AZIZAN BABA

Episode 16

by @zinariya0102




_________________Matar maigari da ta dawo daga asibiti ta na tafiya a hankali ga yunwa ga ƙishirwa, "ɗiii,ɗii!ɗit!ɗit!ɗit, ba ta yi aune ba ta ji anyi ciki da ita, saura kaɗan ta faɗi, "ke AZIZA ni kika bige wallahi sai na je har gidan ni za ki yi wa ɗiban albarka" 

Bata san ma tana yi ba, garam ta banka gida, Baba Tabawa na banɗaki ta ji shigowar AZIZA, Inna Gaji da ke zaune tana kaɗin audiga ta ce"to bisimillahi ke da wa?" AZIZAN BABA ta ja ta tsaya ta ce" ba su Lantana ba ne da wata" Inna Gaji ta ce" au watukun ba ta ji abinda maigari ya faɗa ba ko, ba zan yarda da wannan ba kuma, ina ita ina ke saboda Allah".


Baba Tabawa ta ce"ina alkakin?"

AZIZA ta ce "ba tare ni sukayi a hanya ba kuɗin ya faɗi" to ina kwanon ?" Baba Tabawa ta faɗa.

"Yana can ai"


Inna Gaji ta ajiye kaɗi, ta ja zani a jikin ƙofa ta ce "wajen maigari zan je, banga wanda zai hana yarinya fita ba ".Tayi soro karo sukayi da Binta uwargidan maigari.


Inna Gaji ta ce" sannu da zuwa Yadikko shiga ciki"

Binta ta ce"ƙarar AZIZAN BABA na kawo" Inna Gaji ta ce" kiyi haƙuri do Allah, daman can gidan zanje kai ƙara" Binta ta ce "haba Gaji yarinyar nan fa saura kaɗan ta kadani a titi garin gudun" 

Baba Tabawa ce ta tawo soron ta ce" ba dai ta ka da ke ɗinba ko?" Binta matar maigari ta hau masifa, Baba Tabawa ta na ramawa, Inna Gaji ta rufe ido ta ce Binta ta zo har gida ta hau su da faɗa.



Abunka da ƙauye mata suka fito akayi cahh a ƙofar gida ana faɗin Binta bata kyauta ba, dan tana taƙama da maigari sai ta zo har gida ta ci wa mutane mutunci, abu kamar wasa, rigima ta ɓarke tsakaninsu AZIZAN BABA ta na ɗaki ta janyo kwanon fura ta kama sha, ko a jikinsa.


Gaba ɗayansu aka nufi wajen maigari har da shaidu.Inusa yaron maigari na niyyar zuwa dan ɗauko AZIZAN BABA, ya ga su Inna da Matar maigari da zugar mutane an tawo.


BABA da yake zaune yana kallon ikon Allah, dan Lawisa da Babarta ne suka kawo ƙarar AZIZA a gaban BABA, ganin wai wannan ƙatuwar ce, wai aka ce AZIZA ta buga ya cika da mamaki, yana ji aka ce a ɗauko AZIZA bai tanka ba, yasan halin AZIZA da su Inna ko maigarin ne ya je ɗauko ta ba ba shi zasuyi ba,sai yaga wani yaƙin daban kuma.


Gaba ɗayansu suka zauna a gaban maigari, Matarsa,Maigari ya ce, ya akayi?" Binta ta ce" ranka ya daɗe AZIZAN BABA ce ta hankaɗe ni a kan hanya, shi ne na kai ƙararta gida,amma da ke waɗan nan ba mutanen ƙwarai ba ne suka hayayyaƙo min za su cinye ni"


Inna Gaji ta ce" ke Binta ki iya bakinki, kaf zuri'armu wallahi babu maye, kin kawo ƙara an baki haƙuri to me kuma kike so?"

Maigari ya ce" yanzu akan AZIZA kuke wannan abun saboda Allah" 

Baba Tabawa ta ce" idan kunyi haƙuri ma ta kusa bar muku garin ta huta"

Maƙota suka hau faɗin" a gaban mu Yadikko ta shiga gidan ta hau yi musu ɗiban albarka" gaba ɗaya aka bawa Binta rashin gaskiya, Maigari sai kunya yake ji, a ce wai yau da matarsa ake sulhu a ƙofar gida.


