forget to vote and comments 



MOMYN ZARAH