GADAR ZARE…

73

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*







73






Dab'asss Zainab ta zauna a k'asa had'i da sanya hannunta ta toshe bakinta saboda kukan dayake cinta,, 

tama rasa meke yi mata dad'i a duniya, 

ji tayi gwamma mutuwar ta da ganin wannan mummunar ranar, 

shiko Mannir in banda Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un babu abinda yake maimaitawa, 

ya kasa yin komai yau ga matar sa da 'yarsa d'auke da cikin shege, 

Dady, Momy da Naseer, Zarah duk sunyi jugum-jugum a tsaye jikinsu yayi mugun sanyi sun rasa ma mai zasu ce, 

a hankali Zarah ta taka wajen Zainab ta d'ora hannunta bisa k'afarta tana massaging, batare data ce komai ba, 

a hankali hawayen bak'in ciki ya fara zubowa Zainab cikin k'unar zuciya da takaicin rayuwarta, 

cikin mutuwar jiki hannunta na kerrrrma 

 ta d'ora shi akan cikinta, 

wata irin razananniyar k'ara Mannir ya saki had'i da buga kansa da bango yana gwarawa, 

cikin bak'in ciki yake ihuuun kuka yana wani abu kamar zararre,

a hankali Naseer ya taka inda Mannir yake ya dafa shi had'i da girgiza masa kai, 

wani irin kuka Mannir ya kuma saki wanda yayi masifar bawa Naseer tausayi yaji gaba d'aya tausayin d'anuwansa ya kama shi, 

cikin mutuwar jiki Naseer ya d'ago Mannir ya rungume yana bubbuga masa bayansa, 

cikin kuka Mannir yace " Bro mai nayi? 



" Wanne irin laifi nayiwa Allah dayake jarrabta ta da irin wannan masifun kala-kala? 



" Wanne irin mummunan laifi na aikata a rayuwa da nake had'uwa da iftila'i? 



" Bro ka duba ciwon danake fama dashi, wanda bayan ku 'yan uwana da iyaye, 

kowa gudu na yake saboda wari da ruwan gembo, wallahi tunda nake a duniya ban tab'a jin sunan cutar PENIS CANCER (GWAIWA) ba sai a kai na, 

me nayi haka da nake fuskantar hukunci mai tsakanin gaske? 



Mannir ya k'arasa maganar cikin rikitaccan kuka, 

k'ara matseshi Naseer yayi a jikinsa, cikin rawar murya yace,, 

" please ka daina magana irin haka kamar ba musulmi ba, 

kai fa cikekken musulmi ne, makaranci mai tarin ilimin addini, 

ya kamata ka d'auki k'addara, ka kuma yarda da ita, 

ba sai mutum yayi wani laifi Allah yake jarabtaa ba, Allah yana iya zartar da abinda yaso akan wanda yaso a kuma lokacin daya so, 

idan ka tuna duk Annabawan Allah babu wanda wata mummunar jarabawa bata same shi ba, 

haka ma sahabai da sauran 'yan Adam, 

babu wani mahaluk'i da zayyi rayuwa cikin zallar farin ciki da walwala, 

batare da 'an tab'a shi an jarrabi imaninsa ba, 

kai ka godewa Allah ma da Allah yasa kai kalar taka k'addarar kenan , 

idan kaji k'addarar wani kalar jarabawar wani kai sai kayi sujjada ka godewa Allah saboda taka ba komai bace, 

kuma haka suke ci gaba da rayuwar su suna ci masu godewa mahaliccin su, 

kai ma kazama d'aya daga cikin masu godewa Allah a duk hali da yanayin rayuwar da ka tsinci kanka please, 

kar ka zama d'aya daga cikin masu yiwa Allah butulci dan ya jarrabe imanin ka,

ni dai abu d'aya na sani shine duk abinda kaga Allah yayi, 

to akwai dalilin yinsa dan Allah baya tab'a yin abu babu dalili. 



Wani irin mugun tausayinsu ne ya kama Dady da Momy, a hankali Dady yaje inda suke, 

ya dafa kafad'ar su had'i da rad'awa Naseer ka kai su gida, 

ba musu Naseer ya kama hannun Mannir yana yima Zarah alama data kamo Zainab, 

tun da suka shiga mota babu mai yiwa wani magana har suka isa gida, 

suna isa harabar tun kafin motar ta gama tsayawa Zainab ta bud'e ta fito da gudu tayi cikin gida, 

jikin Mannir a sanyaye shima ya fito yabi bayanta, 

Zarah tana k'ok'arin bin bayan su Naseer yayi saurin rik'o ta had'i da cewa "ina zaki? 



