GADAR ZARE…

69

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*







69






Ya fisgota a haukace yace " Zainab d'in banza Zainab d'in wofi,, 

ita harta isa na sawa 'yata ta ciki na sunanta? 

ashe ma ni ba d'an halak bane, 

shiru kawai Zarah tayi had'i da zuba masa ido batare da tace komai ba, har ya gama bambaminsa ya fita,, 

bayansa tabi da kallo har ya bar d'akin, 

ajiyar zuciya ta sauke had'i da girgiza kanta,

kwanciya tayi akan bed tana tunanin irin muguwar k'iyayyar da Naseer ke yiwa Zainab da Mannir wanda ita kuma bazata tab'a yarda ta d'auki hakan ba,, 

saboda duk lalacewa dai sune gatanta har yanzu kuma har gobe, 

Zainab itace wacce ta shayar da ita da ruwan nononta, 

kuma ita ce tayi mata duk wata wahala da d'awainiyar da uwa keyiwa 'yarta har ta girma,, 

haihuwarta ne kawai Zainab batayi ba, amma duk wani abu da uwa takewa d'an data durk'usa ta haifa da kanta Zainab tayi mata fiye da haka ma. 



Haka ma Mannir shine ubanta dan shi yayi mata komai da uba kewa d'ansa a rayuwa, 

sun nuna mata so fiye ma da 'yar da suka haifa da cikinsu,, 

sun bata gata, da kulawa, sun bata ilimi boko da addini,, 

dan haka bazata tab'a yarda da raini ko wulak'anci balle kuma k'ask'ancin da Naseer yake yi musu ba, 

sai dai duk abinda zai faru ya faru dan har gobe suna a mazaunin iyayenta dan bata da iyayen da suka fisu,, 

sune gatanta kuma sune rayuwarta, 

a haka har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. 



Bata farka ba sai wajen 8:00pm koda ta tashi ta fita, 

iskewa tayi su Warda sun gama komai, 

har yaran sunci abinci anyi musu wanka sun kwanta, 

ganin ba Naseer ba dalilinsa yasa Zarah ganewa fishi yake da ita, 

k'udura tayi matuk'ar akan sunan data zab'awa 'yarta ne yake wannan fishin sai dai yayi tayi amma ba zata bashi hak'uri kota janye k'udirinta na sawa 'yarta sunan Zainab ba,, 

dan haka ta mik'e tayi shigawarta bedroom ta fad'a wanka, 

wasa-wasa har wajen kwana 4 Zarah bata sanya Naseer a idanta ba,, 

tun da akayi abun, dan haka taji ta shiga damuwa sosai, taji kuma tana buk'atar san ganin mijinta,, 

dan haka ta fesa wanka ta shirya ta nufi part d'insa, a parlor ta iske shi kwance akan 3 sitter, 

da sallama ta shiga, bai d'ago ya kalle ta ba ya amsa sallamar dakyar kamar wanda akayiwa dole,, 

murmushi Zarah tayi had'i da zama a kusa dashi, tsaki yayi mtswwwwwww had'i da kawar da kansa gefe,, 

sanin halin kayanta yasa Zarah yin shiru dan tasan Naseer akwai bak'ar zuciya, 

harga Allah bata ji dad'in yadda yayi mata ba, 

amma ta daure ta kalle shi fuskarta d'auke da murmushi tace " sweetheart kaci abinci? 



Banza yayi mata baiko kalli inda take ba, 

yaci gaba da harkar gabansa, 

murmushi ta kuma yi had'i da cusa hanunta a cikin gashin kansa tace " ni ce ko?

" ni na b'ata ran haka? 



