CIKI DA WAJE

Page 02

by @ibrahimaliey


CIKI DA WAJE



IBRAHIM ALIYU YAKUBU



Page 02


A.S.A SARAKI HALL, ALMAWA STATE.


Katafaren ɗakin taro ne da ya amsa sunansa na ɗakin taro, an gina shine shekarar farko ta mulkin A.S.A SARAKI wanda ya yi sa a cikin almawa federal University waccan ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya.

Daga wajen ɗakin taron wanda ke zagaye da wasu fulawoyi masu matuƙar ɗaukar hankali, yayinda a daidai wannan lokaci jami'an tsaro sun zagaye kowanne ɓangare na ɗakin saboda wani babban taro da ake gabatarwa wanda ya haɗa duka kusashen gwamnatin jihar, da masu faɗa aji har da ma masu ƙumbar Susa wato masu arziƙi lamba ɗaya wanda ƙungiyar ALDYF ta shirya, bisa jagorancin manyan na saman teburin ƙungiyar.

A daidai wannan lokaci da yayi daidai da tara da wasu mintoci harabar ɗakin taron ta cika maƙil da motoci, yayinda har a wannan lokaci basu daina zuwa ba, har ma ana sa ran sai goma da rabi za'a fara gabatar da abin da ya haɗa mutane a taron saboda ana son kowa ya sami halatta kamar yadda masu ruwa da tsaki na ƙungiyar suka tsara.

Masu shirya taro kuwa sai shige da fice a CIKI DA WAJEn ɗakin taron domin tabbatar da an samar da dukan abin da zai ƙawata taron, a gama a tashi lafiya.

A cikin ɗakin taron kuwa ya tsaru ainun fiye da hasashen mai hasashe, ɗakin taron kuwa a wannan lokaci ya cika maƙil da al'umma yayinda kowa yake harkokin gabansa, wasu kuma suna gaisawa da abokan arzika, abokai kuma suna gaisawa da abokanan su.

Ko ina ka duba baka ganin komai face wulƙawar hasken cameras na ƴan jaridun suka halacci ɗakin taron.

Idan ka kalli can saman ɗakin taron kuwa anan ne aka ware wuri domin gwamna da muƙarrabansa a dai matsayin sa na gwamna, daga can bango kuma wata ƙatuwar poster ce wacca ke ɗauke da tambari, manufa da sunan ƙungiyar ALDYF har ma da manufar taron.

Haƙiƙa komai an gama tsara shi a daidai wannan lokaci taro kawai ya rage a fara, wanda kuma ake da bukatar halattar kowa tukun, sannan ko ba haka ba ma har a daidai wannan lokaci gwamna da muƙarrabansa ba su samu halattar ɗakin taron ba, ka ga ko ba komai wajibi ne a jira ƙarasowar sa a matsayin sa na lamba ɗaya a jihar.

Ƙungiyar ALDYF wato ALMAWA STATE YOUTH DEVELOPMENT FOUNDATION kafaffiyar ƙungiya ce shekaru biyu baya wacca ta taka rawar gani ainun wajen kawo cigaba sosai ga matasa har ma ta rage matsi da takuri, da lalacewar matasa ta hanyar bada shawarwari, samar da ayyukan yi da abubuwa masu amfani duk domin cigaban matasan jihar almawa.

Wasu matasa kuma ɗalibai na jami'ar tarayyar almawa sune suka gina ginin wannan ƙungiya wanda da farko ya fara commonly a matsayin ƙungiyar ɗalibai, itama ƙungiyar iya cikin makarantar ne daga baya kuma a lokaci guda sai suka yi shawarar kafa wannan ƙungiya inda aka ɗauki lokaci suna tsara yadda ƙungiyar zata kasance, daga baya suka samu mafita.

A cikin ƙananan hukumomi ashirin da shida dake jihar sun samar da waɗanda zasu wakilce su wajen yaɗa manufar su ta ginin wannan ƙungiya, Inda anan ma waɗanda aka wakilta aka yi yunƙurin gabatar da ita ga gari-gari yayinda waɗanda suka san ya kamata suka dinga shiga saboda idan har aka tsaya aka yi musu bayani akan yadda ake buƙatar cimmawa da wannan ƙungiya ko waye zai ji ya kamata ya shiga a dama da shi.

