CIKI DA WAJE

Page 03

by @ibrahimaliey

CIKI DA WAJE


..

..


Ibrahim Aliyu Yakubu



Page 03

Bilal ya samu nasarar shiga makarantar jami'ar tarayya ta almawa inda ya zaɓi ya karanta sashen na'ura a matsayin abinda yake matuƙar burgesa, haka ma mafi yawancin sa'anninsa da suka gama primary tare sun yi iya bakin ƙoƙarin su don ganin cewa sun cigaba da karatun da mafi yawancin su suka dakatar Tun farkon shigar su makarantar secondary ɗin.

Anan ne kuma cigaba da karatunsa tare da tafiyar da shagonsa wanda mahaifinsa ya ɗauki nauyin buɗe masa shi tare da yarjejeniyar matsayin rance ne, shi da mahaifin nasa yayi haka ne don kada ya je ya yi ta kashe kuɗaɗen amma a tunanin sa idan yace da shi rance ne to zai dage ya kula da shagon daga baya sai yace ya bar masa, amma kuma tun da daɗewa ya biya shi kuɗinsa, batare da ɓata lokaci ba ya karɓa da niyyar ko taimakon sa ne yayi wajen ginin gidansa idan lokaci ya zo da kuɗin.

A haka ya cigaba da karatu, ya ƙware ainun sosai wajen sarrafa na'ura mai ƙwaƙwalwa wacca ya mallaka tun farkon shigarsa makarantar, har ma wasu kamfanoni kan bashi aikin ginin manhajar kamfanin su da sauran aikace-aikace, wanda ya kan yi cikin ƙanƙanin kuma ya samu kuɗi masu yawa ta wannan hanyar, haka zalika ilmin na'ura ilmi ne da ba ka da bukatar sai ka yi wa wani aiki domin samun kuɗi, kai da kanka zaka iya samarwa da kanka hanyoyi marasa adadi da zasu dinga kawo maka kuɗi masu yawa, to shi ma ba'a barsa a baya ba, domin kuwa a cikin ƙanƙanin lokaci har ya mallaki filin sa a cikin garin gayar wanda shi ma tun farkon fara karatunsa mahaifinsa ya koma can, saboda a asibitin garin yake aiki, shi ma anan ya mallaki filinsa har ya fara gini amma har zuwa wannan lokaci dai ana aikin ba akai ga kammalawa ba.

Idan ya zo hutu kuma aikinsa da system ya kan hana shi kwana a jangefen saboda rashin wadataccen network, amma ya kanzo su ɗauki lokaci da abokansa.

A shekarar ƙarshe da zasu gama suka ƙirƙiri ƙungiyar ALYDF inda yanzu ya fi maida hankali wajen yin aikace-aikacen sa duk da haka bai Hana shi aiwatar da ayyukansa ba da na'ura, kuma shine chif planner, CEO kuma chairman na ƙungiyar, a yau kuma ga shi za'a gabatar da taron da ƙungiyar ta ɗauki lokaci tana jiran zuwansa, har ma an turawa da kowa saƙon katin ta duk hanyar da aka san zai isa gareshi.

Har wannan lokaci da Bilal ya girma kuma mutum ne shi da bai cika surutu ba, murmushi na ɗaya daga cikin abinda ya zama alamarsa domin kuwa ba zaka taɓa ganinsa yana dariya ba, ko abin dariyar aka yi sai dai kawai yayi murmushi sannan ya Basar, shi dai halayyar sa daban ce, har ma wasu kan yi tsammanin girman kai ne da shi wanda abokanan sa suke ƙoƙarin karesa daga wannan tunanin na mutane.