Duk akan sunan Babyn ne kake fushi haka dan na saka mata sunan kakarta Zainab,, 

a tsawace yace " stop Malama, kije ki saka mata duk sunan da kike ganin ya dace da ita, 

imma sunan uwar Zainab zaki saka kina iya saka mata,, 

cike da mamaki Zarah ta mik'e tsaye tana kallan shi, 

take hawaye suka fara zarya a a fuskarta, 

cikin muryar kuka tace " Naseer Kakata fa kenan! 

a fusace yace " sai me kakar taki,, 

cikin kuka tace " Naseer wacce fa ta haifi mahaifiya ta Naseer kake zagi, 

Naseer ban tab'a danasanin aurenka ba sai yau, 

Naseer tun har ka iya bud'e baki ka zagi mahaifiyar mahaifiyata to wallahi koda mahaifiya ta na raye zaka iya zaginta,, 

tunda nake dakai ban tab'a yiwa koda 'yan aikin gidan ku kallan banza ba balle d'aya daga cikin ahalinka,, 

dan nace kasa sunan wacce ta rik'eni ta shayar dani, 

take tamkar uwa a waje na, shine ka had'a su gaba d'aya ka zaga Naseer, 

amma dayake Mannir shi d'an uwanka ne kuma jininka ai sunan d'anka na farko ka saka masa,, 

ita Zainab dayake bare ce ai kayi haka, kuma shima dai yayi duk irin abinda Zainab tayi dan tare ma sukayi, 

koma ince ya fita tunda shi har karya ni yayi, amma saboda kara ta cikakkun fulanin asali babu wanda a cikin ahalina ya kalle shi balle yayi masa magana.



Amma kai.... tsawa Naseer ya daka mata wacce ta sanya ta yin shiru dole,, 

cikin fad'a yace " daga Mannir har Zainab ni duk d'aya suke a waje na kuma ina hukunta sune a bisa laifin da sukayi miki,, 

ba wai dan kai na bane, 

"to tunda badan kanka bane, danni kake yin komai ka daina, 

danni har yanzu bani da kamar su, 

bani da wasu iyayen da suka kai min su balle su fisu,,

a fusace yace " kin kyauta, amma ba laifinki bane laifin zuciya ta ne datake miki uncontrollable love, 

tsananin san danake miki ne yasani tsanar su nake kuma ganin laifin su akan abinda suka yi maki,, 

itama cikin fad'a tace " san me, wannan irin naka san na zagin iyaye na da kakanina? 



"Ni ban zagi iyayenki ko kakaninki ba, 

idan kuma kince na zage su gaya min sanda na zage su, 

hawayenta ta share tace " ok naji kana yi mun mugun so, to idan har san da kake min gaskiya ne, 

kuma kana so na gaske ka sawa yarinyar nan Zainab, 

Naseer duk duniya bani da kamar Mannir da Zainab,, 

da sauri ya kalle yace " duk duniya fa kike ce kina nufin harni yayi maganar yana nuna kansa,, 

bata bashi amsa ba, taci gaba da da maganar ta, 

"sun rik'e ni tamakar 'yarsu ta cikin su, basu tab'a nuna min bambamcin komai tsakanina da 'yar da suka haifa da kansu, 

Zainab ta shayar dani da nononta ta raineni, tayi min duk abinda uwa keyiwa d'iyarta, 

haka ma Mannir ya so ni, ya kula da ni yayi min gatan da kowanne uba yake yiwa 'yarsa, 

dame kake san nasaka musu? 

bayan kai sanin kanka ne bani da abun saka musun, duk abinda ya faru akan idan magabatan mu ya faru amma babu wanda ya iya cewa komai,, 

wannan kad'ai ya isa ya tabbatar maka da suna da martabar rik'o na da sukayi a idan kowa, 

a fusace Naseer yace " tambayar ki nayi kuma har yanzu baki bani amsar tambayar da nayi miki ba, 

nace miki har ni sun fi a wajenki? 



Ya fad'a yana kallanta ido cikin ido, idan nasa sunyi masifar yin ja, kamar gauta, 

ganin yanayinsa da kuma sanin halinsa yasa Zarah cewa " ni dai nace idan har san da kake ikirarin kana yi min gaskiya ne, ka sakawa 'yarka suna Zainab, 

tana kaiwa nan tayi saurin barin d'akin, dan tasan idan ta tsaya komai yana iya faruwa a yadda taga ransa yayi masifar b'aci, 

bango Naseer ya nausa cikin matsanancin zafin zuciya.



