SARKI SAMEER

Episode 17

by @azeemadahiru

 💅SARKI SAMEER....💅

       by❤xeemat....love❤


        🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


Episode17 


Tana gama ayyana hakan kuwa ta daga qafa zata gudun kawai taji an ruqeta saura kadan tasaki futsari tsabar tsoron da ta shiga jin anyi shiru ba taji saukar duka ba kuma ba ayi mara komai ba yasata juyo wa ahankali ganin ko waye tana dagowa kwa idon ta ya sauka akan lami wata mahaukaciyar ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa kai aunty lami wai daman kece duk kikasa nabi na tsora ta dan wlh kinban tsoro sosai lami dake faman boye dariyar ta sai yanzu tasamu damar yi tace ai nasani shiyasa nayi miki haka tace aikwa kin dau alhakina wlh kinsande yanda nake tsoron mu hadu da masu gidan amma kikai min haka harda boye Murya yanda zanfi tsorata ko dariya ta qara yi tace wlh tsoranki yayi yawa tace ai tsoro wajibi ne saida tagama nutsuwa sannan tace wai ke sai yau kika ga damar dawowa duk kinbar ni da aiki nikade yanzu komai na gidan nan ni nakeyi katseta tayi da cewa Allah sarki har na tausaya miki Allah yakawo miki dauki danni nan dakike ganina ma daga yau baza ki qara ganin qafata agidan nan ba yanzu ma gurinki nazo muyi sallama saboda barin unguwar nan zamuyi tashi zamuyi yau yau dinnan  lami hannu tadaga sama ta dora akai tace nashiga aljanna nayi tsudum tsudum naqi fitowa kuma bazan fito ba 😂yanzu dan Allah dagaske kike ko da wasa tace wlh da gaske nake tace yanzu bazan qara ganin ki ba ko zakirin ga kawo mana ziyara tace a'a wlh bazan zo ba saide ke kizo tace inda zaku kona yana da nisane da zakice bazaki zo ba ba amana wallahi tace wlh ba nisa mukai ba tace wacce unguwar zaku koma Ameesha tace mata nima bansan sunan unguwar ba da mamaki lami tackalleta tace kamar ya baki sani ba wai tsaya ma me yafaru zaku tashi matsala kuka samune da gidan da kuke zaune ko wani abunne yafaru da har takai ku ga tashi wlh banji dadi ba Ameesha tace wlh lafiya qalau gidan su bossay zamu koma shida maman sane suka ce mukoma can da zama baki tasaki tana kallon ta saida tagama sannan tace ke dan Allah amma wane bossayn kike nufi tace bossay nawa kika sani tace daya ita kuma ta daga mata kai alamar tabbatar wa tafa hannu tayi tace amma na tayaki murna har yanzu nakasa yarda wai gidan su bossay zaku koma da zama amma fa na taya ki murna dan wlh kakar ki ta yanke saka Ameesha ta bude baki zatai magana kenan suka ji andaka musu wata mahaukaciyar tsawa da ta karade gidan gaba daya saboda safiya ce sai da gidan ya bada sauti Rasheeda ce tsaye abakin qofa da ta fito cikin shirinta na zuwa makaran ta saboda yau da wuri zata fita saboda test zasuyi shigowar ta kenan dan ta dan samu wani abun taci kafin ta fita shine kunne ta yajiye mata maganar da tasa zuciyar ta bugawa da qarfi tana shirin fitowa waje kuma ba komai taji azancen nasuba sai maganar lami ta qarshen da tace wlh har yanzu nakasa yarda wai gidan su bossay zaku koma amma nataya ki murna dan wlh kakarki ta yanke saqa jin an ambaci abun sonta yasata jin faduwar gaba Qarasowa tayi inda suke ta qara daka musu tsawa dacewa wane bossayn naji kuna magana akai Ameesha da har tafara ruwan hawaye tace aunty dan Allah kiyi hakuri wata tsawar taqara buga mata tace dan ubanki hajuri nace kiban ba tambayarki nake ba amsa zakiban wuqi wuqi ta farayi da ido takasa magana dan bata san ta yanda ma zata fara yi mata bayani ba suna cikin haka sai ga mom tashigo tana tambayar su me yake faruwa dukan su ba wanda yaba ta amsa saida tace daughter wai neke faruwa duk tunda natshi nake jin muryar ki daga hannu tayi ta na nuna mata Ameesha da yatsa tana cewa mom wannan munafukar yarinyar ce sai kuma tayi shiru tana hararar Ameesha Mom batai mamakin ganin Ameesha ba saboda da dad yagaya mata zata dawo aiki to amma abun da yadaure mata kai me yasa yarta haka hartake kunfar baki alahalin kuma jiya da kanta tace ita bata damu da dawowar tata ba amma gashi kuma tazo ta tarar dasu to me ya hadasu bata da wanda ze bata amsa