Bai taɓa yin budurwa ba, duk da kuwa tun da ya fara jami'ar sa ƴan mata da yawa kan kawo masa hari akan suna sonsa amma bai taɓa kula su ba, ba zai dai wulakanta yarinya amma zai sanar mata da cewa bai shirya ba, ta yi haƙuri, kuma fah shi har yanzu bai taɓa damuwa da hakan ba, duk sa'anninsa da abokansa kowa yana da mata a daidai wannan lokaci wani ma har da ƴaƴa daya ko biyu amma ban da shi, wanda hakan ya sa shi kansa abin yake ba shi mamaki, har tunanin wai shi yaushe ne zai iya firtawa mace kalmar so ya ke yi, duk da kuwa ba wai bai taɓa ganin waccan yake so ba ne amma ta ya zai yi hakan ,?, Wannan shine babban ƙalibalen sa game da soyayya wato tsoron mota, yana matuƙar tsoron shiga cikinta duk da dai abokansa kan ce masa yadda yake tunanin soyayya ko ɗaya ba haka take ba.

To ku biyo mu dai ku gani ya ya zata kaya da Bilal a cikin wannan dogon labari da na ɗauki ɗamarar kawo muku shi..


* -------------------- *


ALMAWA STATE SECRETARIAT.

Qugin (siren) motoci ne ya karaɗe harabar sakateriyar jihar wacca aka gina ta shekaru kaɗan baya da suka gabata a farkon tenure governor saraki, sai dai ba'a ko dauki watanni biyar da kammala ta ba, wanda hakan ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta daga ƴan jam'iyyun adawa inda suke zargin gwamnatin da rashin adalci na gyaran inda za su zauna a matsayin office daga safiya zuwa dare shima banda ranakun asabar da Lahadi da ake lissafa su a matsayin weekend, da barin tituna, da makarantu a wargatse inda suka dinga bayyana cewa kuma da za'a yi amfani da kuɗin da aka gyara sakateriyar ba makawa zasu iya kawo ƙarshen duka matsalolin.

Bai yi magana akan hakan ba, duk da kuwa muƙarrabansa sun bukaci hakan amma yayi banza da abin saboda shi dai bai san abin da zai ce ba, saboda maganar ta su idan a ka yi duba na tsanaki tana a kan hanya kuma sune suka takura a gabatar da wannan aikin, Kasancewar tsohuwar sakateriyar ba laifi ya tsufa don an yi shine tun farkon kafuwar mulkin farar hula a jihar.

Don haka sai dai su ne suka dinga mayar da martani domin kare kansu a wurin wadanda ake so su ga laifin na su wato talakawa, duk da kuwa su ma waɗancan bai zama lallai idan su ne su wuce aikata kalar kuskuren da suke aibata jam'iyyar mai ci da shi ba.

Bayan gungun motocin da suka rako gwamnan sun gama shigowa cikin harabar sakateriyar bai wani jira an zo an buɗe masa ƙofar ba, ya buɗe yana mai fitowa saboda gaba ɗaya yau ɗin komai ɓata masa rai yake yi, yana da ayyukan yi masu yawa a gabansa, ga kuma taron da ya san dole za'a ɗauki lokaci ana yi wanda yake da muhimmanci a garesa, ga makarar da yayi, duk da kuwa bai saba hakan ba sai idan da akwai wata matsala.

Simple kaya ne a jikinsa, hula zanna sai kuma simple jamfa, a haka ya nufi shiga cikin sakateriyar kaitsaye yayinda ƙananun ma'aikata kan ƙaraso su gaisa, shi ma bisa dole kan ƙago murmushi tare da amsa musu cikin sakin fuska.

Duk ƙananun ma'aikatan sun san saraki mutumin kirki ne ba kamar yadda da yawan talakawa kan aibata shi da zagin shi ba, walau kai Hausa ne ko wata kabila da bata shi ba, ko kuma kirista ne ba zaka taɓa ganin banbancin mu'amalarka da shi ba.

Tun da ya shigo ya fahimci da yawan mutanen sun tafi wurin taron saboda rashin motoci a harabar sakateriyar kamar yadda take kasancewa kullum, amma dai tun daga nesa ya hangi su hon. Yohanna Ezekiel wanda yake a matsayin chief of staff ɗinsa, sai kuma Vice ɗinsa ALHAJI DAUDA MALALAI wanda da alamu shi suke jira da har matsuwar su da zuwan na sa ya sanya su fitowa kofar sakateriyar, Dukansu fuskarsu kuwa babu alamun mutunci da sassautawa da alamu sun ƙunshi haushinsa.

