Kawaye ne guda biyu masu so da kaunar juna kwatsam sai wani babban al'amari ya gibta a tsakaninsu, a bangaren guda cin Amana, yaudara, son Kai da Kuma hakuri, ku biyoni danjin yadda zata kaya

BABI NA BIYAR

by @mamannour

_*YAN UWAN JUNA*_

   _(zumincin mu a yau)_



               *NA*


*_RUKAYYA HARUNA(MAMAN NOUR)_*

       



*_✍️ HAZAKA WTITERS ASSOCIATION_*



*Page 5*



"Aziza dan zo mana" yana fada ya yi hanyar kitchen, babu jimawa ta biyo shi tana yamutsa fuska. Kallonta ya yi zuciyarsa fal takaici sannan ya fara magana cikin lallashi. "Haba Aziza ai ko wani daban na kawo gidan nan zaki bashi ruwa da abinci balle mahaifiyata." Dan murguda baki ta yi sannan ta ce.


 " Kajimin bawan Allah! Nikan Dr wani irin hali kake so ka sakani a ciki ne? To ma banda abinka yau ka fadamin babarka tana hanya ne? To ni banyi girki ba."


Bai jira ta karasa maganar na ya fice daga gidan zuciyarsa kamar zata fito waje. A kafa yake tafiya tsabar kunar zuciya, sau tari yana danasanin auren Aziza, amma na yau yafi na kowanni lokaci. Sam bata daraja mahaifiyar shi, a lokacin baya ya tabbatar auran kwadayi ya yi da Kuma son zuciya, amma a yanzu kullum tuba yake gurin Ubangiji yana nadama a kowani lokaci. A sannu ya karasa wani restaurant da yake gaba da link dinsu kadan, order ya yi na tuwon semo da miyar agushi, sai jelop rice da soyyayen kifi. Babu jimawa aka hado masa sannna ya fito ya hau napep ya karaso gida. A inda yabar Baba anan yazo ya sameta Islam da Aslam suna gabanta sai muzurai suke, da dukkan alamu yinwa suke ji. Ganin baban da ledoji ya saka suka fara murna suka tafi a guje suka karbo. Kowa ya dauki abinda ransa keso aka fara wadaka, sosai yaran suke cin abincin domin sunji yinwa sosai, Baba itama tuwonta take ci cikin kwanciyar hankali. 

  Aziza na kwance a daki tana tunanin yadda zata yi amfani da magungunan da boka ya bata ta tsinkayi muryar Islam tana cewa. "Dady abincin ya yi dadi yafi na Kaka dandano." Dukkansu dariya suka saka, Baba ta ce "Imirana kajimin Ja'irar yarinya, to nima bari nayi miki gori, ai nawa girkin kika ci kika girma ehe." Dukkansu suka Kuma shekewa da dariya, ana haka Aziza ta fito ba kunya ta zari takeaway guda ta hau ci, ita lumshe ido ta hau yi domin itama yunwa ta ratsata.


Yau kwanansu inna shida, amma babu wani abu daya canza a gidan, a takaice dai inna ita take girkin safe rana da kuma dare. Domin ta lura idan har ta yi zaman jiran ganin kwano daga Aziza tabbas tsakanin ita da jikokinta ciwon yunwa zai kashe wani. Duk wannan diramar da ake yi Dr Imran bai sani ba, Baba itama bata bada wata kofar da zai gane ita ke girkin gidan ba, domin gidan ya dade da rasa yar aiki, saboda masifar uwar dakin nasu, duk wanda yazo aiki tofa ko sati biyu bazai rufe ba yake guduwa, aiki kamar zai kashe mutum, ga shi bata girki Kuma bata bari su yi, dole tasa duk mai zuwa neman kudi gidan hakan bata samuwa.

 Yau Dr ya dawo da wuri ya shigo cikin gida yanata fara'a, domin yanzu ya dena damuwa da lamarin Aziza, ganin mahaifiyar shi da yaransa kadai yana saka shi nishadi, dadin dadawa yana samun wadataccen abinci, duk a tunaninsa gimbiyar ce take yi. A parlour ya tarar dasu Aslam suna kallo, tambayarsu Inda Auntynsu take suka ce tana dakinta, bai tambayi Baba ba dan yasan itama tana daki, dakinta ya nufa yaga wayam hakan yasa yazauna zaman jiranta yana tunanin tana tailet, rashin jin motsi a cikin toilet yasa ya tabbatar bata ciki, fitowa ya yi parlour gurin yaran sannan ya tambayesu, Aslam ya ce.

 "Oh Kaka tana kitchen din baya tana mana girki." Zaro ido ya yi sannan ya Kuma maimaita kalmar kitchen din baya a zuciyarsa, a sanin shi dai ba'a amfani da wannan kitchen din sai lokacin sallah sabida aikin nama, domin itace aka amfani da shi a wajen. Da sauri ya fito harabar gidan kitchen din ya nufa zuciyarsa cunkushe da takaici. A zaune ya ganta sai faman hura wuta take tana hawaye, domin itacen mai hayaki ne sosai .

  "Baba!" Ya fada zuciyar cike da takaici, da hanzari ta goge hawayen fuskarta tare da tasowa .

