70
'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: ***
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*
70
Shiru Naseer yayi na d'an wani lokaci,
kafin yace " cikin biyu dole ayi d'aya ya k'arasa maganar yana kallan ta,
itama shi take kallo idanta cike da alamar tambaya,
tace " uhnnnn ina jinka,
ajiyar zuciya Naseer ya sauke sannan yace " ko dai mu sanar dasu Momy gaskiyar al'amari ko kuma mukai su Nouwaf da Noor gidan Asheer abokina,
kallansa Zarah taci gaba dayi batare datace komai ba,
"ya kuma kika yi shiru? cewar Naseer yana kallan ta,
ajiyar zuciya itama ta sauke had'i da kallan yaran tace " hmmmm kana ganin kai su gidan Asheer d'in shine mafita?
Murmushi Naseer yayi wanda ya k'ara fito da tsantsar kyan fuskarsa gami da yarintarsa,
sannan ya kalle ta yace " ni fa zab'i na baki dan ma karna yanke hukunci kai tsaye kiga kamar banyi maki adalci ba,
"to amma dai kasan halin Na'eem da shegen surutun tsiya kana ganin bazai fad'a ba?
shiru Naseer yayi yana ci gaba da kallanta,
dan ya gano manufarta, san rabuwa da yaranta ne batayi shine take ta wannan 'yan kame-kamen,
cigaba da magana Zarah tayi " kuma kasan a yadda suka saba a tsakaninsu ma babu yadda za'ayi a raba su kasan bazasu tab'a jin dad'i ba matuk'ar basa tare da junan su,
shi dai Naseer ido kawai ya zuba mata yana kallan yadda take ta faman rirrik'e su kamar wani zai kwace mata yaran.
Kwata-kwata Zarah bata kula da yadda Naseer ya zuba mata ido ba,
ta cigaba da magana " kuma ma ni banga wani amfanin b'oyewa ahalin mu gaskiyar al'amari ba,
tun da dai mai afkuwa ta rigada ta afku,
kawai mu sanar dasu gaskiya dan ina ganin hakan ne kad'ai mafita,
dan........ d'ago kanta datayi taga yadda Naseer ya zuba mata idonunsa ne ya hana ta k'arasa fad'ar abinda tayi niyya,,
hannuwanta ta hard'e a k'irjinta, ta zuba masa idanuwanta itama had'i da d'aga masa gira d'aya,
murmushi yayi had'i da cewa " oh ikon Allah wai su Zarah har an san dad'in 'ya'ya,
Oh ni Naseer yau naga ikon Allah, ya fad'a yana dariya,
cikin shagwab'a ta tab'e baki had'i da fara diddira k'afarta a k'asa,
dariya Naseer yake sosai yama kasa magana, sai Na'eem ne yace " sorry sweet Mom, Dady ne ko?
Cikin dariya Naseer ya shafa kansa had'i da cewa " no son, bani bane ku ne,
ya fad'a yana nuna sauran yaran,
Noor tace " Dad me muka yi mata?
" Sanku ne yayi mata yawa harta manta da kanta tana 'yan kame-kame,
sosai Zarah ta fara kukan shagwab'a had'i da cewa " Allah ba haka bane, kawai bana san a raba min kan yara na ne,
kuma gashi sun riga sun saba da junansu, idan aka raba su bazasu ji dad'i ba,
tayi maganar cike da shagwab'a da yarinta,
dariyarsa Naseer ya kanne ganin da gaske kukan takeyi yace " ayya na fahimce ki, I'm so sorry nine ko?
ya fad'a yana goge mata hawayen fuskarta, had'i da rungume ta a k'irjinsa,
" to yanzu dai meye mafita? tunda naga baki san rabuwa da yaranki abar maganar kai su gidan Asheer,
a sake samo mafita,
da sauri Zarah ta d'aga kanta daga k'irjinsa tace " yawwa, kasan meya kamata ayi?
