1
*👑PRINCE SALMAN👑*
by teemarh cool
*Elegant online writer's*
Bismillahi rahamanirrahim
wannan littafin free ne amma rashin comments,zai sa na mai dashi na kudi,natsara labarin ban yadda wata ko wani ya juyamun labari ba, sai da izini na.
wannan littafin sadaukar wane ga masoyana, kuma masoyan Elegant online writer's.
page 1
_______Zaune take tana duba takardar dake hannunta,ajiyar zuciya ta sauke kana ta ajiye takardar kan tabarmar da take zaune akai, ta tashi cikin nitsuwa ta buta ta shiga banÉ—aki,
tana ganin shigar ta bandakin yasata fitowa É—aki da sauri ta É—auki takardan ta fara karantawa kasan cewa da hausa aka rubuta,dariya tasa mai sauti tana cewa "Umma fito ankuma halin,"fitowa Umma tayi cikin sauri jin taji abun da yake faranta mata rai,wanda yayi daidai da fitowar Tasleem daga ban É—aki,Husnah ce tace" kinji kunya Tasleem anrasa mashin shini shima wannan din ma ya gudu"tayi mgnr cikin tsantsar farin ciki, Umma ma nataya ta sanda sukayi mai isarsu sannan Umma ta kalleta a yatsine tace" me kika tsaya kallo yar tawa kikeso ki cinye da manyan idanun naki kamar na mayu,tayi mgnr tana jan Husna ciki daki tana cewa" karta cinyeki naga ta kureki da idon nan nata da bata kiftawa. tsakin butar hannunta Tasleem tayi tashige É—aki da gudu tana kuka, saman gado ta kwanta tana rera kuka mai ban tausayi, dahaka har bacci ya dauke ta.
Shigowa gidan Mama tayi da sallama a baƙin ta,"jin an amsa mata ciki-ciki yasata yin tsaki ta shige ɗakinta tana cire mayafinta,ganin Tasleem kwance ne yasata karasawa kanta da sauri dan tasan Tasleem bata baccin rana sai dai in batada lafiya,"gani tayi idonta sun kubbura fuskarta yayi jajir kasan cewa ita fara ce, jikinta yayi zafi sosai,
hankalin mama yatashi sosai,"fita tayi sakar gida dan ta hura huta ta daura girki kafin Tasleem ta tashi,"
"Umma ce ta fito tana cewa ashe kin dawo"eh Mama tace rai a ɓace,dariya tayi kasa kasa tana cewa"ah a ina Tasleem din keda kanki zaki hura hutar? "shiru tayi bata kulata ba dan batada lokacin magana yanzu,
Umma ganin ba fuska tayi É—aki abunta,
ta gama girka abincin ta Tasleem bata tashi ba dan haka tashiga É—akin ta taso ta,
mai ya same ki Tasleem?"shuru ta ɗanyi kana tace mama yaushe kika dawo ne?"kallon ta Mama tayi tace ki amsamun tambayata nace,ganin ran Mama ya ɓaci yasata ne yasata sa karwa mama tana cewa,"Nabil ne ina dawowa daga school shine ya bawa abokin sa letter ya bani,"
daga nan kuma sai ta saki kuka mai tsuma zuciya,
"Umma itama jikin ta yayi sanyi amma bata nuna mata hakan ba"
dukkan su shiru sukayi na naÉ—an wani lokacin,
"kiyi hakuri Tasleem wannan jarabawane daga Ubangiji,kiyi kokarin cinyewa dan allah Tasleem "
cizan laɓanta tayi tare da girgiza mata kai"
yauwa tashi kije kiyi wanka
tashi tayi jiki ba gwari ta fita danyin wanka,
tattare É—akin Umma tayi,tare da zibawa Tasleem Abinci.
*********************
*Borno state*
fadar Shehu Muhammad Ali
shiru akayi dukkan fadan "da alama jiran fitowar sarki akeyi"
"sai da aka dauki wajen 20 kafin nan sarki ya fito cikin kasaita yake tafiyar cikin izza da mulki,karasowa yayi ya zauna akan kujeran da aka tanadar masa"gaishesa suka farayi tare da sun kuyar da kai, daga musu hannu yayi"
fadar ce ta sake shiru sai da aka jima a haka kafin sarki yace…....!
Comment and shared
By teemarh cool