Zarah tana shiga bedroom d'inta ta fad'a kan bed, 

had'i da sakin nannauyar ajiyar zuciya, 

dan yadda taga idanun Naseer sunyi masifar tsorata ta. 



Haka suka ci gaba da zama babu mai yiwa wani magana a tsakanin su, 

duk da Zarah taso tayi masa magana, 

ganin ba fuska ne yasa ta yin shiru ta kame kanta, 

dan ta luta rigima yake nema da ita, 

ranar da yarinya ta shiga kwana shiga da haihuwa Naseer ya shigo d'akin,, 

d'aure da towel ya iske ta agaban mirror tana shafa lotion a soft skin d'inta,, 

ko kallanta bayyi ba ya wuce gadon babyn a hankali yasa hannu ya d'auki Babyn had'i da k'ura mata ido,, 

yana hango tsantsar kamar Babyn da Zarah, 

ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi har sai da Zarah ta juyo ta kafe shi da lulu eye's d'inta, 

sanin tana kallansa ne yasa shi cewa "kallan na meye, 

yayi maganar batare daya d'ago ya kalle ta, 

murmushin yak'e tayi had'i da d'auke idanta daga kansa,,, 

jin ya fara yiwa yarinyar hud'uba yasata sake juyowa ta kafe shi da ido,, 

har ya gama bai kuma ce mata komai ba, 

a hankali ya mik'e ya mayar da Babyn kan Baby bed,, 

batare daya kalle ta ba yace " wannan kallan fa? 



Da sauri ta kawar da kanta gefe had'i da cewa " meye sunanta, 

cikin rawar murya tayi maganar, 

ko kallan inda take bayyi ba yayi ficewarsa,, 

yana fita parlor yaran gaba d'aya sukayo kansa suna cewa our sweet Dad, 

murmushi yayi had'i da cewa " my sweet kids, 

hannunsa Na'eem ya kama ya zaunar dashi akan sofa had'i da cewa Dady ina Mommy ta siyo mana Baby? 



Dariya Naseer yayi yace " a kasuwa mana, 

da sauri Noor tace " Dady nima ina so ka siyo man, 

kanta ya shafa yace " to zan siyo miki,, 

yayi maganar yana kallanta fuskarsa d'auke da simple smile, 

suna hira da yaran Zarah ta fito bayan ta gama shiryawa cikin doguwar rigar material mai shegen kyau da tsada,, 

simple make up kawai tayi, akan sofar dake gefe ta zauna tana kallansu cike da sha'awa tana murmushi,, 

Na'eem ya dawo kusa da ita yana cewa " Momy Dady yace zai siyo mana Baby muma a inda ya siyo miki kema ya fad'a yana nuna Babyn dake kan cinyar Zarah, 

dariya tayi batare datace komai ba, 

suna haka Doctor Jennifer ta shigo parlor'n bakinta d'auke da sallama,  

a parlor ta iske Zarah da yaran suna tayi mata surutu, tana binsu da eh ko a'a kawai dan gaba d'aya hankalinta yana kan Naseer dake zaune a gefe tunda ta shigo parlor'n bai ko kalli inda take ba,, 

 balle ta iya tantance yanayinsa. 



Jin sallamar Doctor Jennifer yasata d'ago da kanta tana kallan bakin k'ofar,, 

k'arasa shigowa parlor'n tayi fuskarta d'auke da fara'a tace " happy family, 

cikin d'oki Zarah ta mik'e ta tare ta tana dariya, a sofa Doctor Jennifer ta zauna tana kallan Zarah, itama tana dariya, 

hannu ta mik'a ta karb'i Babyn daga hannun Zarah tana cewa " sannu Zarah ya k'arfin jikin? 



Murmushi Zarah tayi had'i da zama a kusa da ita tace " lafiya lau, Alhamdulalillah,, 

fuska a sake Naseer ya kalli Doctor Jennifer yace " sannu da zuwa, ina wuni? 

dan shi Naseer mutum ne mai bak'ar zuciya mara san raini da wulak'anci kwata-kwata, 

amma bashi da rik'o, kuma duk tsiya Doctor Jennifer ta rik'e masa mata har da 'ya'yansa har guda biyu, 

ita ce cin su da shan su, da kuma karatunsu, da sauran buk'atun rayuwa, 

ita tayi musu komai, aiko ta wuce wulak'amci duk girman laifin data yi masa taci wannan darajar da albarkacin yaransa,, 

sai lokacin ta kula dashi, fuska a sake tace " Oga Naseer ana gida kenan? 