"A'a Naseer yace yana kallanta,
" kawai muce yaran sister nace, shine da zamu taho suka mak'ale suka ce sai sun biyo mu,
saboda akwai shak'uwa da sabo sosai a tsakanin su da Na'eem,
kuma ko can Holland yawanci sunfi zama a gidan mu wajen Na'eem ko school d'insu d'aya kuma tare suke zuwa,
ta k'arasa maganar tana kallan kwayar idansa,
ajiyar zuciya Naseer ya sauke had'i da cewa " wow that is amazing, gaskiya wannan shawarar taki tayi,
kanki yana ja sosai, ya fad'a yana yi mata murmushi,
Zarah ta bud'e baki zatayi magana, Noor tace " I'm very tired Mom, my legs are shaking and I need to rest,
Nouwaf ma yace " I'm very hungry Dad,
da sauri Naseer da Zarah suka saki juna had'i da kama hannun yaran suka k'asara inda motar take suka shiga.
Zainab da tun ranar da Mannir ya dawo ya sanar da ita Naseer da Na'eem sun tafi batare daya samu damar d'auko mata Na'eem ba,
ta shiga cikin matsanancin hali da muguwar damuwar da suka haifar mata da ciwo
wanda kusan kullum a kwance take yau da lafiya gobe ba lafiya,
kwata-kwata bata iya cin wani abincin kirki, ta daina kwalliya, wanka kawai take yi, ko mai bata shafawa balle hoda,
dan wani lokacin ma dakyar Mannir ke matsa mata tayi wanka ta canja,
sosai tayi muguwar rama ta k'ek'ashe kallo d'aya zakayi mata ta baka mugun tausayi duk tsananin k'iyayyar da kake mata,
ga gidan ita kad'ai dan har lokacin Ikram tana gidan su Momy da Dady,
idan Mannir ya tafi aiki sai gidan ya zame mata so lonely,
duk kewar yaran ta ya dame ta, taji kamar tayi hauka,
danasani da danama ko tayi su sunfi dubu, dan ba k'aramin hauka da kuka tayi ba, har dai daga k'arshe ta dangana,
tun da Mannir ya sanar da ita Naseer zaizo da matarsa daya aura acan gabanta keta muguwar fad'uwa,
haka nan taji wani mugun tsoro da fargaba sun shigeta a lokaci d'aya.
Sosai taji hankalinta yayi mugun tashi, hankalinta yak'i kwanciya,
ranar da su Zarah zasu iso kuwa ji tai gaba d'aya jikinta ya d'auki rawa da kerrrma gami da muguwar tsuma,
haka nan taji ta shiga mugun tashin hankali, gabanta ya tsananta fad'uwa,
amma duk da haka da Mannir yace mata tazo suje gida taryar Naseer k'iyawa tayi,
saboda yadda take jin jikinta, lokaci d'aya zazzab'i da ciwon kai mai mugun zafi ya shigeta,
ta shiga rawar sanyi tana kerrrma a cikin bargo wanda ita kanta ta rasa taka mai-mai dalilin faruwar hakan,
wannan dalilin ne ya hana Mannir zuwa tarbar su Naseer ya tsaya jinyar matarsa.
Motar su Zarah nayin parking a harabar gidan gabanta yayi muguwar fad'uwa,
take ta shiga zubar da kwalla had'i da sauke ajiyar zuciya da k'arfi,
hannunta Naseer ya rik'e gam cikin nashi had'i da zuba mata idan shi cikin nata,
cikin sanyin murya ya kira sunanta " Zarah,
a hankali ta d'ago kanta ta kalle batare datace komai ba,
yayinda hawaye keci gaba da zuba daga idanta,
hannu Naseer yasa yana goge mata hawayen yace " Zarah you have to be very strong until we done our plan,
kika iya jure rashin mijinki dana d'anki na cikin ki wanda kika durk'usa kika haifa da kanki ma,
balle wasu mutane k'alilan, dan Allah ki daure ki kawar da kanki daga kan kowa,
ki jure ki bani had'in kai, kamar yadda kika jure a abaya please,
kai ta d'aga masa had'i da cewa in sha Allah I will try my best,
" yawwa my matar, ya fad'a yana goge mata hawayen ta, sai da ta saita kanta sannan suka fito suka jera rik'e da yaransu,
cike da tsokana Naseer ya kalle ta yace " yawwa ko kike fa, ai daman nasan zaki iya tunda kika iya jure rashin mijinki da kuma...... ya fad'a yana kanne mata ido d'aya had'i da d'age mata gira d'aya,
basarwa Zarah tayi itama tace " me kenan?