A cikin ƙanƙanin lokaci sunan ƙungiyar ya zagaye ɗaukacin jihar, yayinda ƴan ƙungiya da kansu suka kafa ƙungiyar su bayan gabatar da ita ga gwamnatin jihar, sun ɗan bayar da gudunmawar su ta shawarwari da kuma kuɗi domin kuwa dole ana buƙatar kuɗaɗe kafin ƙungiyar ta kafu ta tsaya bisa ƙafafunta.

Da yawa ƴaƴan masu hannu da shunin da ke cikin ƙungiyar sun taimaka da iya abinda Allah ya basu iko, su ma ƴan tagajan-tagajan mai sule, mai duka an haɗa domin tayar da ƙungiyar tsaye ta tsaya bisa ƙafafunta har a tunkari cimma manufar da aka kafa ƙungiyar domin ta, bayan haka ga kuɗin shiga ƙungiyar da shi ma ba laifi an samu kuɗaɗe, ƙalilan daga ƴan siyasa sun ɗan bayar da agajin su da shima bai taka kara ya karya ba, sai dai masu kishin al'umma da son cigaban su, ciki kuwa harda gwamna A.S.A SARAKI daya bayar da taimako a gwamnatance da kuma a karan kansa.

Da wannan kuɗaɗe suka samar da ofishin ƙungiya na jiha, da kuma ƙananun ofisoshin ƙaramar hukuma, daga nan kuma kamar yadda suka tsara ba kai tsaye za'a fara gabatar da tsarin ba, suna da bukatar wani lokaci, inda har za su samu damar sanya kuɗaɗen nan na su a wani kasuwanci da zai samar musu da riba, ta yadda kuɗin zuwa wani lokaci zasu kai matsayin da duk abin da suka tunkara za su kawo sauyi cikin ƙanƙanin lokaci, don haka su ma abinda suka yi kenan.

Da farko a ƙananun hukumomin da noma ya shahara sun sanya kuɗaɗen ƙungiya a harkar noma, ta hanyar karɓar gonaki su noma da kansu, siye, sarrafawa da siyar da kayan gonar kamar shinkafa, waccan suke siya a matsayin tsabar, sannan su sarrafa ta harda packaging su siyar ga mabuƙata, citta, auduga, da duk wani kayan Noma sun ba da muhimmanci sosai a wannan harkar kuma ana ganin cigaba tsawon wannan lokaci.

Haka zalika sun ƙoƙarta ƙwarai wajen samar da wuraren ayyuka irin na matasa kamar wurin kafinta, cafe, wurin gyaran mashin da mota da sauransu, wanda shi ma a hankali suke samar da su a mabanbanta wurare ta hanyar amfani da ribar kasuwancin da suke samu, da kuma tallafin da lokaci zuwa lokaci suke samu.

Sai kuma Abu mafi muhimmanci shine wayar da kan matasa, da samar musu da ayyukan yi, magana ta gaskiya sun kawo tallafi ga tsananin rashin aikin yi da matasan kan shiga, da waɗannan aikace-aikace na su,sai kuma rage tsamarin rikicin ADDINI da KABIKANCI da tunanin kawo haɗuwar kan matasan musulman, da Kirista da nusar da kowa ya san me ya je yi game da lamarin addinin, kuma su kansu matasan sun gaskata hakan, don haka a kullum suna alfahari da shugabannin ƙungiyar har ma wasu kan yi fatan da ma sune a matsayin gwamnatin jihar.

To a wannan lokaci da zaɓe ya ƙarato ne suka tsara wani abu da suke zaton insha Allah zai kawo musu mafita ga wannan ƙungiya, duk da dai mutane da yawa daga mashawarta sun soki tsarin amma dai daga ƙarshe suka ce ba zasu gwada, sannan a nemi taimakon Allah kawai.

