GADAR ZARE…

65

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*







65







Da sauri Zarah ta k'arasa wajen Na'eem tana kuka ta rungume shi tsam a jikinta, 

ta yadda bazai iya kwacewa ba, 

aiko yayi ta mutsu-mutsun kwacewa amma ya kasa, 

cikin kuka Zarah tace " am so sorry Na'eem, 

I know I hurt you, but am so sorry dear, 

shiru Na'eem yayi ya kasa k'ok'arin barin jikin Zarah, 

had'i da kwantawa lufffff a jikinta, cikin kuka Zarah taci gaba " I'm your beloved mother, your sweet Dad has not lied to you, jin tace itace Mom d'insa yasa shi saurin barin jikin ta had'i da zuba mata ido kawai yana kallanta. 



"Yes Na'eem nice mahaifiyarka, nice mamanka, halak malak. 



"To Momy me yasa kika bar mu ni da Dady na, mu kad'ai? 



Shiru Zarah tayi ta kasa cewa komai, ci gaba Na'eem yayi " Momy meyasa baki zo mun kwana tare a the same bed ba? 



"Meyasa baki bani abinci a baki na kinyi wasa dani ba? 



"Momy meyasa kika ce ke ba Momy na bace, ko bakya san mu ni da Dady na? 



Gaba d'aya tambayoyin Na'eem k'ara rud'a Zarah sukayi,ta rasa abincewa kuka kawai take yi duk jikinta na kerrrma. 



Naseer na tsaye sak'ale da hannayensa a k'irjinsa ya zuba musu ido kawai,, 

yana mamakin wayon Na'eem kamar ba yaro k'arami ba, ganin Zarah bata da abincewa yasa Naseer durk'usawa a gaban Na'eem had'i da rik'o hannayensa cikin nasa yana kallansa, 

fuskarsa d'auke da murmushi yace, 

" ba san mu ne bata yi ba, kasawa ranka Momynka na sanka fiye da kowa da komai a duniya,, sannan ka sawa ranka cewar duk uwa ta gari bazata tab'a yin nesa da yaranta haka nan ba,, 

sai dai idan akwai wani kwakkwaran dalilin kaji, 

kuma daga yau karna kuma jin kace you hate her, she is your real beloved mother,, 

so love her so much until your last breath, 

kai Na'eem ya d'agawa Naseer yana dariya, murmushi Naseer yayi had'i da mik'a masa hannu yace " promised me you u'll love her dearly,, 

dariya Na'eem yayi had'i da cewa " yes Sweet Dad I promise you,, 

dariya Naseer yayi had'i da ja masa hanci yace " dats my boy, 

go an say sorry for her, 

ba musu Na'eem ya tafi wajen Zarah had'i da kama kunnansa dan haka Naseer ya koya masa yace. 




" Am so sorry sweet Mom, rungume shi Zarah tayi tana kuka tace " am so sorry too dear, 

I'm really sorry for what I did to you, 

and I promise I will never repeat it again, 

dariya yayi had'i dacewa " apologize accepted Mom, 

komawa wajen Naseer yayi yace " Sweet Dad na bata hak'urin, 

kansa Naseer ya shafa yana murmushi yace " good boy. 



Nourrr da Nouwaf na gefe tsaye sun yi sororo suna ganin ikon Allah, 

dan su basu kai Na'eem wayo sosai ba,

ya fi su wayo duk da ba wata tazara ce sosai a tsakanin su ba, just 10 months ya basu, 

sai lokacin Naseer ya juya ya kalli su Nouwaf da Nourr dake tsaye a nutse, 

dan yaran sun samu ingantacciyar tarbiyya duk da kasancewar a turai aka haife su kuma suke rayuwa da yaran turawa,amma a nutse suke cikin kamala da tarbiyya. 


Naseer ya nunawa Na'eem su yace " another surprise,, 

cikin matsanancin mamaki Na'eem ya bud'e baki yana kalan su, 

had'i dayi musu dariya, yace " friends are you here? 