dan haka ya ta maida kallon ta ga lami da ta rakube gefe guda tana tsoron kar adawo kanta mom ce tace ke lami me yake faruwa yimin baya ni cike da tsoro tafara yi mata bayanin duka tattauna war da sukayi ita da Ameesha wata uwar shaqa takaiwa wuyan ta tace dan uban wane bossayn kike nufi bade bossay na ba har yanzu bata ce komai ba saboda shaqar da tai mata mom ce tace wai kin tabbatar da shidin take nufi shi me zesa shi yin hakan qara shaqeta tayi tace baza kigaya min ba sai na halakaki agun nan da kyar ta iya bude bakin ta tace eh shi yaya bossayn ki da qarfi tace what! how dare you mom kinji me tace ko mom tace naji meye abun tada hankali aciki kinsande dad dinki na gida idan kika bari yazo yasame ki ahaka baza kiji da dadi ba kuma zaki gayawa aya zakinta dan haka nide ba ruwana jiki magayi tana gama fadar haka tai ficewar ta daman so take tasamu damar rama abun da tayi mata jiya kuma ta rama dan kwa Rasheeda ba karamin shaqa tayi ba ganin yanda mom din tata ta nuna bata damu da ita ba hasala ta qayi tana kallon Ameesha tace to wlh yau sai kin gaya min alakar ki da shi da har kika samu damar komawa gidan su gaya min shegiya munafuka me kama da 'ya'yan aljanu fada min ko kuma in kasheki kowa ma ya huta ko kuma maular da kikasaba kikaje gidan su yar matsiyata kawai to wlh baki isaba ba inda zaki fita daga cikin gidan nan dan acikin store zan sakaki in qulle daga nan ki mutu aciki inga uban da ze tsaya miki banza shegiya yar gidan shegiya tana gama fadar haka ta fara kokarin janta Ameesha tayi saurin katse ta cikin shashekar kuka tace nifa wlh aunty da wasa nake mata ba gidan su bossay za mukoma bafa a unguwar sune de gidan dazamu koma shima kuma aikatau zamuje saboda dadda tace bazan qara zuwa aiki nan gidan ba shine nikuma bazan iya zama ba aiki ba shine nafito ko zan samu wani gidan su dauke ni saida naje wajen gida biyar amma bansamu ba ina kan hanyar komawa gida sai na hadu da wata qawata yar makaran tar mu itama aikatau take yi sai nagaya mata tace inzo muje unguwar da take aiki bazan rasaba zan iya samu haka tayi mana kudin mota muka je shine muna zuwa muka tsaya muna tunanin inda zamu fara shiga saiga yaya bossay ya fito yana fitowa na gaida shi yake tambayata me muka zo yi unguwarsu nace ai bansa ma nan unguwar suba sai yanzu daga nande mukai mishi bayanin aiki nake nema sai ya nuna mana wani gida yace mushiga gidan su abokin shine yaji suna neman me aiki mushiga muce shi ya turo mu mukai mishi godiya ni tunda ga ranar ma ban qara ganin shiba ba har yau bayan munshiga gidanne kuma suka ga nayi qarama sukace min ina iyaye na suke nace musu banda su ni da kakata muke zaune shine suka ce inzo da kakar tawa suyi magana da ita danaje gida nagayawa dadd.....bata qarasa ba ta daga mata hannu tace dalla malama yimin shiru sai wani yimin dogon jawabi kike sai kace na tambayeki tana gama fada ta kama kunnen ta da qarfi taja tace Allah ya taimakeki amma wlh wlh kinji na rantse koda wasa nakama ki da shi na lahira sai yafi ki jin dadi duk wani abu da kikasan zesa ku hada hanya karki bari hakan tafaru kar kiga ba unguwa daya muke ba duk wani motsun ki da zakiyi acikin unguwar za asanar dani dan zansa asaka miki ido a ringa min bincike akanki dan haka ki kiyaye ni nidin nan da kike gani ba kanwar lasa bace duk yanda kike tunani na na wuce haka tana gama fadar haka ta turata gefe tare da ficewa daga kitchen din dan tama manta abun da yakawota kitchen din Ameesha zubewa tayi awajen tana sauke ajiyar zuciya lami dake makale gefe guda taje ta dakko mata gorar ruwa ta kawo mata tana bata kwa ta karba ta bude tunda tadaga bata ajiye ba saida ta shanye tas sannan ta ajiye robar aqasa lami ce ta tsugunna agaban ta tana yi mata sannu kai kawai ta daga mata saida ta dan samu nutsuwa sannan ta mike tace aunty lami saduwar alkhairi lami tace muje in rakaki tare suka fito saida suka dan yi nesa da wajen kitchen lami da abun ya daure mata kai to me yasa tayi mata qarya tace agidan su bossay zata zauna alahalin tasan qarya take yi kasa daurewa de tayi tace wai nikam intambaye ki me yasa kikai min qarya da kikace