AZIZAN BABA

Episode 17

by @zinariya0102




________________Kashegari da wuri Mami ta tashi, ɗakin Abdul-azeez ta nufa dan ganin ya jikinsa, knocking tayi ta na faɗin "son, my son are you okay" Abdul-azeez da ya ke ta baccin safe ya ji muryar Momi sama- sama cikin bacci.

Tashi yayi yana amsawa daga shi sai boxer ya buɗe ƙofar, Mami ta shigo tana duba jikinsa da fuskarsa, ya dawo normal babu komai, ya ce"good morning mami" Mami ta na shafa fuskarsa tana duddubawa.

Kiss ya yi mata yana murmushi ya ce "mami na fa samu sauƙi, babu inda yake min ciwo" ita ma ta saki murmushi ta zauna a gefensa, ta ce "son ashe wai mutanen nan dawowa nan za suyi?" Abdul-azeez ya ce " su waye?" ta ce " Su BABA mana baka sani ba kenan" Abdul-azeez ya ce " bansaniba Daddy ne ya faɗa miki?" ta ce "eh kuma ba zan bari su dawo ba, adalci ɗaya zanyi musu shi ne idan hidima ta tashi su zo su koma, amma ba wai da zama ba, su da Kano sai dai kallo" Abdul-azeez ya ce " ai ko kowa zai dawo banda wannan mummunar yarinyar Mami, bantaɓa shiga halin hauka kamar jiya ba" Mami ta dafa kafaɗarsa ta ce" yanzu ma akwai inda zanje jira nake ƙawata ta zo mu tafi" ba tare da ya ce komai ba, ya miƙe ya shiga toilet.


Fita tayi, ta sauka ƙasa dan ganin abinda aka shirya musu na breakfast.


Daddy da ya shirya, zai fita dan daya gama breakfast yake wucewa office, ya ɗauki wayarsa dan ƙara kiran BABA, cikin sa'a kuwa ta shiga. Daɗi yaji sosai daga can BABA da ya gama shan kunun tsamiya da wainar geronsa ya ji wayarsa na ringing kwanon da yake adanata ya buɗe ya amsa.


"Assalamu akaikum,barka da safiya BABA" 

"barka dai Aminu kun sauka lafiya" 

"lafiya ƙalau, ya gidan ya kowa da kowa?" BABA ya ce "alhamdulillah, iyalin dai ƙalau ko" Daddy ya ce "lafiya lau, ina su Innan mu gaisa" BABA ya hau ƙwara musu kira, "Gaji, Tabawa ku zo ga Aminu" Baba Tabawa da take wankin kayan AZIZA ta washe baki ta tawo da sauri tana faɗin "Alhaji Aminu ne" ta karɓa ta yi sallama, Daddy ya durƙusa kamar a gabanta yake ya ce" ina kwana Baba" lafiya lau, kunje gida lafiya dai" 

"lafiya lau Alhamdulillah, nagode sosai Baba Allah ya ja kwana" Baba Tabawa ta ce " amin Allah ya albarkaci rayuwarku a gaishe min da iyalin"ta bawa BABA wayar, Inna Gaji ce ta karɓa, Daddy ya gaisheta ta amsa tana tambayarsa ya suka je gida, bayan sun gama gaisawa ne BABA ya karɓa, Daddy ya ce " BABA kamar yaushe zaku gama harhaɗa kayan in zo?" BABA ya ce "kai Aminu matsalata da kai gaggawa abi komai a sannu, ka bari zan sanar da kai ai" 


Daddy ya ce " to shikenan BABA, a gaishe da AZIZA" BABA ya dashare baki ya ce" ja'iri ai na ɗauka ba za ka nemi AZIZAN BABA ba, ta tafi bokoko a wuta ai sun kusa fara jarabawa" Daddy ya yi murmushi ya ce" to Allah ya ba da sa'a, yauwa BABA duk abinda ake buƙata ka sanarwa da Auwal dan Allah BABA kar ku zauna haka, na bawa Iro mai nama kuɗin duk lokacin da kuke so a aika a karɓo muku" BABA ya ce "to,to Allah yayi albarka" sallama sukayi ya mai da wayarsa cikin kwano ya rufe yana faɗin gobe sati guda, zan bawa Amir ya sa mata wuta(charge) kar ta ƙare.