Kafin su bashi amsa Naseer yayi saurin cewa " they're not just a Friends to you, 

they're your beloves sister and brother, 

they're your junior bro & sister,, 

suma 'ya'yana ne kamar kai,kuma suma Momynka ce ta haifesu, uwarku d'aya ubanku d'aya kai da su, 

ya fad'a yana jawo su Nouwaf jikinsa, 

" wow this is amazing Dad, gaskiya am very happy to day, 

Momy na da 'yan uwa na sun dawo gida,,

da sauri ya saki Naseer yaja hannun su Nouwaf cikin gidan,, 

Naseer ya bi su da kallo yana murmushi, 

yana k'ok'arin mik'ewa Zarah ta rik'o k'afafunsa da sauri ta zube a gabansa ta shiga bashi hak'uri, 

k'afa Naseer yasa ya tsallake ta yayi shigewarsa cikin gidan ya barta anan. 



Da sauri ta mik'e itama ta shiga gidan har tana tuntub'e, 

amma bata ko tsaya tabi takan tuntub'en datayi ba, 

a parlor ta tsaya tana bin Naseer da ido zaune a tsakiyar yaransa, 

a hankali ta zauna akan sofa tana ci gaba da kuka, d'a da mahaifi sai Allah,

a hankali Na'eem ya taso yana sharewa Zarah hawayen ta dake ta faman zuba yace, 

" Mom meyasa kike ta kuka? 



Murmushin dole Zarah ta k'ak'aro had'i da cewa " ba kuka nake ba ido na ke ciwo, 

ayya Mom sorry kinji, 

ya juya ya kalli Naseer yace " Dad Momy bata lafiya ka kai ta hospital,, 

shima murmushin dole yayi had'i da cewa " daga hospital d'in muke yanzu, 

daga nan bai kuma cewa komai ba. 



K'arfe 10:30pm na dare gaba d'aya yaran sukayi bacci,, a hankali Naseer ya mik'e ya kwashe yaran ya kai su bedroom d'in sa ya kwantar, 

kasancewar 3 bedroom ne a gidan Rose tana cikin d'aya, 

d'aya kuma Naseer da suke kwana tare da Na'eem,, 

sai d'aya dake cike da kayan wasan Na'eem, 

tsaye yabar Zarah ta rasa inda zata shiga, tana nan zaune har around 11:30pm na dare, 

ga yunwa da bacci gashi batayi sallah ba, 

a hankali ta mik'e ta nufi bedroom d'in Naseer wanda dama ta riga tasan shi, 

tunda tana yin satar layi tazo gidan, 

tsaye ta iske shi yana safa da marwa a d'akin yana zubar da hawaye, 

bata yi mishi magana ba, ta wuce bathroom cikin sanyin jiki tayi wanka had'i d'auro alwala, 

wardrobe d'in kayansa ta bud'a ta d'auko jallabiyyarsa ta saka a jikinta, sannan ta sanya hijab ta tada sallah, 

duk abinda take yi idan Naseer na kanta, 

dan gaba d'aya hankalinsa na kanta, 

sai da ta gama rama sallolin da ake binta sannan ta fita ta nufi kitchen kwai ta soya, sannan ta hada tea mai kauri ta sanya bread ta nufi bedroom d'in Naseer dashi. 



Yadda ta barshi haka ta dawo ta iske shi, a hankali ta ajeye tray d'in akan table sannan ta koma ta kama hannun Naseer batare datayi mishi magana ba, 

da sauri ya fisge hannunwasa a fusace yace " karki kuskura ki k'ara gigin tab'a ni, 

cikin sanyin murya tace " please ko tea d'in ne kawai kasha, dan Allah. 



A k'ufule Naseer yace " dacan da kika barni har tsayin 4yrs ke kike ci dani? 



"Ko da kika dawo kinga alamun yunwa a tattare dani? 