Cikin muryar kuka tace " binsu cikin gidan zanyi, 

kai ya girgiza mata had'i da cewa "no ki bar su suna b'ukatar privacy, 

batare data kuma cewa komai ba ta koma ta zauna tana share hawayen dake zubo mata, 

ganin yadda take zubar da hawaye yasa hankalin Naseer yayi masifar tashi, 

dan bak'aramin d'aga masa hankali kukan nata yake ba, 

yana jin kukan ta har cikin k'ok'on ransa da zuciyarsa, 

a hankali Naseer ya jawo ta jikinsa ya rungume, yana shafa kanta, 

abinka dama damai jiran kad'an sai ta k'ara faahewa da kukan, 

yana san ya rarrashe ta amma bai san ta ina zai soma magana ba, 

bai san mai zai ce mata ba, shi kan shi zuciyarsa a karya take, 

cikin kuka Zarah tace " mu kuma irin tamu k'adarar kenan haihuwar shegun yara, 

ni na fara haifa yanzu gashi nan Momy da Ikram ma, 

yanzu haka zamuyi ta haihuwar 'ya'yan zina? 



Wani irin mugun b'acin rai Naseer yaji, take kalar idansa ta canja ta koma red, 

gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa da kerrrna, 

cikin matsanancin b'acin rai Naseer yayi ma motar key ya fige ta a guje yayi waje, 

yadda yake tsala gudu yasa Zarah d'ago kai ta kalle, 

ganin yadda idansa da yanayinsa suka canza yasa ta fahimtar ransa ya b'aci abinka dama damai bak'ar zuciya, 

yana d'ago ido karaf suka had'a ido da ita, saurin d'auke idansa yayi daga kanta, 

cikin sanyin murya Zarah tace " please kayi hak'uri idan na b'ata maka rai, 

murmushi yayi mata batare daya ce komai ya mayar da kansa wajen tuk'i. 



Zainab na shiga gidan direct bedroom d'inta ta wuce ta fad'a kan bed, 

had'i da sakin kukan bak'in ciki, jikin Mannir a sanyaye ya shigo d'akin, 

tsayawa yayi had'i da rungume hannunsa a k'irjinsa yana hawaye, 

cikin muryar kuka Zainab tace " abinda muka shafe shekara da shekaru muna nema bamu samu ba amma sai gashi lokaci d'aya k'addara ta bamu, 

a k'alla munkai 18yrs muna rok'on Allah akan ya bamu haihuwa,, 

Allah bai nufa ba, bai bamu ba amma..... sai kuma tayi shiru dan batasan abinda zata ce ba, 

tsaye kawai yayi yana kallanta ya rasa abinda zaice. 



Sai da Ikram tayi wata guda cur a hospital sannan aka sallame ta lokacin cikin ta yakai wata biyar, 

gidan Dady ta koma, yayinda da Zarah keta aikin lallab'ata ta rarrashinta had'i da bata hak'uri, 

tana kuma k'ara nuna mata ta yarda da k'addara, 

to Alhamdulillah dan Ikram akwai tawakkali da dangana, 

ta d'auki k'addararta ta runguma hannu bibbiyu, 

tana rayuwarta kamar ba komai, 

yadda kasan bata cikin d'umbin b'akin ciki mai tarin yawa da nadamar rayuwa, 

yayinda Zainab da Mannir suke cikin k'unci da matsanancin bak'in ciki, 

kullum cikin kuka suke, 

Mannir ya shigo bedroom d'in Zainab ya iske ta kwance tana aikin kuka, 

a hankali ya tsuguma a bakin gadon, dan yanzu baya iya zama saboda ciwon dake jikinsa, 

"Zainab ya kira sunanta cikin sanyin murya, 

bata d'ago ba amma ta tsaida kukanta, 

magana yaci gaba da yi " yanzu Zainab bazaki hak'ura ki d'auki k'addara ba, bazaki sakawa zuciyar ki salama da dangana ba? 



" Ki duba Ikram 'yarki ta cikin ki yadda ta yarda da tata k'addarar amma ke da girmaki da komai sai abu kike irin na yara, 

kamar wara k'aramar yarinya, 

cikin kuka Zainab tace " wannan dalilin ne yasa ni nake kukan, 

Ikram yarinya ce k'arama bata san ciwon kanta ba har yanzu, 

amma ni tsofai-tsofai dani har da jikoki a ganni da ciki, 

cikin ma na shege, haba Mannir taya za'ayi hankalina ya kwanta na samu nutsuwa dan Allah? 