Haka kawai ya tsinci kansa da yin murmushi, har ya zuwa lokacin da ya ƙarasa garesu tare da gaisawa da su ɗaya bayan ɗaya, yana mai basu haƙurin rashin zuwansa da wuri har ya ga alamun jiransa ma suke yi.

"Haka ne Mr. Excellency, ai tun ɗazu muke jiran zuwan ka halan dai wata matsalar ce ta tsayar da kai." Yohanna ya faɗa yayinda suke jerawa suna masu nufar office din gwamnan, shi ma Dauda malalai haka ya bi bayansu

Shiru yayi batare da ya bashi amsar tambayar sa ba, ya ce " yau ga taron waɗannan yaran ga kuma na ga alamun ayyuka sun yi mini yawa me ka shirya zai faru ne."

Murmushi Yohanna yayi tare da kallon Alhaji malalai wanda sai da gwamnan ya sawa kallon Ayar tambaya, amma sai Yohanna ɗin yace "Mr. Excellency mu ƙarasa sai mu samar da mafita a tsanake."

Shiru yayi batare da ya ƙara cewa uffan ba yayinda ƙwaƙwalwarsa ta harba wata duniyar tunanin ta daban har ya zuwa lokacin da suka ƙarasa office din, dukan su sallama suka yi harda Yohanna kasancewar zamansa cikin musulmai idan har ba ka san cewa shi ba musulmi ɗin ba ne rayuwa da shi ba zai taɓa sanyawa ka gane hakan ba, hatta rantsuwa, sunan Allah yayi mugun zama a bakinsa, amma sai dai babu alamun hakan zai nasabta shi ga karɓan gaskiya, domin kuwa shi kaɗai ne ya san abinda ke zuciyarsa game da yadda yake jin tsanar musulmai, dama kam mun sani dai su ba zasu taɓa son mu ba face sai lokacin da muka zama tamkar su.

Gwamna yana shiga katafaren offishin nasa da aka ƙawata shi fiye da zato da dukan kayan na'uin ƙawa, haka zalika ofishin ya rabu ɓangare biyu wato wurin da zai zauna ya huta a lokacin da baya aiki wanda ke ɗauke da kujeru Waɗanda ake kira wing chair, ga wadatacciyar iskar A.c da ke kaɗawa har ka kan iya manta duniyar da kake idan ba ka saba shiga wurin ba, da akwai tv da kayan more rayuwa, duk da zaka samu a parlor ko wani abu mai kama da haka.

Sai kuma ɓangaren aikinsa wanda shima ya ƙawatu, don haka yana shigowa can wurin aikin nasa ya wuce yana mai zama a wurin da yake mallakinsa.

Su kam a tsaye suka dakata har sai da ya basu umarnin zama kamar yadda ƙaidar office take.

Gaisawa suka ƙara yi kafin gwamna ya kalli Mr. Yohanna domin jin ƙarin bayani kamar yadda suka saba ya dakatar da su wanda shi yayi hakan ne don su yi saurin zantawa kafin su zo an samu mafita amma yanzu ba za ya ji ta tashi ɗin ai hakan ba laifi ba ne.

Kallon malalai ya ƙara yi a karo na biyu sannan yace "yallaɓai ai yanzun nan muke tattauna wannan magana da malalai, har ma yake ba da shawarar da ni ma na aminta da ita, ƙwarai da gaske amma sai dai yadda ka ce.".

Ƙura masa ido gwamnan yayi tamkar mai nazarin wani abu har sai da ya tsargu, yanayin fuskar sa ya fara canzawa daga murmushin da zaka iya kiransa na yaƙe zuwa cin serious don fah kar ma dai gwamna ya kawo raini don ya ga take-takenaa kenan.

Daga can gwamna ya ja dogon numfashi tare da yin murmushi sannan yace " okay to Mr Yohanna faɗa min me kuka tattauna kuwa?.".