Dariya yayi sannan ya kalle ta yace " ai nasan kinyi mugun missing d'inta,,
"ni fa bangane abinda kake nufi ba, Zarah ta fad'a tana kallanshi ido cikin ido,
hantsar wandonsa ya kalla had'i dayi mata nuni da hannunsa yace " nan!
baki ta tab'e had'i dayin rolling lulu eye's d'inta tace " still am don't understand what you mean,
kai tsaye Naseer yace "Buret!
wani guntun murmushi Zarah tayi had'i da dafe k'irjita tace " abin amaii, ni bana so akai kasuwa,
dariya Naseer yayi sosai sannan yace " ah wallahi k'arya ne, tunda har akan bani maganin k'arfin maza saboda tsabar jaraba da kuma missing d'in buret, kina so a ci ki takai miki karo kiji ta har wuya,
aiko kin ciyu, kin had'u da jarumin jarumai,,
, zakin zakuna, ingarmar maza, gwarzon namiji tayi miki fata-fata,,
har da su zuwa hospital jinya,
cikin shagwab'a Zarah ta kai masa duka Naseer ya goce yana dariya,
dai-dai loakcin Dady da Momy suka fito.
Momy na d'ora idanta akan Zarah tayi baya zata fad'i saboda tsabar kid'ima da tsananin rud'ewa,
cikin firgici Dady ya taro ta, duk da shima kad'an ya rage ya zube k"asa wanwar, dan hankalinsa yayi mugun tashi,
daga Zarah har Naseer sun lura da yanayin dasu Dady suke ciki amma sukayi fuska kamar ba wani abu,
cikin fara'a Naseer ya nufe su Dady amma Momy tayi sauran ja da baya had'i da rik'e hannun Dady gammm cikin nata,
ganin haka yasa Naseer yin dariya had'i da cewa Momy yau kuma tsoron Naseerun ake yi?
Cikin wani irin yanayi na rashin yadda ta d'ago idanta tana kallan Naseer,
idanta cike da tuhuma, shima Dady kallan rashin yadda yake yi masa, da kwata-kwata bai yarda da shi ba,
ganin kallan da suke yi masa yasa shi yin murmushi had'i da nuna Zarah yace " Linah this is my home an my family, they're my parent,
murmushi tayi wanda ya k'ara bayyanar da ainahin kamarta ta zahiri tace " nice to meet you,
tayi maganar tana kallan Dady da Momy,
daga Dady har Momy babu wanda yace k'ala sai ido kawai da suka zuba musu suna kallan wasan kwaikwayon had'i da zunzurutun rainin hankalin da suka zo musu dashi,
cikin shagwab'a Naseer yace " Momy no missing hug, ya fad'a yana ware hannuwansa,
har lokacin babu wanda yace komai tsakanin Dady da Momy kallan Naseer da Zarah kawai suke yi,
cikin muryar kuka Nouwaf yace " Dady I'm very hungry,
da sauri Na'eem yace " me too Dad,
ita kuma Noor tace " me am so tired, ta fad'a tana dafe kanta kamar wata babba.
