GADAR ZARE…

75

by @hauwaausmanjiddarh

'''GADAR ZARE!!!'''


_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_




      ~NA~




*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh


Gmail: ***


Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh 




*GARGAD'I*



'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA''' 




~DEDICATED TO~

*AISHA A BAGUDO*




*BEST FRIEND FOREVER & EVER* 

'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''

       *~(UMMU AMAN)~*






75


Cikin mutuwar jiki Naseer ya d'aga masa hannu had'i da matsar da ita gefe, 

ba tare da yace masa komai ba, 

ita ko duk ta rirrik'e Naseer kamar wacce za'a kashe, 

Zainab dake durk'ushe a k'asa tana kuka ta mik'e cikin zafin nama taje gabansa,, 

tace " da kake mik'a hannu me zaka kuma yi mata? 



Ko..... shiru tayi saboda yadda take jin yanayin jikinta ya canja, 

k'irjinta na sama da k'asa da kyar tace " tsakani na da kai Mannir Allah ya isa, Ubangiji yayi mana sakayya ni da Zarah, da Ikram, 

a hankali numfashinta datake iyakar k'ok'arin fisgowa ya d'auke gaba d'aya ta zube k'asa a sume, 

mik'ewa Naseer yayi da Zarah tsaye a jikinsa, ya fita ba tare daya furta koda kalma d'aya ba, 

da sauri Mannir ya bi su suna gaf da barin parlorn ya durk'ushe had'i da rik'o k'afafuwan su, 

cikin matsanancin kuka yace " please ku yafe min, idan baku yafe min ba wallahi na shiga uku, yanzu ma kuna ganin yadda Allah yayi dani da rayuwa ta, 

a hankaki Nasser ya durk'usa yasa hannunsa ya zame rik'on da Mannir yayiwa k'afuwansu, 

Dady da Momy kasa motsi su kayi saboda kunya da tashin hankali, 

Alhaji Abdullahi da Abban Zarah sauran mutane suka mik'e jiki a sanyaye, 

a hankali Abban Zarah ya sunkuya ya sungumi Zainab dake kwance a sume yayi waje da ita ba tare da kowa yayiwa kowa magana ba, 

suka fita ko a mota babu wanda yayi magana har suka k'arasa hospital da Zainab. 



Da sauri aka karb'e ta aka shigar da ita emergency an d'auki lokaci mai tsayi kafin Doctor ya fito ya sanar da su, 

ta samu mutuwar b'arin jiki saboda tsananin tashin hankalin data shiga, 

sosai hankalin su yayi masifar tashi, Abban Zarah yayi kuka a b'oye har ya godewa Allah, 

bak'in cikinsa biyu na farko halin da Zainab ke ciki, 

na biyu abinda mannir yayiwa Zarah, 

lalle Mannir ya cika cikkekken maci amana butulu, mugu macuci azzalumi, 

amma ba komai shida Allah, tunda gashi nan tun yanzu ya fara girbar abinda ya shuka, 

bedroom Nasser yakai Zarah, ya ajiye ta akan bed sannan ya d'auko mata ruwa a fridge ya bata tasha jikinta sai rawa yake yana tsuma, a hankali Naseer ya zauna a kusa da ita ya jawo ta jikinsa ya rungume ba tare dayace komai ba, 

sai ajiyar zuciya da yake ta faman saukewa, ya k'i yin magana ne tun a parlor saboda yasan halinsa da bak'ar zuciya, 

muddin yace zayyi magana to komai ma b'aci zaiyi, dan ba'a k'are lafiya ba, 

dan haka ya zab'i yayi shirun dan shi ya fiye masa sauk'i.



A gigice Zarah ta d'ago kai ta kalli Naseer tace " dama na fad'a maka Na'eem ba d'anka bane, 

ko sau d'aya ban tab'a alak'anta ka dashi ba, kwata-kwata zuciya ta tak'i yarda shi d'anka ne, 

dan nasan bazaka tab'a yi min haka ba, ina da cikekken yak'ini akan ka Uncle, 

na yarda dakai d'ari bisa d'ari, nasan bazaka tab'a cutar da ni da rayuwa ta ba, 

dan Allah Uncle ka d'auke mu bar nan, muma tafi ko'ina ne, Uncle bazan iya ci gaba da zama anan ba, 