"Ni wallahi na gwamci mutuwa ta da wannan bak'ar rayuwar, 

cikin kuka ta d'aga hannu sama tace " ya Allah ya Ubangijin al'arshe, ya Ubangijin sammai da k'assai Allah na rok'e dan darajar fiyayyan halitta ka kawo sadaniyyar rabuwata da cikin nan, 

Allah idan abinda nayiwa Zarah ne Allah na tuba, Allah dan darajar fiyayyan halitta ka rabani da cikin nan kar ka bani ikon haihuwar sa ya Ubangiji ta k'arasa maganar cikin kuka, 

can k'asan mak'ogwaro Mannir yace " Amin, 

sosai Mannir ya rarrashe ta ya bata hak'uri, sannan ya lallab'a ta shiga wanka shi kuma ya koma parlor, 

bayan Zainab ta gama wankan tazo fitowa tana taka step santsin tail ya kwashe ta, 

tayi sama sannan ta fad'o akan cikin, wata irin gigitacciyar k'ara ta saki had'i da zubewa k'asa a sume, 

da guda Mannir dake parlor ya nufo bedroom d'in, a kid'ime ya sure ta yayi hospital da ita, 

da sauri Nurses suka karb'e ta suka yi Emergency da ita, 

sai da akayi wajen 2hrs sannan Doctor ya fito, 

da sauri Mannir ya tare shi yana tambayarsa abinda ke faruwa, 

d'an b'ata fuska Doctor d'in yayi kafin yace " I'm so sorry cikin dake jikinta ya zube har ma munyi mata wankin ciki, 

suman tsaye Mannir yayi saboda tsananin murna da farin ciki, 

Doctor dayaga haka tsammanin sa ko shock Mannir yayi saboda bak'in ciki, 

a hankali ya dafa kafad'arsa had'i da cewa " am so sorry, ga d'akin da aka kai ta can yayi maganar yana nuna masa wani d'aki, 

da sauri Mannir ya shiga d'akin, ido biyu ya samu Zainab, yana isa gareta ya rungume had'i da fad'in " Alhamdulillah Allah maji rok'on bawan sane, Allah ya amshi addu'ar mu, 

murmushi Zainab tayi , 

sosai sukayi farin ciki da zamubewa cikin, 

sai dare Mannir ya sanarwa Dady da Momy, Naseer Zainab na hospital kuma cikin ya zube har ma anyi mata wankin ciki, 

kowa yayi murna da zubewar cikin musamman Zarah da Ikram.



Haka dai rayuwa taita tafiya har cikin Ikram ya shiga watan haihuwa, 

duk wanda ya ganta yasan ta canja gaba d'aya kamanninta sun sauya ta zama wata iri kalar tausayi, 

kullum cikin addu'a take Allah ya raba ta da abinda ke cikinta lafiya dan wani irin yanayi take ji a jikinta, 

jikinta yana bata kamar lokacin ta yayi, kamar bazata rayu da abinda zata haifa, 

tun da cikin Ikram ya shiga watan haihuwa Zarah ta koma kwana a bedroom d'in ta, 

kuma iya k'ok'arin ta wajen kwantar mata da hankali, 

yayinda ciwo ya gama cin jikin Mannir sosai har ya kai ga ya kwantar dashi, 

gaba d'aya al'aurarsa ta gama rub'ewa, 

babu yadda bayyi da Zainab ta koma gidan su momy ko gidan su, 

amma fir tak'i tace idan mutuwa ce sai dai tazo ta d'auke su tare, 

amma matsawar yana raye bata tab'a barinsa duk irin mawuyacin halin dazai shiga, 

tana tare dashi rai da rai mutuwa ce kawai zata raba su,

saboda warin da Mannir yake yi duk ma'aikatan gidan sun gudu, 

har sabon mai gadi da su kayi ya kasa zama dan warin yana kaiwa har bakin get, 

yanzu idan babu kowa daga shi sai matarsa Zainab. 