Nan aka ba wa su Inna Gaji haƙuri, sannan ta ce " ranka ya daɗe daman nan zan zo, akan Lantana ƴar wajen Malam Barau mai faskare" 

Maigari da sauran jama'a aka nutsu dan jin me ya faru.


BABA ya ce "au watukun kenan ba ta rabu da yarinyar nan ba, ina anan nan aka yi musu tsakani, to Allah ya sa a gaban Aminu akayi wannan abu, shi ma ya san da hakan"

Maigari ya ce" Inna Gaji me kuma ya haɗa su?" sai Inna Gaji ta hau inda-inda dan ba ta san ko mene ne ya haɗa faɗan ba.

"saboda Allah ace ba dama yarinya ta fita waje daidai da aike sai ta rarakota ta hanata sakewa garin nasu ne su kaɗai?" take maigari ya sa a kira Lantana, Lawisa ta ce" wallahi ita ce ta fara tsokanarmu muna tafiya a hanya" BABA ya ce "ubanme tayi muku iye?"

Lawisa ta ce"dariya take yi mana, kuma a tambayi su Amaduduwalle"

"dariya wace irin dariya" Maigari ya faɗa yana jiran amsa, Lawisa ta ce"muma ba mu sani ba kawai dariya take yi mana" aikuwa sai a ka hau Lawisa da faɗa ana faɗin tsarguwa ne sukayi ƙila ba ma da su take ba, rashin wayewa ya sa Lawisa kasa kare kanta.



BABA ya ce" ashe ma ita ku ka cuta,shi ne kika ɗauko wannan yagwalgwalɗin taki kawo ƙarar ƙaramar yarinya" 

Nan aka sulhunta ita ma Lawisa aka ce babu ita babu AZIZA, aka ba wa su Inna haƙuri suja tashi suka koma gida.



Da magriba BABA na zaune Malam Yusuf ya aiko da saƙon rubutun AZIZAN BABA, nan BABA ya dinga murna ya na faɗin, dole in dafaki da dafa'i saboda halin mahassada, ya shigo gidan yana kiran Inna Gaji.

Gaji zo ga rubutun nan na AZIZA ne maganin sammu da makaru ne" AZIZAN BABA ta take kwance akan cinyar Inna Gaji ta riga Innar fitowa.


Wangwale wawulan bakinsa BABA yayi ya ce" zo ki fara sha tun yanzu saboda tsaro AZIZAN BABA ta karɓa ta ce "ni ba Inna ce zata ajiye ba Baba zan bawa" 

Baba Tabawa da take ɗakinta ba'a neme ta ba, jin abinda AZIZA ta faɗa sai taji daɗi.


BABA ya ce "yo ai duk ɗaya ne, Tabawa ke Tabawa zo ki karɓi ragowar ki ajiye mata" ta ce "to Malam" a tare da Inna Gaji suka fito.


Bayan AZIZA ta sha, aka bawa Tabawa.

Inna Gaji ta gyara zama ta ce"yauwa ni kam Malam wai da gaske kake maganar komawa gidan Ɗansu nan da kayi?" BABA ya ce "ƙwarai kuwa Aisha tunda AZIZAN BABA ta furta tanaso to kuwa in sha Allahu zamu koma ko AZIZAN BABA".

Kai ta ɗaga tana murmushi, Baba Tabawa ta ce" anya kuwa malam, ni da za'a bi ta shawarata da akaita ta kwan biyu acan, amma ace gaba ɗaya a koma maraya da zama Malam wannan abun kuwa anya" 


Inna Gaji ta ce"kinga Tabawa idan ba za ki koma ba, ai ba dole sai kiyi zamanki anan ɗin" BABA ya ce 'barta Gaji, barta ta gama kinibibin nata, anya kuwa Tabawa ba so kike ki raba ni da AZIZA ba, anya kuwa, ke banyar da da ke ba, akwai abinda kike kitsawa a ranki" Tabawa ta hau rantse-rantse Inna Gaji ta ce "hmm wai sai yau ka san halin wannan matar, kai dai bar sumu-sumu macijin sari ka noƙe" AZIZA da hankalinta baya kansu, tunani kawai take, da sauri ta ce" BABA, kasan me Baban birni ya ce min kuwa?" BABA ya ce "a'a me ya faɗa?".