Inna Gaji ta ce "yau fa sunan gidan malam Haruna anjima za mu ɗan leƙa" BABA ya ce "au aikuwa hakane naji an yi suna da asuba kuwa a masallaci yo ai na sha'afa, to ku jira AZIZA ta dawo sai ku tafi" Inna Gaji ta ce" to wai da ka bamu mu sai mata ko sabulu ne mukai" BABA ya ce " ina wanda Aminu ya baku iye, ko kuwa ɗan nawan da ya ba ni kike hari" Inna Gaji ta ce "to shikenan, ayi haƙuri" ya bita da harara ya na ɓame baki.



fita tayi daga ɗakin aikinta ta kama yi, Baba Tabawa na shanya ta yarfawa Inna Gaji ruwa ba tare da ta kula ba.



Kai, kai, kai, ni kika jiƙa, Tabawa abun naki har ya kai haka?" Tabawa ta ce "ayya Yaya kiyi haƙuri ban kula ba" 

"Malam,Malam, alkur'an ba zan yarda ba, kai ka sa ta rainani a gidan nan, abun ya kai ga har ruwa take kwara min sai ta hau kuka.


Jikin Baba Tabawa har rawa yake tana ta faman bata haƙuri, BABA ya fito yaga yanda Inna Gaji ta ke kuka, ya kalli Tabawa ya ce "ke dai Tabawa baki ƙaunar zaman lafiya, dan mugun hali shi ne kika jiƙa mata taguwa, meyasa kike haka ne" Baba Tabawa ta ce "wallahi ban kula da ita ba, bansan ta kawo kai ba na yarfe rigar AZIZA zan shaya, kuyi haƙuri dan Allah" Inna Gaji ta ce " nagaji da cin kashin da ake min a gidan nan, ni sai na koma gidan ƴaƴana na zauna a can, daɗin abun na haifa ma" 

Kukan da Baba Tabawa take riƙewa ne ya suɓuce mata, sai ta fashe da kuka, ta na faɗin Allah ya baku haƙuri, ta ajiye shanyar ta shiga ɗakinta.



Inna Gaji ta dinga mita" a ce zaman gidan mijinka na nema ya gagareka, ana cin arzikin mijina da ƴaƴana ana kallona sheƙeƙe" Baba Tabawa ta ɗaga labule ta ce " miji dai ba naki bane ke kaɗai, ƴaƴa kuma ba laifi nayi wa Allah ba da bai ba ni, Nana Aisha matar manzon Allah (S.A.W) ma bata taɓa haihuwa ba, kuma kinsan annabi ya fi sonta duk cikin matansa, dan haka, kinsan ni ce mowa a wajen Malam ko ki ƙi ko ki so" ta mai da labulenta ta ci gaba da sharɓar kukanta.


Inna wuta Inna Gaji ta sa Tabawa, nan da nan ta ji haushi, BABA kuwa yana zaune kan turmi yana ɓantarar goronsa yana dariya dan sometime faɗansu yakan ba shi nishaɗi.


Malam kana jin ta ko, daman ai nasan kafi sonta a gidan nan, ni yanzu ba ni da mamora an ci moriyar ganga ko, daɗin abun ai nima da jajayen sawuna ka auro ni, kuma idan aka zalunce ni alkur'an ban yafe ba, sai ita ma ta nufi ɗaki tana kuka.


BABA ya ce " wallahi babu wacce za ta cinye ni, kukanku sai dai ya cinye ku alkur'an, kowa kishi, kishi ai sai kuyi tayi" ya ɗogara sandarsa ya fice daga gidan.



Har ƙarfe ɗaya babu wacce ta fito.

Muryar AZIZAN BABA suka jiyo, ta na sallama tare da jifa da sandal ɗin ƙafarta ta yarda jakar a nan, ta zare hijab ɗin ta cire rigar da wandon duk ta zubar a tsakar gidan daga ita sai pant ta zauna ta na faɗin "Baba na dawo, yunwa nake ji" Baba Tabawa tana jinta, ta yi shiru, so take ta koyi kame kanta daga komai na Inna Gaji.