Cikin dare Ikram ta tashi da matsananciyar nak'uda ganin ta fara zubar da jini yasa tayi muguwar tsorata, 

a kid'ime ta tada Zarah daga bacci, itama Zarah tana farkawa taga jini hankalinta yayi mugun tashi, 

da gudu ta fita daga bedroom d'in tama mantataga ita sai rigar bacci kanta ko d'an kwalli babu, 

tun daga parlor take kwalawa Naseer kira, 

duk gidan suka fito a kid'ime da gudu Dady da Naseer su kayi bedroom d'in, 

da sauri Dady ya sungumi Ikram yayi habarar gidan wajen motor park, 

Zarah na niyyar fita harabar gidan a haka Naseer yayi sauri rik'o ya danna a bedroom yace " baki da hankaline ji fa a yadda kike amma kina k'ok'arin fita a haka, 

sai loakcin ta tuna a yadda take, da sauri ta canja kayan jikinta ta zura doguwar rigar atamfa, 

ta sungumi Nailah tayi waje da gudu har tana tuntub'e zata fad'i, 

cikin zafin nama Naseer ya rik'e ta had'i cewa " control mana Mrs Naseer, 

Naseer ya ja motar, tun a mota Dady ya kira Mannir da Zainab ya sanar dasu, 

suma cikin tashin hankali suka nufo asibitin. 



Ana shiga da Ikram Emergency Doctor ya fito da hanzarinsa, 

dai-dai lokacin Mannir da Zainab suka k'araso, 

kallan su Doctor yayi yace " Babyn a bakin mahaifa yake dole sai dai ayi mata CS a ciro abinda ke cikinta, 

yayi maganar yana mik'a musu takadar dasu saka hannu, 

kasa karb'ar paper Mannir yayi sai Dady ne ya amsa yayi signing, 

da hanzari Doctor ya amsa ya koma ciki, 

sai da akayi a k'alla 4hrs akafin Doctor ya fito, 

sunan zaune a bakin theater room suna ta zarya masu addu'a nayi, 

suna ganin Doctor Naseer yayi saurin mik'ewa ya tare shi, 

ya bud'e baki zayyi magana Nurse ta fita da Baby a hannunta tana tsala kuka, 

da sauri Zarah ta mik'e ta amshi Babyn, 

murmushi Doctor yayi sannan yace " anyi aikin cikin sa'a ga Baby girl nan an samu, 

Baby fara sol mai kama da Ikram sak kamar an tsaga kara, 

sai kuka take tana wawure-wawuren nono, tana kai hannu bakin ta, 

murmushi Zarah tayi tana kallon Babyn hawaye na zubo mata, 

Nurse d'ince tace " muje na kai ku d'akin da aka kai mamanta, 

daga bakin tagar d'akin ta nuna musu ita kuma ta koma, 

jiki a sanyaye suka shiga suka iske Ikram tana bacci, 

Momy ta mik'a hannu ta amshi Baby, ajiyar zuciya ta sauke had'i da cewa " ikon Allah, 

a hankali ta mik'ewa Dady Babyn addu'a Dady yayi mata sannan ya mik'e ma Zainab, 

kamar bazata amsa ba, zai kuma ta karb'a, ido ta k'ura mata tana ganin tsananin kamar yarinyar da Ikram sosai, 

da yadda kasan lokacin da Ikram tana jaririya, take taji hawaye ya taru a idanta , 

da sauri ta mik'ewa Mannir dake tsaye, 

hannunsa na rawa ya amsa shima yayi mata addu'a. 



A hankali Ikram ta bud'e idanta ta fara bin jama'ar dake d'akin da kallo,

hannu ta mik'ewa Zarah da sauri Zarah ta k'arasa bakin gadon, had'i da mik'a mata Babyn, 

murmushin k'arfin hali Ikram tayi sannan ta amshi Babyn, 

ta k'ura mata ido na wani lokaci kafin tace " Allah ya isan mu tsakanin mu da mahaifinki daya samar dake ta wannan hanyar, 

Allah yayi mana sakayya ni dake daya kasance d'an fashi, 

Allah ya shiryar dake a bisa turba ta gaskiya, Allah ya baki ikon gane gaskiya, 

gaskiya ce ya kuma baki ikon binta, 

Allah ya baki ikon gane k'arya, 

k'arya ce ya kuma baki ikon kauce mata, 

Allah yasa kina cikin salihan bayi wad'anda Annabi zayyi alfahari dasu ranar alk'iya, 

Allah yayi miki albarka ya sanya haske a rayuwarki ya tsareki daga dukkan abin k'i, 

a hankali ta mik'ewa Zarah Babyn had'i da cewa gata ki kula min da ita, 

bazan ce na baki ita amana ba, dan nasan zaki kula da ita kamar yadda zaki kula da rayuwar yaranki, 

dan girman Allah kar wanda ya sanar da ita asalinta da kuma hanyar da aka same ta, 

ku dai sanar da ita Mamanta ta rasu kodan ta rink'a yi min addu'a, 

a hankali ta juya wajen Naseer tayi mishi murmushi tace " Uncle nasan zaku kular min da ita sosai, kuma nagode Allah yasaka muku da alkhairi, yabar zumunci, 

ta juya wajen Zainab da Mannir tana murmushi tace " Momy, Dady please ku yafe min idan nayi muku wani laifi koda akan rashin sani ne, 

ina matuk'ar san ku, ina san ganin ku cikin farin ciki, ta kalli Momy da Dadyn Naseer tace " grandfa please kuma ku yafe min, 

kuma dukkan ku kular da Baby na dan Allah, 

ta k'arasa maganar tana hawaye. 