Hawayen dake zubo mata ta goge cikin muryar kuka tace " please Uncle kayi hak'uri ka yafen laifin danayi maka, 

ka tuna Allah yana san mutane masu yafiya, 

kuma ko Ubangijin daya halicce mu muna yi masa laifi mu tuba ya yafe mana, 

dan Allah ka zamo mutum mai yafiya, da saurin manta sharri da tuna alkhairi, ta k'ara maganar hawaye na zubo mata, 

bai ce mata komai ba ya bud'e wardrobe ya d'auki plow da blanket yayi ficewarsa, 

durk'ushewa Zarah tayi had'i da fasa kuka. 



Washe gari wajen k'arfe 2:00pm na rana Doctor Jennifer tazo ta kawo musu kayan su gaba d'aya, yanayin data iske Zarah yasa tasan har lokacin Naseer bai hak'ura ba, 

dan haka taja hannun Zarah ta zaunar da ita a gefenta tana kallanya tace " Zarah kiyi hak'uri, 

hak'ik'a mun taru munyiwa Naseer babban laifin da duk wanda akayiwa irinsa zeyi abinda Naseer yayi koma fiye da haka,ki sakawa ranki hak'uri da dauriya, gami da juriya, 

ki jajirce ki dage kiyi ta bashi hak'uri, 

sannan kin san lagon mijinki,kibi duk hanyar da zaki bi ki shawo kan kayanki, 

 ki daure karki bari ciwonki ya tashi please, 

sosai Doctor Jennifer ta bawa Zarah shawarori sannan tayi mata nasiha sosai gami da k'ara mata kwarin gwiwa. 



Ganin gidan yayi musu kad'an yasa Naseer canja musu gida, 

mai shegen kyau babba sosai wanda yasha kayan alatun more jin dad'in rayuwar duniya, 

sosai gidan ya tsaro, mai d'auke da part 2, 

part d'in farko yana d'auke da 4 bedroom sai babban parlor, kitchen & dinning area, 

kowanne bedroom akwai toilet & bathroom cikin sa, sannan a parlor ma akwai toilet and bathroom, 

part na biyu 1 bedroom 1 parlor and 2 toilet & bathroom, 

kun dai san tsarin ginin turawa akwai kyau, girma da tsaruwa,, 

Inda nan ne part d'in Naseer.



Kasancewar Rose ta d'an manyanta yasa Naseer yi mata kyauta ta kud'i mai yawa yace taje ta dogara da kanta ta kuma kula da kanta, sannan ya sallameta, 

bayan yasa ta nemo masa wasu 'yan Philippines 🇵🇭 guda biyu,, 

mai suna Rosiline & Warda, 

inda aka basu bedroom d'aya, duk da Zarah bata barin su suyi mata girki, 

kula da yara da gyaran gida kawai suke mata, 

shima banda part d'in Oga Naseer dan ita take gyara masa, 

Zarah ta d'auki bedroom d'aya, 

Sai Nouwaf & Na'eem bedroom d'aya

sai kuma bedroom d'in Nourr daban, 

sai part d'in kayan wasan yara, wanda ya had'a komai kamar a childrens park, 

sai gym (wajen motsa jiki), 

sai swimming pool and garden. 



Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin Naseer da Zarah, 

kwata-kwata baya kula ta, baya shiga harkarta, 

tayi iya yinta a banza, 

dan haka bak'in ciki yasa Zarah shiga bedroom d'in ta had'i da zaman dirshan ta fasa kuka,, 

Na'eem ne yaga bata parlor dan haka ya shiga bedroom d'in ta nemanta,, 

ganin tana kuka yasa shi fita da sauri ya kira su Nouwaf da Nourr, 

a gaba suka saka ta suna tambayarta meke damunta ganin bata basu amsa ba yasa su fashewa da kuka gaba d'ayan su,, 

kasancewar Zarah tana cikin matsananciyar damuwa yasata mantawa da wad'anda take tare ta shiga basu labarin komai.