Ƴar dariya tayi ta ce" ya ce min idan muka koma birni har ɗakin Allah zai kai ni, kasan ɗakin kuwa hmm wanda yake cikin kallo-kallo fa"BABA ya ce "kai ma sha Allah, ashe Hajiya AZIZA ce anan" Baba Tabawa ta tashi dan shiga ɗakinta ta gyara shimfiɗa, AZIZAN BABA ta yi sauri ta tashi, ta ce " sai da safe mun tafi" BABA da Inna suka ce" har an gama hirar kenan"suka shige tare da Baba Tabawa, kaya ta cire mata ta sa mata marasa nauyi ta hau gado ta yi kwanciyarta hankali kwance,dan ta manta da abinda ta yi yau gaba ɗaya.





KANO 



"Ke fa babbar mace ce, Khadijatul kubra, kiyi koyi da halin mai sunan mana ba ta fushi haba uwargida sarautar mata" Mami ta yi murmushi ta na ƙara kau da kai, Daddy ya kuma ce wa "wai duk fushin ma na me ne ne?"

Mami ta ce "yanzu Alhaji ka na gani a ka kusa hallaka min ɗana, abun kuma ya koma har a sa ƙaramar yarinya, wannan wace irin ƙiyayya ce haka danginka suke yi mi ni tunda ka aure ni suke nuna min rashin kauna, ni idan ba ta su ba ce su Abdul-AZEEZ ai nasu ko?" sai ta hau kukan kissa.


Daddy ya rasa abinda zai ce mata, sai haƙuri yake bata, ya na nuna mata ta daina yarda da maganar yara, cikin ƙunar rai ta ce" ai dai kasan Abdul-AZEEZ ba yaro ba ne, daman tun da na haife shi ake baƙinciki"

Daddy ya kai zuciyarsa ne sa ya ce" Hadiza ki daina ganin laifin dangina, ni nasan AZIZA ba wanda zai sakata hakan, akwai abinda ya haɗa su shiyasa kika ga har tayi haka, amma na ce kiyi haƙuri,a bar wannan maganar" 


Mami ta ce "ai shikenan, an dawo lafiya" sai yanzu hankalinsa ya kwanta ya amsa, nan suka hau hira, cikin hirar ne yake sanar da ita, dawowar su BABA garin kwanan nan, ba ƙaramin tashin hankali ta shiga jin abinda ya faɗa, ta ce" ke nan sai da ka ɗauko su ko, Allah ya kawo su lafiya" ta shanye damuwarta.




Daddy ya dinga yi mata lissafin irin abubuwan da ya kamata ya sa a gidan kafin BABA ya sa lokaci.

Yaƙe kawai take har ya gama lissafinsa.

Ya tashi ya nufi ɗakinsa, yana faɗin sai kin zo.




Yana fita ta miƙe ta dan na uban ashar " kutumar uba!!! watukun dawowa za suyi dan su samin ido, to wallahi ba su isa ba, ni kam na shiga uku, da waɗan nan tsofaffi, dan bala'i sun ƙi mutuwa, aikuwa ba ku isa ba , zuwan ma bazan bari kuyi ba wallahi" 

Sai da ta gama saita ɓacin ranta, sannan ta nufi ɗakin Daddy.




Abdul-AZEEZ kuwa har ya kwanta bai dawo normal ba, duk juyi da ɗaukar fansa a ransa, bai taɓa zaton haka yarinyar ta shahara da rashin mutunci ba.



Ta shi yayu zaune ya na ta saƙa abinda zai yi mata wanda har ta bar duniya ba za ta manta ba, duk abinda ya ce zai yi sai yaga ba shi da lokaci, tafiyar nan da zai yi ba za ta bari ba, dole ya ajiye komai har sai ya dawo daga Spain..........




Zinariya ce✍🏻