Inna Gaji ce ta fito ta ce"kin dawo, kwashe wannan kayan da kika zubar anan, ke meyasa bakya girma ne?" AZIZA ta cuno baki ta ce "Baba na dawo, ko ba kya nan ne?" shiru ta ji, tashi tayi ta shiga ɗakin tana zaune tana ta harhaɗa kayan AZIZA tana ninke wa, AZIZA ta ce "ina ta kiranki ki na ji na ko Babata" Baba Tabawa ta ƙirƙiro murmushi ta ce" banji ki ba ai, sannu da dawowa ƴar albarka" AZIZA ta kalleta ta ce "waye ya saki kuka?" ta na duba fuskar Baba Tabawa ta taɓa, ta ce"Allah idanunki sunyi ja wace ta yi miki rashin kunya?"

Baba Tabawa ta ce " ke wani ƙwaro ne ya faɗa min ido, ina wanki" AZIZA ta ce "ayya sannu" ta juya ta buɗe kofin silver ta ɗauki kunu ta zauna ta hau sha.



Fita BABA Tabawa tayi ta tattara kayan AZIZA ta kwashe ta kai ɗaki tana faɗin na hanaki zubar da kaya haka ko, ba kya ji" AZIZA ta sa dariya ta ce "mantawa nayi ai" Baba Tabawa ta ce "haka dai kika iya" 

Ta fita ta ƙarasa shanyar ta yi alwala ta koma ɗaki ta ce,je kiyi alwala ki yi sallah"


Tana gama wa kuwa ta yi alwala sai ta shiga ɗakin Inna ta ɗauki kaya ta saka tayi sallah ta ce "Inna ina BABA ya tafi, birni fa zamu koma na faɗawa malamanmu ma, da ƙawayena ma fa" Inna Gaji ta ce " bansaniba sarkin zance ai kin dawo kenan" AZIZA ta cuno baki gaba ta fita daga ɗakin, Baba Tabawa ta ce " kar ki fita ko ina, akwai islamiyya" AZIZA ta ce" yanzu zan dawo Baba gidan su indo zanje " ta kwasa a guje dan kar a hanata.




Inna Gaji ta fito ta ɗora girki, macaroni ta dafa ya ji kifi da albasa, Baba Tabawa ta fito ta ɗebi ruwa a rijiya dan ta fara kawowa kaɗan-kaɗan tayi wanka, ta sheƙa kwalliyarta Inna Gaji ta kalleta ta taɓe baki, ta na faɗin a banza.





KANO 



Misalin sha ɗaya Hajja Fatu ta zo gidan Mami ta ce wa Daddy zasu je gaisuwa wata class mate ɗinta ce ta rasu, yana office ma ta sanar da shi, fatan a dawo lafiya yayi mata, ta ce nagode ta kashe wayarta.


Su siyama duk sun tafi school, Abdul-AZEEZ ne kawai a gida shima fita zaiyi zai je gidan Hajiya kakarsu.


Mami ta ce " idan ka je ka gaishe su, nima zan shigo kwanan nan" ya yi musu a dawo lafiya, suka fita.


Hajja Fatu ta ce "Allah ya sa ba layi, kinsan shi fa sammako akeyi wallahi" Mami ta ce "ko zan kai dare sai naga malam gobe da nisa, kinsan halin da nake ciki kuwa, ai idan na bari ƙauyawan nan sukayi nasarar dawowa nan wallahi na gama yawo, kinsan yanda yake sonsu kuwa" Hajja Fatu ta ce "kai Hajiya Hadiza ba iyayensa ba ne ai dole ya sosu ko da kuwa gawarwaki ne bare ma da ransu" suna tafe suna hira, can hanyar Ɗanbatta sukayi, hanya suka ɗauke suna ta tafiya ta ƙananan ƙauyuka, har suka zo wajen wani rafi, anan suka sauka Mami ta kashe motar suka ƙarasa wajen, kwale-kwale suka hau dan a haure da su zuwa wajen malamin nasu, ko tsoro ba su ji, aka haure da su, Hajja Fatu ta ce " yauwa mu ƙarasa can sai mu hau machine" Mami ta ce " ni fa shiyasa banason zuwa mtswww" Hajja Fatu ta ce "kinga sai mu koma babu dole wallahi" Mami ta ce " a 'a yi haƙuri ƙawata mu je"Hajja Fatu ta ce "ke ce ai da wani zance, idan ba za ki iya ba ba sai mu koma ba, ƙauyawan su zo su ƙwace ɗansu hahhhh" Mami ta ce " mu dai je uwar mita" a cikin yashi suke tafiya sai da suka fito sannan suka ga masu hayar machine kowacce ta hau suka nufi gidan Malam gobe da nisa............





Zinariya ce✍🏻