Daga Zarah har yaran kuka suke, 

sosai take basu labarin komai kamar suna fahimtar abinda take gaya musu, 

kasancewar akwai soyayya da shak'uwa mai k'arfi tsakanin ta da yaranta, 

dan tare take kwana dasu, dan koda taje bedroom d'in Naseer ma korota yake, ko ya gaya mata bak'ak'en maganganun da zata kwana tana kuka, 

ko kuma kafin taje ya kulle, dan haka ta mai da hankali sosai akan yaran take jan su a jikinta, 

komai itake yi musu wanka wani lokacin ma tare suke wasa, da gym and swimming, 

sai da ta gama basu labarin kaf sannan Na'eem dayake yana da wayo yace " to Mom yanzu mai zamuyi mu taimake ki, 

dad'i Zarah taji har ranta, cikin kuka ta rungume yaranta tana cewa " ku taya ni bawa Dadynku hak'uri ya yafe min laifin dana yi, 

Na'eem yace " Momy ki koya mana yadda zamuyi. 



Koya musu duk yadda zasuyi tayi sosai, 

dukkan su kuka suke sosai sun rungume ta, 

suna haka Naseer ya shigo neman yaran dan ya kira phone babu wanda yayi picking, 

kai tsaye ya shigo bedroom d'in, 

yanayin daya gansu sosai ya tab'a mishi zuciya suka bashi tausayi, 

dan ba k'aramin so yake yiwa yaran sa ba, 

dan sun tarbiyantu, sosai Zarah ta zage ta bawa su Nouwaf ingantacciyar tarbiyya irin ta addinin musulci, 

abinda yasa ya rage masa jin haushinta gami da tsanarta kenan, 

ya tabbatar koda baya raye yaran sa sunyi sa'ar uwa ta gari wacce zata tsaya tsayin daka akan tarbiyarsu. 



Yakai wajen 15 minutes tsaye yana kallan su kafin hankalin Na'eem yakai kansa, 

da sauri Na'eem ya saki jikin Zarah, 

sai lokacin duk suka lura dashi, 

a hankali Zarah ta mik'e taje gabansa tayi kneel down had'i da kama kunnenta, 

tana zubar da hawaye tace " am sorry Uncle, 

banza yayi da ita ya juya yana k'ok'arin fita, 

da sauri gaba d'aya yaran suma sukayi kneel down a gabansa had'i da rirrik'e kunnuwansu suma su kace 'we are sorry Dad, 

murmushi Naseer yayi had'i da umarta su dasu tashi, 

amma fir yaran suka k'i tashi suka ce har sai ya yafewa Momyn su, 

tsawa Naseer ya daka musu had'i cewa I said get off, 

gaba d'aya yaran da Zarah suka saka kuka mai rikitarwa a lokaci d'aya, 

Ido Naseer ya zaro cike da mamaki, 

komawa sigar rarrashi Naseer yayi, cikin wayo Naseer yace " ok to ku tashi shikenan ya wuce kuzo na kai ku shan ice cream, 

mak'e kafad'a yaran suka yi had'i da cewa " no Dad, we don't need, 

Please Dad forgive our Mom, 

dan Allah Dady ka yafewa Momy matuk'ar kana san ganin mu cikin farin ciki da walwala, 

idan kuma kak'i yafe mata bazamu tab'a tashi daga kneel down d'in nan ba, 

suka fad'a cikin kuka, 

babu yadda Naseer bayyi su tashi ba amma suka k'i sai ma matsanancin kukan da suke ci gaba dayi, 

a hankali Naseer ya kalli Zarah yaga yadda take kuka, kamar ranta zai fita, 

suna had'a ido ta langwab'ar masa da kanta, 

da sauri ya kawar da kansa daga gare ta, 

ya kalli yadda Na'eem, Nourr, Nouwaf ke kuka, 

jin kukan yake yi har cikin ran sa, yana k'ona masa zuciyar sa, 

yayinda yake jin zafin kukan nasu sosai kamar ana yankar namar jikinsa, 

ido Naseer ya runtse da k'arfi yana tuna irin so da kulawa gami da halaccin daya nunawa Zarah, 

sannan ya tuna girman laifin data yi masa, amma babu yadda zayyi dole ya yafe mata kodan albarkacin yaranta. 