Wannan tsarin kuwa shine miƙa gayyatar taro ga duka wani ɗan takara da muƙarrabansu ko da na kansilan mazaɓa ne, za kuma a miƙa saƙon gayyatar ta hanyar mabiyansa da ke cikin ƙungiya, haka ma ga masu hannu da shuni ga wanda zai iya, wanda suna tunanin a wannan lokaci da zaɓe ya ke kusantowa za su samu ribar wannan dabara ta su, daga nan suna kyautata zaton za su.

Kafin yanzu babu wanda suka taɓa neman taimakon sa da kansu face sai dai idan ya ga dama da kansa ya basu, walau don Allah da kuma cigaban matasan jihar ko kuma don wani kudirin zuciyarsa su dai ba su da sani akan hakan, amma wannan karon ko ba komai za su farfaɗo da ƙungiyar, kuma suna kyautata zaton a wannan lokaci ne za ta fara aikin da shine suka tsara.

Saboda haka a cikin ƙanƙanin lokaci aka tsara yadda komai zai gudana, tattaunawa da shugabannin ƙungiyar a matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu inda a ƙarshe aka fitar da rana, lokaci da kuma yadda komai zai kasance, kuma sai ga shi a wannan rana ana shirin gudanar da taron wanda duk wanda suka faɗawa wannan shawara ta su daga manyan masana da hangen nesa kan jinjina musu, sai dai abin da ake nusar da su shine, kamar yadda ƙungiyar ba'a ƙirƙire ta ƙarƙashin kulawar siyasa ba to ka da su sake ta koma hannun wani ɗan siyasa da niyyar cigaba da kula da ita, kawai su dage ka da wani ɗan siyasa ya cigaba da juya su, saboda ma kada ƙofar hakan ta shigo sai suka gayyaci taron gaba ɗaya jam'iyyun kuma a wuri ɗaya wato A.S.A SARAKI HALL wanda suke tunanin zai ɗauki duk adadin mutanen da suka halatta, don haka babu wani da ƙungiyar zata umarta da a zaɓa ko kar a zaɓa, za dai su tabbata sun wayar da kan matasa game bangar siyasa, da kuma zaɓen waɗanda suke kyautatawa zato, kuma suke tunanin zai kawo ƙarshen matsalolin su.

BILAL SHU'AIB MAGWAI shine matsayin founder na ƙungiyar kuma wanda mafi yawancin tsare-tsaren da ƙungiyar take tafiya a kan su shi yake samar da su.

Saurayi ne da bai wuce shekaru Ashirin da bakwai ba, yayi matuƙar yawa ya kai shekaru talatin amma kuma shi sai dai a kira sa genius wato ɗan baiwa idan dai ɓangaren kaifin basira ne.

Tun farkon rayuwar sa yana matuƙar son ganin cigaba a kowanne ɓangare na ƙasar, ba ma iya yankin sa ba, duk da kuwa kasancewar sa daga ƙauye ƙarami wanda ba'a san shi ba a ko'ina kuma a can cikin daji wato ƙauyen MAGWAI da ke ƙaramar hukumar DAILE, wacca ta zama itace ƙaramar hukuma ta ƙarshe dake kudancin jihar.

  Ƙauyen MAGWAI ƙaramin ƙauye ne da bai wuce gidaje ɗari ba, rashin haɗin kai tsakanin mabiya addini biyu, rashin kyakkyawar hanya ta shiga gari, da duk wani abu na rashin cigaba, farkon rayuwar bilal ya kasance mutum ne shi mara son shiga jama'a, hakan ya jawo masa raini ƙwarai a wurin sa'anninsa, tun lokacin da ya kammala secondary ɗinsa ya bukaci sa'anninsa da su kafa ƙungiyar da zata iya kawo cigaba a garin, da kawo ƙarshen matsalolin garin, wanda suke ci masa tuwo a ƙwarya ƙwarai da gaske, dariya suka yi masa gaba ɗaya saboda ganinsa da ake yi a matsayin wawa ko mara cikakken hankali, sai dai shi yana da wasu tsari da ya daɗe yana tunanin tabbas za'a iya cimma wata manufa idan aka bi a hankali.