na tsani garin nan, na tsani kowa da yake ciki, ni kai na ma na tsani kai na, 

ganin yadda take magana a burkice duk ta fita daga hayyacinta yasa Naseer mai da ita k'irjinsa ya rungume, 

had'i da runtse idansa da k'arfen tsiya, yana shafa kanta, 

yana tunanin yadda rayuwa da duniya ta canja, 

da yadda mutanen cikin duniya suka zama marasa amana, da alk'awari, 

ashe duk yadda kake da mutum yana iya cin amanar ka, 

duk kusancinka da d'an Adam da alak'ar dake tsakanin ku yana iya cutar dakai, 

to kau idai haka ne duniya da mutum ba abin yarda bane, 

Dady da Momy sun kai magrib anan babu wanda iya furta koda kalma d'aya a cikin su, 

kowanne yayi jugum yana sak'a abubuwa da dama a ransa, 

kiran sallar magrib da akayi ne yasa dukkan su mik'ewa jiki a matuk'ar sanyaye suka bar parlor'n. 



Bayan kwana biyu Naseer ya gama duk wani shirin komawar su holland, 

dan shi kansa ya tsani Nigeria da abinda ke cikinta jinsa yake kamar acikin wuta, 

haka tunda abin ya faru Dady da Momy suke wasan b'oya da Zarah da Naseer dan muguwar kunyar su suke ji, 

musamman ma ita Zarah, dan sunfi jin kunyarta akan kowa, 

itama tunda abin ya faru bata fito ko parlor ba, kullum tana bedroom tana faman kuka, 

ji take dama itace ta mutu ta huta ba Ikram ba, sai yanzu tayiwa Allah godiya da mutuwar Ikram, 

dan tasan mutuwarta ta fiye mata data rayu taga tarin abin kunyar da mahaifinta yayi, 

babban burinta a duniya bai wuce su bar k'asar ba, kwata-kwata ko yaran ma ta daina shiga harkar su, 

ta daina kula su, dan ji take ta tsani kowa da komai, ji take gwamma mutuwa tazo ta d'auke ta, 

haka yaran zasu zo su hau kanta su k'araci surutun su amma a banza ko kallan inda suke bata yi, 

a parlor Nasser ya iske Dady da Momy zaune kallo d'aya yayi musu ya kauda kansa gefe da bazai iya jurar kallan mahaifansa a cikin matsananciyar damuwa ba, 

duk sun rame sosai kamar ba su, duk wannan walwalar dake fuskar su yanzu kwata-kwata babu ita, 

sai tulin bak'in ciki da damuwa. 



Suma kallansa su kayi cike da tausayawa dan shima yayi muguwar rama acikin kwana biyu kawai, 

ya rame ya kod'e sosai, Momy na shirin tashi Naseer yayi saurin cewa " no please Momy ki tsaya bana san ki tafi magana zanyi daku gaba d'aya, 

cikin sanyin jiki ta koma ta zauna, sai da Naseer ya d'an numfasa kafin yace,, 

" please kuyi min izini ina san barin k'asar nan ni da iyalai na, 

zamu d'anyi nesa da nan kafin komai ya lafa, hankula su kwanta, 

in yaso sai mu dawo daga baya, 

daga Momy har Dady babu wanda yaso haka a ransa amma dan sama musu sauk'i duk suka amince batare da nuna masa alamar komai ba, 

zai mik'e Dady yace " kuje kai da Zarah ku dubo Zainab a hospital kafin ku wuce, 

cikin sanyin murya Naseer yace " bata da lafiya ne Dady? 



Dan shi bai ma san ta fad'i ba a lokacin, 

bayani Dady yayi mishi na rashin lafiyar Zainab, aiko sosai hankalin Naseer yayi mugun tashi dan yasan hakan yana da nasaba da tsananin so da k'aunar da Zainab keyiwa Zarah, 

haka ma yasan idan Zarah taji abinda yake damun Zainab d'in hankalinta zai k'ara tashi, 

amma dai koma meye dole ne suje su dubo ta kafin su wuce, dan ba'a san me Allah zayyi gaba ba, 

jiki a sanyaye Naseer ya fita ya shaidawa Zarah ta shirya ita da yaran zasuje hospital, 

ba musu ta amsa da to, bata wani b'ata lokaci ba ta fito ita da yaran,

a parlor ta iske Naseer zaune rik'e da Nailah, kallanta Naseer yayi yaga duk ta zama wani iri, 