Sai a lokacin Dady da Momy suka lura da yaran,
fafare tass b'ul-b'ul dasu abin sha'awa,
kallan yaran Dady yayi sannan ya mayar da kallansa ga Naseer batare dayace komai ba,
Naseer ya gane kallan tambaya Dady yayi masa amma sai basar yace " oh am so sorry dears muje ciki kuyi wanka lunch sai kuyi bacci,
Nouwaf yace " no Dad is better to take our lunch first, then bath and sleep,
ok Naseer yace, had'i da rik'e hannun su yayi cikin gidan dasu,
bayansu Momy da Dady suka bi da kallo had'i da sauke nannauyar ajiyar zuciya,
direct part d'insa suka wuce dan yasan an gyara, kamar yadda ya zata hakan ne ya kasance an gyara part d'in tass an canja komai, even paint sai da aka sake,
Furniture ko sabo aka saka, even spoon sabo ne,
3 bedrooms including toilet an bathroom, an 1 parlor with kitchen an dinning area,
inda yaga an saka gadan yara da wardrobes d'in su, yakai kayan su Nouwaf & Noor da Na'eem,
bedroom d'in kusa da yaran Zarah ta kai kayanta,
shi kuma ya d'auki bedroom d'in dake can gefe,
komai na gidan neat, Zarah ta ajiye kayanta a bedroom d'inta bata ko zauna ba ta yi bedroom d'in Naseer,
iske shi tayi shima yana k'ok'arin fitowa, da sauri Zarah tasa hannu ta tura shi baya, had'i da rufe k'ofar.
Da kallan mamaki ya bita "ya naga kin shigo kuma kin rufe k'ofa, kodai jarabar ce ta motsa? yayi maganar yana sakar mata silent killer smile ,
" no ni ba wata jaraba, kawai dai ina san muyi magana ne,
" amma dai ai kinji me yaranki suka ce ko?
dan haka kibar maganar sai sun ci abinci, sun huta tukunna,
yayi maganar yana k'ok'arin barin d'akin,
da sauri ta tari gabansa had'i da cewa " amma kana ganin su Momy bazasu gane ba?
"Ya danganta da yadda kikayi reaction d'inki, yayi maganar yana barin d'akin,
direct bedroom d'in yaran ya shiga ya iske basa nan har sun koma part d'in su Dady,
da sauri shima yayi part d'in Zarah na biye dashi a baya har suka k'arasa part d'in,
iske su sukayi zaune a dinning gaba d'ayansu har da Momy da Dady,
murmushi Naseer yayi sannan ya k'arasa wajen ya zauna shima,
bayan sun gama cin abinci, Naseer da Zarah suka koma part d'in su, sukayiwa yaran wanka had'i da shiryasu, sai da sukayi bacci sannan Naseer da Zarah sukayi wanka, had'i dayin sallah,
sannan suma suka kwanta dan a gajiye suke lik'is.
Washe gari sai around 9:30am suka fito bayan sun shirya,
basu iske yaran a bedroom d'in su ba dan tuni sun tashi sun fita, har sunyi breakfast Ikram tayi musu wanka,
a parlor suka iske Momy da Dady zaune su biyu kawai suna hira,
tare suka k'arasa wajen su had'i da durk'usawa har k'asa suka gaida su,
fuska a sake Dady da Momy suka amsa kamar ba komai a ransu,
nan ko a k'agare suke ayi musu bayani dan ko bacci basuyi ba,
kwana sukayi suna alhinin abin,
Dady yace " ga breakfast d'in ku can kan dinning kuje kuci,
ba musu suka mik'e dan wata irin muguwar yunwa suke ji dan kwana akayi ana duty (kashe arna),,
bayan sun gama breakfast d'in parlor suka dawo suka zauna inda Dady da Momy ke zaune,
a hankali Naseer ya d'aga kai yana waige-waige, murmushi Momy tayi dan ta kula da yaran yake nema, tace " oh su Naseer manyaan gari har an san dad'in 'ya'ya,
ai tuni sun tashi sunyi breakfast,
tunda naga alamun yaran suna riga iyayen su tashi,
kai ya shafa yana murmushi batare dayace komai ba,
itako Zarah kanta ta sunyar k'asa saboda kunya,
Dady yace " ai su Naseer an girma an zama manya,
cikin shagwab'a Naseer ya d'ora kansa kan cinyar Momy yana cewa " Momy ai har yanzu ban girma ba ko? yaro ne still a wajenki har yanzu,
dariya Momy tayi tace " ka tab'a ganin mutum yayiwa iyayen sa girma duk tsofansa?