Murmushi yayi yace " wallahi, 

tace " kullum kai kana cikin iyalinka, kana basu farin ciki da kulawa, Allah dai ya had'e maka kan zuri'arka, 

sosai Naseer yaji dad'in addu'ar data yo masa, dan haka yace " Amin da sauri, sosai suka shiga hira da Naseer, 

kafin ta kalli Zarah da ko sau d'aya bata saka musu baki ba sai dai tayi gutun murmushi kawai idan anyi abin dariya,, 

tace " Zarah ya sunan Babyn ne?


Ido Zarah ta k'urawa Naseer na tsawon lokaci, 

shima ita ya kalla, aiko karaf suka had'a ido,, 

 fuska ya b'ata had'i da kawar da kansa

ganin haka yasa Doctor Jennifer kallan Naseer tace " Oga ya sunan Babyn tamu ne? 



Murmushi yayi had'i da cewa ZAINAB!!! amma za'a rink'a kiranta da NAILAH,, 

ya k'arasa maganar yana kallan Zarah, 

aiko a zabure Zarah ta d'ago idanuwanta ta zuba su cikin nashi, 

take kwallah ta taru a idanuwanta, tana kok'arin zubowa, 

kai ya girgiza mata alamar a'a, 

duk abinda suke yi idan Doctor Jennifer nakai, 

Naseer ne ya kula da haka dan haka ya mik'e yayi part d'insa, 

babu yadda Doctor Jennifer batayi dan taji abinda ke faruwa tsakanin su ba amma Zarah tak'i sanar da ita, 

sai cewa tayi kawai ya tuno mata da Momynta Zainab ne, 

sama-sama sukayi hira da Doctor Jennifer, dan ba sosai Zarah ke bata amsa ba, 

dan hankalita gaba d'aya baya jikinta,, 

ganin da da Doctor Jennifer tayi ne yasata mik'ewa had'i dayi mata sallama. 

bedroom Zarah ta shiga ta fad'a kan bed ta fasa kuka mai cin rai,, 

tana tunanin abinda tayiwa Naseer akan Zainab bata kyauta ba, 

shi saboda ita ya hak'ura da zafin zuciyarsa, ya kuma danne k'in dayake yiwa Zainab yasa sunanta saboda farin cikinta,, 

meyasa itama bata bi zab'insa dan farin cikinsa? 

meyasa bata fara tambayar shi zab'in ransa akan sunan da yake san sawa yarinyar sa ba? 

meyasa tayi haka? 



Ta k'ara fashewa da kuka, sai da tayi kukan harta gaji sannan ta mik'e ta nufi bedroom d'insa idanuwanta duk sun kumbura sunyi ja, 

a parlor ta iske shi, ya kwanta akan sofa had'i da lumshe idanuwansa yana sauraran karantun Qurani,, 

a hankali ta zube a gabansa bisa gwiwoyinsa had'i da fashewa da kuka, 

da sauri ya bud'e idanuwansa yace " Zarah lafiya meke damunki? 

baki da lafiya ne? 



Yayi maganar a lokaci d'aya, cikin kid'ima, 

ta kasa yin magana sai kukan datake yi, a hankali ya d'ogota ganin idanuwanta sunyi masifar yin ja sun kumbura ne ya k'ara d'aga mai hankali,, 

a rud'e ya shiga tambayarta abinda ke damunta, 

a hankali cikin muryar kuka tace " Iam really sorry, am so sorry, 

"da kikayi min me? kike bani hak'uri, 

cikin kuka tace " ni dai dan girman Allah kayi hak'uri ka yafe min, 

idan baka san sunan ka canja dan Allah, 

rungume yayi a k'irjinsa yana sauke ajiyar zuciya had'i da bubbuga mata bayanta yana rarrashinta, kawai batare dayace komai ba, 