dan ya sani bata cin komai, ko ruwan tea dak'er take sha, shima sai ya matsa mata, 

haka ma bata bacci yadda taga rana haka take ganin dare, 

bata runtsuwa, tayi bak'i ta rame sosai kamar ba ita ba, 

batare dayace mata komai ba ya mik'e yayi waje, 

bin bayansa su kayi ita da yaran, 

har suka isa asibitin babu wanda yacewa kowa komai a tsakanin su, 

sai yaran dake ta faman damun su da surutu, 

 a harabar asibitin yayi parking ya fito d'auke da Nailah da Noor, 

ita dai Zarah bin bayansa kawai take dan bata san wanda bai da lafiya ba, 

bata tambaye shi bane dan bata san yawan magana yanzu.



Suna shiga d'akin taga Zainab kwance bata motsi sai na'ura dake aiki, 

ko numfashi bata iyawa sai da oxygen, 

da k'arfi ta saki k'ara had'i da fashewa da rikitaccen kuka ta fad'a kanta tana jijjiga ta, 

cikin kuka ta kalli Naseer tace " Uncle ka taimake ni ka d'auke ni dani da Momy na mubar k'asar nan, 

dan Allah mu tafi mubar kowa, ku biyu kad'ai kuka rage min a duniya da nake su, 

idan wani abu ya samu d'aya daga cikin ku bazan iya jurewa ba, dan Allah ka taimaka min kar Momy ta mutu, 

itama ni kad'ai na rage mata a duniya wacce zata kira tata dan Allah please, 

ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka, 

kanta Naseer ya shafa had'i da rungumo ta jikinsa, 

yama rasa abinda zayyi sai kawai shima ya saki kukan, 

dan dama ya dad'e yana rok'on Allah yasa yayi kukan ko zai samu sassauci a zuciyarsa, 

Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dake gafe, tsaye sukayi suna kallan su cikin tausayawa, 

dan su Naseer basu san da su ba, 

sosai da k'arfi Naseer ya rungume Zarah yana rusgar kuka kamar ransa zai fita, 

sun ma manta da yaran su dake tsaye, 

itama Zarah kukan take sosai tana sambatun da bata san me take cewa ba,, 

yaran tsaye sukayi sororo suna kallan Dad & Mom d'in su dake kuka, 

a hankaki Na'eem yaje kusa dasu yana share musu hawaye, shima yana kukan, 

sai Noor da Nauwaf ma suka nufe su, 

gaba d'aya suka saka hannu suna share musu hawaye, 

cikin kuka Na'eem yace " Dad nine na saka ka kuka? 



Yayi maganar yana nuna kansa, 

cak Naseer da Zarah suka tsaida kukan su had'i da zuba masa ido, 

a hankali Naseer ya shiga girgiza masa kai alamar a'a, 

Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dake tsaye sukayi gyaran murya dan sun lura daba susan suna wajen ba, 

da sauri suka d'ago kai ganin Abban Zarah da Alhaji Abdullahi dake tsaye yasa su saurin sakin juna, cike da jin kunya, 

sosai suka yiwa su Zarah nasiha mai ratsa jiki da zuciya, wanda a take duk suka ji zuciyoyin su sunyi musu sanyi, 

Abban Zarah ya rink'a kawo musu misalai akan Annabawan Allah, da salihan bayi na gari, 

ya rink'a jawo musu ayoyin Al-Qur'an, 

daga k'arshe kuma ya basu hak'uri on belf of Mannir, 

shiru duk sukayi babu wanda yace komai, 

sai Naseer daya nemi izinin tafiya da Zainab Holland, batare da gardamar komai ba suka amince. 



Washe gari jirgin su ya d'aga zuwa Holland gaba d'ayan su da yaran su, da Zainab, 

cikin ikon Allah satin Zainab d'aya a hospital ta farfad'o, sai da har lokacin b'arin jikinta a shanye yake, 

dan ko magana bata iyawa, ko zama da gane mutane bata yi, 

haka Zarah ta rink'a jinyar ta a hospital, itace wankan ta, itace aikin kashi da fitsarinta, 

had'i da sauran aikace-aikace har sukayi wata uku a hospital kafin akan sallamo su daga hospital suka dawo gida, 

dan yanzu ba laifi tana iya gane mutane musamman Zarah da Naseer, 

kuma tana iya zama a wheelchair, kwata-kwata bata barin 'yan aiki su kula da Zainab ita da kanta ke kula da ita,, 

haka rayuwa taita tafiya Zarah na kula da Zainab har Allah yasa ta samu sauk'i garau kamar bata tab'a yin ciwo da jinya ba, 

ta warke sosai tayi garau, sai lokacin Zainab ta yarda da maganar hausawa da suke cewa 