A hankali ya bud'e idansa da suka gama komawa jajaye ya sauke su akan su, 

yace " is okey, na yafe mata, 

ai da sauri suka mik'e gaba d'ayansu sukayi kansa cike da murna.



Tun daga wannan rana Naseer ya d'an sakarwa Zarah, 

duk da ba wani sosai bane, 

yana dai zama parlor ta yanzu, 

yana kuma zama a dinning tare da ita da yaran suci abinci, 

wata mu'alace dai kwata-kwata babu ita, 

dan bama taga fuskar yin hakan ba, 

to yanzu zaman nasu zamu iya cewa ba laifi, 

dan ba yabo ba fallasa, 

duk da har yanzu baya barinta ta shiga part d'insa, 

magana ma sai ta kama a tsakanin su ko ta zama dole yake mata jefi-jefi, 

duk ta rame ta shiga muguwar damuwa ko abinci ba kasafai ta fiye ci ba. 



Haka dai suka ci gaba da rayuwa a cikin wannan halin, 

ranar Sunday babu aiki Naseer ya kwashi duka yaransa ya fita yawo dasu, 

duk da Zarah taso bin su amma ya hana ta dan baima bata fuskar cewa zata bisun ba, 

tana zaune ita kad'ai a gidan ta rasa inda zata saka ranta da damuwar ta, 

abun duniya ya ishi rayuwata, 

Doctor Jennifer tayi sallama, 

cike da murna Zarah ta mik'e ta rungume ta, had'i da fasa mata kukan da ita kanta bata san dalilin yin sa ba, 

shiru Doctor Jennifer tayi ta rasa abin yi, 

a hankali cikin mutuwar jiki ta ja hannun Zarah zuwa bedroom d'in ta, 

a bakin bed ta zauna ta zaunar da Zarah a gefenta, sai da ta rarrashi Zarah tayi shiru sannan ta tambaye ta abinda ke faruwa, 

ba wani b'oye-b'oye Zarah ta zayyane mata duk abinda ke faruwa tsakanin ta da Naseer. 



Shiru Doctor Jennifer tayi na wani lokaci had'i da zubawa Zarah ido, 

sai da tayi wajen 7 minutes sannan ta sauke ajiyar zuciya tace " ke yanzu Zarah duk hannunka mai sandar danayi miki ashe baki fahimci abinda nake nufi? 



Kallanta kawai Zarah keyi batare data ce komai ba, 

Doctor Jennifer taci gaba " ai lusarar mace kuma sakaryar mace ce zata tsaya tana gaba da mijinta har na tsawon 3 months, 

haba Zarah kamar ba mace ba, 

har ki tsaya namiji yana sha miki k'amshi yana basar dake, 

akwai hanyoyi da dama wanda Naseer ko dutse ne shi da k'arfe tsabar taurin kai sai ya bada kai bori ya hau, 

ke wallahi da kansa ma zai kawo kansa yana gurfane a gabanki yana bada hak'uri koda kece kikayi masa laifin, 

haba ni ina mamakin mata irin ki, 

da zaku zauna namiji yana rejecting d'inki, 

bayan yanzu kai ya waye, ido ya bud'i ilimi yazo mana, akwai hanyoyi da dama dazaki iya shawo kan mijinki kuma ki mallake kayanki batare da asiri ko tsafi ba, 

ba kuma sai kinyi shirka ko kin sab'awa Allah ba. 