a hankali ta d'ago kai cikin kuka tace " ka tamabaye ni har kai sun fi ka,, 

wallahi duk duniya bani da kamar ka, 

kai ne uwata, kai ne ubana, ka so ni a lokacin da kowa ya k'ini, 

baka tab'a juya min baya ba, kai haske ne a rayuwata, kaine, rayuwata, duniyata, farin ciki da walwala ta kai ne komai nawa, 

ina sanka fiye da komai da kowa, 

you are my everything, I love you more most, 

ban iya had'a ka da kowa a rayuwata, 

ban iya had'a sanka da komai a duniya, 

ta k'arashe maganar cikin kuka, 

a hankali Naseer ya maida ita jikinsa yana murmushin jin dad'i, 

cike da matsanancin farin ciki ya shiga rarrashinta, 

dan shi dama a maganar babu abinda yafi b'ata masa rai sai cewa datayi bata da kamar Mannir da Zainab a duniya,

tun daga nan Zarah da Naseer suka shirya suka d'inke suka koma fiye da baya,, 

suka shiga nunawa junan su tsantsar so da kulawa, 

babu mai b'ata ran wani, kowa burinsa ya farantawa d'an uwansa. 




BAYAN SHEKARA D'AYA




Sosai Nailah tayi girma, dan har ta fara tafiya da magana irin ta yara,, 

yayinda sosai Dady ya matsawa Naseer akan ya dawo Nigeria, 

sosai Dady da Momy suka yi masifar matsa masa lamba akan lalle sai ya dawo Nigeria, 

a rana Dady da Momy sai su kira shi yakai sau 10 suna nanata mishi maganar lalle ya dawo Nigeria, 

yauwa suna zaune wayar Naseer tayi ringing, a hankali ya kalli wayar sannan ya kalli Zarah, 

murmushi tayi dan tasa kowaye, itama a ranta tana masifar san komawa Nigeria musamman ma yanzu data tara iyali, 

kuma tana san ganin Ikram, Momy, Dadynta, da kuma Abbanta, 

da sallama a bakinsa ya d'aga wayar, 

jin muryar Momy na kuka yasa Naseer saurin mik'ewa had'i da cewa " Momy lafiya dai? 



Cikin kuka tace " Naseer Dadynka bashi da lafiya sosai, 

sai a nkwantar dashi an tayar, ko hannunsa baya iya motsawa, 

Naseer ko wanda ke kansa Alhaji baya iya ganewa ta k'ara fashewa da kuka, 

ai take hankalin Naseer yayi mugun tashi, gaba d'aya jikinsa ya d'auki muguwar tsuma da kerrrma,, 

ganin haka yasa Zarah mik'ewa itama tana kallansa dan tasan ba lafiya, 

gabanta ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku addu'arta d'aya Allah yasa ba wani mummunan abun ne ya faru ba,, 

cikin tashin hankali Naseer yace" Momy bashi wayar, k'ara fashewa da kuka tayi tace " tayaya zai iya amsar wayar bayan bai ma san inda kansa yake ba,

balle yasan wanda ke kansa, cikin kuka ta kuma cewa " dama last week da muna magana yace wata k'ila rabon ganawar mu da Naseer ne ya k'are,,

bamu da rabon sake ganin juna ido da ido, 

idan na mutu yanzu ai dolensa yazo, Momy ta k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka. 



Cikin tashin hankali Naseer ya kashe wayar dan bazai iya jure sauraren kukan Momyn rsa, 

a firgice Zarah ta kalle shi tace " lafiya kuwa? 



Idansa wanda ya gama yin ja ya kalle ta dasu had'i da cewa " Dady ne ba lafiya sosai, yayi maganar muryarsa na cracking,, 

da hanzari yace "had'a mana kayan mu, yayi maganar yana saka kayansa, 

yana gamawa ya d'auki wayarsa da key d'in mota yayi waje. 



Momy na kashe wayar ta kalli Dady dake zaune gefe yana shan fruits,, 

tace " nasan acikin satin nan zakaga shi, dariya Dady yayi had'i da cewa MATA!!! kenan akwai basira,, 

kinga ni ai nayi na gaji amma ke kina gwadawa gashi anyi nasara, 

murmushi kawai Momy tayiwa Dady batare data k'ara cewa komai ba. 