_" D'A DA DUKIYA BA'A YI MUSU BAK'IN CIKI KO MUGUNTA DAN BA'A SAN MAI MORAR SU BA_



_KUMA BA LALLE D'AN DAKA HAIFA DA CIKIN KA NE ZAI TAIMAKE KA KOYA KULA DA KAI BA,_

_HAKA KOWANNE D'A, D'A NE_



Mannir kam ba'a magana dan dashi da tsumma duk d'aya, 

ya yargwale, ya k'ek'ashe, ya bushe yadda kasan ba mutum ba ya koma kamar skeleton, 

duk wani hospital daka sani a duniya sun k'i karb'arsa saboda warin da yake yi, 

ya gama rub'ewa ya lalace ga al'aurarsa data fara tsutsotsi, 

saboda yawan complain d'in da jama'a keyi a kansa na ya dame su da wari yasa human right ta shigo cikin maganar babu yadda zayyi dole yana ji yana gani aka mayar dashi daji aka yi masa gida, 

shi kad'ai yake rayuwar sa dan babu wani d'an Adam d'in dazai iya yi masa aiki ko nawa za'a bashi saboda d'oyi, 

tun abinda yayiwa Zarah Momy da Dady suka cire hannunsu daga kansa, 

suka zuba masa ido, babu wanda ya k'ara kula shi acikin su, 

balle su shiga harkarsa, 

suka cire duk wani tausayi dake tsakanin d'a da mahaifi suka bar shi da halinsa, 

dan sun san abinda yayi ne yake binsa, 

koda Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suka zowa Dady da maganar Mannir fututtukewa yayi yace babu ruwansa, 

kuma duk wanda yasa masa hannu bai yafe ba, dole tasa suma suka kyale shi, 

sun san Allah ne da kansa yake hukunta shi abisa cin amanar marainiya dayayi, 

sosai Naseer, Zarah, Zainab, Momy da Dady suka koma normal kamar babu wani abu daya tab'a faruwa a rayuwar su, 

Zainab ce ta matsa musu akan lalle ya kamata su je Nigeria suga iyayen su, 

akan dole Naseer ya nema musu visa, 

suka yo Nigeria, sai da suka zo Dady yake sanar musu halin da Mannir yake ciki, 

aiko Zarah taita rusgar kuka saboda tausayin sa, 

Zainab da Naseer kuwa ko a ajikin su, 

yadda kasan ma basu san wanda ake magana akan shi ba, 

kwata-kwata babu tausayinsa a zuciyar su, 

dole Zarah ta matsawa Zainab da Naseer akan dole sai sunje sun dubo shi, 

dakyar ta shawo kansu, suka tafi har su Dady. 



Tun daga nesa kafin su k'arasa inda Mannir yake suka fara jiyo d'oyinsa, 

kuka Zarah ta k'ara fashewa dashi, 

koda suka isa dakyar suka rink'a yin numfashi saboda d'oyin da yake yi, 

komai rashin imanin mutum yaga yadda Mannir ya koma dole ne ya tausaya masa, 

tsakanin d'a da mahaifi sai Allah take zuciyar Dady da Momy ta karye suka shiga zubar da hawaye, 

shi kansa Naseer take yaji mugun tausayin d'an uwansa ya kama shi, 

bai san sanda ya fara zubar da hawaye ba shima, 

Zarah dama uwar kuka balle an samu mai dalili baki ta bud'e tayi ta rusgar kuka kamar ranta zai fita, 

da farko Mannir bai gane su ba, sai da yayi musu k'uri da ido sannan ya gane su, 

dakyar Mannir ya bud'e baki yace " kunga yadda Allah ya maida ni ko? 