" ai duk tsufan mutum matuk'ar yana da iyaye jinsa yake kamar yaro k'arami musamman ma idan yana gaban iyayen nasa,
sai da sukayi wasa da dariya sosai sanann Dady ya kira sunansa "Naseer,
yanayin yadda Dady ya kira sunansa yasa Naseer sanin cewa he is serious about what he want to say,
it's an important issue, dan haka ya tashi zaune had'i da tattsara gaba d'aya nutsuwarsa ga Dady yace " na'am,
ajiyar zuciya Dady ya sauke kafin yace " Naseer ni dai a sani na, yaranka biyu ne, na farko Na'eem sai kuma Nailah,
amma yanzu na ganka da yara har hud'u wanda kallo d'aya zakayi musu asan suna da nasaba da kai,
kuma a iya sani na Zarah ta mutu dan da hannunmu muka saka ta a kabari,
amma yanzu ga Zarah a gaban mu, dan Allah Naseer ka warware mana zare da abawa,
murmushi Naseer yayi sannan yace " yaran sister Linah ne....... daga nan ya sanar dasu plan d'in da suka shirya akan yaran,
sannan yace " Dady kai ka haife ni nasan kuma shekarunka sun ninka nawa sau uku,
Dady a iya tsayin rayuwarka ka tab'a ganin wanda ya mutu ya dawo?
Murmushi Dady yayi sannan yace " a'a ban tab'a gani ko naji labarin mutum yayi mutuwar gaskiya ya dawo ba,,
amma nasha jin labari na kuma sha ganin mutum yayi mutuwar k'arya,
na wani lokacin kafin ya bayya saboda wani dalili,
da k'arfi Naseer ya sauke ajiyar zuciya da har sai da su Dady sukaji sautinta, a ransa yace lalle babba babba ne, wanda kuma ya rigaka zuwa duniya dole ya fika sanin takan rayuwa,
a fili kuma yace " to kuma Dady har asaka mutum a kabari?
" Sosai ma kuwa, long sleep injection ake yiwa mutum, cewar Dady ya k'arasa maganar yana kallan Naseer,
murmushin yak'e Naseer yayi sannan yace " to amma Dady kai kana ganin hakan zata iya faruwa da Zarah?
Dady ya bud'e baki zayyi magana yaran suka fito da gudu, daga bedroom d'in Ikram,
jikin Zarah suka fad'a suna cewa " we missed you sweet Mom, kafin
Zarah tayi magana Dady yace " they are her niece and they call her Sweet Mom,
da sauri Naseer yace " eh Dady haka suka ji Na'eem na kiranta, kuma sunfi zama a gidan mu fiye da gidan su shiyasa suke kiran mu,
sweet Mom & sweet Dad,
Noor tace " sweet Dad Aunty tayi mana wanka,
cikin rashin fahimtar wacece Aunty ya kalli Momy,
murmushi Momy tayi had'i da cewa " oh Ikram suke nufi, da sauri Zarah ta d'ago idanuwanta,
Naseer yace " tana nan ne?
"Eh tana nan tun bayan mutuwar Zarah take fushi da iyayen tak'i zuwa gidan ko sau d'aya,
ko nan suka zo iyakacinta dasu gaisuwa, ko parlor bata fitowa kullum tana bedroom,
rana d'ai-d'ai ne bata kukan rashin 'yar uwarta Zarah,
ta hanawa kanta duk wani jin dad'i ta takure kanta,
tayi maganar idanta yana kan Zarah,
shiru kawai Zarah tayi, dan ita kad'ai tasan me take ji a zuciyarta,
Naseer yace " to su iyayen nata fa?