  Da farko ya kawar da abin a ransa, amma wasu abokansa biyu su suka yi masa magana, bayan su ma sun yi nazari, Dukansu kuma musulmai ne kamar su, saboda haka suna buƙatar kiristi ɗaya wanda shi ma zai jawo hankalin wasu daga cikin ƴan uwansa, don haka da ƙyar suka jawo wani wai shi Daniel ɗanjuma cikinsu kuma ya fahimce su ƙwarai, daga nan suka kafa tushen ƙungiyar wacca a hankali ta samu mutane kimanin goma sha biyar a matsayin member.

  Da farko ƙungiyar tana ƙoƙari ne wajen dakile duk wani rikice da ya Kunno Kai kuma suna samun nasara ƙwarai da gaske, sai kuma shawarwari ga juna akan muhimmancin aikin yi, inda sukan haɗu su ziyarci mahaifin mutum ɗaya a cikin su tare da bashi shawarar samarwa da ɗansa abin yi tun a waɗannan ƙananan shekaru, domin hakan zai kare yaro matuƙa daga faɗawa kowacce irin mummunar hanya, kawai dai abin da ya rage shine samar masa da tsarin yadda zai gabatar da aka sama masa a matsayin aikin yi, da ba shi shawara akai, a haka har sai da suka ziyarci mahaifin kowa suka kuma karɓi shawarin su ƙwarai da gaske.

  Kafin wannan lokaci babu shago ko ɗaya a garin, komai ake buƙata sai dai a wurin mata masu sarowa kaɗan-kaɗan suna siyarwa, ko kuma a shiga ƙauyen dake kusa da su, idan kuma kana buƙatar abu dayawa sai dai kaje mazaɓar su wanda yake da tasar tafiyar 2km tsakanin su, wato GAYAR .

  Amma a cikin ƙanƙanin lokaci wasu daga cikin iyayen yaran suka fitar da kuɗi aka buɗe shaguna, wasu kuma jari aka basu su samu abin yi, ko wasu kasuwannin sa fara.

  Su a karan kansu suka dinga tsarawa juna yadda kowa zai amfanu da abin da aka basa, kuma cikin ikon Allah kowa ya fara ganin buɗi.

  Da akwai kuɗin da suka ware a karon kansu duk sati biyu, kuma alhamdulillah kowa yana ba da hadin kai, a haka suka gina ƙungiyar.

  A wannan lokaci ne ƙarshen shekarar suka ɗauki wasu kuɗade daga cikin waɗanda suka tara tare da sanya su a gona, da kuma siyan garmar shanu da kafin wannan lokaci babu ita a garin.

  A takaice dai kafin shekaru biyu sai da a sanadiyar wannan ƙungiya garin Jangefe ya samu cigaban da kafin wannan lokaci babu, da yawa waɗanda suka yi dariya sai gashi sun tsinci kansu a cikin ƙungiyar, daga nan da shawarin su aka fara ginin makaranta a garin, wanda daga ƙarshe suka miƙa ta ga ɗan majalisar jihar shi ma ganin sun fara da kansu ya ƙarasa musu, tare da samar da malamai wadatattu, sai kuma Abu mafi muhimmanci yadda sanadiyyar su aka dinga samun waɗanda suka dinga cigaba daga makarantar secondary wanda kafin nan waɗanda suka yi hakan basu taka kara sun karya ba, don bayan mahaifin Bilal ɗin malam SHU'AIB da ya zama likita da daɗewa sauran basu wuce biyu ba, wasu kuma sai sun fara suke dainawa.

  A takaice dai ƙungiyar sanadiyyar ta an samu hadin kai, har ya kai mutanen garin sun haɗu da kansu tare da harhaɗa kuɗi da samar da kayan aiki, da yin aikin kansa wajen fara gyara, da samar da culverts a garin, shi ma daga ƙarshe wani ɗan siyasar suka miƙawa bukatar su wanda yake matsayin ɗan majalisar tarayya, shi ma ganin kokarin su yace ai ba wai iya zuba birji za'a yi ba ga hanyar kamar yadda suka buƙata titi zai yi musu, an yi hakan kuma har an shigar da wutar lantarki karkarar.

..

Ku jiráye ni.




Ibrahim Aliyu Yakubu.