" Dan girman Allah ku yafe min idan baku yafe min ba, Allah kad'ai yasan me zan gani gaba, 

yayi maganar cikin matsanancin rashin lafiya, da sauri Zarah ta zube a gabansa cikin kuka tace " na yafe maka Dady duniya da lahira, wallahi na yafe maka, kuma ina fatan Allah ma ya yafe maka, 

indai hak'k'i nane ke wahalar dakai haka, na yafe maka, Allah ya rangwanta maka, 

dakyar yayi murmushin k'arfin hali yace " nagode Zarah, Allah ya saka miki da alkhairi, 

ya juya ya kalli Daddy da Momy, suma cikin kuka suka ce sun yafe masa duniya da lahira, 

haka ma Naseer ya yafe masa, 

ya juya wajen Zainab dake tsaye ko gezau, kwata-kwata babu alamar tausayi ko jin k'ansa a tattare da ita, 

kanta da kawar gefe dakayar da bud'e baki murya can k'asa tace " na yafe maka, Allah ya yafe mana baki d'aya, 

ido ya lumshe yana hawaye, da sauri Zarah tace " dan Allah Daddy da Naseer ku taimaki Daddy na dan Allah karku bari yayi mutuwar wulank'anta, 

ganin yadda take rusgar kuka tana neman a taimakawa wanda ya cutar da ita da rayuwarta yasa gaba d'ayan su suka k'ura mata ido, 

musamman Naseer ya kafe ta da ido, a hankali ya furta Fatimatul Zarah kenan mai sanyin hali, 

da tattsausar zuciya, kwata-kwata baki da rik'o mummunan nufi akan mutum koda wanda ya azabtar dake ne, 

kina da tsarkakekkiyar zuciya mai taushi, kina da hak'uri da saurin yafiya, kina da saurin manta sharri kina da rik'o da alkhairi, 

kina da manyan halaye masu kyau, kina da halaye na gari irin wad'anda Annabi (S.A.W) yake so, yake kuma alfahari dasu, 

halayen dake wuyar samu a zamanin nan, dan sai ka shekara dubu kana yiwa mutum alkhairi, 

amma rana d'aya idan ka kuskure shikenan ka shiga uku sai ya mance da alkhairai daka yi masa.




A hankaki Daddy ya dafa shi yace " kwarai kuwa Naseer samun mutum mai irin halayen Zarah sai an tona, 

sai lokacin Naseer yasan a fili yayi maganar ba kamar yadda yake zaton yayi a zuciyarsa ba, 

murmushi yayi had'i da duk'ar da kansa k'asa, a hankali ya saci kallan inda Zarah take, 

ganin itama shi take kallan yasa shi fahimtar itama taji abinda yace, 

a hankali Zarah tace " please Daddy a taimaki Daddy, dan Allah, wallahi mu bar ganin yayi laifi, 

idan muka barshi a wulank'ance muma sai Allah ya kamamu da laifin watsi da zumuncin Allah, 

dan Allah Naseer, kar muyi abinda zamu dawo daga baya muna nadama, 

tsaki Zainab tayi had'i da fita daga wajen ta koma mota ta zauna, 

tana jin yadda zuciyarta ke tsananin yi mata zafi da rad'ad'i gami da k'una, 

ba musu Naseer ya sunkusa ya d'auki Mannir, 

da farko k'in yarda Mannir yayi, dan shi a ganinsa bai cancanci taimako daga wajen kowa ba, 

sai da kyar Zarah ta shawo kansa ya yarda, 

Daddy da Momy da Zainab da yaran suka shiga mota d'aya, 

Naseer da Zarah da Mannir suka shiga mota d'aya, 

BQ Naseer ya fara wucewa da Mannir yayi masa wanka sosai, 

ya canja masa kaya ya fesa masa turare, sannan ya kamo hannunsa suka shiga cikin gidan, 

Zarah ce ta sanar dasu akan taji labarin wani mai maganin gargajiya na Islamic kuma ance maganinsa yana yi sosai. 



Washe gari suka d'unguma gaba d'aya suka tafi amma banda Zainab dan rufe idanuwanta tayi tace bata zuwa, 

kuma ta hana a tafi da yaran har Nailah da an yaye ta tuni, Ikram ma an yaye ta tun suna Holland, 

koda sukaje sukayiwa mutumin bayani, cewa yayi ba komai zasu gwada suga mai Allah zayyi amma subar Mannir anan har tsawon wata biyu, 

kuma duk sati kawai zasu rink'a zuwa ganin shi ranar Friday, 

haka suka bar shi anan bayan sun gama biyan duk abinda ya dace, 

bayan sun dawo gida Zarah ta cewa Daddy bafa zama za'ayi ba, 

dole a dage da addu'a ana rok'on Allah, kuma a saka da saukar Al-Qur'an a masallatai, 

ana bada sadaka ko Allah zaiji k'ansu ya amsa rok'on su, 

kamar yadda Zarah tace haka akayi Daddy ya zuba malamai akayi ta rok'on Allah ana saukar Al-Qur'ani, 

suma kuma suka dage da addu'a. 