Kasancewar a kwai kud'i a ranar Naseer ya gama musu komai na tafiya,, 

ba shi ya dawo gida ba sai wajen 1:30am, 

a parlor ya iske ta tana ta safa da marwa tana tunnin ko yana lafiya, dan bai tab'a kaiwa wannan lokacin a waje ba, gashi dama a birkice ya fita,, 

ko had'a kayan ma su Warda da Rosling tasa suka shirya musu gaba d'aya kayan su dana yaran, 

kayan Naseer kawai ta iya shiryawa da kanta, a waya ta kira Doctor Jennifer ta sanar da ita halin da ake ciki, 

tana ganin shi ta k'arasa da sauri tana sauke ajiyar zuciya, 

sannu da zuwa tayi masa had'i da kai shi bedroom yayi wanka ya shirya, sannan ta kai mishi abinci yad'an ci kad'an, 

kallanta yayi cikin sanyin murya yace " gobe around 11:00am jirgin mu zai tashi, 

kai kawai ta d'aga masa,, 

sai can kuma tace " ya zamuyi da su Warda? 



Shiru yayi yana d'an nazari kafin yace " dole sallamar su zamuyi dan bamu san lokacin da zamu dawo ba, 

tace " nima dai haka nake ganin yafi sauk'i. 



Washe gari tun asuba Zarah ta tashi ta fara shiri, tana k'ara kintsa komai,, 

k'ara kiran Doctor Jennifer tayi ta sanar mata time d'in dazasu tashi, 

itama da wuri ta shirya ta zo gidan, 

tare suka gama shirya kayan, 

around 10:00am Naseer ya fito bayan ya gama shirinsa sannan yasa su Warda suka kai musu gaba d'aya kayan su mota,, 

bayan sun gama shirya kayan a mota ne, Naseer ya basu kud'i masu yawan gaske sannan ya sallame su, 

sukayi godiya sosai had'i da bak'in cikin rabuwa da iyayen gida adalai na gari, 

key d'in gidan Naseer ya bawa Doctor Jennifer yace" mata please kiyiwa mai gidan bayani sannan kice masa na saki gidan, 

dan Allah kad'ai yasan ranar dawowarmu, 

amsar key d'in tayi had'i da cewa "okey, 

a Airport sosai Doctor Jennifer da Zarah suka sha kukan rabuwa, kamar ransu zai fita haka suka rink'a risgar kuka, 

gwanin ban tausayi, har suka shiga jirga, jirgin ya d'aga Doctor Jennifer na nan tsaye tana sharar kwalla, 

haka Zarah acikin jirgin taita kuka, 

sai da yaran suka dameta da tambayar abinda ke damunta sannan tayi shiru. 



_Dama hausawa sunce sabo turken wawa_




*NIGERIA 🇳🇬 (K'ASAR MU TA GADO)*



K'arfe 5:40 jirgin su yayi landing a Aminu Kano International Airport, 

Zarah na fitowa daga cikin jirgin ta shak'i daddad'an iskar k'asarta abin alfaharinta, 

ta lumshe ido had'i da sauke ajiyar zuciya mai k'arfi wacce har sai da Naseer ya kalle ta,, 

murmushi tayi masa, shima ya mayar mata da martanin murmushin batare da kowa yace komai ba, 

sai yaran dake ta faman surutu, Naseer ya rik'e hannun Noor da Nouwaf, Zarah na rik'e da Na'eem da Nailah, 

suna fita harabar Airport d'in Naseer ya hango driver'n su, 

da sauri ya nufe shi. 



Cak Zarah ta tsaya had'i da rik'o hannunsa cikin nata tana kallansa, 

shima tsayawar yayi had'i da kallanta, 

cikin rawar murya tace " Sweetheart ya zamuyi dasu Noor da Nouwaf? kasan fa ba'a san dasu ba, 

tun da har yanzu babu wanda yasan ni ainahin Zarah........... 




Don't forget to vote and comments





MOMYN ZARAH