Matuk'ar kika rik'e gaskiya da amana, kika kuma ji tsoran Allah akan lamuranki, 

kika dai-dai ta tsakanin ki da Allah da kuma shi Oga, 

sannan kika kasance mai hak'uri, juriya da kawar dakai daga abubuwa da dama, kina ganin an cuce ki an kuma zalunce ki amma ki kawar da kanki,

bayan kina da yadda zakiyi, akwai magana ko abinda baya buk'atar martani ko ramuwa ido kawai ya ishe mai hankali, 

Idan kika zuba masa ido shi da kansa zai dawo yana jin kunyar ki, 

duk iskancinsa da rashin kunyarsa. 



Cikin rashin fahimta Zarah tace " wallahi ban fahimci abinda kike nufi ba. 



Murmushi Doctor Jennifer tayi had'i da cewa " ina nufin bayan wad'anan abunuwan sai kin had'a da abubuwa uku, 

KISSA

KARUWANCI da kuma

BARIKI. 



Da sauri Zarah ta zaro ido tace " KARUWANCI da BARIKI kuma? 



Murmushi Doctor Jennifer ta kuma sannan tace " eh Zarah, 

matuk'ar kina san ki tsira ki kuma yi fice a gidan mijinki dole sai kin had'a da wad'annan abubuwan, 

da farko sai kin cire kunya kin zama tantiriyar mara kunya karuwa kuma 'yar bariki a gidan mijinki, 

karki sake kunya ta cuce ki ta hana ki kwatarwa kanki 'yanci a gidan auren ki, 

wannan shine babban k'alubalen dake damun matan Hausawa, 

shiyasa duk duniya da kuma k'abilar duniya babu inda aka fi sakin aure da yawan ZAWARAWA kamar a Hausa, 

da wuya kaga, bayerabiya, inyamura, banufiya, Igbo, Indian Arabian da sauran k'abilun aure ya mutu ko kaga bazawara, 

wannan ya samu asali ne saboda dalilai biyu zuwa uku, 

na farko k'addara, 

na biyu rashin hak'uri, fahimta, juriya da kawar da kai, 

na uku sakacin mu, shiyasa matan waje da matan banza ke kwace mata mazajen mu a waje, 

kiga miji idan yana k'aunar mutuwarsa yana k'aunar ya dawo gidansa, yafi san zaman waje da wata akan zama dake matarsa, 

so muma mu zage dantse mu zama irin su fitsararru a gidan auren mu, 

dan mu kwaci 'yancin mu, mu rink'a sakin towel intentionally, sannan mu rink'a wawan zama, mu rink'a sakin layi, muna daty talk (batsa) da mazajen mu, 

mu rink'a bank'ara k'irji muna juya k'ugu had'i da lasar leb'e muna d'an cije shi, 

a fagen kwanciyar aure ma mu zage mu bada gudummawa sosai, 

ba wai mu kwanta kamar ruwa ba sai yadda yayi damu,

ki rink'a k'ok'arin neman mijinki da kanki, 

sannan ki kasance mai tsafta da kwalliya da k'amshi a kowanne lokaci. 



"Kuma idan kunyi fad'a kirink'a using maganin k'arfin maza dan shawo kansa, 

batare da saninsa ba zaki zuba masa a abin shan sa, 

ke kuma idan yazo karki wani b'ata lokaci ko ki ja aji ki bada kai kawai buri yahau da mazan yanzu sai da cuwa-cuwa, kissa, bairiki, da karuwanci, 

shiyasa nake yi miki hannunka mai sanda ina ce miki, 

ki shawo kan mijinki dan kifi kowa sanin halinsa da kuma abinda yafi so, 

to ai abinda nake nufi kenan. 



Shiru Zarah tayi tana d'aukar darasi, kuma sosai darasin ke shigar ta tana fahimta sosai, 

Murmushin mugunta Zarah tayi had'i da cewa " sorry NASEER yanzu aka fara wasan, 

dan sai na zama fiye da tunanin Doctor Jennifer, sai na zama cikekkiya kuma tantiriyar karuwa cikin kissa a gare ka, 

gani nan gare ka Naseer.................. 




Don't forget to vote and comments 




MOMYN ZARAH