Allah maji rok'on bayinda dan da su Naseer suka koma bayan wata biyun da mai magani ya basu, 

Mannir ya warke sumul yayi garau dashi, 

yayi fresh yadda kasan bai tab'a yin wani ciwo ba, 

sai ma yafi da yarinta da kyau, 

farinsa ya k'ara fitowa sosai, gashin kansa yayi lufluf, 

k'arfi da girman zindariya ya k'aru, 

dama ba'azo da Zainab ba dan k'in zuwa tayi,

dad'i Daddy da Momy su kaji sosai ganin yadda Mannir ya koma so fresh, & handsome guy kamar d'an 30yrs, 

Zainab ma da hankalinta ya kwanta sosai, kuma dama ga kud'i da hutu sai ta koma yarinya 'yar 30yrs so fresh da ita, 

tunda Mannir ya dawo gida kwata-kwata baiga Zainab ba tak'i yarda su had'u ta ganshi, 

ta koma zaman bedroom, in banda Mommy da Daddy ma sun hana ta tafiya da tuni ta kama gaban ta, 

Mannir sanarwa Daddy yayi akan please yana san su raka shi yabawa Alhaji Abdullahi da Abban Zarah hak'uri , 

ba musu Daddy ya kira amininsa a waya ya sanar dashi zuwansu, 

haka ma ya kira Abban Zarah ya sanar dashi su had'u a gidan Alhaji Abdullahi, 

dole mommy ta matsawa Zainab ta shirya, motar su Naseer da Zarah ta shiga dan ita duk abinda zai had'a ta da Mannir bata san shi, 

shi kuma da mommy da daddy suka shiga mota d'aya, 

su Naseer sun riga isa har sun shiga parlor sun zauna, tare da Abban Zarah da Alhaji Abdullahi, 

koda Mannir ya shigo ya d'ora idansa akan Zainab yaga yadda ta koma kusan hantsilawa yayi, 

ya kafe ta da ido k'uri ya kasa cewa komai, 

itako ta had'e girar k'asa data sama, taci magani babu ko alamar fara'a, 

sai da Daddy yayi gyaran murya kafin ya dawo hayyacinsa, 

murmushi Zarah tayi ganin yadda Mannir yake kallan Zainab, 

sai da aka gaggaisa sannan Mannir ya fashe da rikitaccen kuka '


Kowa yace ya yafe masa, gaba d'aya parlor aka k'ara neman afuwar juna da ban baki,

sosai jikin kuwa yayi mugun yin sanyi, kuma suka k'ara tsorata da al'amarin mutane da duniya, 

bayan an gama komai za'a watse Zarah tayi saurin cewa dan Allah ina san neman alfarma d'aya, 

murmushi Zainab tayi had'i da cewa a wajen wa? 



Kai tsaye Zarah tace " a wajenki mommy, 

cike da mamaki Zainab tace " fad'i komai kike so nayi miki alk'awarin zan baki, 

murmushi Zarah tayi tace " ki rantse da Allah komai nake so zaki min, 

batare da tunnain komai ba Zainab tace " wallahi na rantse miki da girman Allah duk abinda kike son nayi miki alk'awari zan miki, 

dan yadda Zainab take jin Zarah a ranta, ko ranta tace tana so idan tana da ikon cirowa ta bata to cikin gaggawa zata bata, 

musamman yanzu da bata da wata 'yar sai ita, 

ga jinyar datayi sosai har tsawon shekara d'aya da watanni amma bata tab'a gajiya da ita ba, 

dai-dai da second d'aya bata tab'a nuna alamar gajiwa da ita ba, 

itako me Zarah zata nema a rayuwarta matuk'ar tana dashi ta hana ta, 

kai tsaye Zarah tace " SO NAKE KI KOMA GIDAN DADDY, 

da sauri Zainab ta mik'e tsaye a matuk'ar firgice take kallan Zarah ta kasa cewa komai, 

Zarah tace " eh Mommy so nake ki koma gidan Daddy na Mannir da zaman aure............. 






Don't forgot to vote, comment & follow 





MOMYN ZARAH