 "Ah ah Imirana yau da wuri haka? Sannu da zuwa ya Kuma aikin?"


Bai amsa mata ba tsabar takaici ranshi a bace ya fara magana.

 "Baba har tsawon wani lokaci kika kai kina girki a gidan nan?" Murmushi ta yi sannan tace

 "Ah ah nifa yau ne naji ina sha'awar dambu, kuma naga Zogalen gidan nan ya yi ganye sosai shine yasa na yi." Tunda ta fara magana ya zuba mata idanu Yana son fuskantar gaskiyar magana, tuni ya gano Baba naso boye masa wani abu ne, fatan gamawa lafiya ya yi mata sannan ya koma ciki. Dakin Aziza ya nufa zuciyarsa kamar zata bullo waje dan takaici, a zaune ya ganta gaban mudubi ta jingina wayarta tana video, ba but shakka yasan bidiyon tiktok take yi, cikin zafin rai ya fara magana.

  "Nikan Aziza yaushe zaki gane annabi ya faku ne, yanzu Dan..."

  Da hannu ta yi masa alamar ya yj shiru sannan ta daura da cewa. "Haba Dr friends dina ne suka ce tani musu new update gashi ka batamin bajet."


Wata tsawa ya daka mata wadda tunda suke bai taba yi mata irinta ba, idanunsa sun yi jawurr kamar garwashi. "Ashe iskancin naki ya wuce inda nake zato? Wai ke baki san darajar Baba kike ci nake saurara miki ba, amma wai kina gidan nan take girki da kanta bama da gas ba da itace, to bari Kiji duk da a shekarun baya ta yi girki da itace amma a yanzu tafi karfin haka, domin Allah ya horewa danta abin dawainiya da ita, ai wannan iskancin banza ne...."



"Kaga Imran dan Allah saurara min, bana son maganar banza. To dan nace karta kara shigarmin kitchen shine zata je ta fada maka, eh ni nace karta kuskura ta kuma shigarmin domin ba iya amfani da kayan cikin kitchen din ta yi ba, haka kawai taja min asara tunda kauyanci har yanzu bai barta....."

  Tauuuuu wasu tagwayen mahaukatan mari Imran ya zauke mata, tare da kwarfeta ta fadi kasa. Sosai yake dukanta kamar tsohon mahaukaci, jiyo ihunta ne yasa Baba ta shigo dakin da gudu tana ah ah Imirana ba halinka bane Dan Allah ka kale diyar mutane. Sai da Baba ta yi karfin zaki sannan ta iya bambare Aziza a hannunshi, ya yi mata jina jina tuni fuskarta ta canja kala, fizge hannunta ta yi daga na baba, cikin tsiwa ta cigaba da magana.

  "Hankalinki ya kwanta, kin zama tauraruwa mai mutsiya...." Wani Marin ya kara kwasheta da shi muryar shi na rawa hawaye na gangarowa a kumatun shi ya furta kalmar Aziza kije gidanku na sakeki saki daya." Sulalewa ta yi kasa tana sakin kukan takaici, duk irin iskancin da take mishi bata yi zaton zai iya sakinta ba, domin boka ya bata tabbacin babu saki a tsakaninsu. Baba tana hawaye ta fara magana.


"Imrana baka kyauta min ba, dana san abunda zanzo na riska kenan wallahi daban zo ba, na zama silar lalacewa Aure nikan da wani ido kake son na gana da Ubangiji na." Itama kukan take sosai, shikuwa wani karfin zuciyarsa ta kuma yi masa, a yanzu gani yake idan har ta Kuma wata kalma guda daya komai sanyi ce sai ya kuma sakinta, cikin tsananin bakin ciki ya ce.


"Aziza na baki minti goma, idan kika Kara koda minti daya ne a gidan nan wallahi wallahi Allah daya kenan sai na Kuma yi miki wasu sakin." Yana fada ya fice daga dakin ya koma parlour yana duba agogo, cikin tashin hankali ta zari mayafinta da wayarta sai jakarta dake gefe tayi waje da sauri tana ta shiga ukunta.



Hahahaha ashe dama Yar iskar banza ce, tab nikan idan nasan da matakin da zaka dauka wanda zai sakani damuwa bama hawaye ba, ai wallahi bazan fara ba. Amma na sarawa Imran na dade Banga namiji irinsa ba, uwa ai ba abun wasa bace. Naso shegiyar ta kai minti sha daya a Kara mata biyu🤣🤣🤣


Gidansu Kareema ta nufa hankalinta a tashe sai kaka take zuciyarsa kamar zata fito waje. A tsakar gida ta sami Kareema tana wanke wanke, tana ganinta tasan Babu lafiya, duk da suna kawance sosai Aziza bata fiya zuwa gidansu Kareema ba, koda kuwa matsala ta yi mata yawa sai dai ta kira a waya ita tazo su warware komai. Cikin daki suka shiga Aziza ta juyewa Kareema komai, sosai ta nuna mata hankalinta ya tashi, amma a zuciyarta farin ciki ne marar misaltuwa. A nan Kareema ta bawa Aziza shawarar ta kwana a gidansu idan yaso da sassafe sai ta kama hanyar kano.



Matafiya a sha hanya lafiyaaaaa



Maman Nour taku ce

***