Ajiyar zuciya Momy ta sauke cike da jimami tace " hmmm Naseer ai idan kaga Zainab yanzu sai kayi mata kuka,
ta goje, ta kod'e, ta rame, ta k'ek'ashe, tayi muguwar rama,
tun bayan mutuwar da Zarah da tafiyarka da Na'eem ta shiga mummunan tashin hankali had'i da matsananciyar damuwa,
har hawan jini ta kamu dashi, tanan yau da lafiya gobe ba lafiya,
baka ga yadda ta koma, ta takura kanta da rayuwarta had'i da k'untata duniyarta, ta hana kanta farin ciki da walwala,
tana ta azabtar da kanta, ta hanawa kanta jin dad'in duniya,
kuma tana cikin k'uncin rayuwa,
Momy tayi maganar cikin mutuwar jiki, idanta nakan Zarah,
aiko take Zarah taji hankalinta yayi mugun tashi, jikinta ya d'auki rawa da kerrma,
launin idanuwanta suka canja daga farare zuwa ja,
ta rink'a jin zafi gami da k'una a k'irjinta yayinda zuciyarta take tafasa, mak'ogwaranta na tiriri saboda jin halin da Momynta Zainab ke ciki,
Naseer ko baki ya tab'a had'i da cewa " hisabi ta fara yiwa kanta kenan?
Jin abinda yace yasa Zarah yunk'urawa zata tashi,
da sauri Naseer yasa hannunsa ya danne hannunta batare daya kalle ta ba,
dole tasa Zarah ta zauna, amma Allah kad'ai yasan zugi da azabar da zuciyar ta keyi mata.
Washe gari jikin Zainab yayi d'an sauk'i yasa Mannir cewa Zainab ta tashi suje gida kar su Dady suyi fushi dasu kan basu je taryar Naseer ba,
da farko k'in zuwa tayi sai da Mannir yace mata kodan Na'eem ai taje,
jin abinda yace yasata mik'ewa zumbur had'i da surar hijabinta tayi gaba,
murmushi Mannir yayi sannan yabi bayanta,
tunda suka nufi gidan gabanta yake muguwar fad'uwa had'i da bugawa da tsananin k'arfin gaske,
suna shiga harabar gidan gabanta ya kuma fad'uwa da k'arfi,
koda sukayi parking kasa fitowa tayi, tayi shiru a mota tana sauraren yadda k'irjinta ke bugawa da k'arfi,
har sai da Mannir yayi mata magana sannan ta fito cikin sanyin jiki, suka shiga main parlor gidan.
A parlor ta iske yaran suna wasa, da sauri ta k'arasa inda suke had'i da rungume Na'eem gamm a jikinta had'i da sakin kuka,
tana d'aga kai ta hango Naseer yana k'ok'arin barin wajen, da sauri ta mik'e had'i da nufar wajen,
tsaiwarsa Naseer ya gyara yana jiran ta k'oraso dan dakowacce tazo yana dai-dai da ita,
tana zuwa ta rungume shi had'i da sakin rikitaccen kuka mai cin rai tana cewa " Naseer I made a mistake, I'll never forgive me self, ever Naseer,
munyi rashin da har abada bavzamu tab'a mayar da kamar shi ba,
na cuci kai na, nayiwa kai na illar da har in mutu bazan manta ba,
Ikram dake bedroom jin maganar Momynta yasa ta fitowa,
yadda take kuka ya tab'a zuciyar Ikram sosai, ta fara zubar da kwalla batare data sani ba,
Naseer ji yayi zuciyar sa tayi mugun yin sanyi har yaji mugun tausayinta ya shige shi,
a hankali ya cireta daga jikinsa ya zuba mata ido, sai lokacin ya kula da yadda ta koma,
tayi mugun bak'i ta rame, kamar wacce ta shekara tana jinyar HIV & blood cancer,
gaba d'aya ta yarkwale ta lalace,
ji yayi duk wannan zafin zuciyar da k'iyayyar da yake yi mata sun gushe,
lokaci d'aya kuma tsananin tausayinta ya mamaye duk wata gab'a da jijiya had'i da gangar jikinsa,
a hankali ya shiga goge mata hawayen dake zubowa yana girgiza mata kansa alamar ta daina,
dai-dai lokacin idan Ikram ya sauka akan Zarah dake shigowa part din,
ji tayi kanta yayi dum durum dum,
cikin tsananin tashin hankali bakinta na wara tace " Z... A... R... A... H!!! had'i da sulalewa k'asa sumammiya,
da sauri Zainab ta juya had'i da sauke idanta akan ZARAH............
Please don't forget to vote, follow and comment
MOMYN ZARAH