"Yawwa abin da kawai muka zanta shine da yau tunda ayyukan sun maka yawa, kuma kai ma kana da tabbacin da cewa zuwa gobe ake buƙatar komai ya kammala,me zai hana kawai ka zauna ka yi aikin ka, a office idan ya so mu da malalai sai mu wakilce ka, da ofishin gwamnati ma dai gaba ɗaya." Ya faɗi cikin dogon bayaninsa.

Tun da ya fara bayanin gwamna ya fahimci da akwai wani makircin da suke shiryawa a ƙasa amma ba za ya bi su yaga iya ƙarshen gudun ruwansu.

Kallon malalai yayi tare da cewa " malalai haka yayi."

Murmushi malalai yayi wanda tun farkon shigowar sa bayan gaisuwa bai ƙara furta ko kalma guda ba, tunani kawai yake a ransa yadda yai sakaci waccan lokacin har ya amince da ƙudurin jam'iyyar ta su, na ɗauko wani bare da bai taɓa sanin siyasa ba, ya hau takarar akan wani banzan ƙuduri na su da zasu iya cewa ya cika, amma inda gizo ke saƙar shine ya fahimci gwamna ya fara canza salo tun lokutan baya wanda hakan ke nuna da akwai matsala dangane da abubuwan da suke shiryawa.

Duk rintsi yana so ya kasance wannan karan shine a matsayin ɗan takarar gwamna kuma zai yi iya bakin ƙoƙarin sa wajen ganin haƙan sa ya cimma ruwa na ɗarewa gwamnan almawan komai rintsi da tsanani, yanzu abinda yake shiryawa shine yadda zai tabbatar shine aka ɗora a matsayin ɗan takarar amma bai taɓa fara tunanin rashin yiwuwar hakan ba sai a ƙarshen tenure ɗin.

Alhaji malalai baban mai faɗa aji ne a ƙasar, ya riƙe nuƙamin speaker har zango biyu, kafin ya wuce ɗan majalisar tarayya na MALALAI/SHIRMA CONSTITUENCY, sai kuma shekarar da ta gabata ya buƙaci gwamnatin jihar sai dai aka dakatar da shi tare da alƙawarin sanya shi a matsayin VG wanda hakan ko ɗaya bai burge shi ba, duk da ya ci karensa ba babbaka amma zai fi so ace shine dai a matsayin.

Idan ka zo ɓangaren ilmi da gogewa ba makawa Alhaji malalai yana da gogewa, ya kuma yi degree a fannin ɓangaren ruwa, a ɓangaren addini ma ba'a barsa a baya ba, amma hakan bai hana shi tsula tsiyar sa ba.

Shi babban tunaninsa a daidai wannan lokaci shine ganin cewa ya cimma manufar sa ta zama ɗan takarar jihar, sai kuma Yohanna a matsayin VG ɗinsa kamar yadda suke shiryawa.

"Mr. Excellency hakan shine ya dace, wannan shi idan ya wuce yau ɗin ya wuce kenan za kuma a iya samun matsala, amma maganar taro ko daga baya zaka iya zuwa har ma ka bayar da gudunmawar ka, sannan kuma Mr. Excellency na tabbata za'a haska duka abinda zai wakana a ɗakin taron live hakan zai baka damar ganin duka abinda zai wakana."

Girgiza kai gwamna yayi alamar gamsuwa da bayanin nasa kafin yace "Tom shikenan za ku iya tafiya kawai, saboda na san yanzu isowar ku kawai ake jira."

Daga nan sallama suka yi masa tare da fita daga ofishin shi kuwa ya bi su da ido yayinda murmushi ya suɓuce daga fuskarsa, kafin ya taɓe bakinsa da girgiza kansa ya fara ƙoƙarin duba jadawalin ayyukan da zai gabatar kamar yadda yake a tsare.

...

Ku jira ye ni.

Comments ɗin ku ƙwarin gwiwata, don haka ku hanzarta yin sharhi akan wannan labari da zai cigaba da zuwa muku daga lokaci zuwa lokaci.



Allah ya taimakemu


Ibrahim Aliyu Yakubu.