agidan su zaku zauna yanzu kuma ga abun da kika gaya wa Rasheeda saida Ameesha taja wani lokaci kamar ma baza ta bata amsa ba sai kuma tace duk abun da kikaji nagaya musu qarya nake wanda nagaya miki ne gaskiya lami kasake tayi kamar wata sokuwa tace wai kina nufin duk wannan uban labarin da kika bayar qirqirq kikayi ba gaskiya bane tace mata eh tace gaskiya na jinjina miki zubaida kin iya tsara labari kamar gidan radio Ameesha tace ko kece kika ga ana shirin rabaki da duniya akaiki barzahu sai kinyi irin wacce tafi tawa lami tace rabani ina ni ina iya wannan qaryar ai tayi yawa fada fa kike tayi bawanda zece zancen ki akwai karya aciki Ameesha tace ni dan Allah kibar ni da abun da yake damuna da jikin zanji ko kuma da surutun ki lami tace nidin kuma yau ake gayawa haka lalle manya sunji shaqa bata kulata ba tayi gaba har de suka qaraso bakin gate din sannan sukayi sallama lami ta dawo ciki ita kuma tafita dan ko baba me gadi batayiwa sallama ba ta wuce ta tafi abin ta saida ta fito ta qara fashewa da kuka tana tunani wai ita kam me tayiwa aunty Rasheeda ba da bata sonta kwata kwata bata qaunar ta ta tsaneta arayuwar ta duk sanda zasu hadu sai taci zalinta ko kuma tayi mata zagin wulakanci da cin mutun ci yanzu yazatayi idan kuma tagane qarya ta shirya mata gashi kuma tace zata sa ayi mata bincike in aka gaya mata ga agidan datake fa yazatayi wata zuciyar ce tace mata sai ki zamanki basai kin fito ba bare ma aganki agaya mata bashike nan ba tana wannan tunanin har ta qaraso qofar gidan su sai kuma abun da tayiwa dadda ya fado mata ashe fa dadda batace taje ba tafita gashi kuma taje ta jawowa kanta wulakanci Allah yasa de dadda kartayi mata fada sadaf sadaf tayi ta leka cikin gidan sai taga ba kowa dan haka sai tashiga da sallama ciki ciki da inba akusa da ita kake ba baza kataba jin me tace ba tana shiga saiga dadda tafito daga bandaki sai kawai ta tsaya bata shiga dakin da take shirin shiga ba dadda tunda taga fuskar ta tasan tasha kuka dan haka tace daga gidan uban wa kike kasa bata amsa tayi tana wasa da yatsun hannuta dadda tace wai ba magana nake miki ba dagowa tayi zatai magana dadda naganin fuskar ta kawa sai ta fashe da dariya saida tayi me isarta sannan tace Allah yaqara ya qara qarawa wanda beji bari ba ai bayaji hoho ba tana kaiwa nan tayi gaba abunta tana qara yi mata dariya ganin haka yasa Ameesha zaman dirshen agurin  harda bubbuga qafafu aqasa me yasa dadda zatai mata haka me makon ta rarrasheta amma kawai sai takama yi mata dariya haka ta ringa kuka me sauti dadda da tundazu tana jinta bata kulata ba sai yanzu da kukan ya isheta tafito Ameesha baji fitowar dadda ba kawai sai jin saukar doruna tayi agadan bayan ta aikwa wata mahaikaciyar qara tasaki da kwanciya agun tana burgima dadda sake dagawa tayi ta qara tsula mata bulalar tana cewa uban wani ya aikeki saida nace karkije kidawo amma kika ki da na biki abayama sai ki ka buya ainasan halinki sarai kawai rabuwa nayi dake jikin ki yaga miki ni naso ma kindawo wani sashen jikin naki aballe da ma sun karkar yaki da sun burge ni wlh tana gama fadar haka tacqara daga bulalar zata zuba mata aikwa ta kwasa aguje tayi qofar gida tana kuka dadda taja tsaki ta koma daki tana cewa gwara da sukai miki hakan dan kinga ina lallabaki shiyasa kike min iskancin da kika ga daman to muzuba nida ke sha shasha kawai wacce bata da zuciya

Ameesha nafita tasamu waje tazauna taci gaba da kukanta sai yanzu take kewar iyayen ta Allah sarki tasan da suna nan da bazasu taba yi mata haka ba amma yanzu gashi ba me rarrashin ta saitaji gaba daya kamar duniyar ta juya mata baya ba me kula da ita haka taci gaba da kukanta gwanin ban tausayi kamar wacce tarasa gata gaba daya yau daya dan dadda ta dake ta shine take ganin kamar ma kowa ya tsane ta tana cikin kukan taji tsayiwar mutum agaban ta tazata dadda ce tazo ta lallasheta ta bata hakuri shiyasa taqi dagowa sai da taji andafa ta sannan sannan ta dago idon ta sai tai tozali da..........



Allah sarki yau ga yar shalelen dadda awaje dadda ta rufe ido ta dumama mata jikin ta da bulala 😂



   ❤xeemat....love❤