Kowa ka gani a d'akin jikinsa yayi mugun yin sanyi, 

Zainab, Mannir, Zarah sai kuka suke, 

a hankali Zarah da Zainab suka fad'a jikin Ikram, Zainab tace " ya kika magana irin haka kamar wacce zata bar duniya please ki dai na bada wasiyya keda kanki zaki raini 'yar ki, 

murmushin k'arfin hali Ikram ta kuma yi, 

tace " na sani Momy mutuwa zanyi, 

a hankali Mannir ya tako gabanta yasa hannu yana shafa kanta hawaye na zuba daga idansa yace " bazaki mutu ba Ikram, 

kanta ta d'aga a hankali ta kalle shi tayi mishi murmushi tace " please ni dai Dady kona mutu kar kuyi min kuka, 

kar ku d'aga hankalin ku dan Allah. 



Ta bud'e baki zata kuma magana, ta fara tari sai jini kafin kace me idanuwanta sun kakkafe, 

da gudu Mannir da Zainab suka fita kiran Doctor, 

Dady da Momy, Naseer da Zarah suka rirrik'e ta suna kiran sunanta, 

a hankali Ikram tayi kalmar shahada, 

kafin jikinta ya saki, ido Naseer ya runtse da k'arfi had'i da ja baya a kid'ime, 

Dady yasa hannu ya rufe mata idanuwanta dake kallan sama tana murmushi, 

a gigice Zarah tace " Dady meke faruwa? 



Cikin rawar baki yace " ta rasu, 

wata irin k'ara Zarah tayi had'i da sulalewa k'asa sumammiya, 

dai-dai lokacin Mannir da Zainab suka dawo daga kiran Doctor, 

da sauri Doctor ya k'arasa yayi 'yan dube-dubensa, 

ganin ta mutu yasa shi ja mata bed shirt ya rufe ta, cikin mutuwar jiki, 

wani mahaukacin kuka Zainab ta saka tana jijjiga Ikram had'i da kiran sunanta, 

taimakon gaggawa aka bawa Zarah, 

sannan ta farfad'o cikin matsanancin kuka, 

Mannir yayi kuka sosai kamar ransa zai fita, 

yana ji yana gani aka shirya Ikram aka kaita makwancinta, 

yayinda Zarah ke rungume da Babyn tana faman kukan, 

bayan andawo daga kai Ikram Naseer yayiwa Babyn hudubaa da sunan Mamanta Hafsat ana kiranta IKRAM d'in, 

sosai Mannir ya shiga dawo hankali shi yayi mugun nadama, 

ranar sadakar bayan an gama zaman makoki, 

yace yana san magana da Abban Zarah, Naseer, Zainab, Alhaji Abdullahi, Momyn sa da Dadynsa. 



A babban parlor'n gidan dake sama aka hallara, yayinda Mannir keta aikin kukan cike da matsananciyar nadama, 

bayan duk kowa ya zauna akayi shiru ana jiran Mannir, ganin bashi da niyyar magana ne yasa Dady cewa " Mannir kayi magana ka tara mutane kuma kayi shiru kak'i cewa komai, 

a hankali Mannir ya mik'e yaje gaban Zarah ya zube, ya durk'usa ya kasa cewa komai sai kukan dayake kamar ransa zai fita, 

Momy tace " Mannir kayi magana mana, 

kasa magana yayi illa kallan Zarah da yaci gaba dayi yana kuka, 

tsawa Dady ya daka masa cikin b'acin rai yace " karka mai da mutane sakarkaru mana, 

idan bazakayi magana ba mu tashi, 

still shiru Mannir yayi yana ci gaba da kallan Zarah yana kuka, 

tsaki Dady yayi ya mik'e a fusace yana k'ok'arin barin wajen, 

da sauri Mannir yace " kayi hak'uri Dady zanyi magana, 

komawa Dady yayi ya zauna cike da tausayin Mannir, 

k'ara fashewa Mannir yayi da kuka mai tsanani, 

yana kallan Zarah, cikin kuka yace "............. 





Don't forget to vote and comments 




MOMYN ZARAH